Amsoshi

DAGA


MUSA SHEHU


 


Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.


msyauri@yahoo.com


0703 131 9454


 


 


 


 

Gabatarwa


Sana’o’in zamani sana’o’i ne akasin sana’o’in gargajiya wad’anda Hausawa suka gada kaka da kakanni, wato sana’o’i ne da Hausawa suka tsinta da rana tsaka bayan zuwan Turawan mulkin mallaka a k’asar Hausa a wajajen k’arshen k’arni na goma sha tara har zuwa yau. Turawan sun fara shigowa ne k’asar Hausa a matsayin ‘yan kasuwa, daga baya kuma suka juye suka zama Turawan mulki. Kafin dai shekarar 1906 kusan dukkan k’asashen Hausawa da na mak’wabtansu sun koma a k’ark’ashin mulkin Turawa. Turawa suka zama su ne wuk’a su ne nama wajen tafiyar da mulkin wad’annan k’asashe. Da yake babbar manufarsu da mulkin mallaka shi ne don kafa ak’idarsu ta Yahudanci da Nasaranci, da kuma k’arfafa tsarin tattalin arzikin k’asarsu (Ibrahim 1987).

Bayan da suka sami gindin zama na dindindin a k’asar Hausa, suka shimfid’a tabarmarsu suka zauna, sai suka fara shigowa da kayayyakin da za su rage musu wahalhalun rayuwa da more wa rayuwar kamar yadda ya kamata. Ta haka ne suka rik’a shigowa da injunan rage wahalar noma da tafiya k’asa kamar wajen fatauci da kasuwanci, da sauran abubuwan jin dad’in rayuwa. Wannan ne ya samar da motocin noma da na d’aukar kaya da na hawa da babura da kekuna da injunan ba da hasken lantarki da makamantansu da dama. Yawaitar wad’annan abubuwan more rayuwa a k’asar Hausa su suka haifar da samuwar wasu muhimman sana’o’i ga Hausawa irin su kabu-kabu da kanikanci da faci da tuk’in mota da gyaran wutar lantarki da walda da makamantansu da dama.

Da tafiya ta yi tafiya, sai harkar sadarwa ta kunno kai gadan-gadan a k’asar Hausa, inda aka samar da kamfanoni daban-daban na sadarwa da suka had’a da MTN da GLO da ZAIN da sauransu. Wannan ya ba da kafar samuwar wayar salula a kusan kowane sak’o na k’asar Hausa. Ita ma wannan harkar ta taimaka wa Hausawa wajen amfana da sana’o’i kamar sayar da wayar salula, da gyaranta, da cajin batirinta, da kuma sayar da kati, da sauransu.

Ta la’akari da irin gudummuwa da bunk’asa tattalin arziki da inganta rayuwar Hausawa da wad’annan sababbin sana’o’i suke bayarwa, aka ga ya dace a gudanar da binciken ire-iren wad’annan sababbin sana’o’i kamar yadda masana da manazarta suka yi wa takwarorinsu na gargajiya domin haska wa jama’a k’imarsu da gudummuwarsu wajen ci gaban rayuwar Hausawa a yau. Saboda haka, wannan takarda za ta fi ba da k’arfi ne ga manyan sana’o’in na zamani kamar kabu-kabu da kanikanci da tuk’in mota da sana’ar wayar salula da kuma ayyukan gwaunati.

1.0    MA’ANAR SANA’A


Kalmar sana’a bak’uwar kalma ce ga Hausawa, wato ararriyar kalma ce daga harshen Larabci wato “sun’a” mai nufin aikin da mutum zai yi na yau da kullum domin samun abin amfanin rayuwa. Da Hausawa suka aro ta ne sai suka yi mata gyaran fuska zuwa “sana’a” domin ta saje ta zama ‘yar gida ba tare da sauya ma’anarta ta asali ba. Da wannan ne Yahaya (1992) ya bayyana ma’anar sana’a da cewa, “wata hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da d’an Adam ya mallaka don buk’atun yau da kullum”. Sana’a abu ce wadda ta danganci tono albarkatun k’asa da sarrafa hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da d’an Adam da sha’anin kasuwanci na saye da sayarwa da ciniki da sauransu. Sana’o’i irin su noma da farauta da su da fawa da k’ira da makamantansu, su ne mafiya girman matsayi da Hausawa suke amfani da su domin  dogaro da kai da biyan buk’atun rayuwa.

