NA
MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato
0703 131 9454
DA
Muhammad Mustapha Umar
Sashen koyar da Harsunan Nijeriy
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
O086 546 6400
Gabatarwa
Manufar kowane jigo daga cikin jigogin wak’ok’in sarauta shi ne, ya yada haske sosai ta yadda za a iya ganin gwarzonsa wato “sarki”(Bunza 2009). Jigon sarki muhimmin jigo ne daga cikin jigogin wak’ok’in sarauta, ko ma a ce shi ne k’ashin bayan wak’ok’in sarauta, domin daman duk wani abu da za a ambata a cikin wak’a tana bayani ne a kan basaraken da ake wak’ewa. Sani Aliyu ‘Dandawo yana daga cikin mawak’an sarauta da suka k’ware wajen kwarzanta basarake a fito da shi fili ta yadda tilas talakawa da ma masu adawa za su sallama masa su ba da kai bori ya hau. Manufar wannan takarda shi ne fito da jigon basarake a wak’ok’in Sani Aliyu ‘Dandawo wanda ya k’unshi k’ananan jigogi da suka shafi jaruntakar basarake da buwayarsa da mallakar k’asar sarauta da alherinsa ko kyautarsa da da zarce tsara da zatinsa da k’warewarsa wajen mulki da iliminsa da asalinsa da makamantan wad’annan. Wad’annan jigogi ne da Sani Aliyu ‘Dandawo yake yawaita kai-kawo a cikinsu a wak’ok’in da yake yi wa sarakuna wanda kuma su ne ke haskaka sarki da k’ara masa k’ima ga jama’arsa da ma sauran al’umma baki d’aya.
Basarake a Wak’ok’in Sani Aliyu ‘Dandawo
Babbar manufar kowace wak’ar sarauta shi ne a fito da basarake a ji shi a ji irin k’wazonsa da martabarsa da sauran kyawawan halayensa. Daga cikin manyan jigogin wak’ar sarauta sarki na ciki. Idan aka duba sarauta, aka dubi masarauta, abu na uku da ya kamata a duba shi ne “sarki”. Dalili kuwa shi ne, ba a sarkin da ba ya da sarauta kamar yadda ba za a yi sarkin da ba ya da masarauta ba (Bunza 2009). A tsarin rayuwar Hausawa tun zamanin zamunna da suka gabata har zuwa wannan zamani, basarake mutum ne ko shugaba da ake girmamawa, ake tsoronsa, ake bin umarninsa na a yi ko a bari, saboda d’aukaka da kwarjini da martabar da Allah Ya ba shi. Duk da wad’annan matsayi da basarake ke da su bai hana ya samu magauta ko abokan hamayya da suke neman su yi takin-sak’a da mulkinsa ba. Wannan ne ya sa mawak’an sarauta idan suka zo wak’e basarake sukan kururu ta shi su cicci’ba shi bisa ga abokan hamayya domin tsoratar da su ko karya musu guiwa. A k’ok’arinsu na yin haka ne za su rik’a fito da jigogi iri daban-daban kamar wad’anda aka ambata a baya suna tabbatar da su zuwa ga basarake. Za mu d’auki d’auki ire-iren wad’annan k’ananan jigogi na basarake daga wak’ok’in Sani Aliyu ‘Dandawo mu ga yadda ya k’awata su ga sarakunan da yake wak’ewa.
