Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na kasa da kasa na farko a kan nazarin harshen Hausa a ƙarni na 21 da Jami’ar Bayero Kano ta shirya a ranar Litinin 10 - Alhamis 13 ga Nuwamba, 2014.
CIGABAN MAI GINAR RIJIYA: ILLOLIN DIMOKURAƊIYYA A RAYUWAR HAUSAWA A YAU
NA
MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
07031319454
msyauri@yahoo.com
1.0 Gabatarwa
Hausawa na ɗaya
daga cikin al’ummomin duniya da ke a sahun gaba idan aka yi batun tarbiyya da
kyawawan tsarin zamantakewar al’umma. Tsarin zamantakewar Bahaushe ya taimaka
wajen samar da kyawawan ɗabi’u da al’adu abin alfahari ga mai su. Hausawa sun
ci gaba da tafiya bisa waɗannan kyawawan ɗabi’u da al’adu waɗanda suka zama
musu abin ado a tsakanin mutane.[i] Daga cikin kyawawan ɗabi’un Hausawa na
zamantakewa akwai gaskiya da riƙon amana, da zumunci, da tarbiyya tagari ga
‘ya’yansu maza da mata, ga ladabi da biyayya, da taimakon juna, da kyautata wa
maƙwabci, da makamantansu da dama. Sai dai kuma, dukkan waɗannan kyawawan ɗabi’u
da halaye na al’ummar Hausawa sun wanzu ne tun kafin tasirin Turawa na samuwar
dimokuraɗiyya a ƙasar Hausa, domin a yau al’amurra sun sassauya, kyawawan ɗabi’un
da aka sani ga Hausawa sun yi rauni matuƙa. Zama lafiya ya kau, biyayya ga
iyaye da magabata ta salwanta, tarbiyya tagari daga iyaye ta sha ruwa, zumunci
ya kama gabansa, wai duk da sunan ci gaban dimokuraɗiyya, wanda nike ganin
cewa, ci gaba ne amma irin na mai ginan rijiya. Kar dai in cika ku da gafara sa
ku kasa ganin ƙaho. Maƙasudin wannan takarda shi ne, nazarin illolin da
dimokuraɗiyya ta haifar a rayuwar Hausawa a yau, da dalilan faruwarsu, da kuma
hanyoyin magance su ko kuma rage musu ƙarfi ta yadda rayuwar Hausawa za ta iya
sake ginuwa kamar inda aka fito ko fiya da haka. A sakamakon shigowar dimokuraɗiyya
a ƙasar Hausa a yau, kyakkyawar rayuwar Hausawa ta sukurkuce ta yadda take
neman agaji daga mawuyacin halin da ta shiga a yau. Tarbiyyar yara maza da mata
ya sukurkuce, sai shaye-shaye da ayyukan ta’addanci ga matasanmu. ‘Yan siyasa
sun tsunduma cikin tsafe-tsafe domin samun nasara. Zalunci da rashin gaskiya da
amana da adalci ya share fili ya shimfiɗa tabarmarsa a rayuwar shugabanninmu,
abin dai sai wanda ya ji ko ya gani. Allah Ka yi muna agaji.
2.0 Ma’anar Kalmar Dimokuraɗiyya
Kalmar
dimokuraɗiyya asali ba kalmar Hausa ba ce, ararriyar kalma ce daga harshen
Ingilishi, woto “Democracy”. A ma’ana ta Mac Millan Dictionary,
kalmar tana nufin, wani tsari na gwaunati wanda jama’a ke jefa ƙuriar zaɓen waɗanda
za su shugabance su.[ii] A ƙamusun Hausa kuwa, dimokuraɗiyya na
nufin, tafarkin mulkin da mutanen ƙasa ke zaɓar shugabanninsu ta hanyar jefa ƙuri’a.[iii] Dimokuraɗiyya tsari ne da ke ba kowa
‘yancin shigowa a dama da shi a fagen neman shugabanci matuƙar ya samu
amincewar al’ummar da yake son shugabanta dangane da kyawawan halaye da ɗabi’unsa.
