MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato
07031319454
msyauri@yahoo.com
TSAKURE:
Kasancewar ƙarya abin ƙyama da Allah wadai ga rayuwar Hausawa, ya sa a
koyaushe suke gargaɗi da jan kunne domin hani ga aikata ta. A kan haka ne ya sa
Hausawa suke yawaita bayani a kan illar ƙarya da matsayin mai aikata ta a
cikin al’umma ta ɓangarori daban-daban na rayuwarsu da suka haɗa da waƙoƙinsu
na baka, da karin magana, da tatsuniyoyi, da kirari, da sauran ɓangarorin
adabinsu. Wannan takarda za ta yi nazarin illar ƙarya daga bakin makaɗan baka
daban-daban da suke yawan ambatawa a waƙoƙinsu na yau da kullum domin a guji
aikata ta saboda matsaloli ko illar da take iya haddasawa a tsakanin masu yin
ta ko ma ga al’umma baki ɗaya.
Gabatarwa
K’arya
na daga cikin munanan ɗabi’un da al’ummar Hausawa ke ƙyama a rayuwarsu. Ba ma
Hausawa kawai ba, kusan dukkan al’ummu na duniya ba su amince da ƙarya ba da
kuma mai aiwatar da ita, wato maƙaryaci. Saboda haka ne maƙaryaci ba ya da ƙima
ko mutunci a idon jama’a, hasali ma duk inda ya yi magana ba a ɗagawa da ita
nan ake barin ta, don an san maganar banza ce. Kasancewar ƙarya mummunan ɗabi’a
da rashin ɗorewarta da zubar da mutuncin mai yin ta ya sa Hausawa sukan bayyana
ta a ɓangarori daban-daban na rayuwarsu domin nuna illarta da kuma matsayin mai
yin ta, kamar a ɓangaren karin maganganusu da waƙoƙinsu da tatsuniyoyi da
kirari da makamantansu. A taƙaice, wannan bincike ya mayar da hankali ne wajen
bayanin yadda mawaƙan baka na Hausa ke bayyana illolin ƙarya musamman ga masu
yin ta a cikin waƙoƙinsu na yau da kullum. A wasu lokuta ma idan mawaƙan suna
son su muzanta wani ko su aibanta shi, sukan danganta shi da yawan ƙarya
domin kawai su zubar da mutuncinsa ko darajarsa a idon jama’a.
MA’ANAR K’ARYA
A K’amusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar ƙarya da cewa, “maganar da ba ta
gaskiya ba ce”. Maƙaryaci kuma “mutumin da ya saba da rashin faɗar gaskiya”. Ga
al’ada ƙarya ita ce faɗar abin da ba a yi ba, ko ba a gani ba, ko ba a tabbatar
ba, da kuma yin ƙari ga abin da aka ji, ko aka gani, ko yin ragi gare shi idan
aka so a ƙarasar (Bunza 2009). K’arya wata ɗabi’a ce da al’adar Hausawa ke ƙyamar
aikwatawa da kuma ƙyamar mai aikata ta. K’arya ɗabi’a ce da ke zubar da mutunci
da ƙimar duk wani mai aikata ta a cikin al’umma. Kasancewarta abin ƙyama
da Allah wadai ga al’ummar Hausawa ya sa suke yawaita ambaton matsalarta da
kuma matsayin mai yin ta a ɓangarori daban-daban na rayuwarsu, wanda suka haɗa
da waƙoƙinsu da karin magana da kirari da tatsuniyoyi da makamantansu.