https://www.amsoshi.com/2017/10/12/bugun-gaba-salon-san-ni-ji-ni-gane-ni-ne-wane/
Zatin Basarake
Sarki shugaba ne da ya kamata ya zama mai kwarjini da cika fuska da matsakaicin tsawo da isasshen lafiya domin zarce tsara da abokan hamayya. Alhaji Sani Aliyu ‘Dandawo yakan yawaita fito da wannan jigo na zati da kamalan basaraken da yake wak’ewa domin d’aga darajarsa da kwarjininsa a idon talakawa da takwarorinsa na sauran k’asashen Hausa. A wak’ar da ya yi wa marigayi sarkin Yauri Shu’aibu ya siffanta zatinsa da ingarman doki, wanda aka sani cewa doki ne da ya zarce tsaransa lafiya da k’oshi da kwarjini da cika ido. Ga dai abin da mawak’in ke cewa:
Jagora: ‘Dan Yakubu dogon sarki
: Ingarma mai kyawon kallo
Yara: Da ganin ka Tukur ya dawo
G.W: Shu’aibu mad’auki hwansa
: Yakubu nuhinai ya kai
: Mai Yauri sabon sarki
Haka ma mawak’in ya kawo wannan jigo a wak’arsa ta sarkin Sudan na Kwantagora inda yake bayyana irin zati da kamalar shigarsa har jama’a suna ta kallonsa. Ga bayanin kai tsaye daga bakin mawak’in:
Jagora: Mai kallo shi taho ga giwan nan
Yara : Da gare ka babu sauran kallo
: In ka wuce na Madawaki
Jagora: Ga shugaban k’asa ga gwauna
: Kai kowanensu ke ta kallo
: Yau sun ga d’aukakak sadauki
G.W : Sarkin sarakuna Namaska
: Mai martaba na Madawaki
: Giwa buwayi masu ja ma
Dauwaman Basarake
Babu wani sarki da ke son a tsige shi daga karagar mulki ko ya yi shekaru k’alilan ya kwanta dama. Babban burin kowane basarake ko mai mulki shi ne ya yi tsawon rayuwa bisa mulki, daga k’arshe ya mutu a gadon sarauta. Fatarsu a koyaushe ita ce dauwama bisa mulki. A kan haka ne mawak’an sarakuna sukan rik’a yi wa sarakunan da suke wak’ewa fata ko addu’ar d’aukan shekaru masu tsawo a karagar mulki kafin daga bisani mutuwa ta kawo musu ziyara. A wani lokaci ma mawak’an sukan kawar wa sarakunan da mutuwa kamar babu ita domin d’orewar mulkinsu har zuwa bayyanar Mahadi. Bari mu ga yadda Sani Aliyu ‘Dandawo yake yi wa marigayi sarkin Yauri Sha’aibu fatar dad’ewa ko dauwama bisa mulki.
Jagora : Ku ‘yan sarki na yi mahwalki
: An ce min sarkin nan
: Wada yay yi tsawo yam mik’e
: Sai yai dogayen shekaru
Yara : Shi kwashe tamanin shi d’ai
: Ya bak ku kuna kallonai
: Koz zaka yai tsaye bakin garka
Mawak’in ya ci gaba da cewa basaraken ya ci gaba da mulki har zuwa bayyanar Mahadi. Ga abin da yake cewa:
Jagora : Ka zama sarki ka ba su haushi
: Na yanzu kak ka ji tsoron giwa
Yara : Rik’a bahago sai Madi
: Mai Yauri sabon sarki
G.W : Sha’aibu mad’auki hwansa
: Yakubu nuhinai ya kai
: Mai Yauri sabon sarki
Har wa yau, a wata wak’a da Sani Aliyu ‘Dandawo ya yi wa sarkin Minna Alhaji Umar Faruku ya fito da wannan jigo na dauwamar sarki bisa mulki har zuwa bayyanar Mahadi, yana mai cewa:
Jagora: Allah jik’an Amadu Bak’o
: Kai kuma Ummar Allah
: Shi rik’a ma ka ga Madi
Yara : Kowa na ta du’a’i
: Ka dad’e kuma ka yi k’ark’o
G.W : Minna zan shek’e ayata
: In ga Hwaruku sadauki
: Ummaru ja a sakam ma
Har wa yau, mawak’in ya jaddada wannan jigo ga marigayin sarkin Yauri Sha’aibu yana cewa:
Jagora : Allah shi ja zamanin sarki
: Saboda Annabin Allah
Yara : Kai kyawon k’ark’o sarki
: Kana gidan ga koyaushe
G.W : Sha’aibu dangalin dangi
: Mak’i gudu uban Audu
Jaruntakar Basarake
Ba a sarki rago ko matspraci ko mai sanyin jiki. An fi son sarki ya kasance jarumi mai ban tsoro wanda duk inda ya sa gaba tilas a ja da baya. A zamanin da ya gabata, k’asar Hausa k’asa ce da ake za’ben sarki ta la’akari da jaruntakarsa kasancewar yawaitar yak’e-yak’e a kowane lokaci. A dalilin wannan za’ben jarumi ya shugabanci jama’a, mawad’an sarauta suke amfani da wannan dama suke yawan bayyana wannan jigo ga basarken da suke yi wa wak’a domin tabbatar da shi bisa turban magabatansa. Sani Aliyu ‘Dandawo a wak’ar da ya yi wa marigayi sarkin Yauri Sha’aibu Yakubu Abarshi inda ya tabbatar da wannan jigo ga basaraken na fatattakar arna ko abokan gaba har ma babu mai iya taronsa saboda jaruntakarsa, yana cewa:
Jagora: Sha’aibu kan kada mai k’wari
: Zakaran yak’i na Amadu
: Hwalalen dutci uban Kabir
: Ka hwar ma mutum shi kakkare
: In yah hwar ma shi rikkice
: Tsawa kake mai wuyat taro
Yara : Goga mai shan kwaram kake
: A gani a tare ka wa mutum
G.W : Sarkin nasara Abarshi ne
: ‘Dan Yakubu mai tawakkali
A wata wak’a da ‘Dandawo ya yi wa Madawakin Yauri ya nuna irin jaruntakar basaraken na tunkarar abokan gaba ba tare da wata fargaba ko shakka ba, da kuma nuna cewa gadon jaruntaka ya yi har ma ya gadi mashin da mahaifinsa ya yi yak’i da shi.
