Amsoshi

NAMUSA SHEHUSashen Koyar da Harsunan Nijeriya


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato


msyauri@yahoo.com


07031319454

Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani na k’asa da k’asa a kan ta’bar’barewar


 al’adun Hausawa a yau, da  Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina


ta shirya, a ranar talata 25-26 ga watan Yuni, 2013.


 

 

TSAKURE


 

A zamanin da ya gabata, Magungunan Hausawa na gargajiya sun kasance abin bugun gaba da alfahari ga al’ummar Hausawa.  Duk wata cuta da take addabar ciki da wajen jiki, ko kariya daga barazanar wata cuta, ko neman biyan wata buk’ata ta rayuwa, ana amfani ne da gargajiya wajen neman waraka ko biyan buk’ata. Kwatsam! Sai ga shi da rana tsakiya bayan shigowar Turawa a k’asar Hausa, wad’annan magunguna na gargajiya sun  fara fuskantar barazana na koma bayan martabar da suke da shi a jiya. Akasarin Hausawa a yau sun k’yamaci wad’annan magunguna, sun daina amfani da su, wai sun zama tsofaffin yayi sai kawai na zamani. Su kuma masu ba da maganin gargajiyar suna yi wa sana’ar tasu rik’on sakainar kashi, wasu ma sun fara watsi da ita suna kama gabansu. To wad’anne dalilai ne suka jawo wannan ci baya ko barazana ga amfani da magungunan na gargajiya a wannan zamani?  Kuma yaya za a yi a farfad’o da martabar magungunan domin su sake daidaita sahu a ci gaba da damawa da su? Wad’annan abubuwa ne wannan takarda za ta yi nazari domin farfad’o da wannan muhimmiyar al’ada.

https://www.amsoshi.com/2017/06/29/kutsen-zamani-cikin-makadan-fada-3/

 

1.0  Gabatarwa


Hausawa al’umma ce da tun asali  ta dogara da kanta wajen samar wa kanta hanyoyin neman waraka daga wata cuta da ta kamu da ita, ko take neman kariya daga barazanar cutar, ko neman wani amfani na  rayuwar yau da kullum.  Kazalika sukan kar’bi abubuwan  da zamani ya zo da su domin kada jirgi ya bar su tasha. Sai dai kamata ya yi a duk lokacin da wani sabon al’amari ya shigo wa al’umma wad’anda ba su cikin al’adunta na gado, kamata ya yi ta tsaya ta yi musu tankad’e da rairaya ta kwashi nagartattu ta gwama su da nata na gado, sa’annan ta yi watsi da bara-gurbi, ba ta yi watsi da nata ba ta kwashi kara da kiyashi. Watak’ila  da wannan ne  guguwar zamani ta kwashi wasu Hausawa musamman ‘yan boko suka yi wa magungunansu na garagajiya da suka gada kaka da kakanni rik’on sakainar kashi, wasu ma suka daina amincewa da su baki d’aya. A kan haka ne wannan takarda za ta yi nazarin irin barazanar da zamani ke yi wa magungunan Hausawa na gargajiya a yau na koma bayan martabar da suke da ita a baya. Sa’annan kuma a nazarci irin abubuwan da suka haifar da wannan barazana da sunan zamani, da yadda za a shawo kan matsalar domin sake gina al’adun Hausawa kamar yadda suke a baya.

https://www.amsoshi.com/2017/11/06/adabin-rukiyya-goshin-karni-na-ashirin-da-daya-waiwayon-tarihi-da-diddigin-bunkasar-rukiyya-yau/

