Ticker

6/recent/ticker-posts

Yunk’urin Samar Da Zaman Lafiya Da Sasantawa: Bincike Kan Wakar Zaman Lafiya Ta Bashir Musa Liman

NA

Musa Shehu

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya

Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato

msyauri@yahoo.com

07031319454

DA

Rabi’u Aliyu Rambo

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya

Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato

dirindaji12aa@gmail.com

08140736435

TSAKURE


Masu iya magana na cewa, “zaman lafiya ya fi zama d’an sarki”. Yunk’urin da ake ta famar yi na ganin zaman lafiya ya samu inuwar hutawa a k’asar Hausa da ma Nijeriya baki d’aya bai bar sha’iran Hausa a bayan fage ba. Akwai rubutattun wak’ok’in Hausa da dama da wasu sha’irai suka rubuta domin ba da tasu gudunmuwa ga samar da zaman lafiya da sasantawa. Manufar wannan takarda dai shi ne fed’e wak’ar zaman lafiya ta Bashir Musa Liman domin fito da hikimomi ko falsafar da ke cikin wak’ar, wanda suka had’a da bayanin amfanin zaman lafiya, hanyoyin samar da zaman lafiya, dalilan da ke haddasa rashin zaman lafiya, da illolin rashin zaman lafiya da sauransu.

 

https://www.amsoshi.com/2017/10/16/hyperbole-peak-stylistic-adornment-hausa-oral-songs/

 

1.0    Gabatarwa


‘Dangambo (1981) yana vewa, “wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti, d’ango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (k’afiya), da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba”. Shi kuwa Gid’ad’awa cewa ya yi: “wak’a dai magana ce tsararriya wadda ake shiryawa a bisa wasu muryoyi na musamman, wadda kuma ta bambanta da maganar yau da kullum”. Tsara wak’a baiwa ce ta Ubangiji sai wanda Allah ya hore wa ita zai iya. Hausawa sun fara rubuta wak’a ne ta dalilin isar da sak’on Allah, wato domin yin wa’azi ga jama’a domin su koma tafarkin Allah makad’aici. Ladan (1975) ya bayyana cewa, marubucin wak’ok’in Hausa yana nazarin abin da aka fi shagalta da shi, idan na zarafin duniya ne, ya fad’i ra’ayinsa a kansa, idan kuma na addini ne ya yi wa mutane wa’azi. Misali, a cikin k’arni na 18 da na 19 lokacin da aka himmatu kan jaddada addini, wak’ok’in Hausa na wannan zamani da yawa sun k’unshi wa’azi ne. A wajen tsakiyar k’arni na 20 kuwa, lokacin da aka shagalta da yak’in duniya na biyu, da ilimin zamani da siyasa da tafiye-tafiye zuwa k’asashen Turai, an sami hazik’an marubuta wak’ok’i da suka wak’e wad’annan al’amurra, kamar Malam Sa’adu Zungur wanda ya rubuta wak’ar “Jihadin neman sawaba” da wak’ar (Arewa Jamhuriyya ko Mulukiyya” da Malam Mu’azu Had’eja wanda shi ma ya rubuta wak’ar “Tutocin Shehu da waninsu” da wak’ar “Ilimin Zamani” da Alhaji Mudin Sipikin wanda ya rubuta wak’ar “Gadar zare” wak’ar “Rasha abokan fita kunya” da makamantansu.

To sai dai kuma, wannan zamani na k’arni 21 ya zo ne da rikice-rikice da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na k’asar Hausa da ma Nijeriya baki d’aya. Zaman lafiya ya kasa samun gindin zama, don haka aka sami wasu marubuta wak’ok’in Hausa da suka had’a da Aliyu Muhammad Bunza da Bashir Musa Liman da Malam Sambo Wali da Dr. Aliyu Tilde da sauransu da dama wad’anda duk sun rubuta wak’ok’in zaman lafiya, da suka shafi alfanun zaman lafiya, da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, da hanyoyin kariya daga aukuwar rikici, da illolin da ke tattare da rashin zaman lafiya, da makamantansu. Wad’annan abubuwa ne wannan takarda za ta mayar da hankali wajen  nazarinsu daga wak’ar “Zaman Lafiya” ta Bashir Musa Liman.

2.0   Ma’anar Zaman Lafiya


Bunza (2015) cewa ya yi, “Zaman lafiya a Bahaushen tunani shi ne, zama cikin natsuwa, da sakewa da rashin fargaba da tashin-tashina ta kowace fuska. Zama ne da ba ka cuta ba, ba a cuce ka ba. Zama ne na aminci ga k’asa da wad’anda ke cikinta, da wad’anda za su ziyarce ta, da wad’anda za su fice daga cikinta, da wad’anda ke mak’wabtaka da ita. Zama ne da zai bai wa duk wanda ke cikin k’asa d’an asalinta, da bak’inta na arziki, da ‘yan gudun hijirarta, da masu zaman mafakar siyasa a ciki, natsuwa da kuranye firgita a zukatansu. Zaman lafiya zama ne na d’ebe d’ammaha ga duk wata hayagaga da ru’bushi da ta da zaune tsaye da wata halitta za ta haddasa ga wanda ke cikinta, face abubuwan da babu makawa aka k’addaro gare ta daga mai k’addarawa (Allah)”.