Ana cikin wannan yanayi ne sai aka wayi gari a yau zamani ya haifar da wasu sababbin sana’o’i wad’anda suka sanya akasarin Hausawa suka jingine sana’o’insu na gargajiya suka rungumi wad’annan sababbin sana’o’i gadan-gadan domin tafiya da zamani. Ga bayanin ire-iren wad’annan sababbin sana’o’i da yadda suka faro da kuma irin bunk’asa da samun kar’buwa da suka yi a hannun Hausawa.

https://www.amsoshi.com/2017/06/21/191/

1.1    SANA’AR KABU-KABU


          Sana’ar kabu-kabu na daga cikin manyan sana’o’in da Hausawa suke gudanarwa a wannan zamani da ke tafiya. Kabu-kabu sana’a ce ta d’aukar mutane bisa babur (mashin) daga wannan wuri zuwa wani, ko daga wata unguwa zuwa wata, ko daga wani k’auye zuwa wani, da dai sauransu. Dangane da samuwar wannan sana’a kuwa, wasu maji’binta sana’ar sun bayyana cewa, sana’ar ta fara gudana ne bayan zuwan Turawan mulkin mallaka da samun ‘yancin kai a wajajen shekarar 1970. Sana’ar ta soma ne tun ana k’yamar yin ta kasancewarta bak’uwar sana’a ga Hausawa. A da can, ana kallon masu yin ta a matsayin marasa aikin yi, amma sannu a hankali sana’ar ta fara bunk’asa ta kuma samu kar’buwa musamman ga masu k’aramin k’arfi tun lokacin mulkin Shagari har ya zuwa yau. Sai dai kuma sana’ar ta fi kankama a cikin birane domin nan ne jama’a suka fi yawa, duk da yake a yanzu sana’ar ta soma kutsa kai a cikin k’auyuka. Sau da yawa mutanen k’auye ke baro k’auyukansu zuwa birane domin gudanar da sana’ar, idan maraice ya yi su koma k’auyukansu. Wani lokaci ma sukan d’auki tsawon lokaci kimanin watanni kafin su koma su ga gida.

Galibi sana’ar kabu-kabu wani mai kud’i kan sayi mashin ya ba d’an kabu-kabu bisa yarjejeniyar abin da zai rik’a bayarwa a kullu yaumin. Sai dai a yanzu an samu wani ci gaba wai shi “inshora” (insurance). Wannan wani tsari ne da mai kud’i zai sayi mashin a misalin dubu d’ari, sai ya ce mai kabu-kabu zai biya kud’in mashin d’in a k’imanin dubu d’ari da hamsin bisa wasu k’ayyadadden watanni kamar a cikin wata goma. Ma’ana a kullum zai kawo balas d’in k’imanin naira d’ari biyar har tsawon adadin da aka tsara. Idan ya cimma wannan adadi na wata goma ko yadda aka tsara, ya gama biya kenan mashin ya zama mallakinsa.

Wannan sabon tsari ya taimaka wa mutane da dama wajen mallakar mashin d’in kansu suka ci gaba da dogara da kansu ba tare da wata matsala ba.

Sana’ar kabu-kabu sana’a ce da ta ke’banta da maza musamman matasa. Dangane da lokacin gudanar da sana’ar kuwa, kusan kowane lokaci ana yin ta, ba dare ba rana, ba rani ko damana. Sai dai wata matsalar ita ce, wasu na kallon sana’ar a matsayin sana’ar matasa wadda ba ta d’orewa har zuwa manyanta, wato sana’a ce ta masu k’arancin shekaru daga shekara ashirin (20) zuwa arba’in (40). Kabu-kabu sana’a ce mai k’arfi wadda ke iya d’aukar nauyin masu yin ta su biya buk’atun rayuwarsu ta yau da gobe. A halin da ake ciki yau, da wuya ka sami sana’ar zamani da take d’aukar nauyin dubban mutane kamar kabu-kabu. Kasancewar sana’ar ta tsayu sosai da k’afafuwanta, wannan ya sa masu gudanar da sana’ar samar mata shugabanni maji’binta al’amurran da suka shafe ta, kamar dai yadda sana’o’in gargajiya suke da sarakunansu masu kula da al’amurran da ke kai kawo a cikin sana’o’insu. Don haka ne ma da wuya ka sami gari ko k’auyen da wannan sana’a ta kabu-kabu ke gudana ba tare da shugaba.

