Ticker

6/recent/ticker-posts

Bukin Hawan Sadaka Na Maguzawa


Maƙasudin wannan nazarin shi ne duban irin yadda al’ummar Maguzawa suke aiwatar da wani ƙasaitaccen buki wanda ke yi wa mutuwa rakiya....


Bukin Hawan Sadaka Na Maguzawa

Dr. Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato.
e-mail: ibrasskg@gmail.com
Lambar Waya: 0803 6153 050

1.0       GABATARWA


Mutuwa babban rashi ne da kan sa baƙin ciki da juyayi a kowace al’umma ta duniya. Wannan rashin yakan sa dangin mamacin su shiga cikin wani hali na kaɗaici da kewa da matsaloli iri-iri musamman idan ya kasance wani ginshiƙi ne aka rasa. Duk da irin wannan hali da akan shiga na sakamakon irin wannan rashin, al’ummomi da yawa musaman a nahiyar Afrika suna gudanar da bukukuwa daban-daban haɗe da shagulgula don yi wa mutuwa rakiya. Dalilan wannan bukin yakan bambanta daga al’umma zuwa wata. Haka ma ko a cikin al’umma ko ƙabila ɗaya, matsayin mamaci ko jinsi ko yawan shekaru kan iya bambanta nau’in bukin da za a yi.



Maƙasudin wannan nazarin shi ne duban irin yadda al’ummar Maguzawa suke aiwatar da wani ƙasaitaccen buki wanda ke yi wa mutuwa rakiya.[i] Wannan buki kuwa shi ne bukin cika shekara da mutuwar Bamaguje. Wasu Maguzawan suna kiran wannan buki da suna Bukin Juya Kafaɗa. Maguzawan da suke zaune a ƙasar Katsina  (ta yanzu) sun fi sanin wannan buki da suna Bukin Hawan Sadaka.  Masu gudanar da wannan bukin sun tabbatar da cewa, ba su sami wannan sunan ba sai bayan da wasu Maguzawa suka zama Musulmi. A lokacin ne suka maye gurbin wannan bukin na shekara da yin sadaka. Maimakon a yi tsafe-tsafe da kaɗe-kaɗe, sukan tara mutane ne a yi addu’oi, a ba jama’a abinci a matsayin sadaka. Su kuma ’yan’uwansu da ba su musulunta ba sai suka sauya wa bukin da suka saba yi suna da Bukin Hawan Sadaka maimakon Bukin Juya Kafaɗa wataƙila don su tafi da ra’ayin ’yan uwansu musulmi ko don ganin su ma kwatankwacin sadakar suke yi a nasu bukin. Sun cusa kalmar Hawa ne saboda sukan hau dawaki a yi sukuwa a lokacin bukin. Wannan ya sa sunan ya sami karɓuwa ba ma ga Maguzawan kaɗai ba, har ga musulmin da ke zaune kusa da su. Abin da kawai suke ganin ya bambanta bukin hawan sadaka na Maguzawa da sadaka ta mutuwar Musulmi shi ne shan giya da tsafe-tsafe da sukuwar dawaki da kuma kaɗe-kaɗe. Ta fuskar bayar da abinci ga jama’a, in dai ba a ce sun ɗara na Musulmin da suke Maguzanci da ba, to ba za a  ce an ɗara su ba.

https://www.amsoshi.com/2017/10/19/hutawa-ka-alewa-man-gyada-ka-tuyar-kosai-barazanar-yanayi-da-kutsowar-lokaci-ga-aladunmu-aliyu-muhammadu-bunza/