3.0   Ma’anar Sasantawa


Sasantawa (Conflict Resolution) wani al’amari ne mai muhimmancin gaske a rayuwar kowace al’umma. A duk lokacin da wasu rikice-rikice ko yak’e-yak’e ko tashin-tashina suka wanzu a tsakanin al’umma, hanya mafi dacewa da ya kamata a yi amfani da ita domin warware su cikin ruwan sanyi da kuma dawo da zaman lafiya mai d’orewa ita ce hanyar sasantawa ko yin sulhu a tsakanin masu husuma. K’amusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar sasantawa da shiga tsakanin masu husuma biyu, ko kuma sulhu. A cikin K’amusun Oxford (seventh edition) an kawo ma’anar sasantawa da cewa, yanayi ne na warware ko daidaita matsala, ko jayayya, da sauransu.

4.0   Musabbabin Rikice-Rikice


Sani (2007) ya bayyana cewa, akwai abubuwa da dama da ke haddasa rikicin addini ko k’abilanci ko siyasa ko na makiyaya da manoma ko na sarauta, da ma kowane nau’i na rikici. Abubuwan kuwa sun had’a da rashin aikin yi da talauci da zamantakewa wuri d’aya tsakanin ‘yan k’asa da bak’i, da wajen rarraba muk’aman gwamnati da kuma iyakokin gona. Misali, rikicin addini da na k’abilanci sun sha faruwa a Kano tsakanin Hausawa da sauran k’abilu mazauna Kano musamman k’abilar Igbo. A jihar Zamfara ma ana ci gaba da samun rikicin manoma da makiyaya. A fagen sarauta, an samu rikici a Kano lokacin da aka nad’a sabon sarkin Kano Sanusi Lamid’o, inda aka rik’a k’one-k’one a cikin gari. Don haka ana iya cewa, abubuwan da ke haddasa rikice-rikice a k’asar Hausa da ma Nijeriya sun had’a da addini da k’abilanci da siyasa da talauci da rashin aiki da rashin ilimi da mulkin danniya da rashin hak’uri da makamantansu.

4.1   Addini

Kamar yadda Anugwon (2002) ya bayyana, addini na daga cikin manyan abubuwan da ake amfani da su wajen haifar da fitina tsakanin addinin Musulunci da Kiristanci, kowa na ganin shi ke bisa tudun mun tsira, kamar yadda wani masani ke cewa: “Musulmai sun yi imani da mallakar duniya a k’ark’ashin tutar Islama ta hanyar k’addamar da jihadi. Su kuma Kirista suna da yak’inin ba wanda zai sami rahama ko Aljanna sai ta hanyar koyarwar Yesu Almasihu”. Irin wannan tunani  ya yi tasiri ainun tsakanin Musulmi da Kiristan k’asar Hausa ake zaman doya da manja kamar Annabi da kafiri. Wannan ya sa duk lokacin da wata ‘yar matsala ta faru tsakanin wani Musulmi da Kirista nan take sai a juya matsalar ta koma addini, daga nan sai fitina ta kaure. Lamarin ya kai a wasu lokuta idan ana rikici sai jami’an tsaro su rik’a taimaka wa Kirista domin su samu galabar Musulmi. Bashir Musa Liman kira ya yi a wak’arsa ta zaman lafiya a baiti na 7 yana nuna illolin rikicin addini yana cewa:

Baiti na 7        A Arewacin k’asat har da Maiduguri

Ana ta rikici na addini babu tsari

Rayuka da dukiya sun ‘bata ba ik’irari

Wanda hakan ya haifar da k’iyayya

 

4.2   K’abilanci

K’asar Hausa k’asa ce mai fad’in murabba’in kilomita dubu d’ari biyar da shida, da yawan jama’a k’imanin miliyan sittin da tara a k’ididdigar shekarar 2006. Kuma k’asa ce da bak’i ke yawan kwararowa  ciki domin cin gajiyar tattalin arzikin da Allah ya zuba a cikin k’asar. Wannan ya sa ake samun k’abilu masu yawa suna rayuwa a cikin k’asar. Hausawa na cewa: “Zo mu zauna zo mu sa’ba”. A al’adar zamantakewa, duk inda aka zauna tare dole a sami sa’bani nan da can. Saboda haka rikicin k’abilanci ya sami gindin zama a k’asar Hausa, yau tsakanin Hausawa da Igbo, gobe tsakanin Hausawa da Yarbawa, jibi tsakanin Hausawa da k’abilun jihar Filato ko Taraba ko Nasarawa, ga su nan dai. Albert (1999) yana cewa, da zaran wata matsala da ba ta taka kara ta karya ba ta faru tsakanin wannan k’abila da waccan, sai a yi ta k’ok’arin rura rikicin har sai ya koma rikicin k’abilanci. Wannan ya faru a shekarar 1995 a Kano inda fad’a ya ‘barke tsakanin wani d’an k’abilar Igbo da wani Bahaushe, daga bisani aka rura rikicin har ya koma na k’abilanci aka rasa rayuka har 25. Bashir Musa Liman a wak’arsa ta zaman lafiya a baiti na 31, ya nuna k’abilanci na daga cikin abubuwan da ke haddasa fitina, don haka ya yi kira da a kauce masa domin a samu zaman lafiya a cikin k’asa, yana cewa:

Baiti na 31   Idan muna so mu zan walawa

‘Bangaranci ya zamto mun wullarwa

Yarenci da k’abilanci mu zan kaucewa

Hakan zai sa a yi daddad’ar dariya

 

 

4.3  Siyasa

Turawa sun kawo siyasa ne a Nijeriya wai don a ba kowa ‘yancinsa na za’ben shugaba wanda zai kyautata wa al’umma. To sai dai lamarin ya zama akasin haka a k’asar Hausa, domin siyasa a yau ta haddasa rikice-rikice masu munin gaske a rayuwar Hausawa. Sau da yawa za ka iske ba a ko ga-maciji tsakanin magoya bayan wannan jam’iyya da magoya bayan waccan jam’iyya. Ko ka iske ana sa-in-sa tsakanin ‘yan’uwa ko abokai, wani lokaci ma har a kai ga tashe-tashen hankula da rasa rayuka. Haka ma, siyasa ta haddasa wanzuwar k’ungiyoyin ‘yan daba wad’anda ba su da aiki sai ta’addanci a tsakaninsu da kuma sauran jama’a. A duk lokacin da aka ce siyasa ta kunno kai hankulan mutane kan tashi saboda fargabar abin da ka iya kai ya kawo na fitintinu. Idan kuma an k’are za’be, nan ma ba a rabu da Bukar ba, domin nan ne ma aka fi samun rikici a lokacin da aka yi sanarwar wanda ya sami nasara. A nan ma, Bashir Musa Liman a baituka na 10 da na 25, ya yi kira ga ‘yan siyasa su guji tayar da zaune tsaye yayin da suka ci za’be ko suka fad’i, yana mai cewa:

Baiti na 10   ‘Yan siyasa suna alkawartawa

Idan sun ci za’be za ai morewa

Suna ci sai su zam ‘bacewa

Hakan ma na jawo hatsaniya

 

Baiti na 25   ‘Yan siyasa su san cewa

A za’be akwai ci da fad’uwa

In sun fad’i su zam hak’urewa

Hakan zai haifar da zaman lafiya

 

4.4   Cin Hanci da Rashawa

Cin hanci da rashawa babbar musiba ce a cikin al’umma. duk al’ummar da cin hanci ya yi mata katutu tilas rikice-rikice su addabe ta. Idan aka dubi yadda rayuwa ke tafiya a k’asar Hausa da Nijeriya baki d’aya, tilas zaman lafiya ya kasa samun gindin zama. A wajen shari’a,  mai abin hannunsa shi ne mai gaskiya. A wajen d’aukar ma’aikata sai kana da dogon k’afa ko saya a sayar maka. Samun wani muk’ami sai ana d’asawa da kai. Wad’annan abubuwa a zahiri suke aukuwa a Nijeriya. Alal misali, wasu abokai biyu suka samu matsala, sai d’aya ya garzaya wurin ‘yan sanda ya ba da kud’i ya ce da abokin nasa ya zo bai son a yi wata magana sai an rufe shi. haka kuwa aka yi, abokin na zuwa aka hana shi magana aka k’argame shi, da k’yar muka yo belinsa. A fagen neman aiki kuwa, akwai wani d’alibinmu da ke fad’a mini cewa, babansa ya matsa masa da ya hanzarta ya kammala karatunsa saboda an yi wa baban alkawalin aiki ga d’an nasa da zarar ya kawo satifiket. Su kuwa shugabanni da aka ba amanar dukiyar jama’a sai wawarewa suke yi suna sawa a aljihunsu. Wannan ma a zahiri yake musamman idan aka yi la’akari da yadda hukumar yak’i da yi wa tattalin arzikin k’asa ta’annuti suke ta faman zak’ulo irin wad’annan mutane. Irin wannan yanayi da muke ciki ya taimaka wurin aukuwar rikice-rikice da ke addabar k’asarmu a yau.

4.5  Mulkin Danniya

Irin mulkin danniya da kama-karya da ke gudana a Nijeriya ya taimaka wajen rura wutar rikicin da ake fama da shi a yau. Allah ya albarkaci Nijeriya da albarkatun k’asa da na ruwa irin su zinari da azurfa da kwal da gur’bataccen mai da sauransu wanda ya kamata a ce kowane d’an k’asa na morewa gwargwadon hali, amma sai aka sami akasin haka. Talaka ya kasa samun wutar lantarki da ruwan sha da magani da ingantaccen ilimi, balle kayan more rayuwa kamar abinci mai kyau da motar alfarma da gida mai nagarta, sai dai ya sa na mujiya ya yi kallo ga dangi. Ga rashin aikin yi da hanyoyi marasa kyau, sai had’urra kawai ake yi rayuka na salwanta. Don haka, tilas k’ungiyoyin ta’addanci su wanzu, ‘yan fashi da makami su yawaita, masu fasa bututun mai su ci gaba da gashi, ‘yan k’unar bak’in wake su kama ta da bamabamai, ga su nan dai. Bashir Musa Liman ya yi kira ga masu mulki da su guji mulkin danniya wanda ke haddasa fitina a cikin al’ummarsu a baituka na 12 da 10, yana cewa:

Baiti na 12   Masu mulki suna shek’a mulki

Wanda ya sa wasu ke take hak’k’i

Almundahana, danniya da zulak’i

Wanda ta sa talaka yin gogayya

 