https://www.amsoshi.com/2017/06/21/191/

1.2     SANA’AR TUK’IN MOTA


          Sana’ar tuk’in mota sana’a ce dad’ad’d’iya da wasu suka bayyana cewa ta samu ne bayan zuwan Turawa a k’asar Hausa. Galibi tuk’in mota sana’a ce ta maza inda mutum kan sayi mota ko wani ya saye ya ba shi don a rik’a d’aukar mutane (fasinja) ko kaya zuwa garuruwa daban-daban na kusa da ma na nesa. Saboda muhimmancin wannan sana’a ne ya sa aka tanadi wuri na musamman da ake kira “tasha” inda mutane ke zuwa suna shiga mota zuwa wuraren da suke buk’ata. Ana kiran masu wannan sana’a da suna direbobi. Daga cikin direbobin akwai na manyan motoci, akwai kuma na k’ananan motoci. Direbobin manyan motoci direbobi ne da ke tuk’a manyan motoci wad’anda galibi kaya kawai suke d’auka, sai dai sukan d’an had’a da fasinja a wasu lokuta. Direbobin k’ananan motoci kuwa direbobi ne da ke tuk’a k’ananan motoci wad’anda suka ta’allak’a wajen d’aukar fasinja kawai tare da d’an kayansu da bai taka kara ya karya ba.

Direbobi mutane ne da ke zagayawa kusan kowane sak’o na k’asar Hausa da ma Nijeriya baki d’aya. Tuk’in mota sana’a ce mai ban samu, duk da yake  mafi yawan direbobi ba motocin kansu suke tuk’awa ba, wasu masu hali kan saya musu don kowanensu ya amfana. Wannan sana’a ta kankama k’warai da gaske a k’asar Hausa, kasancewar matasa sun tsunduma gadan-gadan a cikinta saboda d’imbin albarkar da ake samu a ciki, domin sau da yawa direba ke tuk’a motar wani a wayi gari ya kai ga sayen tasa ya ci gaba da tuk’awa, ko shi ma ya ba wani direban ya tuk’a masa.

1.3     SANA’AR KANIKANCI    


          Kanikanci na daga cikin sana’o’in zamani da Hausawa suke gudanarwa a yau. Sana’a ce ta gyaran injuna da suka had’a da injin mota da na babur da na janareta da sauran injimomi. Masu gudanar da wannan sana’a ana kiransu kanikawa. Dangane da samuwar wannan sana’a kuwa, maji’binta sana’ar sun nuna cewa, sana’ar ta fara ne tun bayan samuwar ‘yancin kan k’asar nan, wato kimanin shekaru arba’in da suka wuce. A da can Hausawa ba su kar’bi sana’ar da hannu biyu ba kasancewarta bak’uwa da kuma wahalar koyo kafin a k’ware. A haka dai aka ci gaba har ta samu kar’buwa, aka wayi gari yau tana daga cikin sana’o’in zamani da Hausawa ke tink’aho da su. A yau, birni da k’auye na k’asashen Hausa ana samun kanikawa Hausawa masu gyaran injin iri daban-daban. Kamar yadda ake da injin iri daban-daban, haka ma kanikawansu suka bambanta, wato kowane bakanike da irin injin da yake gyarawa. Ga dai ire-iren kanikawan kamar haka:

Kanikawan Mota: Wad’annan  kanikawa ne da suka k’ware wajen gyara injimin motoci idan sun sami wata tangard’a. Saboda haka ba su ta’ba wani injimi da sunan gyarawa in ba na mota ba, kuma sun kasu zuwa gida biyu. Akwai kanikawan manyan motoci, akwai kuma na k’ananan motoci.

Kanikawan Mashin: Kanikawan mashin kanikawa ne da suka ji’binci gyaran mashin. Su ma wad’annan kanikawa ba su gyara kowane irin injimi in ba na mashin ba.

Kanikawan Janareta: Su kuwa wad’annan kanikawa ne da suka k’ware wajen gyara janaretar hasken lantarki da makamantansu.

Kanikawan Injimin Ruwa: Kanikawa ne da suke gyaran injimin jiragen ruwa. Sai dai su wad’annan kanikawa ba ko’ina ake samun su ba sai wuraren da ake hada-hadar jiragen ruwa.