2.0 MAMACIN DA AKE YI WA BUKIN HAWAN SADAKA




Bukin hawan sadaka na mutuwar Maguzawa shi ne kusan buki na ƙarshe mai muhimmanci da ake gudanarwa idan Bamaguje ya mutu. Kafin wannan buki, Maguzawa suna gudanar da bukukuwa na kwana uku, da na kwana bakwai da kuma na kwana arba’in da mutuwar mutum. Idan yaro ya mutu ba a kan yi wani buki sosai. Da zarar an haɗu a bukin rana ta bakwai da mutuwa, an ƙare ke nan. Ita kuma mace komai girmanta ko matsayinta, akan ƙare nata bukin mutuwar ne a rana ta arba’in da mutuwa. A al’adance babban mutum (namiji) kaɗai ake yi wa bukin hawan sadaka. Ko shi ma sai tsoho wanda ya bar zuri’a da yawa, ko wani shahararren Sarkin noma wanda ya yi dubu.[ii] Abin kunya ne ga ’ya’yan da irin waɗannan mamata suka bari idan suka kasa yi wa iyayensu wannan bukin, domin akan yi musu gorin da sukan kasa sakin jiki a al’umma. Haka shi ma mamacin, abin alfahari ne ya yi ƙoƙarin kaiwa wannan mataki ko matsayi a al’umma da zai tabbatar da ko ya mutu ya bar zuri’a da halin da za a yi masa bukin hawan sadaka.


3.0  SHIRYE-SHIRYEN HAWAN SADAKA


Bukin hawan sadaka  buki ne da ba  kamar sa idan  ana maganar bukukuwan Maguzawa na mutuwa. Wannan  ya sa suka yi masa tanadi dangane da  shirye-shirye mataki-mataki. Muhimmancin wannan buki da shagulgulan da akan yi da ɗaukar ɗawainiyar mutanen da ke halarta kan sa sai wanda ya isa yake yi, kuma sai an yi kyakkyawan shiri. Duk da yake dangi da ’yan’uwa suna kawo gudummawa da yawa, akwai buƙatar wanda zai ɗauki ɗawainiyar ya shirya sosai. Idan shekarar mutuwar ta zagayo ba a gama shiri ba to ana iya jinkirtawa, sai wata shekarar ko kuma duk lokacin da aka sami hali. Abin kunya ne mutum ya kasa yi wa ubansa bukin shekara. Haka kuma, yakan zama abin jinjinawa da burgewa da nuna isa ga Bamaguje ya ɗauke wannan nauyin a rayuwarsa. A ƙoƙarin tabbatar da an yi wannan bukin yadda ya kamata, Maguzawa sukan aiwatar da shirye-shirye waɗanda suka haɗa da:


3.1       Neman  Izini 


Kafin Bamaguje ya ce zai yi wa ubansa bukin hawan sadaka sai ya nemi izini daga shugaban wannan ƙasar da ake ƙarƙashin riƙonsa. Ga misali Maguzawan Lezumawa idan za su yi bukin hawan sadaka sai an sanar da Babban Kada wanda shi ne shugabansu. In bai amince a yi ba, ba yadda za a yi sai a haƙura. In kuma ya amince sai a ci gaba da sauran shirye-shirye. Za a sami lokaci na musamman a sanar da shi. Ko dai ya amince nan take, ko kuma ya ce a ba shi lokaci. Wannan kan ba shi damar ya yi shawara da makusantansa dangane da waiwayen ayyuka da mu’amalar mamacin a lokacin da yake raye. Idan sakamakon bai gansar da su ba, misali mamacin ya yi wasu munanan ayyukan da suka saɓa wa zamantakewa, sai a yanke shawarar rashin cancantar a yi masa bukin. Haka kuma shugaban tsafin yakan yi ƙoƙarin sanar da iskokin da suke bauta wa don neman yardarsu.