Baiti na 10  Masu iko sun yi k’i-mudu-gus

Wajen bai wa talaka hatsin gus-gus

Su kuwa suna ta tauna gurus-gus

Hakan ya haifar da zaman k’iyayya

 

4.6  Talauci

Duk lokacin da talauci ya addabi mutane, a koyaushe hasale suke, abu kad’an sai ya tunzura su. Don haka, da zarar an sa’ba musu ko a bisa kuskure ne sai su ga izgili ne don ba su da komai, daga nan sai rikici ya kaure. A cewar Shehu Sani (Sanata mai wakiltar Kaduna), talauci na iya sa wasu fad’awa cikin ayyukan ta’addanci da ganin k’yashi da haddasa fitina mai munin gaske. Irin talaucin da mutanen k’asar nan ke ciki da wasu ‘yan tsirarun mutane suka haddasa na wawure dukiyar k’asa suna shek’e ayarsu sun bar mutane cikin k’unci, babu yadda zaman lafiya zai hango inuwa balle ya shiga ya huta. A shekarar 2015 gidan rediyon BBC Hausa ya kawo tattaunawar da aka yi da wasu ‘yan Boko Haram da aka kama ana bincikensu dalilinsu na shiga k’ungiyar. Sai d’aya daga cikinsu ya ce, talauci ne ya addabe shi sai aka rud’e shi da dubu talatin don kai hari a Masallacin shugaban k’ungiyar Izala, malam Sani Yahaya Jingir. Wannan ya nuna talauci musiba ce da ke tayar da zaune tsaye. Bashir Musa Liman ya k’arfafa wannan ik’irari a batiti na 18  na cewa talauci yana haddasa fitina a cikin k’asa:

Baiti na 18   Talauci ya sanya fashi da makami

Kana gida ka ga ‘barayi da makami

A kan hanyar tafiya ma da makami

Ka bayar da kud’i ka zauna lafiya

 

4.7  Rashin Aiki

Rashin aiki fitina ce ga kowace al’umma, wanda a yau ya zama ruwan dare a k’asar Hausa da Nijeriya baki d’aya. Akwai matasa masu tarin yawa da suka k’are karatu a matakai daban-daban amma babu abin yi. A bayanin da Shehu Sani (Sanata mai wakiltar Kaduna), ya yi a gaban Majalisa a ranar 10 ga watan Nuwamban 2015, aikin gwamnati ko na kamfani ya koma wa ka sani, wa ya san ka, idan ba ka da kowa sai dai ka yi ta yawon jarabawar neman aiki kana cika taro, bayan an rigaya an d’auki na d’auka. Daga nan ne idan zama ya yi zama sai wasu su fara tunanin kama mugunyar sana’a ta fashi da makami ko sufurin miyagun k’wayoyi da sauran ayyukan assha da ke haddasa fitintinu a cikin al’umma. Wannan matsala ta sa wasu da dama shiga k’ungiyar Boko Haram. Gidan Rediyon BBC Hausa ya kawo zantawar da aka yi da wasu ‘yan Boko Haram da aka kama a Gombe ind d’ayansu ya ce rashin aiki ne ya sa su fad’awa cikin k’ungiyar, sai aka ba shi dubu tamanin don ya kai wannan hari. Wannan ya nuna musibar da rashin aikin ke haifarwa a cikin al’umma. Bashir Musa Liman ya ankarar da mutane a kan wannan matsala ta rashin aikin yi wanda a lokuta da dama ke haddasa fitina a baiti na 19 yana cewa:

Baiti na 19   Matasa ba aikin yi sai zaga gari

Ba su da ko sule balle zancen d’ari

Hakan kuwa ya sa su cikin garari

Wanda ya sa suke ta hatsaniya

 

4.8  Rashin Ilimi

Rashin ilimi yana jawo fitina a cikin al’umma. Da zaran akwai jahilci ko k’arancin ilimi ga al’umma, koyaushe fitina na iya ‘barkewa domin ilimi shi ke sa mutane su rik’a tunanin abubuwan da za su yi don ci gaban rayuwarsu da al’ummarsu baki d’aya. A halin da ake ciki a k’asar nan, ilimi na k’ok’arin buwayar talaka, saboda an kusa a kashe makarantun gwamnati baki d’aya sai makarantun kud’i wad’anda talaka bai iya karatu a cikin su. Idan ba a d’auki matakin gyara ba, wannan na iya haddasa wata fitinar da ba a yi tsammani ba. Sai dai gwamnatin da ta gabata na PDP ta yi k’ok’arin bud’e Jami’a a kowace jiha don gyara harkar  ilimi, amma har yanzu ba ta sauya zane ba. Bashir Musa Liman a baiti na 37 yana cewa:

Baiti na 37   A yi ilmin addini da na kimiyya

Kuma a k’asa idan aka samu tarbiyya

Mu lura k’asa za ta zauna lafiya

Da rayuwa ba kwan gaba kwan baya

 