1.1  Ma’anar Magani


Masana daban-daban sun tofa albarkacin bakinsu dangane da abin da ake nufi da kalmar magani. Bunza (1989) ya bayyana ma’anar magani da cewa, wata hanaya ce ta warkarwa ko kwantar da ko rage cuta ta ciki ko ta waje, ko wadda   ake samu daga had’ari ko kuma neman kariya ga cutar abokan hamayya ko cutar da su ko neman d’aukaka ta daraja ko ta buwaya ta hanyar siddabaru da sihirce-sihirce na ban al’ajabi.” Ahmad (1984) yana cewa, magani shi ne duk wani abu da za a yi, ko wata hanya, ko kuma dabara da ake yi don gusar da cuta daga jikin mutum d’ungurungum, ko kuma kwantar da ita don kawo jin dad’i ga jiki ko ga zuciya da sawwak’e duk wata wahala da damuwa da ita cutar kan iya haifarwa. Musa (1986) yana cewa, magani wata hanya ce kawai ta neman biyan buk’atar  wata matsala da ke damun mutum, ko kuma yana ganin matsalar tana yi masa barazana. Sarkin Sudan (2013) cewa ya yi, kalmar magani na nufin duk wata hanya da d’an Adam zai bi wajen warkar da cuta ko rauni ko neman kariya daga cutar. Saboda haka, ana iya cewa, magani shi ne duk wani abu da aka yi amfani da shi domin magance wata cuta, ko cutar da wani aka saka ta ga jikinsa.

A ganina, magani shi ne duk wata hanya da aka yi amfani da ita domin samun sauk’i ko waraka ko mafita a kan wata matsala da take damun jikin mutum ko zuciya ko kuma rayuwarsa gaba d’aya. Maganin gargajiya kuwa shi ne, yin amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle, don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa wani abu saboda biyan buk’ata (Alhassan da wasu 1986).

2.0  Magungunan Gargajiya a Jiya


Maganin gargajiya sana’a ce da ta yi matuk’ar bunk’asa a k’asar Hausa, don haka ma da wuya a sami gari ko k’auye wanda ba mai magani a cikinsa. (Alhassan 1986). Maza da mata suna gudanar da wannan sana’a maganin gargajiya, kuma suna da k’ima da muhimmanci a k’asar Hausa. Dalili kuwa shi ne, a wajensu ne ake neman waraka daga kowace irin cuta da ta shiga jiki take addabarsa. Gare su ne kuma ake neman maganin riga-kafin barazanar wata cuta da ka iya kawo wa jiki hari. Hakazalika a wajensu ne ake neman kusan dukkan wasu buk’atu da rayuwa take burin ta cim ma. Daga cikin masu ba da maganin gargajiya a k’asar Hausa, akwai mak’era da manoma da masunta da mafarauta. Su kuwa wad’anda suka rik’i ba da maganin gargajiya a matsayin sana’a sun had’a da bokaye da ‘yar maiganye da magori da malaman tsibbu. A wani lokaci ma likitocin zamani sukan nemi taimakon wad’annan masu magani na gargajiya.

2.1  Tussan Maganin Gargajiya

Wasu magungunan gargajiya na Hausawa akan samo su ne daga tsirrai da itace. Wasu daga dabbobi da k’wari. Wasu kuma daga sassan jikin mutane, wasu daga ruwa ko k’asa. A yayin da wasu  kuwa addu’o’i ne da surkulle ko karance-karance da yanka da zubar da jini da dai sauransu (Sarkin Sudan 2013).  Saboda haka, masu ba da maganin gargajiya sukan sarrafa wad’annan abububwa da aka ambata domin magance cututtuka iri daban-daban da ke damun jiki. A wani lokaci sukan ba da sassak’en itatuwa, wani lokaci su ba da tsime. Sukan kuma ba da turare wanda za a rik’a yin hayak’i da shi da kuma suraci. Akwai kuma wad’anda suka shafi k’ulle-k’ulle da tofe-tofe da na shafawa da na jik’e-jik’e da dai makamantansu. Haka dai al’amarin yake gudana a k’asar Hausa, kusan kowace irin cuta da irin nau’in maganin da ake amfanin da shi domin samun waraka ko kariya daga kamuwa da ita.

2.2  Rabe-Raben Maganin Gargajiya

Sarkin Sudan (2013) ya kalli magungunan gargajiya ta fuskoki kamar guda hud’u, ta la’akari da buk’atocin mutane na magani wajen karkasa su:

·         Magungunan warkarwa: Su ne wad’anda suka k’unshi duk wani magani da ake amfani da shi don warkar da cuta ta zahiri ko ta cikin jiki ko rauni da dai makantansu.

·         Magungunan kariya: Wato wad’anda suka k’unshi magungunan da Hausawa ke sarrafawa ko amfani da su don kare kai daga cuta ko cutarwar mutum ko aljani ko wata dabba ko k’waro.