3.2       Gayyatar  Jama’a


Bayan shugaba ya amince za a aika wa dangi na kusa da na nesa. Su kuma su haɗu a aika da goron gayyata ga jama’a. Duk yankin da ke da Sarkin Noma da jama’arsa, za a aika musu da goron gayyata. Da yake buki ne da ke bukatar shiri sosai, duk Sarkin Noman da za a gayyata yana bukatar ya sami labari da wuri don ya sa a shirya dawaki da tsafe-tsafe da makamai da kuma shirya adadin mutanen da zai zo da su. Ana riƙa makamai ne saboda bukin kamar wani yaƙi ne da nuna bajinta ko buwaya ko fifiko a tsakanin Maguzawan da suka fito daga muhalli daban-daban. Da makaman ake amfani wajen gwagwarmayar fasa gidan mamacin.


3.3       Abinci da Muhalli


A lokacin da ake bukin hawan sadaka, shi uban sadakar (wanda zai yi wa ubansa sadaka) shi ke da alhakin saukar da duk waɗanda aka gayyata. Shi ne abincinsu, shi ne giyar da za su sha. Shi ne abincin dawakan da za su zo da su, shi ne wajen kwanansu. Don haka sai ya tabbatar da ya tanadi waɗannan kafin ya kira bukin. Wannan ne ma ya sa Maguzawa suke yi wa bukin kirari da “Hawan sadaka sai wanda ya shirya.” A nan ana nufin shiri na magani (neman buwaya ta hanyar tsafi) ga shi wanda aka gayyata da kuma shiri na ɗaukar ɗawainiya ga wanda ya gayyato jama’a. Uban sadaka zai tabbatar da rumbunan gidansa a cike suke da hatsi. Wannan hatsin za a ci, shi za a ba dabbobi su ci, domin akan sami dawaki fiye da ɗari biyar a lokacin bukin hawan sadaka. Kuma kowane doki damin dawa akan ajiye masa in ya cinye a ƙara ajiye masa wani. Daga hatsin  da aka  tanada za a ɗiba a yi giyar da taro za su sha. Haka kuma, dole zai tanadi sa ko ma shanun da za a yanka wa taro su ci nama. Duk da yake ana samun gudummuwar ’yan awaki daga dangi, idan taro ya yi taro wane ’yan awaki wajen ƙosar da su da nama! Haka kuma zai tanadi turakun da mutanen da aka gayyata za su ɗaure dawakinsu. Za a yi rumfuna inda za a saukar da jama’a.


3.4       Gayyatar Makaɗa


Bukin hawan sadaka bai taɓa yiwuwa ba tare da makaɗa ba. Wannan ne kan sa akan gayyato shahararrun makaɗan da aka san sun yi fice a ƙasar wajen iya kaɗe-kaɗen bukin. Su ma dole a tanadar musu rumfar sauka da kuma abin sallama. Waɗannan makaɗan ne za su riƙa kaɗa taken mamacin a lokacin bukin. Su ma sarakunan noman da za a gayyata, in za su zo, yawanci suna zuwa da makaɗansu. Su kuma aikin su shi ne su rinƙa wasa gwarzayen da aka zo da su.  Uban sadaka yakan yi wa makaɗan da suka burge kyauta ta musamman, baya ga abin da iyayen gijinsu za su sallame su da su. Idan makaɗi ya yi sa’a a wajen bukin hawan sadaka, baya ga ’yan ƙananan kyaututtuka da zai samu daga jama’a, har kyautar doki yana iya samu.

https://www.amsoshi.com/2017/10/19/darussan-daular-sakkwato-ga-musulman-nijeriya-na-hijira-1435a-h/

3.5       Gudummawar Dangi


Tun lokacin da aka tsayar da ranar da za a yi bukin hawan sadaka dangin uban sadaka za su yi ta kawo masa gudummawa musamman ta hatsi da ’yan awaki. Idan mamacin mai mutane ne, akan sami tara ’yan awaki fiye da ɗari da za a yanka wa jama’ar da aka gayyata. Haka kuma, a wurin jikokin mamacin, bukin hawan sadaka wata dama ce da sukan samu don nuna son su da ƙauna ga mamaci ta hanyar kawo masa ɗan akuya. Sai dai su nasu ’yan awakin ba a kawo su sai bukin ya kankama. Idan mutum ya yanka ɗan akuyarsa zai ciri “karfata” ya bar wa uban sadaka sauran.[iii]


