Ticker

6/recent/ticker-posts

Budurcin Maguzawa A Faifan Nazari: Darussa Ga Hausawan Zamani


Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa na farko a kan Nazarin Hausa a Ƙarni na 21 wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano, ta shirya daga ranar Litinin 10 zuwa Alhamis 12 ga Nuwanba, 2014.


 Budurcin Maguzawa A Faifan Nazari: Darussa Ga Hausawan Zamani

IBRAHIM ABDULLAHI SARKIN SUDAN
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna, Kaduna, Nijeria


Gabatarwa 

A yanayin tunani na ɗan’adam, mace takan amsa sunanta ne idan ta fara mallakar hankalinta. Shi wannan mallaka na hankali, yakan zo ne da yawan shekaru. Duk da yake kaifin tunani ko saurin mallakar hankali sukan bambanta daga mutum zuwa mutum. Haka kuma yanayin abincin da aka ɗabi’antu da ci da muhallin da al’umma take zaune, sukan yi tasiri ga bayyanar alamonin shiga budurci ga mace. Duk da haka adadin shekarun da ake ɗammahar mace ta fara ganin ɓullowar wasu siffofi a jikinta kamar nono da gashin hammata da na gaba, suna kamawa daga shekara bakwai zuwa goma. Sannu a hankali har ta fara jin sha’awa musamman ta ɗa namiji a ran ta. Wannan yanayi yakan kai ƙarshe ne idan ta fara ganin al’ada (jinin haila).



Kowace al’umma takan yi tanadi na musamman ga irin waɗannan yara mata na yadda za su tunkari wannan sauyin da kuma yadda falsafar rayuwarsu za ta kasance. Daga cikin irin waɗannan al’adu akan sami hani da aikata wasu al’amurra saboda munin da ke gare su ga yanayin da ake ciki. Wasu al’adun kuma sun ƙunshi horo ne ga aikata wasu abubuwa saboda ganin irin taimakon da za su ba rayuwar ta budurwa a wannan yanayin.



Wannan nazari, zai mayar da hankali ne wajen duban yadda al’ummar Maguzawa suka ɗauki lamarin Budurci da kuma irin tanade-tanaden da al’adunsu suka yi mata. An keɓe wannan nazari ne ga Maguzawa, bisa tunanin cewa, su ne Hausawan asali da al’adunsu na gargajiya suka yi tasiri a kan su. Haka kuma nazartar waɗannan al’adu za su taimaka wajen kwatanta halin da budurcin Hausawa ya sami kansa a ciki a yau ta la’akari da talalaɓiyar zamani.

 Maguzawa

Nazarce- nazarcen da masana suka yi a baya a kan al’ummar Maguzawa, zai iya wadatar da masu nazari a kan ko su wane ne waɗannan mutanen. Amma a ƙoƙarin tabbatar da dugadugan wannan nazarin, akwai bukatar a yi ‘yar shimfiɗa don a waiwayi wasu ayyukan da suka gabata wajen fayyace mutanen da ake kira Maguzawa. Misali, ayyuka irin na Ibrahim (1982) da Last (1993) da Abdullahi (2008) sun tabbatar da cewa, ba wasu mutane ne ake kira Maguzawa ba, illa Hausawan asali waɗanda ba musulmi ba, waɗanda yanayin rayuwarsu ta dogara ne ga tunaninsu da al’adunsu da addininsu na gargajiya. Maguzawa Hausawa ne waɗanda suka sami wannan suna daga ’yan’uwansu da suka karɓi addinin musulunci. Su kuma da suka zaɓi zama cikin yanayin addinin nasu da al’adunsu na gargajiya, aka kira su Maguzawa. Duk da yake musulunci da kiristanci da yanayin zamantakewar Hausawa na zamani  ya yi tasiri matuƙa a rayuwar Maguzawa, har yanzu ana samun su a wasu sassa na jihohin Katsina da Kano, da Zamfara a Nijeriya.     