Haka ma akwai ƙayyadadden wa’adin da aka shata na tsawon lokacin da mutum zai
yi yana gudanar da shugabancin. Saboda haka, idan wannan wa’adi ya cika zai
sauka daga wannan matsayi a sake zaɓen wani. Sai dai tsarin ya ba mutum damar
sake neman shugabancin, ma’ana mutum zai iya sake nema karo na biyu, a wani
matsayin ma mutum zai iya nema fiye da haka har sai sa’ad da wani ya fito ya
kayar da shi. Saboda haka, irin wannan tsari na shugabanci sabon al’amari ne ga
rayuwar Hausawa, domin ba haka lamarin yake a tsarin al’adun rayuwarsu ba.
Shugabanci a al’adar Hausawa gadon sa ake yi, ko dai a wajen iyaye ko kuma a
wajen kakanni. To sai dai kuma, irin wannan tsari na dimokuraɗiyya tsari ne mai
alfanu da kuma ba kowa ‘yancinsa ba tare da wata tawaya ba, amma fa idan an yi
amfani da shi kamar yadda waɗanda suka shigo da shi suka tsara.
https://www.amsoshi.com/2017/11/06/1355/
3.0 Rayuwar Hausawa Kafin Shigowar Dimokuraɗiyya
Kamar yadda aka bayyana a cikin gabatarwa, rayuwar Hausawa kafin shigowar
dimokuraɗiyya ta kasance gwanin ban sha’awa. Shugabanni sun kasance masu adalci
da riƙon amanar talakawansu. Iyaye suna kula da tarbiyyar ‘ya’yansu kamar yadda
ya kamata. Talakawa suna biyya ga shugabanni gwargwadon hali. ‘Ya’ya sun
kasance masu ladabi da biyayya ga iyaye da ma magabata saboda kyakkywar
tarbiyyar da suka tashi da ita. Iyaye sun sa ido ga ilimn ‘ya’yansu, da kuma
aza su ga tafarkin yin sana’a. Babu mai zaman kashe wando balle ya sa ido ga
abin da ba daidai ba. Zama lafiya ya wanzu a ko’ina, al’amarin dai gwanin ban
sha’awa ga mai sauraro da ɗan kallo. Bari mu dubi bayanin yadda rayuwar take
dalla-dalla domin feɗe biri har wutsiya.
Zaman Lafiya: Masu iya magana na cewa, zama lafiya ya fi
zama ɗan sarki.`Kafin gurɓatar dimokuraɗiyya, ƙasar Hausa ƙasa ce da aka sani
da zama lafiya da kwanciyar hankali. Babu tashe-tashen hankula balle a samu
salwantar rayuwa da dukiyoyi. Zalunci da babakere ba su sami gindin zama ba
balle su baje kolinsu. Shugabanni suna kwatanta adalci, don haka ba su fuskanci
tawaye daga talakawansu ba. Saboda yanayin zama lafiya da ke akwai a ƙasar
Hausa, ya sa al’ummomi daban-daban suke yin tururuwar shigowa ƙasar domin a ci
gajiyarsa da su. Hakan ya sa duk ɗan wata ƙabila da ya ɗanɗani zama a ƙasar
Hausa bai iya komawa ƙasarsu domin ya ga wurin zama, sai dai ya riƙa zuwa ganin
gida daga lokaci zuwa lokaci. Faɗace-faɗace da ayyukan ta’addanci sai dai
Hausawa su ji labarinsu a wasu ƙasashe. Rayuwa a ƙasar Hausa in dai babu sa
albarka, babu ko Allah wadai.
Ladabi Da Biyayya: Ladabi da biyayya manyan ƙusoshi ne a
cikin tarbiyyar Hausawa, wato muhimman halaye ne da Bahaushe yake so ya ga ana
yi. Girmama na gaba da kyautata wa na baya su ne halayen da ake kira ladabi da
biyayya (Alhassan da wasu 1982). A kullum burin iyaye ba ya wuce ganin
‘ya’yansu sun girma cikin halaye kyawawa masu nagarta, don haka suke koya musu
yin ladabi da biyayya ga iyaye da ma na gaba gare su. Sukan koya musu ladabin
magana wanda ya shafi koya musu tausasa murya lokacin magana da babba, kuma kar
a tsura masa ido da kallo kamar yadda tumaki suke yi. Haka ma ba a gai da iyaye
ko magabata a tsaye sai an duƙa musamman idan suna zaune. Ba a ƙetare umarnin
iyaye ko ba daɗi, sai dai a daure a aikata yadda suke buƙata.