·         Magungunan cutarwa: Su kuwa wad’annan magunguna ne wad’anda akan tanade su ne da tunanin cutar da wasu bisa wasu dalilai na k’iyayya ko hukunci ko ramuwar gayya ko gyara ma wani zama.

·         Akwai kuma magunguna biyan buk’atocin rayuwa, wad’anda suka k’unshi duk wani magani da zai k’ara wa rayuwa kwarjini da ado da jin dad’i. Magunguna ne da ake amfani da su domin samar wa zuciya abin da take so wad’anda ba ta iya samar wa kanta shi kai tsaye,

3.0  Magungunan Gargajiya a Yau


Babu shakka, kusan kowace daga cikin al’adun Bahaushe na jiya suna nan a yau, tare da sauye-sauyen da ya riske su a zamunan da suka shige su. A wasu lokuta, za a ga kutsawar zamani cikin wasu al’adunmu kamar wata wayewa ce ko bunk’asa. Amma idan aka kalle su bisa kundin tarihin al’ada da martabarta, za a ga ci gaban mai ginan rijiya ne Bunza (2011). Tattare da haka, ba za a ce duk wata gargajiya ala tilas a raya ta a kowane zamani ba. Wasu al’adun zamani ba ya iya tafiya da su saboda irin nauyinsu ga mutanen zamaninsu.

Hak’ik’a magungunan gargajiya sun dad’e ana damawa da su a zamaninsu a k’asar Hausa. Sai dai kuma a halin da ake ciki a yau, zamani na k’ok’arin yi wa wannan muhimmiyar al’ada tarnak’i a kusan dukkanin kusurwoyinta. A yau an wayi gari maganin gargajiya na warkar da cutar da ke addabar jiki an ce ba su dace da zamani ba domin ba su da inganci da tsaftar da ya kamata. Masu tsaftar da aka kawo a yau sun fara gur’bacewa. An ce bokaye k’arya kawai suke shara wa mutane. An yi mana wayo an ce itace da tsirranmu tarkacen banza ne. Amma kuma sai ga shi su ake kwashewa a kai k’asashen waje a sarrafa, daga bisani a sake dawo muna da su, wai su ne masu inganci da tsafta da dacewa da zamani mai ci. A kan haka, maganin gargajiya da muke alfarma da shi a da, a yau ba su da k’ima da daraja ga akasarin jama’ar k’asar Hausa, wai da sunan ci gaban zamani. Saboda haka, muna iya kallon hanyoyi da dama wad’anda suka taimaka wa zamani wajen yi wa maganin gargajiya barazana na koma bayan da yake fuskanta a yau.

3.1  Zuwan Turawa a K’asar Hausa

Bayan da Turawa suka shigo k’asar Hausa suka ci ta da yak’i, sun yi iya k’ok’arinsu na sauya akalar rayuwar Hausawa zuwa ga nasu ak’idu da al’adu na yaudara da babakere domin biyan buk’atocin rayuwarsu. Sun tsara abubuwa ta yadda dole a kwaikwayi al’adu da d’abi’unsu. Sun sauk’ak’a fahimtar fannonin ilimin kimiyya da fasha. Sun kawo abubuwan d’auke hankalin maras wayo. Kusan dukkan al’adun Hausawa na gargajiya da suke alfarma da shi an ce sun zama tsofaffin yayi, wato zamaninsu ya wuce. Magungunanmu da muka jima muna amfani da su tun zamanin zamunna, a yau an ce ba su da tsafta da ingancin da rayuwa ke buk’ata. Ba shakka, Turawa sun yi nasara a kan yak’i da suke yi na gurgunta al’adun Hausawa musamman a ‘bangaren maganin gargajiya. An wayi gari a yau, akasarin Hausawa sun k’yamaci wad’annan magunguna nasu. Wasu sun yi musu rik’on sakainar kashi. Wasu ma sun ba su baya sai idan an ga uwar bari, tilas a koma wa gida ba don rai ya so ba. Su kansu masu ba da maganin na gargajiya wasu sun fara sakin sana’ar suna kama gabansu, wai sana’ar ta zama tsohuwar yayi.