4.0 LOKACIN YIN BUKIN HAWAN SADAKA DA KWANAKIN DA AKE YI


Maguzawa ba su da wani aiki da ya fi noma a rayuwarsu. Wannan ya nuna ke nan, ba yadda za a yi a sa wannan shagalin da ke bukatar ɗimbin lokaci wajen shirye-shirye a lokacin damana. Baya ga cewa in an sa a damana ba wanda zai sami damar zuwa, ruwan sama da ake tabkawa a wannan lokaci zai hana jama’a gudanar da bukin cikin natsuwa. Wannan ya sa ya zama dole a sa bukin a lokacin rani, lokacin da aka tabbatar mutane sun ƙare aikin gona. Haka kuma, a irin wannan lokacin, dangin mamacin suna cikin yalwan abinci wanda sukan ɗiba su bayar a matsayin tasu gudunmuwa.  Gudun kada ranar da aka sa ta yi daidai da ta wasu, a lokacin da aka je neman izini wajen shugaban Maguzawan za a daidaita,  a tsara  shi ta yadda za a gama na wannan kafin a fara na wani. Dangane da tsawon lokacin da akan ɗauka ana yi, wannan ya dogara ne ga irin shirin da uban sadaka ya yi. An fi yin bukin cikin kwana uku, duk  da yake wasu suna kai shi har kwana huɗu.




5.0 YADDA AKE YIN BUKIN HAWAN SADAKA


Idan ranar da za a buɗe bukin sadakar ta zo, tun daren wannan ranar za a fara hallara. Waɗanda ke kusa kuma da safiyar wannan ranar za su iso. Da ma an riga an yi rumfuna da dama a wurare daban-daban. A cikin rumfunan za a saukar da duk Sarkin Noman da ya iso da jama’arsa. Za su ɗaure dawakansu a kusa da rumfar. A nan za su riƙa kwana, a nan kuma za a riƙa kawo musu abinci. Ba a taɓa sauke jama’ar Sarkin Noma biyu a rumfa ɗaya, saboda tsoron yi wa juna makaru da ma ɓarkewar faɗa tsakanin jama’ar juna musamman in akwai wata azazza a tsakaninsu. A cikin tawagar kowane Sarkin Noma ana samun ’yan tauri da mafarauta da shahararrun matsafan garin da ’yan bori da samari majiya ƙarfi masu alfahari da noma. Duk waɗannan mutane kowa zai riƙo makaman faɗa iri-iri ka ce dai rundunar yaƙi ce. Haka ma za a sami makaɗa da maroƙa da za su riƙa kaɗa musu take suna yi musu kirari idan an shigo fage.



A cikin wannan daren ba wanda zai fita waje, domin a ranar Sarkin  Noman wannan gari da aka zo hawan sadaka zai gudanar da nasa tsafe-tsafen. Baƙin da aka gayyato kowa zai kasance cikin rumfarsa. Su ma mutanen gari kowa zai ɗauke ƙafa. An nuna cewa, idan mutum ya haɗu da shugaban tsafin a wannan dare to tasa ta ƙare. Haka su ma iyalin gidan uban sadakar a wannan daren za su ƙaurace wa gidan nasu, inda aka binne tsohon da ya mutu. Za su koma gidajen maƙwabta da na ’yan’uwa. Haka kuma za a yi wa gidan sabon darni inda akan yi wasu ’yan sihirce-sihirce wurin yin sa.



Gari na wayewa bayan an kai wa mutane karin kumallo, za a fara jin kaɗe-kaɗe na tashi daga rumfunan da aka saukar da mutanen da aka gayyata. Kafin a ce an ba su umurni su shigo ƙofar gidan da za a yi bukin, jama’ar gari (’yan kallo) sun taru. Shugaban tsafin da uban sadakar da manyan magabata da duk dangin wanda za a yi wa bukin za a shimfiɗa musu tabarmi a gefe ɗaya su zauna. Kowane Sarkin Noma da jama’arsa za su iso wannan wuri. Bayan an hallara, abin da za a fara yi shi ne cin tuwon noma.