ILLAR
K’ARYA A BAKIN MAKA’DAN BAKA
Waƙa dai kamar yadda masana suka bayyana “tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi
saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum
ba”(A.B.Yahya 1997). Mawaƙan baka mutane ne da Ubangiji ya ba su wata irin
baiwa fitacciya wadda ba kowa ke da irin ta ba. Mawaƙan kan waƙe jama’a a cikin
shiryayyun lafuzza masu kama hankali tare da jan ra’ayin al’umma da yin
hannunka mai sanda a kan lamurran duniya. Dangane da haka ne a wasu lokuta
sukan yawaita ambaton abin da ya shafi ƙarya ko maƙaryaci a cikin waƙoƙinsu na
yau da kullum da suke yi wa jama’a domin bayyana mummunar matsayin masu yin ta
da kuma illolinta a rayuwa. Sukan yi hakan ne ta hanyar bayyana illar ƙarya da
kuma muzanta mai aikata ta. A wasu lokuta ma idan suna son su muzanta wa
mutum sukan ambaci cewa mutum ne mai yawan ƙarya domin mutane su ƙyamace shi. A
kan haka, za mu iya kallon illolin ƙarya daga bakin makaɗan baka daban-daban
kamar haka:
Zubar da
Mutunci
Kamar yadda gaskiya ke ɗaukaka
darajar mutum da samar masa mutunci da ƙima a idon jama’a, hakazalika ƙarya ke ƙasƙanta
darajar mutum da zubar masa da mutunci da ƙima a wajen jama’a. A Hausance, duk
wani ka soka da abu biyu ƙarya da zina ka zubar masa da mutuncinsa ga jama’a.
Duk inda maƙaryaci yake za ka iske mutane suna yi masa kallon hadarin kaji,
wato kallon maras mutunci. Haka ma duk inda ya faɗi magana nan ake barin ta ba
a ɗagawa da ita kasancewar sanin kashi tis’in cikin ɗari na maganarsa babu ƙamshin
gaskiya a cikinta. A wasu lokuta ma ko da gaskiyar ya faɗa ba a aminta da ita
saboda sanin halinsa. Makaɗa Mailauni Bakura ya shigo cikin sahun mawaƙan bakan
da ke yi wa maƙaryaci dubin uku saura kwata. Ga dai abin da yake cewa a kan maƙaryaci
a waƙar da ya yi wa Bafarawa kamar haka:
Jagora: Ga wane na azan ɗan sarki na ɗan kabsu
In ya yin an da ƙarya
Shi yin an shi ruga ƙarya
Ita jiddun a’ aikinai
Yara: Duk abin da kac ce
Ni ban yadda busa ta.
1.
waƙa: Bafarawa ko can bai ɗau reni ba
Alhaji Attahiru jikan Sarkin Rafi
Wannan ɗan waƙa na Mailauni Bakura yana bayyana cewa idan mutum ya kasance maƙaryaci
mutuncinsa kan zube a idon jama’a, duk maganar da ya yi ba a amincewa da ita,
inda ya faɗe ta nan ake barin ta. A wani lokaci ma ko da gaskiyar ya faɗa
ba za a ɗauka ba saboda an san halinsa na sabo da rashin faɗar gaskiya. Don
haka ne mawaƙin ya bayyana maganar maƙaryaci da busar iska, wato magana ce
wadda ba ta da tushe balle makama.
Narambaɗa ma ya taɓo irin wannan illa na zubur da mutuncin maƙaryaci na
kasancewa abin gudu da ƙyama da rashin dattako ga maƙaryaci a waƙar day a yi wa
Sarkin Tudu Bala, inda mawaƙin ya bayyana cewa babu mai son zama da maƙaryaci a
wuri ɗaya hatta ma waɗanda ke ƙarƙashin kulawarsa. Ga dai abinda mawaƙin ke
cewa:
Jagora: Na wuce ƙarya ko ina kiɗi
Na bar ƙarya ko ina kiɗi
Nai sittin saba’in ka hwaɗa
Yara: Mai saba’in yai ƙarya
Ana ta zunɗe nai
Ko yaran da ag garai
Duk warwatse mishi sukai
Shina yawo shi ɗai ɓaran-ɓaran
1.
waƙa: Ya ci maza ya kwan shina shire
Gamda’are sarkin Tudu Bala
A wannan ɗan waƙa, Narambaɗa ya nuna ƙarya ba abin ƙwarai ba ne ko da kuwa ga
bakin makiɗi wanda da man an san shi da wasa. Haka ma ya nuna yadda mutuncin maƙaryaci
ke zubewa warwas na yadda mutane ke gudu da ƙyamarsa saboda mummunar ɗabi’arsa
ta ƙarya.