Kare ‘Diyauci: Bahaushe bai san karuwanci ba balle masu yin
sa.’Ya’yan Hausawa mata tun suna ƙanana akan yi ƙoƙarin cusa musu al’adar
nisantar maza da kuma illar da ke tattare da kusantar su. Don haka ne ko a
wasannin dandali ƙungiyar mata daban na maza ma daban. Wannan tarbiyyar ba ta
tsaya a nan kawai ba, hatta idan aka yi wa mace aure akan kai ta da wani farin ƙyalle
da ake kira bante wanda za ta fara kwanciya da shi. Ta wannan ƙyalle ne za a
gane ta kare ɗiyaucinta ko akasin haka. Idan aka yi nasara ta kai bante wato ba
ta taɓa sanin ɗa namiji ba sai ga mijinta na aure, iyayenta kan yi murna da
kasancewa masu alfahari da ita. Idan kuwa aka sami akasin haka, to yarinyar ta
bar abin faɗe da zubar da mutuncin iyayenta. Wannan al’ada ya yi tasiri ainun
ga ‘yan mata wajen ganin ba su zubar da mutuncin gidansu ba, da kuma barin abin
faɗe a baya.
Gaskiya Da Riƙon Amana: Hausawa mutane ne da suke da
kyakkyawar tarbiyya da himmatuwa zuwa ga ɗaukar halaye nagari irin su gaskiya
da riƙon amana. Babu yaudara ko cin amana a rayuwar Hausawa. Wato mutane ne
masu karimci da shimfiɗar fuska wadda aka ce ta fi shimfiɗar tabarma. Duk wanda
ya haɗa hulɗa ta kasuwanci ko na zamantakewa da Hausawa zai tabbatar da cewa
Hausawa mutane ne masu gaskiya. Wannan ne ya samar wa Hausawa kyakkyawar
dangantaka ta kasuwanci tsakaninsu da al’ummomi daban-daban na cikin gida da ma
sauran ƙasashen duniya.
Zumunta: Ƙoƙarin kusantar ‘yan’uwa da abokan arziki da
ziyartar su a kai-a-kai, ita ce zumunta (Alhassan da wasu 1982). Tarbiyyar
Hausawa tana jaddada ziyarce-ziyarce tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki. A
tsarin rayuwar Bahaushe, maƙwabci tamkar ɗan’uwa ne, domin idan aka wayi gari
sai an gaisa kafin kowa ya fita tasa harka. Don haka, idan wani abin farin ciki
ko akasinsa ya samu maƙwabcin mutum, za a zauna a taya juna murna ko juyayi
idan mara kyau ne. Haka ma duk wani abu da ya samu ‘yan’uwa na murna kamar
haihuwa ko aure akan taru domin a sada zumunci kuma a ƙarfafa shi. Har ta kai
ga Bahaushe kan ɗauki ɗansa ya ba ɗan’uwansa riƙo domin ƙarfafa zumuntar da ke
tsakaninsu.
Mallakar Sana’a: Al’ummar Hausawa tun asali al’umma ce wadda
ta dogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arzikinta. Ta haka ne ya
zama a kowane gidan Bahaushe za ka tarar yana da sana’o’in da yake aiwatarwa.
Don haka, yakan yi ƙoƙarin gina yaransa bisa wannan sana’a domin su girma da
ita, su kuma kauce wa zaman kashe wando da sa ido da yawon gararanba a cikin
unguwa.