4.9  ‘Bangaranci

Kyawon al’umma su had’a kai su zama tsintsiya mad’aurinki d’aya, babu nuna bambancin addini balle na k’abilanci ko ‘bangaranci. Wannan shi zai jawo musu zama lafiya da kwanciyar hankali. Rikice-rikicen da ake fama da shi a Naija Delta rikici ne na ‘bangaranci, suna nuna su ke da arzikin k’asa domin a ‘bangarensu yake, don haka ba wanda zai ci gajiyarsa sai ‘yan ‘bangarensu. Sun manta cewa, da arzikin wani ‘bangare na k’asar (Arewa) aka yi amfani aka samar da arzikin da suke ik’irarin nasu ne. Wannan ya sa ake ta fama da rikici tsakaninsu da gwamnatin Nijeriya har lokacin marigayi shugaban k’asa ‘Yar’adua wanda ya yi k’ok’arin sasanta lamarin har ya kai ga yin afuwa gare su domin dai k’asa ta zauna lafiya. A baiti na 31, Bashir Musa Liman yana cewa:

Baiti na 31   Idan muna so mu zan walawa

‘Bangaranci ya zamto mun wullarwa

Yarenci da k’abilanci mu zan kaucewa

Hakan zai sa a yi daddad’ar dariya

 

4.10  Rashin Hak’uri

Hausawa na cewa: “Hak’uri maganin zaman duniya”. A tunanin Hausawa, hak’uri shi ne sinadarin kawar da duk wata matsala da ka iya tasowa a rayuwa. Rashin hak’uri kuwa yana iya haddasa fitina da da-na-sani. Idan aka yi la’akari da wasu rikice-rikicen aure da ke faruwa a k’asar Hausa za a ga rashin hak’uri ke haifar da su. Ba ma rikicin aure kawai ba, galibin rikice-rikicen da ke faruwa a rayuwar al’umma rashin hak’uri na taimakawa wajen ruruwarsu.     Sauran musabbabin rikice-rikice sun had’a da hassada da gaba da k’iyayya da butulci da zalunci da cin amana da  rashin cika alkawali da rashin gaskiya da munafunci da gulma da bi-ta-da-k’ulli da sauransu.

5.0  Illolin Rashin Zaman Lafiya


Rashin zaman lafiya babbar musiba ce a rayuwar al’umma, domin yakan haddasa talauci da fargaba da ta’bar’barewar tattalin arziki, da hasarar dukiyoyi da rayuwa. Bashir Musa Liman a baiti na 5 da na 7 da na 15, yana bayyana illolin da rikicin Arewaci da Kudancin Nijeriya suka haifar, na hasarar rayuka da dukiya, yana cewa:

Baiti na 5    A Kudu maso gabas ana ta hatsaniya

Suna fasa bututun mai da hauragiya

Tattalin arziki ya zama koma baya

Muna cikin talauci ba zaman lafiya

 

Baiti na 7   A Arewacin k’asata har da Maiduguri

Ana ta rikici na addini babu tsari

Rayuka da dukiyoyi sun ‘bata ba ik’irari

Wanda hakan ya haifar da k’iyayya

 

Baiti na 15   Rayuwa ta zam ta’bar’barewa

Al’amurra sun zam rikirkicewa

Komai da komai yai k’azancewa

Sai lahaula a k’asata Nijeriya

 

 

6.0  Hanyoyin Tabbatar da Zaman Lafiya da Sasantawa


Rubutattun wak’ok’in Hausa ba a bar su baya ba wajen k’ok’arin bayyana hanyoyin da suka dace mutane su rik’a amfani da su domin d’orewar zaman lafiya da sasantawa. Daga cikin wad’annan hanyoyi da marubuta wak’ok’in Hausa sukan bayyana a wak’ok’insu akwai: Hak’uri da taimakon juna da son juna da kauce wa rud’in duniya da neman ilimin addini da ilimin kimiyya da sauransu.

6.1  Hak’uri

Hak’uri muhimmin sinadari ne da za a yi amfani da shi wajen samar da zaman lafiya da d’orewarsa a rayuwar al’umma. Da mutane za su rik’a sa hak’uri a dukkan al’amurran rayuwarsu, da wasu fitintinu ba su addabe su ba. Bashir Musa Liman ya kawo bayanin hak’uri a baiti na 25 a matsayin hanyar zaman lafiya musamman dangane da rikice-rikicen siyasa da ya mamaye Hausawa a yau, yana cewa:

Baiti na 25  ‘Yan siyasa su san cewa

A za’be akwai ci da fad’uwa

In sun fad’i su zan hak’urewa

Haka zai haifar da zaman lafiya

 

Wannan baiti yana kira ne musamman ga ‘yan siyasa da ‘yan bangarsu da ke tayar da k’ayar baya idan ba su samu nasara ba. Kamata ya yi su bar wa Allah su d’auki k’addarar fad’uwa, wata rana za su iya samun nasara.

Kamar yadda Bashir Musa Liman ya bayyana a wak’arsa ta zaman lafiya, hak’uri wani gimshik’i ne na samar da zaman lafiya. Ana iya ganin haka a littafin Nagari na Kowa wanda aka nuna wani manomi mai suna ‘Danduna da matarsa Wakale wad’anda suke hak’uri da juna har suka kwashe fiye da shekara 20 suna zaune lafiya ba su ta’ba samun wata hatsaniya ba. Ga abin da labarin ke cewa:

“......Tun sa’ad da suka fara zama tare yau fiye da shekara 20 ke   nan babu wanda ya ta’ba ji, babu wanda ya ta’ba gani. Dalilin  wannan kuwa shi ne, saboda sun yarda da cewa hak’uri da abokin zama shikan sa a ci ribar zama tare. Matar nan ta nuna wa mijin cewa, ta san samu kuma ta san rashi, don haka duk abin da ya kawo komai k’ank’antarsa ba ta raina masa. Mijin kuma da ya ga yadda take biye da shi sau da k’afa, sai ya rik’a yin iya k’ok’arinsa don ya kyaautata mata.....................”