Wannan sana’a ta kanikanci sana’a ce muhimmiya a k’asar Hausa a yau, birni da k’auye wannan sana’a tana tafiya matuk’ar hada-hadar abin hawa na gudana a wannan gari ko k’auye. Da  yawa daga cikin al’ummar Hausawa rayuwarsu ta dogara ne da wannan sana’a.

1.4     SANA’AR WAYAR SALULA


          Kasancewar Hausawa al’umma ce da ba ta yarda a bar ta a baya ba a duk lokacin da wani bak’on al’amari na ci gaba ya bayyana, don haka a koyaushe suke k’ok’arin sajewa da zamani idan buk’atar hakan ta kama. Bayanai sun nuna cewa, wayar salula ta kunno kai ne a k’asar Hausa a wajajen shekarar 2000 a lokacin mulkin Janar Olusegun Obasanjo. Samun kar’buwa da wayar salula ta samu a wajen al’ummar Hausawa ya sa ta yawaita a kusan kowane sak’o na k’asar Hausa.

Kar’buwa da amfani da wayar salula ta samu a k’asar Hausa ne ya haifar da samuwar hanyoyi daban-daban na samun abin masarufi (sana’a) ga wasu Hausawa musamman matasa. Wasu sun shiga cikin safarar wayoyin suna sarowa daga k’asashen kudu su shigo da su k’asashen Hausa. Wasu ma har k’asashen waje sukan fita su sawo su shigo da su gida Nijeriya. Wannan ya sa Hausawa da dama suka yi ta bud’e shaguna a wurare daban-daban domin gudanar da wannan sana’ar.

Bayan mutum ya mallaki wayar salula, abu na gaba da zai yi shi ne sanya wa wayar kati domin magana da ita. Wannan ya sa wasu Hausawa suka d’auki wannan sana’a ta sayar da katin waya a matsayin sana’ar dogaro da kai, inda sukan tafi kai tsaye su saro katin daga kamfani su rik’a sayarwa. Da yake wayoyin salula sun yawaita kuma sun yi sauk’i ta yadda kusan kowa ma zai iya mallakarta a k’asar Hausa, sai matsalar lalacewar wayar ta fara addabar mutane. Da farko idan waya ta lalace akan kai ta Legas ko Ibadan domin a gyara saboda babu masu gyaranta a k’asar Hausa a wancan lokaci. Da yake Bahaushe mutum ne mai basira, wannan ya sa wasu Hausawa suka fara gwada sa’a na gyara wayoyi masu k’ananan matsala. Ta haka ne wasu suka tafi wajen koyon gyaran domin samun sana’ar dogaro da kai. Sannu a hankali wannan sana’a ta gyaran wayar salula ta zama babbar sana’a a k’asar Hausa musamman a cikin birane. A halin da ake ciki yanzu, masu wannan sana’a sun wadatu gwargwadon hali, domin suna samun dukkan biyan buk’atun rayuwarsu ta hanyar wannan sana’a ba tare da wata matsala ba.

1.5    AIKIN GWAMNATI


          Zuwan Turawa a k’asar Hausa ya haifar da samuwar bak’in al’adu da abubuwan more rayuwa na zamani ga al’ummar Hausawa. Haka ma zuwan nasu ya haifar da assasa harsashin ilimin boko wanda ya mamaye dukkan kusurwoyin k’asar Hausa da ma mak’wabtansu na gida da na waje. Shi dai karatun boko ya fara samun shimfid’ar zama ne a k’asar Hausa tun a wajajen shekarar 1909 bayan da Turawa suka ci k’asar Hausa da yak’i, daular Usmaniyya ta kau, mulkin danniya da kama-karya irin na Turawa ya aza shimfid’arsa ya kishingid’a. A shekarar 1909 gwamnatin k’asa ta fara kafa makarantar boko a birnin Kano a K’ofar Nasarawa wadda ake kira makarantar ‘Danhausa. ‘Daliban da aka yaye daga wannan makaranta su aka rik’a aikawa a k’ananan makarantun larduna don karantar da ‘yan firamare. Haka dai ilimin boko ya ci gaba da samun gindin zama da bazuwa a sassa daban-daban na k’asar Hausa har zuwa yau.