4.0 Illolin Dimokuraɗiyya a Rayuwar Hausawa a Yau
Da ma ana
cewa, duk wani abu mai amfani ba za a rasa illa a cikin sa ba. Dimokuraɗiyya
wani tsari ne na tafiyar da rayuwar al’umma mai alfanu matuƙar dai an yi amfani
da shi kamar yadda aka tsara shi. To sai dai kuma, lamarin Dimokuraɗiyyar a
Arewacin Nijeriya a yau ya ɗauki sabon salo wanda ya sha bamban da na waɗanda
suka kawo shi, wato Turawa. A dimokuraɗiyyar da ake gudanarwa ƙasar Hausa a
yau, an cakuɗa gaskiya da ƙarya, an mayar da gaba baya, ta yadda al’amurra suka
kasa zuwa gaba sai dai baya. Wannan matsalar ta yi tasiri ainun a rayuwar
Hausawa a yau, inda ‘yan siyasar ƙasar Hausa suka mayar da dimokuraɗiyya in ba
ka yi ba ni wuri. Sukan bi duk wata hanya mai kyau ko akasinsa, galibi hanyoyi
marasa kyau domin cimma burinsu na wani matsayi da suke nema. Hakan ya sa
tsafe-tsafe ya samu gindin zama. Safarar miyagun ƙwayoyi domin bai wa matasa
‘yan bangar siyasa ya baje hajarsa. Ƙungiyoyin ‘yan daba suka mamaye unguwanni.
Fitintinu da tashe-tashen hankula da salwantar rayukar al’umma da dukiyoyinsu
ya zama ruwan dare game ƙasar Hausa. Ga dai bayanin irin illolin kamar haka:
4.1 Rashin Zama Lafiya
Zama lafiya da aka sani a ƙasar Hausa inda har wasu al’ummu kan shigo domin cin
gajiyarsa, a yau ya yi ɓatan dabo. Tashe-tashen hankula ya wanzu a kusan kowane
ɓangare na ƙasar Hausa. Allah kaɗai ya san adadin rayukan Hausawa da
dukiyoyinsu da suka salwanta tun bayan gurɓacewar dimokuraɗiyya. A yau za ka ji
an kai hari a wannan sashe an kashe mutane masu tarin yawa da hasarar dukiyoyi,
gobe ka ji an kai a wancan ɓangare, haka dai lamarin ke ci gaba da aukuwa fiye
da shekaru huɗu da suka gabata duk da sunan ci gaban dimokuraɗiyya. To sai dai
kuma, duk da irin waɗannan matsaloli da Hausawa ke huskanta a ƙasashensu, sai
ka iske ‘yan siyasa sun miƙe suna bayyana irin ci gaban da aka samu na tafarkin
dimokuraɗiyya, Allah dai ka yi muna magani.
4.2 Taɓarɓarewar Tarbiyya
Kyakkyawar
tarbiyyar da aka san matasan Hausawa da shi a da, a yau lamarin sai dai a shafa
fatiha a watse. ‘Yan siyasa sun yi ruwa da tsaki wajen tabbatar da gurɓacewar
tarbiyyar matasa a yau. Sukan sawo miyagun ƙwayoyi da miyagun makamai da ɗan kuɗin
da bai taka kara ya karya ba su raba wa matasa don su yi musu bangar siyasa.
Saboda haka, a duk lokacin da waɗannan matasa suka sha waɗannan ƙwayoyi sukan
fita hayyacinsu, daga nan sai ayyukan ta’addanci su wanzu na kai wa abokan
hamayyar ubangidansu da ma junansu hare-hare da lalata dukiyoyi, da yi wa mata
fyaɗe da makamantansu. A wani lokaci ma har hayan matasa ake ɗauka domin
su hallaka wani abokin hamayya. Don haka, maganar mallakar sana’a ya sha ruwa,
sai dai tunanin haɗa ƙungiyoyin daba iri daban-daban. Haka ma lamarin karatun
zamani (boko) da na addini (Musulunci) ga matasa ya yi rauni, domin ‘yan siyasa
sun yi awon gaba da kyakkyawar tunanin matasan suka bar musu gurɓatacce, don
haka maganar neman ilimi ko sana’ar dogaro da kai bai taso ba. A sakamakon
haka, matasa da yawa sun sami taɓuwar hankali, wasu sun zama musakai, wasu ma
sun rasa rayuwa baki ɗaya. Duk waɗannan matsaloli ne da ke faruwa da sunan ci
gaban dimokuraɗiyya, Allah ya kiyashe mu da irin wannan ci gaba na mai ginan
rijiya.