3.2  Samuwar Hanyar Warkarwa na Zamani

Ko shakka babu, samuwar magunguna irin na zamani ya yi matuk’ar barazana na k’wace daraja da martabar da maganin gargajiya yake da shi a jiya. A da can, kowace irin cuta da ke addabar jikin mutum, ko yake neman kariya daga barazanar da za ta iya yi masa, akan garzaya ne wajen masu ba da maganin gargajiya kai tsaye domin samun biyan buk’ata. A yau, idan kai ko cikin mutum na ciwo bai ko tuna cewa akwai maganin gargajiya, sai dai ya garzaya shagunan sayar da magani wato (chemist) ya sawo na zamani. Idan mutum ya samu rauni ko zazza’bi ko ciwon baya ko ma duk wata cuta sai ya tasam ma likita. A da, idan kunama ko maciji suka sari mutum, akan garzaya ne a nemo maganin garagajiya a kuma sami waraka. A yau wannan ya zama labari, sai dai a kai asibiti a sha allurori. Bugu-da-k’ari, a da, idan mutum ya fuskanci wata matsananciyar rashin lafiya, akan d’auke shi ne a kai shi wajen mai maganin gargajiya, a wani lokaci ma a bar shi wajen mai maganin yana yi masa magani har sai ya sami lafiya sa’annan a dawo da shi gida. A yanzu sai dai a kwasa a nufi asibiti a kwantar. Hatta matsalar iskoki a yau zamani ya k’wace wa gargajiya. Akwai asibitoci na musamman da aka yi domin kula da masu ciwon ta’bin hankali. Shi kuwa matsalar shigar aljanu a jikin mata, shi ma ya wuce sanin gargajiya a yau, sai dai a kai wa malaman ruk’iyya.

3.3  Karatun Boko/Ilimin Zamani

A nawa tunani, karatun boko ko samun ilimin zamani na daga cikin abubuwan da suke yi wa maganin gargajiya barazanar ci baya a yau. Galibi ‘yan bokon k’asar Hausa, a yau ba su amfani da mafi yawan magungunan gargajiya a matsayin hanyar neman waraka daga wata cuta ko riga-kafinta, sai dai na zamani. A tunaninsu, wasu magungunan gargajiyar sun zama tsohon alkawari, don haka sun fi dacewa da mutanen karkara su da ba su san zamani ba, amma ba wayayyu ‘yan boko ba. Hatta ‘yan gado da suka yi karatun zamani suka k’are sun guji wad’annan magunguna, wai su ma sun waye sun saje da zamani. Ba a shan sassak’e da tsime, balle a yi hayak’i ko suraci, al’amarin dai sai wanda ya ji ko ya gani.

3.4  Masu Maganin Gargajiya

Hak’ik’a su kansu ma su ba da maganin na gargajiya sun taimaka wajen koma bayan da magungunan suke fuskanta a yau. Da yawa daga cikinsu sun yi wa sana’ar rik’on sakainar kashi, wasu ma sun yi adabo da ita, saboda ganin k’yalk’yalin zamani. A wani lokaci ma sai ka iske magori ya sawo magungunan zamani iri daban-daban yana talla a unguwanni da kasuwannin k’asar Hausa, wai shi ma ya bi romon zamani. Da yawa daga cikin asirran itace da tsirran magani da aka gada daga magabata sun salwanta, an shiga kame-kamen k’arya. ‘Yan gado sun yi watsi da gadon. ‘Yan haye da aron hannu sun yi katutu a ciki, sai yaudara da shara wa marasa lafiya k’arya kawai ake yi domin kar’be abin hannunsu. Ba shakka, masu iya magana na cewa, kowa ya bar gida, gida ya bar shi.