Jagora: Ina mashin da kay yi gado
: Gun Madawaki
Yara : ‘Dauko garkuwakka
: ‘Dauko mashinka Audu
: Ga arna can tare su
G.W : Mu zo mu ga Madawaki
: Bai d’au wargi ba Audu
Bugu da k’ari, ‘Dandawo ya kawo makamancin wannan jigo a wak’ar da ya yi wa Sarkin Sudan Sa’idu Namaska inda yake jinjina wa sbasaraken cewa sadauki ne kuma d’an sadauki, wato shi ma gadon jarunta ya yi a wajen mahaifinsa, don haka duk mai ja masa yana cikin tashin hankali, yana cewa:
Jagora: Sa’idu sadauki d’an sadauki
Yara : Ka zama gaggak’i wandon k’arhe
: Kos sa ka bai shirin zama ba
G.W : Sarkin sarakuna Namaska
: Mai martaba na Madawaki
: Giwa buwayi masu ja ma
https://www.amsoshi.com/2017/10/01/yadda-ake-yin-kayan-ki%c9%97a-na-girgizawa/
Iya Mulki
A duk inda jagoran jama’a yake akan so ya kasance k’wararre mai hangen nesa da sanin ya kamata da jawo talakawa da ma ‘yan adawa a jiki domin kyautata mulkinsa. A kan haka ake son basarake ya zama k’wararre wajen iya tafiyar da mulki, wato ya zama hannu ya iya jiki ya saba ta yadda su da kansu wad’anda ake mulka su san suna da sarki managarci. A dalilin haka mawak’an sarakuna irin su Sani ‘Dandawo yakan yawaita bayyana irin iya mulkin wani basarake na jagorancin jama’arsa bisa turba madaidaiciya, wanda su da kansu talakawan sukan yaba a kan iya mulkin basaraken. Sani Aliyu ‘Dandawo ya fito da irin wannan jigo a wak’ar da ya yi wa sarkin Minna Alhaji Umar Faruk inda ya nuna gamsuwar da talakawansa suke nunawa na irin rawar da basaraken ke takawa na iya mulki, yana cewa:
Jagora: Gwarin Boso Gwatin Minna
: Kai hag Gwarin Paiko
Yara : Dus sun yadda da mulkinka
: Umar Sanda sadauki
G.W : Minna zan shek’e ayata
: In ga Hwaruku sadauki
: Umaru ja a sakam ma
Haka ma wak’ar Adamu Bello ‘Dan’iyan Adamawa Sani Aliyu ‘Dandawo yana cewa ‘Dan’iyan Adamawan ruwan zafi ne ba ka da gefe a wajen iya mulki a gida ko daji, yana cewa:
Jagora: ‘Dan’iyan Adamawa Adamu
Yara : ‘Dan’iyan da ya’ iya mulki
: Na Garba ko dawa ko binni
G.W : Adamu Bello ya d’au girma
: Ya zama ‘Dan’iyan Adamawa
: Allah shi rik’a ma kullum
Alherin Basarake
Hausawa na cewa, “Alheri dank’o ne ba ya fad’uwa k’asa banza”. A al’adar rayuwa, idan mutum ya kasance mai son alheri za ka iske ya samu farin jini da d’aukaka da k’auna ga jama’a. Haka ma idan mutum ya kasance mai kishiyan alheri wato mai rik’e hannu za ka iske jama’a na gudunsa babu mai na’am da shi. A wani lokaci ma za ka iske ko wani abin bak’in ciki ya same shi jama’a ba su tausaya masa. A kan haka mawak’an sarakuna sukan rik’a bayyana halayyan basaraken da suke wak’ewa da son alheri ga talakawansa. A wak’ar da Sani ‘Dandawo ya yi wa sarkin Sudan na Kwantagora Alhaji Sa’idu Namaska yana bayyana irin alherinsa ga jama’a yana cewa:
Jagora : Sarki mai kwana alheri
: Mai bin ka ba shi kukan riga
Yara : Mai bin ka ba shi kukan dawa