4.3 Taɓarɓarewar Zumunci
Mulkin
Dimokuraɗiyya ya zama ummul-haba’isin taɓarɓarewar zumunci a yau. Siyasa ta
shiga tsakanin ‘yan’uwa ta ɗaiɗaita su. Ta shiga tsakanin abokai ta yanke musu ƙauna.
Ta raba soyayyar da ke tsakanin ma’aurata. Ta shiga tsakanin maƙwabta ta
haddasa gaba a tsakaninsu, ta bi komai ta hargitsa. Sau da yawa za ka taras ana
uwaka-ubaka tsakanin ‘yan’uwa, ko wa da ƙani, ko mata da miji, ko aboki da
abokinsa, ko ma ka iske an yi hannun riga tsakanin ɗa da mahaifi kowa ya kama
gabansa. Haka ma sai ka iske ba a ga-maciji tsakanin maƙwabta, sai maƙwabci ya
yo hayar ‘yan daba a kawo wa maƙwabcinsa hari a lalata dukiyoyinsa, duk kawai
saboda bambancin jam’iyyar siyasa. Saboda haka, tilas zumunci ya taɓarɓare,
taimakon juna da ziyara da jinƙai suka nufi inda dare ya yi musu tun lokaci bai
ƙure ba. A yau kowa kansa kawai ya sani, ya nufi inda zai sami arziki a ƙarƙashin
wata jam’iyya, duk mai mutuwa ya rage nasa.
4.4 Wanzuwar Ƙungiyoyin Daba na Matasa (Area Boys)
Saboda irin
taɓarɓarewar da Dimokoraɗiyya ta yi a ƙasar Hausa a yau, har ta kai ga wanzuwar
ƙungiyoyin ta’addanci na matasa waɗanda ake kira “Area Boys” daban-daban
biranen ƙasar Hausa da ma ƙauyukansu waɗanda ke ƙarƙashin kulawar wasu ‘yan
siyasa. Wasu ƙungiyoyin ma har albashi ake yi musu a ƙarshen kowane wata kamar
sauran ma’aikatar gwaunati. Saboda haka, a duk lokacin da za a tafi yawon
kamfe, za a kwashi waɗannan matasa (‘yan daba) cikin motoci a ba su miyagun
makamai don ko ta kwana. Haka ma idan ana buƙatar cin zarafin wani abokin
hamayya ko ma a kawar da shi a doron ƙasa, irin waɗannan matasa ‘yan siyasa kan
samu su biya musu buƙata. Don haka, duk irin ta’adin da suka aikata komai ba a
yi musu, saboda ko hukuma ta kama su sai iyayen gidansu su shiga su fita sai
sun ga an sake su. Alal misali, a kwanakin baya ‘yan daba suka riƙa tsayawa a
tsakiyar randabawul a cikin garin Sakkwato suna tare motocin mutane wai
sai an ba su rabonsu ko mutum ya huskanci walaƙanci.
4.5 Yawaitar Tsafe-Tsafe
A riwayar Bunza (2006) ya bayyana tsafi da bin wasu hanyoyi na gargajiya
musamman yi wa iskoki hidima, da yanka, da bauta, domin biyan wata buƙata, ko
ko wani amfani, ko tunkuɗe wata cuta.[iv] Ya ci gaba da cewa, Tsafi ya yi rawar gani
wajen tabbatar da Bamagujiyar rayuwa ta Hausawan jiya. Da shi ake tinƙaho don
tsare kai da kaya. Da shi ake kuri wajen kariyar martabatar abin da aka gada
kaka da kakanni. Da shi ake yin fice wajen wasanni da bukukuwan gargajiya da
ake aiwatarwa a ko’ina a ƙasar Hausa. Sai dai zuwan Musulunci ya taka masa
birki ta yadda ya kasa motsi balle ya wataya. To sai dai kuma, a wannan zamani
da ake ciki na tsarin dimokuraɗiyya yana neman ya mayar da hannun agogo baya,
domin a yau ‘yan siyasa sun tsunduma dumu-dumu cikin harkar tsafe-tsafe domin
neman matsayi na siyasa. Sun ba Allah baya, sun fuskanci malaman tsibbu da
miyagun bokaye domin biyan buƙata. Saboda haka ake tura su zuwa ga sace-sacen
yara ana cire wasu sassa na jikinsu, ko a tafi maƙabarta a tone ƙabari a ɗibi
wani sashe daga jikin mamaci, domin haɗa miyagun asirrai wai a samu nasara.