5.1       Cin Tuwon Noma


Shi dai tuwon noma a al’adar wannan buki mugan tuwo ne da aka yi wa haɗe-haɗen tsafe-tsafe da magunguna ta yadda ba kowa ke iya cin shi ya kwana lafiya ba,  sai arnen da ya ci magani ya ƙoshi, ya shahara kuma yana son ya nuna bajintarsa. Maguzawa sukan ce duk mai son ya mutu ko ubansa ya mutu, to ya ci tuwon noma. An nuna cewa, abu ne mai wuya a duk lokacin da aka yi irin wannan buki ba a sami waɗanda suka mutu ba a sakamakon cin wannan tuwo na tsafi. Idan har ba a ga wanda ya mutu nan take ba, to kafin wata shekara ta zagayo za a ji wasu da ba su ƙoshi da magungunan kariya ba sun mutu a sanadiyyar cin wannan tuwon. Hakan ya sa in har Arne ko Sarkin noma zai ci tuwon noma to tun daga gida ake fara shiryawa. Idan an san mutum bai shirya ba to akan ja kunnensa da ya fasa, saboda in ba a yi hattara ba ƙarshensa ke nan. Ga duk wanda ya ci wannan tuwo kuma ya kwana lafiya, ko ya shekara garau, to ya zama abin alfahari ga kansa da dangi. Zai zama abin tsoro, kuma za a yi ta nuna shi in an zo wani taro ana ba shi girma.



A al’adance, babban maroƙin shugaban tsafin garin ke kawo wannan tuwon kamar malmala uku, ya ajiye a tsakiyar fili. Haka kuma za a kawo gasasshen ɗan akuya da aka banƙare a ajiye tare da tuwon nan. Su kuma masu niyyar cin wannan tuwo za su fito daga cikin sansaninsu su taru a gefe ɗaya. Bisa al’ada, ba  wanda zai ci wannan tuwon sai in mutum yana da tabbacin zai iya yi wa tsohonsa da ya mutu ko wani nasa irin wannan buki idan shekara ta zagayo. Shugaban tsafin zai umurci wannan maroƙin da ya gabatar da tuwon ga arna masu niyyar ci. Maroƙin zai fito tsakiyar fage ya yi ihu a yi tsit! Sai ya ce:

“To, Arna!

Ga fa tuwon sadaka nan!”



Yana rufe baki zai koma gefe ɗaya. Daga cikin masu cin wannan tuwo za a sami wanda zai buɗe taro, ya tsakari dokinsa a guje ya nufo inda wannan tuwon da naman suke, ya ridi wani sashe na gasasshen ɗan akuyar nan. Ba zai sauko daga kan dokin ba, yana sama zai sunkuyo ya ɓalli wani sashe na naman ya goga a bakinsa, ya yar da suran. Haka duk za su yi ɗaya bayan ɗaya sai kowa ya ƙare. Tun a lokacin da arne ya rugo a guje kan doki, idan akwai wani abokin adawarsa da suke da azazza yana can gefe ya shirya masa. Da ya kalle shi ya kau da kai wanda ke kan dokin yana iya faɗowa ya mutu nan take. Saboda haka ba kowa ke iya kaiwa ga tuwon ba sai wanda ya ƙoshi da magani.