: Bai san ana rashin kud’i ba
G.W : Sarkin sarakuna Namaska
: Mai martaba na Madawaki
: Giwa buwayi masu ja ma
Mawak’in ya k’ara fito da wannan jigo na alheri a wak’arsa ta marigayi sarkin Yauri Sha’aibu Yakubu inda yake bayyana irin alherin da basaraken ya yi masa a lokacin da suka had’u a k’asa mai tsarki (Makka) da kuma wanda ya yi wa iyalansa da ya bari gida a lokacin sallar layya, yana cewa:
Jagora : Bana na je Makka wurin sallah
: Mai girma sarki ya je
: A Makka yai man alheri
: Na dawo a nan gida Sani
: Na ishe mata na murna
: Ragon da baba yab ba ni
Yara : Duw wanda yay yi layya a Yauri
: Ragonsa bai kaman nau ba
: K’iba da mai da dad’in ci
G.W : Sha’aibu dangalin dangi
: Mak’i gudu uban Audu
Haka ma a wak’ar da ya yi wa Turakin Zazzau yana bayyana alherinsa ga dukkan musulmin Allah matuk’ar dai ya kai kukansa a wajen basaraken, yana cewa:
Jagora : Turaki mai taimakon musulmin Allah
Yara : Duw wanda yat taho
: Turaki yana taimakonsa in ya gan shi
G.W : Ni za ni in gano Turaki
: Aminu wan maza na sarkin Zazzau
Mallakar K’asar Sarauta
A tsarin sarautun k’asar Hausa, kowane basarake yana da iyakan k’asar da yake mulka ko yake iko. Don haka, duk wani abu da ke cikin wannan yanki yana k’ark’ashin ikon wannan basarake ne, sai abin da ya ce a yi ko a bari, babu mai d’aga masa hannu komai arzikinsa bale marashi. Saboda haka, mawak’an sarakuna ke k’ara tabbatar da wannan matsayi ga basarake domin k’ara cicci’ba shi a saman magauta. Ga abin da Alhaji Sani Aliyu ‘Dandawo ke cewa a kan sarkin Yauri marigayi Sha’aibu:
Jagora : Kai ad da k’asag ga tun hwarko
: Kai ad da k’asag ga ko gobe
: Sarauta tana wurin Allah
: Sarauta tana wurin sarki
: Yau babu zarumi sai kai
: Sha’aibu k’anin Abdullahi
Yara : Du’ abin da kash shirya
: K’asag ga ba a tashe shi
G.W : Sha’aibu dangalin dangi
: Mak’i gudu uban Audu
A wak’ar da ya yi wa sarkin Nasarawa Labaran ya fito da wannan jigo inda yake cewa:
Jagora : Ka zama sarki ka hwashe haushi
Yara : Nasarawa ko can taka ce
G.W : An yi sabon sarki jarumi
: Labaran bajini d’an Bubakar
Ilimin Basarake
Hausawa na cewa “Ilimi hasken rayuwa”. Hak’ik’a duk wani abu da ake na ci gaba tilas sai tare da ilimi. Saboda haka, duk inda jagora yake kamata ya yi ya zama mai ilimi na addini da na zamani domin yi wa mulkinsa adalci. Mawak’an sarauta sukan rik’a bayyana zurfin ilimin basaraken da suke wak’ewa domin nuna kamalar jagorancinsa ga jama’a. Sani Aliyu ‘Dandawo a wak’ar da ya yi wa sarkin Zazzau ya tabbatar da zurfin iliminsa na addini da ma na zamani wanda hakan ya yi masa jagoranci wajen gyara k’asarsa, yana cewa:
Jagora : Na ji mutane na godiya ga kurman giwa
: Ga ilimin Arabiyya ga ilimin zamani
Yara : Cikin nuha’ Allah ya gyara k’asa tai haske
G.W : Bi da arna jikan Sambo sadaukin sarki
: Tura haushi saduki Alhaji sarkin Zazzau