Budurci a Yanayin Tunanin Maguzawa 

Budurci a al’umar Maguzawa wata rayuwa ce da ’yanmata suke shiga daga lokacin da suka fara ganin alamar balaga zuwa lokacin da za su yi aure. A wannan lokacin ne ’yanmatan Maguzawa suke gudanar da wasu al’adu da ke ba da dama namiji ya kusance su don samun abokin zama a matsayin ma’aurata. Waɗannan al’adun sun ba da damar budurwa ta saki jiki, ta darje, ta zaɓi saurayin da take ganin za su iya gina dangantakar soyayya da shi, wadda ake ɗammahar ta kai ga aure. Bayan saurayi ya ga budurwa a kasuwa ko a wurin wani buki, ya nuna yana son ta, akwai wata dama da al’ada kan ƙara ba shi don ya tabbatar wa jama’a ko yarinyar ko wasu masu sha’awar ta cewa, da gaske yake yi. Waɗannan al’adu sukan tabbatar wa iyayen Budare cewa, ’yarsu tana da masoya. Wannan zai ba su haske su yi shawarar wanda suka ga ya dace, ta yadda za a ba shi dama, a kuma sallami sauran da ba a so. A tunanin Maguzawa, yanayin budurci wata ishara ce ga iyaye su san cewa, ’yarsu ta fara fafutikar barin gida.   Wasu daga cikin waɗannan al’adu, ba a ɗammahar yarinya da fara aiwatar da su in ba ta kai wannan matsayi na budurci ba.

 Al’adun Maguzawa da Suka Shafi Bayyanar da Budurci





A wannnan fasalin, za a waiwayi al’adun tabbatar da budurcin Maguzawa tare da fayyace abin da aka tanada na aiwatar da kowace al’ada.

 Gaisuwar Makaɗi

A lokacin kaka akan sami makaɗa daga cikin Maguzawa waɗanda sukan zagaya ƙauye-ƙauye don nishaɗantar da jama’a da neman kuɗi. Idan makaɗi ya sauka a ƙauye zai nemi gidajen da ’yanmata suke. Zai tafi wajen maigida ya ce, yana neman izinin ya zo rana kaza ya yi wa Wance wasa. Idan maigida ya amince, to za a sa rana ta musamman. Kafin wannan ranar, makaɗin zai tabbatar da labari ya kai ko’ina musamman ga samarin da ke wannan ƙauyen da kewaye. Idan ranar ta zo, samari da ’yanmata za su haɗu. Makaɗi da jama’arsa za su yi ta kiɗa, ’yanmata suna rawa. Su kuma samari za su yi ta musu kari/liƙi. Wannan ya sa kuɗi, ya ce budurwa kaza ta fito ta yi rawa, wani ya zo ya ɗora a kai. Ta haka ake gane masoyan budurwa da farin jininta. Idan jama’a sun watse, makaɗi kan yi godiya wurin maigida, ya ƙara gaba. Duk karin da samari suka yi wa ’yanmata na makaɗin ne. Su kuma samari sun sami damar da za su nuna son su ga budurwa. Daga nan sai dangantaka ta ƙara ginuwa. Su kuma ’yanmata wata dama ce da za su ƙara tabbatar da masu son su ko farin jinin da suke da shi. Abin murna ne ga budurwa da iyayen ta, a ga ana ta karakaina a kanta. Wannan ya nuna tana da farin jini ke nan. Miji kuma  sai  ta zaɓa.

 Shasshawa/Jarfa

Shasshawa ko Jarfa tsaga ce ƙanana da ake yi a jikin mata don ado. A lokacin kaka ‘yanmatan unguwa ko ƙauye sukan keɓe wani lokaci su gayyaci wanzami don ya yi musu irin waɗannan tsage-tsage a jiki. Wanzaman sukan zo ne tare da makaɗi. ’Yanmata za su zauna bainar jama’a su bayar da ƙirjinsu da bayansu a yi musu Shasshawa. A wannan lokacin ne samari za su ta yi wa makaɗin da wanzamin kari/liƙi. Saurayin da ya yi fice wurin son yarinya shi zai yi wa wanzami kyauta mafi yawa da cika ido. Haka kuma, shi zai kawo wa budurwarsa ɗan akuyan da za ta sallami wanzami da shi. Ita ma uwar budurwa za ta ba wanzamin zani idan an watse taro a matsayin sallama. Wasu Maguzawan sukan yanka kaji, a yi abinci a ci a wurin taron. A wànnán gidan wanzamin da makaɗan za su kwana. Idan gari ya waye, za a sallame su, su tafi, sai kuma an ƙara gayyatar su. Wannan shi ake kira jarfa, wasu kuma su kira shi shasshawa. Duk saurayin da ya kasa ɗaukar ɗawainiyar wannan tsagar, ko ya kasa taɓuka abin kirkin da zai tabbatar wa jama’a lallai shi masoyin ta ne, to zai iya rasa ta a matsayin matarsa.