 

A cikin littafin Duniya Sai Sannu, an nuna hak’uri da yafewa a matsayi abubuwan da ke kyautata zamantakewa da kawar da zogin zuci da zaunar da mutane lafiya. Bayan da aka bayyana irin zalunci da k’azafi da Alhaji Jafaru ya yi wa matarsa Ruk’ayya a zamantakewarsu ta aure har ya yi mata saki uku, daga bisani Allah ya saka mata da wani miji mai jink’ai mai suna Musa, shi kuma Alhaji Jafaru Allah ya jarabe shi da kariyar arziki ya koma goro ko abin saye. Ga abin da Ruk’ayya ke cewa tsakaninta da yayarta Larai:

“...............Na yarda akwai maza na kirki yaya Larai, Alhaji Musa ya yi mini komai na mutunci ba zan ta’ba mantawa da shi ba, tsakanina da shi sai dai fatar alheri. Yaya Larai ta yi dariya ta ce“Shi Alhaji Jafaru fa?” Ruk’ayya ta yi murmushi ta ce, “shi ma sai dai in ce Allah ya yaye masa abin da ya same shi na kariyar arziki”. Yaya Larai ta ce, “duk wuyar da kika sha a wajensa?” Ruk’ayya ta ce, “e duk da haka, domin an ce: “idan mutum ya jefe ka da dutse, kai ka jefe shi da fura shi ya fi dacewa.” Ko da yaushe idan an cuci mutum ana son ya yi hak’uri ko da yana da k’arfin ramawa, hak’uri shi ya fi ramawar alheri, kuma za ka sami lada wurin Allah saboda hak’urin da ka yi...............”

6.2  Amana da Adalci ga Shugabanni

Duk al’ummar da ta ribantu da samun adilan shugabanni masu k’ok’arin kyautata wa mabiya da kare martabarsu da ba su kariya ga duk wani abu da ka iya barazana ga zamantakewar rayuwarsu. Yin hakan zai sa zaman lafiya ya sami sukunin walwala, yayin da rikice-rikice za su k’aranta. Bashir Musa Liman a baiti na 26, kira ya yi ga shugabannin siyasa da su sauke nauyin da aka aza musu na kare martaba da hak’k’ok’in talakawan da suke wakilta, domin yin hakan ne zai kawo d’orewar zaman lafiyar al’umma. Ga abin da yake cewa:

Baiti na 26   Su kuma wad’anda suka kai ga d’arewa

Ga muk’ami, kujera suna masu lilawa

To, su sauke nauyi da hak’k’in talakawa

Don a samu kyakkyawan zaman lafiya

 

Samun shugaba nagari mai gaskiya da adalci da amana da kuma hana zalunci da cin amana yana taimakawa k’warai wajen tabbatar da zama lafiyar al’umma. Idan aka karanci littafin Mai Rabon Ganin Bad’i, akwai wani Sarkin Dogarawa wanda ya hana zalunci da azzalumai baje kolinsu don k’asarsa ta zauna lafiya.Wannan ya sa a lokacin da wani mutum da ake kira Barau ya shigo k’asarsa bak’unta ya sami kyakkyawar tarbo aka ba shi masauki da kuma aron gona domin yin noma. Daga bisani Sarki ya kar’be sarautar sarkin noma ya bai wa Barau domin kawar da zaluncin jama’arsa da ake yi wanda zai iya haddasa rashin zaman lafiya a cikin k’asarsa. Ga abin da Sarkin ke cewa:

“.........Sarki ya kar’be sarautar daga hannun sarkin noma malam Gambo ne saboda laifin zaluncin da ya aikata na kar’be gonakin mutane wad’anda ke kusa da gonarsa ya had’a da nasa. Babu abin da ya k’ara harzuk’a Sarki sai kamar harajin manoman da ya yi ta kar’ba yana sawa cikin aljihunsa ba da sanin Sarki ba...................”

 

Wannan ya nuna cewa, idan al’umma ta sami shugaba nagari, zai yi tsayin daka wajen dak’ushe duk wani tashin-tashina na zalunci da babakere da hak’k’in mutane wanda zai iya jawo rashin zaman lafiyar  al’ummarsa.

Har wa yau, a littafin Magana Jari ce na 3, a wani labari mai take “Kowa ya dogara ga Allah kada ya ji tsoron mahassada balle k’eta”. A cikin labarin an nuna kyakkyawan shugabanci a matsayin sinadarin zaman lafiyar al’umma, inda aka nuna wani Sarki yana k’ok’arin kyautata wa talakawansa mabuk’ata musamman gajiyayyu don samun had’in kansu k’asarsa ta zauna lafiya. Ga d’an tsokaci a kan halayen sarkin:

“A cikin k’asar Sudan ne aka yi wani Sarki wanda duk k’asar babu mai arziki kamar sa. Sarkin nan kuwa Allah ya yi masa wata irin zuciya daban da ta sauran masu arziki, domin yadda masu arziki ke k’ulle kud’insu ba ci ba sha, shi ba ya yin haka. Kullum sai ya tara makafi da musakai da talakawa ya yi ta ba su sadaka. Idan kuwa ya yi wani bak’o har ma a ce yana da ilimi, in ya fara yi masa kyauta sai ya kasa godiya don murna. Wannan d’abi’a na Sarki yana ‘bata ma Waziri rai, wai don me za a rik’a yi wa talakawa irin wannan hidima. Daga nan Sarki ya taka masa birki ya ce: “Maganar banza, kai dai duk hassadarka ta d’an alherin da nike yi wa marayun Allah ne da gajiyayyu. Tukun ma shin in na mutu kana da gadon dukiyan nan tawa ce da za ka damu? Tashi ba ni wuri da irin maganganunka na banza..............”