Daga nan sai kuma waɗanda suka sami kaiwa ga naman su sauko kan doki su rinƙa ɗiban loma ɗaya ko biyu suna kai baki. Hankalin jama’a da dangi kan tashi idan suka ga arne ya yi ƙarfin halin kai wannan tuwon bakinsa sanin cewa, ba da kowa za a ƙare lafiya ba. Wasu sai sun ɗebi tuwon su kasa kaiwa baki dole su ajiye. Wasu tuwon na shiga baki sai ya kasa wucewa, ya maƙale musu a wuya su mutu. Wasu suna kai tuwon nan baki sukan faɗi su mutu. Wasu sai an tafi gida, wasu bayan watanni. Waɗanda suka shirya su ke takewa, sai dai kawai a ga sun kawo wa mutane goron gayyata a shekara mai zuwa. Da an gama cin wannan tuwo sai kowa ya koma sansaninsa. Akan daɗe ana wannan al’ada saboda abu ne da ake yi ɗaya bayan ɗaya. Kuma idan wani ya kasa ko ya haɗu da gamonsa, akan jira a kawar da shi a kai bayan fage kafin a ci gaba. Idan an  gama cin wannan tuwo sai a sallami taro, kowa ya koma masauki ya shirya wa wata dagar da za a yi washe gari wajen fasa gida.

                       

5.2       Fasa Gida


Fasa gida wata gasa ce tsakanin mutanen da aka gayyata daga wurare daban-daban. A wurin wannan gasa ana so ne a ga wanda zai jagoranci karya darnin gidan da aka binne gawar mamacin, a yi kaca-kaca da gidan. A washegarin ranar da aka ci tuwon noma za a ƙara haɗuwa a filin da ake wannan buki.[iv] Kowane Sarkin Noma zai zo da jama’arsa da makamai da makaɗa da maroƙa. Idan kowa ya hallara za a ce duk mai son fasa gida ya zo ya nemi izini a wajen shugaban wannan taro wanda shi ne shugaban tsafin ƙasar. Shi ke ba da izini ga kowane Sarkin Noma da jama’arsa su fasa gidan mamacin, inda kushewarsa take. Wannan ne dalilin da ya sa aka ce iyalin gidan su ƙaurace wa gidan na tsawon lokacin da za a yi wannan bukin. Haka kuma shi ya sa ake yi wa gidan darnin kara wanda ake tsafewa don nuna ƙarfin mamacin da tsafin da ya bari.



Idan aka ba da umurnin fasa gida, kowane Sarkin Noma zai shiga gaba a kan dokinsa a guje, jama’arsa na biye da makamai, ana kiɗa, ana yi musu kirari, ya nufato wannan gidan da niyyar zai fasa darni ya shiga. Wannan shi ma abu ne mai wuya saboda tsafin wannan gida da na mamacin za su ci karo da na Sarkin Noman da ke so ya fasa gidan. A nan ma akan iya rasa rayuka domin yakan zama kamar yaƙi ne. Idan Sarkin Noma ya kasa, ya ji kunya sai ya dawo da baya, wani kuma ya gwada sa’arsa. Baya ga hana fasa gidan da tsafin mamacin da na danginsa za su yi, sauran abokan hamayya da suke nan su ma suna baƙin cikin su ga ya yi nasara. Don haka ba za su bar shi hakanan ba. Wani yana nufato wannan darnin za a ga ya faɗi ya mutu. Wani kuma a ƙoƙarin karya wannan darnin zai iya faɗowa kan doki ya mutu.



Wanda ya yi nasarar fasa wannan darnin ya karya shi ya shiga gidan, duk jama’arsa za su ɗuru cikin gidan ana jin daɗi. Su ma sauran Sarakunan noman kowa zai yi ƙoƙarin neman inda zai fasa ya shiga gidan. Wasu su fasa ta gaba, wasu ta baya. Idan kowa ya sami shiga gidan ta nasa gefen duk jama’arsa za su bi shi da makamansu. Gidan zai rincaɓe. Faɗa tsakanin  ƙungiyoyin mutanen daban-daban yana iya ɓarkewa a yi ta sare-sare har ma da kashe-kashe.