 Wasannin da Bera Kan Shirya

A wasu ƙauyuka na Maguzawa, akan zaɓi wani saurayi a matsayin shugaban ’yanmatan ƙauyen. Ana kiran wannan saurayi bera (béerà). A lokacin kaka, Bera kan karɓi ’yanmata daga hannun iyayensu su rinƙa zagayawa daga ƙauye zuwa ƙauye ko daga unguwa zuwa unguwa suna yin wasa. Zai ba iyaye tabbacin ’yanmatan suna hannunsa. Duk abin da ya same su shi ne. Za su yi kwanaki da yawa ba su gida. Idan aka je fagen wasa, makaɗi zai nemi alfarma wurin Bera da ya ba shi ’yanmatan su yi masa rawa yana kiɗa. Su kuma samari za su yi ta nuna soyayyarsu ga ’yanmatan nan ta hanyar yi musu kari/liƙi. Abin da aka samu za a raba tsakanin makaɗi da Bera. Shi kuma Bera ya sami abin da ya  ba ’yanmata. Bera yana taƙama da makaɗi, shi kuma makaɗi yana taƙama da ’yanmata. Su kuma ’yanmata suna taƙama da samari. Ko da budurwa ta nuna tana son saurayi, ba za ta yarda da shi ba, ko ta amince masa su yi zance, sai da yardar Bera. Shi kuma Bera ganin cewa, ya ɗauko alƙawari tsakaninsa da iyayen ’yanmatan, to ba zai yarda ya bar budurwa ta bi saurayin da bai amince da tarbiyarsa ba. Shi ke da ikon ya ce budurwa ta tafi wurin Wane, kada ta je wurin Wane. Haka kuma shi ke da ikon ya ce ga lokacin da za ta dawo, ko ya ba da sharaɗin kada a wuce lokaci kaza. Shi kuma saurayi, Bera zai ja kunnensa cewa, idan ya saɓa masa, kowane irin mataki soyayyar ta kai zai iya ruguza ta. Ko da suna son junansu, sai dai su haƙura. A lokacin irin waɗannan wasanni, farin jini ’yanmata yakan fito a fili. Haka su ma samari sukan sami damar nuna soyayyarsu da gane budurwar da ke son su ta yadda za a ci gaba da gina dangantakar har a kai ga aure.


Gaɗa

A lokuta daban-dabam, bayan an gama cin abincin dare, ’yanmata sukan haɗu a wani fili a unguwa ko a ƙauye don yin wasanninsu na gaɗa. A nan ma akan sami makaɗan da sukan zo su taya su cashewa. Su kuma samari suna amfani da wannan damar wurin sa kuɗi ko wani abu ga wata budurwa don ta fito ta yi rawa. Idan tana da masoya da yawa a wannan fili, lokacin za su fito su nuna, ta hanyar ajiye kuɗi su sa ta yin rawa. Ita ma a irin wannan wuri takan nuna ra’ayi ko rashin son saurayi. Idan ta ƙi fitowa ta yi rawa na kuɗin da saurayi ya sa, hakan ya nuna ba ta ra’ayinsa. Wanda ta yi rawa a kan bukatarsa, to shi ake gane tana so. Daga nan sannu a hankali wanda ta nuna tana son zai yi ta gina dangantakar har ta kai ga wani mataki.