Abdu Kurna Maradun ya yi wa Sarkin K’ayan Maradun Abubakar wata waƙa inda ya
fito da illar ƙarya na zubar da mutuncin mai yin ta a idon jama’a. Ga dai
bayanin da mawaƙin ya yi kamar haka:
Jagora: Mai bogaza nika tsoro
Na raina dattakunai
Yara: In yag guma
maka ƙarya
Sai ka ji mamakinai
1.
waƙa: Jikan Hassan ɗan Iro
Sarkin K’aya mai gayya
Na Magaji ba togewa
Shi yay yi damben girma
Haɗuwa
da Fushin Ubangiji
Haƙiƙa Allah subhanahu wata’ala ya yi hani da aikata ƙarya kuma yana fushi da
mai aikata ta. Saboda haka ya yi tanadin azaba na musamman ga masu aikata
wannan mummunar ɗabi’a. Narambaɗa bai gushe ba a waƙarsa bakandamiya yana
bayyana mummunan matsayin maƙaryaci da shiga cikin fushin Ubangiji, da
kuma rashin tasirin maƙaryaci na ɗorewa a rayuwa. Ga abin da mawaƙin ke
cewa:
Jagora: Na hore ki gaskiya bari tsoron ƙarya
Yara: Mai ƙarya munahuki Allah shi Yaƙ ƙi
Har yau ba mu ga inda anka yi mai ƙarya ba
Amma ita gaskiya gari da mutane tay yi
1.
waƙa: Gwarzon shamaki na malam toron giwa
Baban dodo ba a tamma da batun banza
Idan aka yi nazarin wannan ɗan waƙar bakandamiyar za a ga cewa ya bayyana ƙarya
a matsayin abin da bai da ƙarfi ko kwarjini, don haka ba abin tsoro ba ne.
Narambaɗa ya ƙara da cewa maƙaryaci munafuki ne da ke haddasa fitina, don haka
Allah ya yi tir da halinsa. Bugu da ƙari, ɗan waƙar na ƙara bayyana cewa, ba a
taɓa samun wani ya shahara har ya samu ɗaukaka ga jama’a ba saboda ƙaryarsa,
amma gaskiya ita ke dawwama a rayuwar ‘yan Adam.
Rashin
Samun Taimako
Da yake ƙarya ta kasance abin ƙyama da Allah wadai ga masu yin ta a cikin
al’umma, wannan ya sa masu yin ta ba su da ƙima ko mutunci a idon jama’a. A kan
wannan muguwar ɗabi’a ma ko da an ga maƙaryaci cikin wani yanayi na buƙatar
taimako za ka iske kowa ya ja da baya ya sa masa ido. Sani Aliyu ‘Dandawo ba a
bar shi a baya ba wajen taɓo bayanin da ya shafi maƙaryaci na rashin samun
agaji da ɗauki ko gudummuwa ga jama’a yayin da ya shiga wata musiba ta neman
taimako. Mawaƙin ya kawo bayanin wannan illa da ƙarya ke haifarwa ga maƙaryaci
na rashin samun taimakon jama’a a waƙar da ya yi wa Madawakin Yauri, yana cewa:
Jagora: Mai ƙarhin halin hwaɗa
Bana an ba shi kashi
Hay yat tsaga kuka
Yara: Han na yunƙuro rabo Sai
nij ja da baya
Nit tuna ƙaryad da yai yi min
Gara a ba shi kashi
1.
waƙa: Mu zo mu ga Madawaki
Bai ɗau wargi ba Audu
A wannan ɗan waƙa, Sani Aliyu ‘Dandawo ya nuna cewa, babu mai ceton maƙaryaci
ko da ya shiga cikin wani hali na neman taimako saboda tsananin tsanarsa da
mutane suke yi na mummunar ɗabi’arsa.
Wawantarwa
A duk lokacin da mutum ya kasance bai da aiki sai yawo da ƙarya, za ka taras
mutane na yi masa kallon jahili maras ilimi ko wawa wanda basira ta ɓace masa.