3.5  Sauyin Zamani

Hausawa na cewa, lokacin abu a yi shi. Hak’ik’a zamani abu ne da ke sauyawa daga lokaci zuwa lokaci. Haka kuma a duk lokacin da ya sauya za a taras al’amurran da ke gudana a wannan zamani su ma sun d’auki sabon salo ba kamar inda aka fito ba. Babu mamaki lamarin da ya faru kenan ga maganin gargajiya a yau. Domin kuwa, kafin shigowar Turawa a k’asar Hausa, maganin gargajiya shi ke ‘barje guminsa yadda ya so ba tare da wata matsala ba. Bayan da aka sami sauyin zamani na shigowar Turawa a k’asar Hausa, sai al’amurran rayuwar Hausawa su ma suka fara sauyawa sannu a hankali, sa’banin wanda aka saba da shi. Daga nan ne fa aka fara raba gari tsakanin maganin gargajiya da zamani, kowa ya san inda dare ya yi masa. Wannan ba mamaki a cikin faruwar hakan, domin kuwa, ba za a ce duk wata gargajiya ala tilas a raya ta a kowane zamani ba. Takin sak’ar da take yi da addini da dokokin k’asa ke sa tilas a yi watsi da wasu. Wasu kuwa zamani ba ya iya tafiya da su saboda irin nauyinsu ga mutanen zamaninsu (Bunza 2011).

3.6  Tasirin Addinin Musulunci

Da yake galibin Hausawa a yau suna bin tafarkin addinin musulunci ne sau da k’afa. Wannan ya sa a wurare da dama addinin musulunci ya ci karo da wasu al’adu da aka dad’e ana amfani da su a k’asar Hausa. A kan haka ne ya tilasta Hausawa yin watsi da wasu al’adu saboda cin karo da suka yi da koyarwar addinin musulunci,wasu al’adun kuma suka gurgunce. Wannan ya taimaka k’warai wajen raunana k’imar maganin gargajiya a yau. Galibi duk magungunan da suka had’a da amfani da iskoki ko zubar da jinin wasu dabbobi ko yi wa iskoki wasu hidima domin biyan buk’ata, ko had’a magani da wasu abubuwa da musulunci bai amince a ci, ko a sha, ko a saka a jiki ba, addinin musulunci ya haramta yin su ta kowace fuska. Bugu da k’ari, irin hawan bori da yin girka da ake yi don samar da waraka ga mara lafiya, musulunci ya yi watsi da wannan al’ada.

4.0  Hanyoyin Farfad’o da Martabar Maganin Gargajiya


A ganina, duk yadda al’amari ya cakud’e ko yake k’ok’arin rinca’bewa, ba za a yanke k’auna ga samun mafita ba. Amfani da hanyoyi mafiya d’aukaka don samun farfad’o da martabar da ke ga maganin gargajiya a jiya daga barazanar da zamani yake yi masa a yau yana da matuk’ar muhimmanci. Akwai hanyoyi da yawa da nake ganin idan aka jaraba su watak’ila a sami maslaha a ceto rayuwar maganin gargajiya daga ramin da yake k’ok’arin afkawa a ciki.

Ko shakka babu, Hukuma na da rawar da za ta iya takawa domin ganin an farfad’o da martaba da darajar maganin Hausawa na garagajiya daga suman da suke k’ok’arin yi a sakamakon barazanar da zamani ke yi musu a yau. Kamata ya yi Hukuma ta tsoma hannunta wajen tabbatar da inganci da kuma tsaftar magungunan gargajiya kafin a yi amfani da su ta kowane fanni. Wato za ta iya samar wa masu wannan sana’a ta maganin gargajiya kyakkyawan muhalli da kayan aiki irin na zamani kamar yadda ake yi wa takwarorinsu na zamani. Haka ma za ta iya yin tankad’e da rairaya ga masu maganin gargajiya domin tsame bara-gurbi daga cikinsu masu yi wa sana’ar tarnak’i na hana ta ci gaba. Har wa yau, za ta iya amfani da kafafen yad’a labarai domin tallata ingancin amfani da magungunan kamar yadda magabata suka amfana da su. Hakazalika, a rik’a shirya taron k’ara wa juna sani domin nuna wa jama’a muhimmancin amfani da wad’annan magunguna wajen samar da biyan buk’atar rayuwa. Amfani da wad’annan hanyoyi zai taimaka wajen rage nisantar da Hausawa ke yi wa maganin gargajiya a yau.

Abu na biyu kuma shi ne, su kansu daga cikin masu maganin gargajiya sun yi wa sana’ar rik’on sakainar kashi. ‘Yan gado sun yi watsi da ita, sun bar ‘yan haye da aron hannu suna ta dawara a cikinta. Dole ne su tsaya tsayin daka su kare martabar sana’arsu. Daman sai ka martaba kanka da abin hannunka ga idon d’an kallo, sa’annan su kalle shi da mutunci.