Da farko dai Turawa sun kafa makarantun ilimin boko ne don koyar da ilimin aikin gwamnati ga wad’anda suka nuna k’wazo don Turawa su ba ‘yan k’asa damar gudanar da wasu ayyuka na gwamnati, da kuma koyar da wad’anda za su zama malaman makaranta a wurare daban-daban na Jihar Arewa, da kuma bai wa ‘ya’yan sarakuna ilmin gudanar da mulki a hanyoyin zamani. (Yahaya1988). Wannan tsari na karatun boko ya d’auki lokaci yana gudana da irin wannan manufa na samar da malamai da kuma inganta lamurran gwamnati. Bayan da tafiya ta yi tafiya, sai lamarin ya d’auki sabon salo, inda Hausawa suka fad’a gadan-gadan wajen karatun boko domin samun aikin gwamnati da za ya tallafa wa rayuwarsu. Wato suka mayar da karatun boko sana’a da mutum zai zuba jari domin ya sami riba. Bayan da Hausawa suka ciza suka ga jini, wato suka fahimci wannan sabuwar sana’a ta aikin gwamnati sana’a ne mai sauk’i da ban samu idan aka kwatanta ta da sana’o’insu na gargajiya, sai suka rungumi karatun boko ba kama hannun yaro domin samun aikin gwamnati ko wani kamfani da dai makamantansu.

A halin da ake ciki yanzu, ba a cikin birni kawai ba, hatta ma mutanen da ke zaune a k’auyuka sun fahimci alfanun karatun boko. Wannan ya sa ba su yarda an bar su a baya ba wajen sanya ‘ya’yansu makarantun boko domin sajewa da zamani da kuma cin gajiyarsa. Saboda haka, a yau akwai dubban Hausawa matasa da ma dattawa wad’anda rayuwarsu baki d’aya ta dogara da wannan sana’a ta aikin gwamnati da ma tallafa wa ‘yan’uwa da abokan arziki kamar yadda ya kamata.

2.0    SAURAN SANA’O’IN ZAMANI


Baya ga sana’o’in da aka yi bayani a baya, akwai sauran sana’o’in na zamani matsakaita da kuma k’anana wad’anda ba su kai girman wad’anda suka gabata ba. Daga cikin ire-iren wad’annan sana’o’i sun had’a da:

 • Walda

 • Kafinta

 • Faci/Hwaci

 • Yankan farce

 • Sayar da bak’in mai

 • Sayar da fiya wata (pure water)

 • Kamisho

 • Gyaran wutar lantarki

 • Wankin mota

 • Gyaran rediyo da talabijin

 • Wasan kwaikwayo

 • Siyasa

 • Gidajen kallon k’wallo

 • Sarrafa kwamfuta

 • ‘Daukan hoto da bidiyo

 • Wanki da guga


 

3.0   GUDUMMUWAR SANA’OIN ZAMANI WAJEN BUNK’ASA TATTALIN   ARZIKIN K’ASAR HAUSA


Daga cikin ire-iren gudummuwar da sana’o’in zamani suke bayarwa wajen raya tattalin arzikin Hausawa sun had’a da:

3.1 Samar da Ayyukan yi

 Hak’ik’a sana’o’in zamani sun ba da gudummuwa ta musamman wajen wanzar da ayyuka mabambanta a daidai lokacin da ake fama da rashin ayyukan yi, musamman ga matasan da suka kammala karatunsu na boko. ‘Dimbin jama’a da suka yi ilimin zamani sun sami ayyukan ofis-ofis a cikin gwaunati da sauran kamfanoni masu zaman kansu. Yayin da su kuma marasa ilimin zamani suka sami ayyuka daban-daban da suka had’a da tuk’in mota da kabu-kabu da kanikanci da aikin masinja da sauran wad’anda aka lissafa a baya. Bayanai sun nuna a halin da ake ciki da wuya a sami wata sana’ar Hausawa ta zamani da ma ta gargajiya da ta kwashi kason jama’a mai yawa kamar sana’ar kabu-kabu.

3.2  Kyautata Rayuwar Hausawa

Wanzuwar wad’annan sababbin sana’o’i sun k’ara inganta jin dad’in rayuwar Hausawa. Ta hanyar wad’annan sana’o’i da yawa wad’anda suka gina gidaje suka zauna, wasu suka tafi aikin haji suka kuma biya wa ‘yan’uwa, wasu suka sayi motocin shiga na alfarma, da dai sauran buk’atocin rayuwar yau da kullum da d’an Adam ke buk’ata.