A wurin wannan bukin ba abin da ya fi ɗaukaka mutum kamar fasa gida. Ba ƙaramin shiri ke sa Sarkin Noma ya iya fasa gida ba. Tun daga wannan lokaci zai sami ɗaukaka a idon mutane. Za a rinƙa nuna shi ana cewa, Ga Sarkin Noman da ya fasa gidan Sarkin Noma Wane. Za a rinƙa jin tsoron sa da ma mutanensa. Yawan fasa gidajen da Sarkin Noma ya yi, yakan samar masa ƙarin ɗaukakar. Bayan Sarkin Noma ya fasa gida, ba ta ƙare a nan ba, dole sai ya koma gida ya ƙara shiri. Domin tun a wannan lokacin ne zai fara fuskantar barazana na rayuwa. Baya ga ƙwanƙwaman mamacin da ya fasa gidansa, abokan adawa da suke jin takaicin ya riga su fasa gidan za su far masa. An nuna cewa, yana iya haɗuwa da wani hatsari a kan hanyarsa ta komawa gida ya ji rauni ko ma ya mutu. Idan kuma aka bari ya kai gidan lafiya, ana iya tsaface shi ya kasa samun lafiyar da zai yi noma a wannan shekarar. Idan kuwa Sarkin  Noma ya kasa noma to babu sarautar ke nan. In kuma har ya gagare su ya sami yin noman, to sai amfanin gonar ya ƙi yin auki. Idan Sarkin  noman ya shiryu, to ba abin da zai same shi. Gani nan bari nan! Sai dai abokin adawa ya ƙara wani shirin in an haɗu a wani bukin hawan sadakar. A haɗuwa ta gaba sukan yi wa Sarkin Noman da ya yi fice wajen fasa gida maganin da zai kasa zuwa.  Wani uzuri  ya hana shi,  ko rashin  lafiya ya rufe shi a daidai wannan lokaci. Suna ganin da zarar an bari ya je to ba su da hus, sai fa in maganin da suka tanada kafin wannan shekarar ya ɗara nasa.


 5.3      Shiga Sayi


Shiga sayi ya fi komai burgewa a wajen wannan buki na hawa sadaka. Sayi shi ne bukka ko ɗakin da aka binne mamaci. Nan ma wani wuri ne da akan tsafe saboda ya ba masu fasa gida wahalar shiga. Da farko dai gane ma inda sayen yake wani bajinta ne na tsafi da magani. Haka kuma, shiga ciki ko tunkuɗe bukkar shi ma abin bugun gaba ne. A daidai lokacin da gidan ya rincaɓe, ba abin da sarakunan noma da jarumawansu sukan duƙufa a kan sa sai ƙoƙarin gano wajen. Idan mutum ya yi sa’a ya gane wajen zai tunkuɗe bukkar ko ya fasa ɗakin ya shiga ya yi ihu, ya yi kirari. Yin haka ya nuna cewa mutumin ya cika gwarzon wannan bukin ke nan. Makaɗa za su taru a kan mutumin ana wasa shi ana yi masa kirari. A nan ma an nuna ana rasa rayuwa saboda sare-sare da buge-buge a ƙoƙarin da kowa ke yi na ganin ya fara shiga Sayi.



Ana ƙare wannan jidali an gama bukin wannan ranar ke nan sai kuma a koma masauki sai gari ya waye a yi sukuwa. Wasu kuma tun a wannan ranar za a fara watsewa musamman waɗanda suka ga ba su yi nasara ba sai su kama hanya a fara shirin na gaba.