Har wa yau, dole ne mu sani cewa, al’umma takan bunk’asa ne kawai ta hanyar abubuwan da take iya samar wa kanta. Idan al’umma ta dogara kawai ga abin da wasu al’ummu ke samar musu ba ta iya ta’buka wa kanta komai, kashinta ya bushe. Kamata ya yi mu dawo cikin hayyacinmu mu fahimci cewa, wad’annan magunguna namu da muke rainawa wai ba su dace da zamaninmu ba, daga cikinsu ne Turawa ke kwasa suna zuwa k’asashensu da su a yi musu gyaran fuska a sake dawo muna da su da sunan magugunan zamani.. Da wuya ka sami wata cuta da za ta iya yi wa jiki ko zuciya barazana, face akwai maganinta a gargajiyance sai idan ba a bincika sosai ba. Da ma Hausawa na cewa, ruwa na k’asa sai ga wanda bai tona ba. Mu sani kuma wad’annan magunguna na zamani da muke zumud’i a kansu, galibinsu sai ka ji an ce, yawan amfani da su na haifar da cututtuka iri daban-daban a maimakon samun lafiya.

https://www.amsoshi.com/2017/07/19/tsiya-adon-yan-tauri-nazarin-ayukkan-%c6%99ungiyoyin-banga-ga-tsaron-%c6%99asa-wasu-sassan-adabin-hausa/

5.0  Kammalawa


Hak’ik’a wannan nazari ya tabbatar mana da cewa, zamani ya taka rawar gani wajen k’ok’arin rusa wannan muhimmiyar al’ada da Hausawa suka jima suna cin gajiyarta, wato neman waraka daga wata cuta, ko riga-kafinta, ko neman biyan wata buk’ata a gargajiyance. Haka ma su kansu Hausawa sun taimaka wajen ruguza wannan al’ada da sunan ci gaba da wayewar kai. Masu iya magana na cewa, har gobe ruwa na maganin daud’a. Sau da yawa akan kwantar da mara lafiya likitoci su yi ta bincike a kansa amma su kasa gono inda matsalar take. Daga k’arshe sai ka ji sun ce, a koma gida a jaraba na gargajiya watak’ila a sami nasarar gano k’ullin da ya buwaye su kwancewa.

                                                  MANAZARTA


Alhassan, H., Musa, U.I., Zarruk’ R.M.  (1982)  Zaman  Hausawa  Bugu  na  Biyu. Islamic

Publications Bureau, Lagos.

Bunza, A.M.  (1989) “Hayak’i  Fid Da  na  Kogo: Nazarin Siddabaru  da  Sihirin  Hausawa”.

Kundin digiri na biyu, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M. (1995) “Magungunan  Hausa  a  Rubuce: Nazarin  Ayyukan Malaman Tsibbu”.

Kundin digiri na uku, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M. (2006) Gadon Fed’e Al’ada. Tiwal Nigeria Limited Surulere, Lagos.

Bunza, A.M. (2008)“Asirran Sata a Riwayar Gambo”.Takardar da aka Gabatar a Taron K’ara

wa  Juna Sani  na Sashen  Koyar  da  Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo,

Sakkwato.

Bunza, A.M. (2011)“Al’adun  Hausawa  Jiya da Yau: Ci  Gaba  Ko Lalacewa”. Cikin  KADA

Journal of Liberal Arts, Volume 5. Kaduna State University, Kaduna.

C.N.H.N. (1981) Rayuwar  Hausawa. Littafin da Cibiyar Nazarin  Harsunan Nijeriya, Jami’ar

Bayero Kano ta wallafa.

Gulbi, A.S.  (2013)  “Tsafe-tsafen Demokorad’iyya”. Takardar  da  aka  Gabatar  a Taron K’asa

na Farko da Cibiyar Nazarin  Harsunan  Nijeriya Jami’ar  Bayero  Kano ta shirya a kan

Harshe da Adabi da Al’ada.

Sudan, I.A.S (2013)  “Muhallin Magani a Adabin Bakan Bahaushe”. Cikin ‘Dund’aye Journal

of Hausa Studies, Volume, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.