 

Wannan matani ya nuna muna cewa, ana son shugaba ya rik’a kyautata wa talakawansa da ba kowa hak’k’in da ya dace da shi, da kuma kwa’bon duk wasu masu kawo masa tsegumin da zai kawo rashin zaman lafiya a cikin al’ummarsa.

6.3   Taimakon Juna

A duk lokacin da al’umma suka had’a kansu wuri d’aya wajen taimaka wa junansu domin warware wasu matsaloli na rayuwa, ba shakka rayuwarsu za ta kyautata, kuma zaman lafiya zai sami filin baje kolinsa a tsakaninsu. Ga abin da Bashir Musa Liman ke cewa dangane da taimakon juna a baiti na 28 da na 30:

Baiti na 28  Masu kud’i ku zan taimakawa

Kayan masarufi ku zam bayarwa

Taimakon talaka ku ci gaba da yowa

Wannan zai sa a samu zaman lafiya

 

Baiti na 30  Mu so juna, mu k’aunaci juna

Mu ji tausayi, mu taimaki juna

Mu agaza, mu kyautata wa juna

Yin haka zai sa a zauna lafiya

 

6.4    Kawar Da Bambancin Addini Da K’abilanci

Nuna bambancin addini da k’abilanci na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rikice-rikice da rud’ani a k’asar Hausa, wad’anda suka jima suna ci wa mazauna k’asar tuwo a k’warya. Bashir Musa Liman a baiti na 31, ya bayyana kawar da nuna bambancin wad’annan abubuwa biyu (addini da k’abilanci) a zukatan al’umma, wani mataki ne na zaman lafiya da kawar da rikice-rikice, yana cewa:

Baiti na 31   Idan muna so mu zam walawa

‘Bangaranci ya zamto mun wullarwa

Yarenci da k’abilanci, mu zam kaucewa

Hakan zai sa a yi daddad’ar dariya

 

6.5    Kauce Wa Rud’in Duniya

Ko shakka babu, duk wanda ke biye wa rud’in duniya zai iya fad’awa cikin halaka ko da-na-sani. Wannan ya sa da yawa daga cikin rikice-rikicen da ke addabar mutane akwai rud’in duniya na biye wa son zuciya suna aikata masha’a ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba, mai kyau ko akasinsa. Wannan ya sa Bashir Musa Liman  baiti na 33 da 34 da 35, yake gargad’in mutane da su guji irin wannan rud’i don a samu zaman lafiya mai d’orewa:

Baiti na 33   Jama’a mu guji rud’in budurwar duniya

K’azamiya, mamugunciya, makauniya

Asharariya, ibilishiya, mayaudariya

Mak’aryaciya, mahillaciya, mazambaciya

 

Baiti na 34  Rud’inta ke haifar da k’iyayya

Har ya zamto ana ta bugayya

Yaudararta ta wuce sanayya

Ta wani, bare a yi zancen dubayya

 

Baiti na 35  Ya kamata mu yo tunani

Don tantance yanayin zamani

Don guje wa sharrin shaid’ani

Wanda ba ya son zaman lafiya

 

6.6    Samuwar Ilimi

Samuwar ilimin addini had’i da na zamani yana taimakawa k’warai wajen wanzar da zaman lafiya. Haka ma, rashin ilimi a cikin al’umma yana haifar da rud’anin tashe-tashen hankula da wanzar da k’iyayya. Haka kuma, samuwar tarbiyya tagari ga al’umma wani sinadari ne na dauwamar da zama lafiya a cikinsu. Wannan ya sa duk al’ummar da ta rasa kyakkyawar tarbiyya musamman ga matasa, tilas ayyukan ta’addanci da rashin zama lafiya su addabe ta. Har wa yau, Bashir Musa Liman a baiti na 37, yana gargad’in al’umma su tashi tsaye wajen neman ilimi da samar da tarbiyya don rayuwa ta sami zaman lafiya, yana cewa:

Baiti na 37   A yi ilimin addini da na kimiyya

Kuma a k’asa idan aka samu tarbiyya

Mu lura k’asa za ta zauna lami lafiya

Da rayuwa ba kwan gaba, kwan baya

 

6.7   Yin Addu’a

A duk lokacin da wani al’amari ya zama tarnak’i ga rayuwar Hausawa, ya k’i ci ya k’i cinyewa, za ka iske an mayar da lamarin ga hannun Ubangiji ana yawaita addu’ar samun mafita domin ku’butar da rayuwa ga irin barazanar da ake yi mata. Wannan ya sa marubuta wak’ok’in Hausa bayan sun bayyana irin hanyoyin zaman lafiya, sai kuma su biyo da addu’a ga mahalicci domin ya sa hannu cikin lamarin. Wannan shi ya haifar da yawaitar amfani da karin maganar Hausawa da ke cewa: “Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya”. Bashir Musa Liman a baiti na 39 da na 40 yana cewa:

 

 

Baiti na 39   Rok’ona ga Ubangiji Makad’aici

Mai halitta har da iccen mad’acci

Wanda ya sa har abinci nakan ci

Ya sa k’asata a yi zaman lafiya

 

Baiti na 40   Tammat a wak’e na zo k’arshe

Don alfarmar Annabin k’arshe

Dace da ganinsa shi ne k’arshe

Allah ya sa a samu zaman lafiya

 

7.0  Nad’ewa


Babu shakka, zaman lafiya wani al’amari  ne da ke da matuk’ar muhimmanci da amfani a tarihin rayuwar d’an Adam. Babu wani mutum d’aya mai arziki ko moro, basarake ko talaka ko mai mulki da zai sami ingantaccen rayuwa mai d’orewa da sakewa ba tare da zaman lafiya ba. Babu wata al’umma da za ta sami d’aukaka ko bunk’asa da ci gaban tattalin arziki da siyasa da zamantakewa da walwala face tana gudanar da rayuwarta cikin k’oshin zaman lafiya. Saboda haka ne za a iske duk wata al’umma da ta sami ci gaban rayuwa, hak’ik’a tana bisa turba ta zaman lafiya. Haka ma, duk wata al’umma ko k’abila ko k’asa da rikice-rikice da yak’e-yak’e da tashin-tashina suka mamaye ta, za a tarar al’amurranta sun ta’bar’bare ko ma sun durk’ushe baki d’aya. Hak’ik’a da za mu yi amfani da karantarwar marubuta wak’ok’inmu na Hausa, da rayuwarmu ta sami walwala da zama abin koyi ga sauran al’ummomin duniya.

https://www.amsoshi.com/2017/10/01/yadda-ake-yin-kayan-ki%c9%97a-na-girgizawa/

MANAZARTA


Abdullahi, J. (1970) Nagari Nakowa. Zaria: Northern Nigeria Publshing Company.

Ahmad, A. (1997) Duniya Sai Sannu. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Albert,  I.O.  (1999)  “Ethnic  and   Religious  Conflict  in  Kano” in  Community Conflicts in

Nigeria: Management, Resolution and Transformation.

Anugwon,  E.E.  (2002)  “Social Change, Social Problems” A Nigerian Experience” in Peace

Studies and Conflict Resolution in Nigeria: A Reader. Ibadan: Spectrum Books Ltd.

Bunza, A.M.  (2015)  “Labarin Zuciya a Tambayi Fuska: Sak’on  Dariya  ga  Sasanta  Tsaro  a

Farfajiyar  Karatun  Hausa”. Takardar  da  aka  gabatar  a Makarantar Harsuna, Sashen

Hausa na  Kwalejin  Ilimi  ta  Adamu Augie, Argungu.

Bunza, A.M. (2015)  “Zama  Lafiya  Ya  Fi  Zama  ‘Dan  Sarki: Shirin  Tunkarar  Za’ben  2015

2015 a  Nijeriya” Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani kan kyautata zama

lafiya a  za’ben  da za  a gudanar a shekarar 2015 wanda  k’ungiyar Orphans and Huffaz

Educational Foudation  Birnin  Kebbi ya shirya.

Bunza, A.M.  (2015) “Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato: Abin Koyi ga

Shugabannin Zamaninmu”. Takardar da aka gabatar a taron yini d’aya da Centre for Intellectual Services on Sokoto Caliphate ta shirya na fad’akarwa a kan muhimmancin tsaro da zaman lafiya.

‘Dangambo, A. (1981) “‘Daurayar Gadon Fed’e Wak’a” Muk’alar da aka gabatar a taron k’ara wa

juna sani a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Ezirim, G.E.  (2009) “The  Role of  Civil  Society  in  Conflict Management” in Peace Studies

and  Conflict  Resolution  in  Nigeria: A Reader, Edited by Ikejiani-Clark M. Spectrum

Books Limited, Ibadan.

Gid’ad’awa,  A.B.  (2006)   Bargon   Hikima.  Cibiyar   Nazarin   Hausa   na  Jami’ar    usmanu

‘Danfodiyo Sakkwato.

Francis, D.J. (2006) “Peace and Conflict Studies: An African Overview of Basic Concepts” in

Introduction  to  Peace  and  Conflict  Studies in West Africa, Edited by Shedrack Gaya

Best Published by Spectrum Books Limited, Ibadan.

Ibeanu, O.  (2006) “Conceptualising Peace” in Introduction to peace and conflict studies in

West Africa.

Imam, A. (1937) Magana Jari Ce na Uku. Zaria: Northern Nigeria Publishing Company.

K’amusun Hausa (2006) Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Ladan, A.A. (1975) Wak’ar Had’a Kan Al’ummar Afirka. Ibadan: University Press Limited.

Oxford Advanced Leaners’ Dictionary Seventh Edition.

Sani, S. (2007) The Killing Fields: Religious Violence in Northern Nigeria. Ibadan: Spectrum

Books limited, Spectrum House.

 www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

  1. […] Yunk’urin Samar Da Zaman Lafiya Da Sasantawa: Bincike Kan Wak’ar Zaman Lafiya Ta Bashir Musa Lim… […]

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.