Alhaji Musa ‘Danƙwairo ya tofa albarkacin bakinsa dangane da tunaninsa a kan ƙarya
da maƙaryaci a waƙar da ya yi wa sarkin Daura Bashar ɗan Musa, inda ya fito da
bayani a kan illar ƙarya a rayuwa da kuma yadda take ƙasƙantar da mutum har
jama’a su riƙa yi masa kallon wawa mara wayo ko hankali, yana mai cewa:
Jagora: Shi ɗan sarkin ga ya ɓakalce
Yara: Kai ku ji yawo yakai da ƙarya
Jagora: Shi ɗan sarkin ga ya kacace
Yara: Kai ku ji yawo yakai da ƙarya
Jagora: Ko jiya na ganai gidan abokinai
Yara: Na iske shina ta yi da
sarki
Jagora: To sheri ba abin ƙwarai ne ba
In ka gane ka bash shi ya hi
1.
waƙa: Babban jigo na Yari
Uban Shamaki, tura haushi
Idan aka dubi wannan ɗan waƙa za a ga cewa, ‘Danƙwairo ya siffanta maƙaryaci da
cewa ya tagayyara ya koma wawa maras basira, wato ya ɓakalce, ya kuma kacace,
saboda mayar da ƙarya sana’a. Bugu da ƙari, mawaƙin ya ƙara da cewa, ƙarya
ba abu ce mai kyau ba, don haka barin ta shi ne alhairi ga mai aikata ta, ba
don komai ba sai don a zauna lafiya a kwantar da fitina ta yi bacci.
Zaɓen Tumun Dare
Ko shakka babu, al’ummar Hausawa na ganin duk wanda ya maid a ƙarya sana’a ya
jingine gaskiya gefe ɗaya, to, kamar wanda ya yi zaɓen tumun dare ne, wato ya ɗauki
mara ‘ya’ya ya bar mai ‘ya’ya, ma’ana ya bar hanya madaidaiciya ya kama muguwa.
Makaɗa Aliyu ‘Dandawo ya taɓo bayanin ƙarya a waƙarsa da ya yi wa Sarkin Kabi
Muhammadu inda ya bayyana cewa, kowa ya saki gaskiya ya kama ƙarya haƙiƙa
ya yi aikin banza wanda ba shi da amfani. Saboda haka yake cewa, kowa ya riƙi ƙarya
a matsayin madogara ba shakka ya sai rariya kuma tilas ne ta yi zuba. Ga dai
abin da mawaƙin ke cewa:
Jagora: Kway ya da gaskiya yaɗ ɗau ƙarya
Shina sanin abin banza yay yi
Godiya Tafidan maiduka
1.
waƙa: ‘Dan Hassan madogara
Mai dama da hauni ka yi jinkiri
Ka gadi Muhammadu shirinka ya zo daidai
Rashin Tabbas
Hausawa na cewa, ƙarya hure take ba ta ‘ya’ya, haka ma komai nisan jifa ƙasa za
ta sauka. Ba shakka ƙarya abu ce da ba ta tabbata, komai daren daɗewa gaskiya
za ta bayyana kowa ya fahimce ta. Makaɗa Aliyu ‘Dandawo ya kawo wani ɗan waƙa
da ke ƙara tabbatar da illar ƙarya na rashin tabbas a rayuwa, don haka kauce
mata da riƙon gaskiya shi ne kawai mafita, yana mai cewa:
Jagora: Wakilin magani Abubakar ya
gwada hali
Haƙiƙa ba ya son wani sai kai
Ya riƙa da gaskiya, ya san ƙarya ba ta tabbata
Yara: Don shi ya ƙi
ta yab bi gaskiya
Bai san kowa ba duniyag ga bayan sarki
Narambaɗa ya kawo irin wannan illa ta ƙarya a wasu ɗiyan waƙoƙinsa da ya yi wa
Alƙali Abu na rashin tabbata da kuma warwarewa a duk lokacin da aka ƙulla wani
al’amari da ita. Ga abin da mawaƙin ke cewa:
Jagora: A ɗauki batun mai gaskiya
Yara: Mai ƙarya komi yah hwaɗi
Kamin a jima ta walwale
G.waƙa: Ya ɗau girma ya ɗau yabo
Mu zo mu ga Alƙali Abu
Haka ma a waƙar da ya yi wa Tudu ƙanen Amadu yana cewa:
Jagora: Kyawon al’amari inda gaskiya ciki
Komi a kai duniya
Yara: Ita ƙarya ba abin yi ba ta
Ramen ƙarya ƙurewa yakai