5.4       Sukuwar Dawaki


Ga waɗanda suke yi wa bukin hawan sadaka kwana uku, a washegarin ranar da aka fasa gida ake yin sukuwar dawaki. Manya za su sami wuri su zauna, suna kallon masu sukuwar. Kowane Sarkin Noma zai zo da mutanensa a sanar cewa, wannan shi ne Sarkin Noma Wane ko shi ne ɗan Sarkin Noma Wane. Su yi sukuwa su koma gefe ɗaya. Haka za a yi ta yi sai kowa ya yi. A nan ma akan gwada tsafe-tsafe. Ba wanda ke so a ce wani ɗan’uwansa ya fi shi gwaninta ko taka rawa a harkar buki ko tsafi. Yawanci akan yi wa mutane tsafin su faɗo kan doki su mutu musamman idan an gabatar da mutum an yi masa kirari ya yi sukuwa. Kafin ya sauka kan dokin nan idan akwai maƙiyinsa to sai fa yadda ta Allah ta kasance. In mutum ya gagari abokan adawa to sai tsafin ya koma wa dokinsa. A nan za a ga dokin ya mutu, sai dai ya koma gida ya bar gawarsa. Don haka wasu ma har da dawakin akan tanadar wa maganin buwaya. A wajen wannan sukuwar akan yi wa makaɗin da ya fi nuna hazaƙa kyautar doki. Sauran kuma a yi musu alheri bakin gwargwado. Idan an ƙare wannan sukuwa, za a koma masauki a ci abinci a huta. Gari na wayewa kowa ya kama yanyar zuwa gida.


6.0 NAɗEWA


A wannan nazarin, an waiwayi  bukin da ya fi kowane buki muhimmanci a al’adar mutuwar Maguzawa. Nazarin ya nuna cewa ba kowa ake yi wa bukin ba. Sai namijin da ya taka wani mataki na bajinta a rayuwa. Duk da yake buki ne da ke tafiya da tsafe-tsafe, wata hanya ce da za a iya tabbatar wa duniya cewa, Hausawa suna da hanyoyin gargajiya na nuna ficen namiji da gano gwarzaye a kowace shekara. Haka kuma bukin ya tabbatar da irin fasahar Hausawa na sanin  matakan tsaro da kariyar jiki da ta al’umma wanda ya yi daidai da irin bajintar da ƙasashen duniya ke tinƙaho da shi a yanzu idan sun mallaki makamai da dabarun tsaro. Bukin hawan sadaka buki ne da ke ƙunshe da hikimar Hausawa ta karrama mamaci musamman wanda ya yi abin a-zo-a-gani a rayuwarsa. Irin wannan ɗaukaka da mutun kan samu ko bayan ya kau ya sa akan tashi tsaye wurin neman na kai da kauce wa abin kunya da kuma ƙoƙarin samun zuri’a na gari waɗanda za su yi musu sakayyar alheri. Hausawa sukan ce, “don gobe ake wanke tukunya.”

[i] Maguzawa su ne Hausawan da ba musulmi ba wa]anda addininsu na gargajiya ke jagorancin rayuwarsu.

[ii] Dubu na nufin Bamaguje ya tara dami dubu na kowane nau’in abinci da ake nomawa a  wannan

muhallin a lokacin da aka cire amfanin gona. Don ganin yadda Maguzawa ke yin bukin dubu, Dubi

Kundin digiri na uku, na  Ahmad Magaji, Ja’mi’ar Bayero, Kano- 2002,  mai take: “Wasu Al’adun

Hausawa: Yanaye- yanayensu a Ƙasar  Katsina,”  shafi na 150- 153.

[iii]  Tsokar cinya ko }afar gaba ta dabba ita ake kira karfata.

[iv] Akwai  saɓanin  bayanai dangane da lokacin da akan  fasa  gida a  lokacin wannan  bukin. Wasu da asubar

ranar da za a  fara  bukin ake  fasa  gida.  Wasu kuma  sai washegarin  ranar  da aka fara, amma  babu

wani  bambanci dangane da  abin da ke faruwa.


Post a Comment

3 Comments

  1. Salam.
    Zuwa ga Amsoshi, bayan gaisuwa da fatan alheri. Na ji dadin ziyartar wannan shafi naku. Allah Ya taimaka.
    Bissalam, sai wani lokaci.

    ReplyDelete
  2. This comment has been removed by a blog administrator.

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.