4.6 Handama da Babakere
A ma’ana ta gaskiya, ba komai ne Dimokuraɗiyya a Nijeriya ba face zalunci da
rashin gaskiya da handamar dukiyar talakawa. A yau ‘yan siyasa suna neman
matsayi ne ba don kare haƙƙin waɗanda suke wakilta ba, a’a, sai don kawai
handamar dukiyoyinsu da kuma barazana ga rayukansu idan suka nemi su yi tawaye.
Hakan ya sa suke bin duk wata hanya na ganin sun kai ga baitil-malinsu.
Talakawan jiha ba su amfana da arzikinsu na aƙalla kashi talatin cikin ɗari da
ake ware musu, an yi ruf-da-ciki da saura. Lamarin ƙananan hukumomi kuwa sai
wanda ya ji ko ya gani, domin da zarar an yi albashi da abin da bai wuce kashi
talatin cikin ɗari ba, sauran sai dai kawai ‘yan siyasa su yi tonton kowa ya
kwashi rabonsa a hari wani wata mai zuwa. Talakawa sun shiga halin ƙaƙa-nika-yi,
abin da za su ci ma ya zama lalura balle a kula da lafiyarsu da sauran buƙatun
rayuwarsu. Allah ya kiyashe mu da irin wannan ci gaba na dimokuraɗiyya.
4.7 Cuɗeɗeniyar Maza da Mata
Cuɗeɗeniyar maza da mata wuri ɗaya abu ne da al’adar Hausawa da ma addininsu
(Musulunci) ba su aminta da ita ba, sai dai idan lalurar hakan ta kama. Amma a
yau tsarin mulkin Dimokuraɗiyya ya nuna cewa, mace za ta iya fitowa neman wani
matsayi na shugabanci a fafata da ita kamar yadda namiji zai iya fitowa. Sau da
yawa za ka iske an kwashi ‘yan mata da zawarawa har ma da matan aure cikin mota
ana yawon kamfe da su kamar yadda takwarorinsu maza suke yi. A yanzu ma har an
fara samun matan Hausawa suna fitowa takara suna tsayawa gaban dubban maza suna
kamfe wai a zaɓe su a matsayin wakilan maza. A faɗar wasu, wai duk abin da
namiji zai iya yi, mace ma za ta iya yin fiye da haka. Wannan mummunan tsari da
tunani a yau ya ratsa ƙwaƙwalwar matan Hausawa na ganin cewa za su iya
gwagwarmaya da maza ta kowace fuska, don haka lamarin sai dai kawai addu’a
Allah shi yi muna magani, ya kuma sa mu gane tafarki managarci.
5.0 Musabbabin Matsalar
A duk
lokacin da al’amurra suka sukurkuce suka sauya kamanni ba kamar yadda aka saba
da su ba, tilas akwai dalilan da suka jawo haka. Don haka, akwai abubuwa da
dama da suka zama ummul-haba’isin waɗannan matsaloli da suke ci wa rayuwar
Hausawa tuwo a ƙwarya a yau. Ga wasu daga cikinsu:
Rashin Amfani da Doka da Oda: Ba shakka, rashin amfani da
doka da oda na daga cikin abubuwan da suka haddasa wasu daga cikin illolin da
aka bayyana a sama. A yau kowa na cin karensa ne babu babbaka musamman ‘yan
siyasa ko masu wani muƙami ko masu hannu da shuni. A yau idan kana tare da
manya, duk laifin da ka yi hukunci ba ya hawa kanka. Don haka, duk dukiyar da
ka sata na al’umma ko wani ha’inci ko kisan kai ko wani ta’addanci, ko an gane
ba a yi ma komai, ka ci bilis. Haka ma, idan ‘yan ta’adda suka aikata wani
ta’addanci aka kama su, sai ka iske wasu ɓara-gurbin mutane sun yi ruwa sun yi
tsaki sun hana hukuma aikinta. Idan ka ga doka ta yi aiki a yau, to ga talakawa
ne waɗanda ba su da kowa sai Allah.