G.waƙa: Tudu madogara
Tudu maza-maza
Gawartacce ƙanen Amadu
Rasa Rayuwa
Kasancewar ƙarya mummunar ɗabi’a da haddasa gaba da fitina a cikin al’umma da
kuma zubar da mutunci da darajar mai yin ta, ya sa wasu ke ganin illarta har ya
kai ga iya salwantar rayuwar masu aikata. Sarkin kotson Kano Alhaji Abdurrahman
ya rera wa Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar III wata waƙa, inda mawaƙin ya nuna
tsananin aibin ƙarya da cewa har ma kisa tana yi ga mai yin ta ya rasa
rayuwarsa baki ɗaya. Ga dai abin da mawaƙin ke cewa:
Jagora: Mai ja da kai ƙarya ta kashe shi
Sarki mai ja da kai ƙarya ta kashe shi
Yara: Mai ja da kai ƙarya ta
kashe shi
G.waƙa: Abubakar ya i da nuhinai
Sarkin Musulmi ya wuce wasa
KAMMALAWA
A lokacin da al’amurra suka sukurkuce a tsakanin al’umma musamman abubuwan da
suka shafi lalacewar zamantakewa da tattalin arziki da tarbiyya da gaskiya da
makamantansu, za a ga cewa tushen zaman rayuwar jama’a ne ya sukurkuce. Saboda
haka, wannan takarda ta mayar da hankali ne wajen bayyana wa jama’a illolin ƙarya
a rayuwar Hausawa ta yau da kullum daga bakin makaɗan baka daban-daban na ƙasar
Hausa da suka haɗa da zubar da mutunci da rashin samun taimakon jama’a da
rashin tabbas a rayuwa ko warware duk wani abu da aka ƙulla da ƙarya, da
wawantar da mai yin ta da zaɓen tumun dare da ma salwantar rayuwa idan ba a yi
hattara ba. Saboda haka, Hausawa su farga su kauce wa sharrinta na ire-iren waɗannan
musibu ko illoli da ka iya biyowa bayanta domin rayuwarsu ta zauna lafiya.
MANAZARTA
Abba, M, da Zulyadaini, B. (2000) Nazari kan waƙar baka ta
Hausa. Gaskiya
Corporations Limited, Zaria.
Bunza, A.M. (2005) “Arashi shi gogi baƙauye: Nazarin karin maganar arashi
da
ke jikin motoci”.Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, sashen
koyar da harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
Bunza, A.M. (2006) Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Limited
Surulere Lagos.
Bunza, A.M. (2009) Narambaɗa. Ibrash Islamic
Publications Centre Limited
Surulere Lagos.
Birniwa, H.A. (2005) “Tsintar dame a kala: Matsayin karin
Magana a cikin
waƙoƙin siyasa”. Cikin ‘Dunɗaye Journal of Hausa Studies, No 2, Jami’ar
Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.
‘Danyaya, B.M. (2007) Karin maganar Hausawa. Makarantar Hausa,
Sokoto.
Gusau, S.M. (1996) Jagorar nazarin waƙar baka. Fisbas Media
Services Kaduna.
Gusau, S.M. (2003) Jigon nazarin waƙar baka. Benchmark Publishers
Kaduna.
Gusau, S.M. (2008) Waƙoƙin baka
a ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da
Sigoginsu.
Benchmark Publishers Limited, Kano.
Nahuce, M.I. (2008) “Karin Maganar Hausa a rubuce”. Kundin
digiri na biyu,
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
Tudunwada, Y.Y. (2006) Hausa a Dunƙule
na ɗaya. Triumph Publishers
Company Limited, Kano.
Yahya, A.B. (1997) Jigon nazarin waƙa. Fisbas Media Services,
Kaduna.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.