Haka ma a wak’arsa ta marigayi sarkin Gombe Shehu Abubakar ya fito da makamancin wannan jigo yana cewa:
Jagora : Ya samu digiri wurin boko
Yara : Sannan wurin ilimin Arbik
: Ko waz zaka yana karantassai
G.W : Mu zo Gombe in gano sarki
: Shehu sauran mazan hwarko
Cikakken Iko/Mulki
Tun fil azal, sarakunan k’asar Hausa mutane ne masu k’arfin iko da fad’a a ji. Babu wani tajiri ko talaka da zai d’aga wa basarake hannu face an yi awon gaba da shi, kowa yana k’ark’ashin ikonsa ne. Sani Aliyu ‘Dandawo yakan ambaci wannan jigo a wak’ok’insa na sarauta domin tauna tsakuwa aya ta ji tsoro musamman ga magautansa. Ga abin da yake cewa a kasance maiwak’ar da ya yi wa marigayi sarkin Yauri Sha’aibu dangane da wannan jigo:
Jagora : Baba talakkan ga naka ya canza
: Bai jin maganam manya
Yara : Yi mai zama guda sarki
: Yana sanin akwai mulki
G.W : Sha’aibu dangalin dangi
: Mak’i gudu uban Audu
Haka zalika a wak’arsa ta sarkin Zazzau yana bayyana cikakken ikon basaraken yana cewa:
Jagora : Kai ake shakka, yau kak ka ji saunak kowa
Yara : Abin da duk kac ce shi za a yi sai dai Madi
G.W : Bi da arna jikan Sambo sadukin sarki
: Tura haushi saduki Alhaji sarkin Zazzau
Kammalawa
Basarake a k’asar Hausa mutum ne da ake girmamawa musamman idan ya kasance mai adalci da kyautatawa ga talakawansa. Wannan ne ya sa al’ada ta tanadar musu da mawak’a na musamman da ba su yi wa kowa wak’a sai su kawai, sai dai kuwa idan sun sami izinin uban gidansu. Saboda haka, idan wad’annan mawak’a sun zo wak’e basarake sukan yi amfani da wasu kalamai na kwarzantawa da kyautatawa domin nuna fifikon da suke da shi ko d’aukakar da Allah ya ba su a cikin al’umma. Wannan ne ya sa mawak’an suke bayyana cikakkiyar halittar da Allah ya yi musu da kuma kyawawan halayyarsa da kwarjininsu da iliminsu da zarce tsara da buwayar magauta da fad’a a ji da makamantansu da dama kamar dai yadda bayanai da misalai suka gabata.
MANAZARTA
Abba, A. da Zulyadaini, B. (2000) Nazari Kan Wak’ar Baka ta Hausa. Published by
Gaskiya Corporation Limited, Zaria.
Bunza, A.M. (2009) Narambad’a. Ibrash Islamic Publications Centre Limited, Lagos.
Gusau, S.M. (1996) Jagorar nazarin wak’ar baka. Fisbas Media Services Kaduna.
Gusau, S.M. (2003) Jigon nazarin wak’ar baka. Benchmark Publishers Kaduna.
Gusau, S.M. (2005) Makad’a da Mawak’an Hausa. Benchmark Publishers Limited, Kano.
Gusau, S.M. (2008) Wak’ok’in Baka a K’asar Hausa: Yanaye-Yanyensu da Sigoginsu.
Benchmark Publishers Limited, Kano.
Gusau, S.M. (2009) Diwanin Wak’ok’in Baka: Za’ba’b’bun Matanoni na Wak’ok’in Baka na
Hausa. Century Research and Publishing Limited, Kano.
Yahya, A.B. (1997 ) Jigon Nazarin Wak’a. Fisbas Media Service, Kaduna.
1 Comments
[…] Basarake A Wak’ok’in Sani Aliyu ‘Dandawo […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.