Sakacin Iyaye: Haƙiƙa akwai sakacin iyaye wajen lalacewar
tarbiyyar matasa a yau. Sai ka iske iyaye sun haifi ‘ya’ya sun sake su kamar
tumaki ba su tsare hakkin da Allah ya ɗora musu na tarbiyyansu da ta danganci
addini da al’ada. Sau da yawa za ka iske iyaye ba su damu da sa ‘ya’yansu
makarantar addini ba balle na zamani. Saboda haka, duk yaron da ya tsinci kansa
cikin irin wannan yanayi rayuwarsa na cikin haɗari. Daga nan ne sai ka iske
yaro ya haɗu da miyagun abokai, sai shaye-shaye da haɗa ƙungiyoyin daba, shi ke
nan rayuwa ta lalace.
6.0 To Ina Mafita?
Masu iya
magana na cewa, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Ba shakka, duk yadda
al’amurra suka taɓarɓare ba za a yanke ƙauna ga samun mafita ba. A kan haka
nike ganin akwai hanyoyi da yawa waɗanda idan aka jaraba amfani da su wataƙila
a sami maslaha a ceto rayuwar Hausawa daga bala’o’in da ke ƙoƙarin ganin baya
gare ta. Daga cikin waɗannan hanyoyi akwai sa hannun gwaunati, da iyayen yara,
da kuma malaman addini.
6.1 Gwamnati
Haƙiƙa
gwaunati ce a sahun farko na waɗanda za su iya ba da tasu gudummuwa wajen samar
da mafita dangane da waɗannan matsaloli na dimokuraɗiyya da suke ci gaba da
addabar rayuwar Hausawa a yau. Gwunati za ta iya daidaita al’amurra su dawo
cikin hayyacinsu ta hanyar fito da wasu hanyoyi na daƙushe bangar siyasa da
amfani da matasa wajen ayyukan ta’addanci. Dole ne a yi amfani da doka da oda
wajen hukunta duk wani ɗan siyasa ko ɗan bangarta da aka samu da hannu wajen
aikata abubuwan da suka saɓa wa doka. Dole ne gwaunati ta samar da wasu
shirye-shirye na faɗakar da matasa illolin da ke tattare da bin ɓara-gurbin
‘yan siyasa, da kuma irin haɗurran da ke tattare da shaye-shayen miyagun ƙwayoyin
da suke yi wanda ke iya kai su ga halaka.
6.2 Iyaye
Iyaye su
suka fi cancanta da kula da halin da yaransu ke ciki, domin su ne Allah ya damƙa
wa ragamar tarbiyyar rayuwarsu tun suna ƙanana har zuwa girmansu. Tilas su
tsaye tsayin daka wajen ba su ilimin addinii da na zamani domin su ci moraiyar
rayuwarsu ta duniya da ma ta gobe ƙiyama. Dole ne iyaye su ɗora ‘ya’yansu bisa
turba ta sana’a domin kauce wa zaman banza wanda shi ke kai su ga faɗawa cikin
miyagun hanyoyi. Dole su sa ido ga ire-iren abokan da ‘ya’yansu suke hulɗa da
su don kauce wa faɗawa hannun ɓata-gari.
6.3 Malaman Addini
Duk da cewa,
malaman addinin Musulunci suna iya ƙoƙarinsu wajen wa’azantar da al’umma a
kusan kowane lokaci, kuma ana yayata faɗakarwar tasu a kusan dukkan kafafen yaɗa
labarai kama daga rediyo da talabijin da jaridu da mujallu da tauraron ɗan Adam
da intanet da makamantansu, zai kyautu su ƙara ba da ƙarfi a kan wannan matsala
da mulkin Dimokoraɗiyya ya haifar a rayuwar Hausawa a yau. Su riƙa bayyana wa
jama’a musamman masu ruwa da tsaki a kan lamarin siyasa irin mummunar sakamakon
da ke jiran duk wani mai ƙoƙarin cutar da al’umma, yake barazana ga rayuwarsu,
ko yake lalata tarbiyyarsu, ya haddasa musu bala’i, ya hana su zama lafiya
balle su bauta wa mahaliccinsu kamar yadda ya kamata.