3.3  Rage Zaman Banza

Ba shakka sana’o’in zamani sun taimaka wajen rage zaman kashe wando musamman ga matasa. Wad’annan sababbin sana’o’i na zamani da suka ‘bullo sun sa da wuya ka iske matashi zaune ga banza ba ya d’aya daga cikin wad’annan sana’o’i musamman kabu-kabu. Kai, hatta ma ‘yan gayu da ‘yan shalinsho za  a tarar suna kabu-kabu ko da dare ne da kuma hada-hadar wayar salula domin dai su sami abin da za su biya wa kansu buk’ata.

3.4  K’arfafa Zumunci

Daga cikin gudummuwar wad’annan sana’o’i na zamani akwai k’arfafa zumunci. Sau da yawa zumunci kan k’ullu ga masu gudanar da sana’a iri d’aya. Alal misali, idan wata hidima ta samu wani d’an kabu-kabu za a iske an yi mai kara ta hanyar taimaka masa wajen hidimomin buki da ma ‘bangaren aljihu. Irin wannan zumunci yakan sa a zama tamkar uwa d’aya uba d’aya. Galibi dukkan masu gudanar da wad’annan sana’o’i na zamani kamar ma’aikatan gwamnati da kanikawa da dai sauransu, za a iske irin wannan zumunci na k’ulluwa a zama kamar ‘yan’uwa.

Kammalawa


          Hak’ik’a wad’annan sababbin sana’o’i da Hausawa suka samu a wannan zamani sun taimaka k’warai wajen raya tattalin arzikin k’asar Hausa da ma Nijeriya baki d’aya, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda suka maye gurbin takwarorinsu na gargajiya wad’anda aka gada kaka da kakanni. Ba shakka wad’annan sana’o’i na zamani sun zama tamkar damina mai ban samu idan aka yi la’akari da irin d’imbin alfanun da ake samu a ciki. Wannan ne ya sa a halin da ake ciki kusan kashi sittin daga cikin d’ari na al’ummar Hausawa sun raja’a wajen gudanar da  ire-iren wad’annan sana’o’i domin kada jirgi ya bar su tasha.

 

https://www.amsoshi.com/2017/06/21/187/

 

MANAZARTA


Abdullahi, R.  (2011) Gudummuwar  Sana’ar Wayar Salula Wajen Bunk’asa Tattalin Arzikin

k’asar Sakkwato.  Kundin   digiri  na  d’aya,   Jami’ar   Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

E.M.  Rimer da wasu. (1966)  Zaman  Mutum  da  Sana’arsa.  Northern  Nigerian Publishing

Company, Zaria.

Garba, C.Y.(1991)Sana’o’in Gargajiya a K’asar Hausa. Kaduna: Baraka Press and Publishers

Limited.

Ibrahim, M.S.  (1987)  Gudummuwar  sana’o’in gargajiya na Hausa wajen  farfad’o da tattalin

arzikin Nijeriya. Takardar da aka  gabatar  a taron k’ara wa juna sani na hud’u a kan   Harshe da Adabi  da Al’adun  Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Madabo, M.H.  (1979)  Ciniki da Sana’o’i  a  K’asar  Hausa. Printed in Great Britain Thorbay

Press Limited Rayleigh Essex.

Namadi, S.  (2004)  Tsarin  tattalin  arzikin  Hausawa  na  gargajiya. Kundin  digiri  na  d’aya,

Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Umar,  M.M. (2005)  Kasuwanci  da  Muhimmancinsa ga Al’ummar  Hausawa. Kundin dagiri

na d’aya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Yahay, I.Y. (1988)  Hausa  a  Rubuce: Tarihin  Rubuce-Rubuce  Cikin  Hausa. Zaria: NNPC.

Yahaya, I.Y. (1992)  Darussan  Hausa  don  Makarantun  Sakandare. University Press Ibadan.

Tattaunawa da Sarki Asoke (Sarkin ‘yan kabu-kabu) a garin Yauri, 2014.

Tattaunawa da wani d’an kabu-kabu mai suna ‘Dankabo a garin Sakkwato, 2014.

Tattaunawa da Idi mai faci a garin Yauri, 2014.