 Hikimomin Al’adun Bayyana Budurcin Maguzawa

Da dama daga cikin Hausawa za su kalli waɗannan al’adu da mummunar fuska musamman saboda ɓirɓishin rashin wayewa ko kwamacalar da ke ciki. To amma idan da za a nazarce su da idon basira, a kuma kwatanta su da yanayin wayewar Hausawa  a yanzu, za a yaba da hikimar Maguzawa da suka assasa waɗannan al’adu kuma suka jaddada su. A wannan fasali, za a baje waɗannan al’adu a faifan nazari don zaƙulo alfanun da suka yi wa rayuwar ta Maguzawa wanda ya samar musu da kariyar mutunci ta fuskoki da dama.

Ba Samari da ’Yanmata Damar Bayyana Soyayya

 Kunya da rayuwar Hausawa kamar tsoka da jini suke. Wannan al’ada ta kunya tana daga cikin ɗabi’un da suka ƙara bayyanar da kimar Bahaushe a idon duniya tun fil-azal. Akwai kunya matuƙa ga saurayi ya fito kai tsaye ya ce wa mace yana son ta. Babu laifi ya yi ta kiwon hankalinta da sha’awar siffofin jikinta da kuma yaba nasabarta. Haɗuwar da ake yi a waɗannan wurare tsakanin samari da ’yanmata, inda za su sa wa budurwa kuɗi ta fito ta yi rawa, ko in tana rawa saurayi ya yi mata kari/liƙi, wata dama ce da saurayi ya samu ta fitowa ya bayyana so. Wannan saɓani ne ga abin da ke faruwa a yanzu, inda samarin Hausawa ke cire takunkumin kunya da al’ada ta ƙargama musu, su tunkari budurwa kai tsaye don su bayyana  mata ra’ayinsu na soyayya. Wannan ba al’adar Hausawa ba ce, kuma ga dukkan alamu samo ta aka yi daga wani tunani na daban. Su ma ‘yanmata ko budare a nasu ɓangaren, wata dama ce da za su fito kai tsaye, su nuna amincewa ko rashin amincewa da saurayi ba tare da munafunci ko yaudawa ba. Da zarar saurayi ya sa kuɗi aka ƙi fitowa a yi masa rawa, ya ga alamar babu haske a wannan wurin. Ita kuma ta sami shedu da yawa da za su tabbatar da cewa, tun farko ba ta amsa masa ba. Wannan saɓani ne ga abin da ke faruwa a yanzu. Sai a yi shekara da shekaru ana yaudarar saurayi, alhalin ba a da niyyar auren sa.


Ishara ga Iyaye da Dangi

Waɗannan al’adu wani hannunka-mai-sanda ne ga iyayen ’yanmata da samari su san ra’ayin ’ya’yan nasu a kan lamarin aure. Da zarar iyayen budurwa ko wakilansu kamar su Bera suka ga alamar inda ra’ayin ta ya karkata a fagen aiwatar da waɗannan al’adu, an ba su hasken fara gudanar da bincike tun kafin iyayen saurayi su fito. Wannan kai tsaye ya saɓa wa irin rayuwar ƙarya da ake gudanarwa a yanzu. Budurwa sai ta yi shekara da shekaru tana tare da saurayi ko ma samari da yawa, ba tare da iyayenta sun sani ba. Wannan yanayi da ake ciki yanzu, ba ya ba iyaye damar sanin halin da ’ya’yansu ke ciki ta fuskar mu’amala da ake sa ran ya kai ga aure.

Kare Ɗiyaucin ’Ya’ya Mata

Al’adun bayyana budurcin Maguzawa, sun yi tanadi na musamman wajen kare ɗiyaucin ‘ya mace. Wannan ya ƙara tabbatar da wayewar Maguzawa. Dabarar da ake yi wajen damƙa amanar ’ya mace ga Bera, wata katangar ƙarfe ce a gare su. Irin amanar da ke tsakanin wanda suka ba ’ya’yansu, da kuma dagewar da yake yi na ganin bai ci amanarsu ba, ta hanyar barin a yi abin da aka ga dama da su, haƙiƙa wani abin sha’awa ne. Wannan dabara ta Maguzawa ta yi daidai da koyarwar musulunci na rashin bayar da dama ga mace ta yi tafiya ita kaɗai ba tare da rakiyar muharraminta ba. Wannan ya ƙara fito da wautar wayayyun Hausawa a yanzu da suke barin ’ya’yansu mata suna tafiya su kaɗai na kwana da kwanaki ba tare da kulawar kowa ba. Ashe ba zai zama abin ka-ce-na-ce ba idan aka ce Bamaguce ya fi wayayyen Bahaushen zamani hankali da zurfin tunani musamman a irin wannan lamari.