Jawabin Kammalawa
Tsarin
dimokuraɗiyya a ƙasar Hausa a yau ya zama tamkar wani mulki na kama-karya da
danniya da babakere da rashin tausayin na ƙasa wanda ya gudana a zamanin
jahiliyya, inda sai yadda shugabanni suka ga daman yi da talakawa. An gurɓata
tunanin matasa ta yadda ba su iya fitar da suhe wuta. An talautar da jama’a
domin a juya akalar rayuwarsu yadda aka ga dama. Aka kuma haddasa fargaba da
rashin zama lafiya a rayuwarsu. Kowa son yake yi ya shiga harkar siyasa domin a
ci karen da babu babbaka tare da shi. Al’amurra a rayuwar Hausawa a yau
musamman talakawa ya zama abin tausayi ga duk wani mai imani na gaskiya. Tilas
mu tashi tsaye mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ganin bayan wannan bala’i da ya
kewaye kusurwoyin rayuwar Hausawa domin sake dawowa da kyakkyawar rayuwar da
muka gada daga kaka da kakanni.
https://www.amsoshi.com/2017/11/08/makamin-dimokradiyya-a-falsafar-alada/
MANAZARTA
Alkali, B. 1968. “Hausa Community in Crisis: Kebbi in the 19th Century”, MA
Thesis, Ahmadu Bello University, Zaria.
Birniwa, H. A. 1987. “Conservatism and Dissent: A Comparative Study of NPC/NPN
and NEPU/PRP Hausa Polical Verse from Ca 1949 – 1983, PhD Thesis, Usmanu
‘Danfodiyo University Sokoto.
Birniwa, H. A. 1987. “Ra’ayin Riƙau da na Kawo Sauyi Cikin Waƙoƙin Siyasa”, Maƙalar
da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero Kano.
Bunza, A. M. 1996. “Gaskiya Ina Laifinki? Tsokacin Diddigin Musabbabin Karyewar
Arzikin Nijeriya Cikin Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana, Ta Alhaji Muhammadu Sambo
Wali Basakkwace,” Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.
Bunza, A. M. 2000. “A Daɗe Ana Yi Sai Gaskiya: Laluben Gurbin Gaskiya Cikin
Adabin Hausa”, Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, Jami’ar Usmanu
‘Danfodiyo Sakkwato .
Bunza, A.M. 2006 Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Limited,
Surulere, Lagos.
Bunza, A.M. 2013. “Makamin Dimokuraɗiyya a Falsafar Al’ada” Takardar da aka
gabatar a
taron ƙara wa juna sani na ƙasa na farko a kan Harshe da
Adabi da Al’adun
Hausawa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.
Burji, B. S. 1997. Gaskiya Nagartar Namiji. Baraka Press Limited,
Kaduna.
Msutapha, S. 2003 “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, kundin digirin MA,
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Nasidi, Y. & Igoil, I. (ed)1997Culture and Democracy. Zaria: Ahmadu
Bello University Press
Sarkin Gulbi, A. 2013 “Tsafe-tsafen Dimokraɗiyya” Takardar da aka gabatar a
taron ƙasa na
farko kan Harshe da Adabi da Al’ada, wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Bayero Kano ta shirya.
[i] Dubi Bugaje 2013, “Tarbiyya da
Zamantakewar Hausawa Jiya da Yau”. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna
sani na ƙasa da ƙasa kan Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa a Yau, Jami’ar Umaru Musa
‘Yar’adua, Katsina.
[ii] Dubi Mac Millan English
Dictionary for Advanced Leaners, International Edition, shafi na 369.
[iii] Dubi ƙamusun Hausa,
2006, wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano
shafi na 104
[iv] Domin ƙarin bayani game da lamarin
tsafi, sai a dubi Bunza 2006, Gadon Feɗe Al’ada, shafi na 35-57.

1 Comments
[…] Ci Gaban Mai Ginar Rijiya: Illolin Dimokurad’iyya A Rayuwar Hausawa A Yau […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.