 Fayyace Kyauta Tsakanin Saurayi da Budurwa

Duk abin da aka yi a ƙudundune, to ƙarshen ta a ji kunya. Waɗannan al’adu sun yi tanadin fayyace kyauta musamman na farko-farkon gina soyayya daga saurayi zuwa ga budurwa a bayyane. Idan saurayi na son budurwa, dole a irin wannan yanayi ya fito bainar jama’a ya sa kuɗi a kan ta, kuma a bayyana wa jama’a. Haka kuma idan kari/liƙi zai yi mata, a fili ake yin hakan. Shi ma Bera, haka yake kasa abin da aka tara a wajen wasa, ya ba ’yanmata nasu. Wannan ya sa Maguzawa suka sami kariya daga tarkon zargi ko ƙazafin cin kuɗin saurayi daga budurwa da iyayenta. A duniyar Hausawa ta yau, Allah kaɗai ya san yawan rikice-rikicen da ke maƙale a kotuna na zargin cin kuɗi ko dukiya daga budare da iyayen su. Wannan yana faruwa ne saboda a duƙunƙune ake yin kyautar a lokacin da ake cikin shauƙin soyayya.

Samun Damar Zaɓe

Duk abin da aka bayyanar da yawa, to mutum yana da damar darjewa ya zaɓa. Ga samari, waɗannan al’adu sun ba su damar ganin ‘yanmata da yawa suna fitowa wajen rawa. Ta nan saurayi zai zaɓa ya darje, kafin ya fara tunanin jawo ra’ayin budurwar da ya ji yake so. Haka su ma ‘yanmatan, sukan yi amfani da damar karakainar samari a kan su, ta yadda sai sun zaɓi wanda ya yi musu.

Dabarun Inganta Tattalin arziki

Ganin irin alherin da wanzami da makaɗi da Bera suke samu a sakamakon aiwatar da waɗannan al’adu, ya nuna a fili cewa, wasu hanyoyi ne na farfaɗo da tattalin arziki. Daga cikin abin da suke samu na kari/liƙin da ake yi wa ’yanmata, za su warware matsalolin rayuwa da suka yi musu dabaibayi musamman a wannan shekarar. Wannan ba ƙaramar dama ba ce da hikima ta amfani da waɗannan al’adu a sami abin da ake so. Al’adun sun ba su damar mallakar abin da zai ƙara wa noman da suka yi auki, kuma su gudanar da hidimomin da suka sa a gaba cikin sauƙi. Haka kuma wannan damar ta kare su daga wulaƙanta a hannun mutane ta hanyar roƙo ko neman gudunmuwar dangi idan wata lalura ta taso.



Naɗewa
Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin fito da wasu al’adun nuna budurcin Maguzawa tare da bayyana hikimomin da ke ƙumshe a cikinsu. Waɗannan al’adu kamar yadda aka yi bayaninsu, sun haɗa da gaɗa da wasannin da Bera kan shirya da shasshawa da ziyarar makaɗi. Iyaye suna amfani da waɗannan al’adu ta hanyar sanin ra’ayin ’ya’yansu mata da kuma bayyanar da su ga mabiɗa ta yadda za su gina dangantakar da ake tunanin ta ɗore har abada. Ta fuskar manema aure kuma, su ma fitowar mata a irin waɗannan al’adun sukan sami damar zaɓe. Su kuwa wanzamai da makaɗa da Bera, wata dama ce ta inganta yanayin rayuwa, baya ga abin da suka samu na noma. Waɗannan al’adu sun taimaka wa Maguzawa kasafta yanayin rayuwa da tsara ta, baya ga nishaɗantarwar da kowane rukuni suka amfana da ita.


Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.