Daga


Jamilu Ibrahim Mukoshy
Jami’ar Usmanu ďanfodiyo Sakkwato
Waya: 08038353662
Imel:jmukoshy@gmail.com


MuƘalar da aka gabatar a taron Ƙarawa juna sani kan ‘Matsayin Harshe da Tarihi da
Addini wajen bunƘasa cigaba da haďin kai da tsaro a Nijeriya’, wanda Tsagayar
Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Usmanu ďanfodiyo, Sakkwato, ya
shirya daga 1 zuwa 3 ga watan Maris, 2016.ABSTRACT


In this era of internet age, numerous potentials can be drived via entrepreneurial
use of the internet. In the developed countries, particularly countries in Europe,
Asia, the use of internet is the key to success in many sectors relating to day-today
activities, such as areas of education, social communication, security,
economic and health care delivery. The aim of this paper is to discuss some of the
economic advantages of the use of internet with reference to Hausa studies. In the
course of the research, the paper studied amongst other things some of the ways
internet can be used to enhance economic growth. However, while making
analysis, the paper made referece to internet banking (hulďa da banki kan intanet),
e-commerce (kasuwanci kan intanet), online advertisement (talla kan intanet),
network administration (kula da kafar shiga intanet), web design (tsarawa da gina
shafukan intanet) and web administration (kula da shafukan intanet) as some of
the ways of economic intergration. All the items listed above are in one way or
the other specific boasting economic development. Thus, the paper also related
these areas to Hausa internet based terminological development as another in its
self developing Hausa language. Finally, the paper concludes that the use of
internet is a key to achieving success in studies and economic development. The
paper also proffered suggestions for proper internet use by students and
researchers of Hausa language.

1.0 Gabatarwa


Wannan muƘala tana bayani ne a kan wasu daga cikin hanyoyin da ake iya sarrafa intanet
domin bunƘasa harshen Hausa da inganta jin daďin rayuwar jama’a, musamman ta hanyar
bunƘasa tattalin arzikin Ƙasarmu Nijeriya. Hanyoyin da ake iya amfanin intanet domin bunƘasa
tattalin arziki sun haďa da hulďa da banki kan intanet (internet banking) da kasuwanci kan intanet
(e-commerce) da talla kan intanet (online advertisement) da kula da kafar shiga intanet (network
administration) da tsarawa da gina shafukan intanet (web design) da kuma (kula da shafukan
intanet) (web administration) da sauransu.

1.1 Ma’anar Kalmar Intanet


Akwai ma’anoni daban-daban da aka ba kalmar intanet, kuma kowace ma’ana tana da
dagantaka da wata., domin dukkan ma’anonin: (i) Sun aminta da cewa intanet hanyar sadarwa
ce. (ii) Sun yarda cewa intanet haďaka ce ta hanyoyin sadarwa. Saboda haka, ta la’akari da
waďannan bayanai, wannan muƘala ta ba nata ra’ayi da cewa:
Intanet kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk
duniya. Tana ba da damar sadar da bayanai kowaďanne iri, kuma
zuwa ko’ina a duniya cikin ďan ƘanƘanin lokaci.

2.1 Gabatar Da KeƂaƂƂun Kalmomin Intanet


A halin da ake ciki, harshen Ingilishi shi ne harshen da ya fi kowane karƂuwa a intanet.
Shi ya sa wasu masana ke da ra’ayin cewa harshen Ingilishi shi ne harshen intanet a wannan
zamani. Ita kuwa intanet wani kandami ce da ke taka muhimmiyar rawa ga lamurran sadarwa na
duniya baki ďaya. Intanet ita ce hanya mafi inganci da ake amfani da ita domin cimma Ƙudurin
globalization (shirin game duniya). Muradin yin hakan kuwa shi ne a samar da tsayayyen harshe
ďaya wanda kowa zai riƘa amfani da shi a duniya. Idan an lura, harshen da zai iya samun wannan
matsayi shi ne Ingilishi. Crystal (2001) da Rumšiene (2004) da Amfani (2007) duk sun yi Ƙarin
bayani a kan wannan batu.
Da yake intanet katafariyar hanyar sadarwa ce, tana da sassa daban-daban a ƘarƘashinta.
Akwai kimanin keƂaƂƂun kalmomin 3000 a harshen Ingilishi waďanda ake amfani da su a
sha’anin intanet na yau da kullum. Akwai keƂaƂƂun kalmomi da suka ta’allaƘa ga kowane sashe
na intanet na daban. Ga wasu daga cikin sassan na intanet waďanda aka kawo a Ƙamusun SYBEX;
(2000):
i. Fannin samar da sofwaya na sadarwa na kwamfuta (application software, operating
systems and enƂironment).
ii. Sashen samar da haduwaya na sadarwa na kwamfuta (hardware, connectiƂity tools,
products and eƘuiptments, cables, cards, connectors, chips, memory and adaptors).
iii. Kamfanoni masu samar da haduwaya da sofwaya na kwamfuta (leading hardware and
software companies, industry standards, certification scheme).
iƂ. Kafofi da layukan sadarwa na intanet (internet protocols and interfaces).
Ƃ. Hanyoyin sadarwa na intanet da intaranet daban-daban (internet and intranet
communication, workstations).
Ƃi. Ra’o’i da fannonin sadarwa na intanet (networking theory and concepts).
Ƃii. Hanyoyin sadarwa na wayoyin salula (mobile communication).
Ƃiii. Tsaro da kula da sadarwa a intanet (security and network administration).
iď. Kamfanonin samar da iso ga intanet (internet service proƂiders).
ď. Fargamin da zayyanawa da bunƘasa shafukan intanet (web programming, design and
development).
ďi. Sashen amfani da intanet (internet usage).

Waďannan su ne muhimman sassan da dole sai da su intanet ke tafiya, a nan, muƘalar ta
taƘaita ga sashe na Ƙarshe, wato sashen amfani da intanet (intanet usage). Bayan nazari kan
wannan sashe, an kasa shi zuwa gida uku domin hakan shi zai ba da damar tattaro kalmomin da
ke da alaƘa da harkokin tattalin arziki a kan intanet. Ga yadda aka rarraba wannan sashe kamar
haka:

a. Fannin samar da shafukan intanet; ya Ƙunshi fargamin da zayyana da bunƘasa intanet da
duk abin da ya danganci haka (Development and Programming Interface).
b. Fannin sadar da bayanan intanet tsakanin kwamfutoci da duk abin da ya danganci haka
(Networking Interface).
c. Fannin mai amfani da intanet (User Interface).
Daga cikin waďannan sassa, muƘalar ta mayar da Ƙarfi ga kashi na uku wato fannin mai
amfani da intanet (User Interface). Wannan Ƃangare shi ya fi cancanta a ba muhimmanci domin
samar da keƂaƂƂun kalmomin intanet na Hausa a mataki na farko. Haka kuma, wannan Ƃangare
ya fi kusa ga mai amfani da intanet. Ke nan ana iya sarrafa wa mai amfani da intanet shi
gwargwadon iyawa. Shi kansa wannan Ƃangare akwai Ƙananan fannoni da dama Ƙunshe cikinsa
da suka haďa da (1) Kai-da-kawo a cikin intanet (burauzin/ browsing ko surfing). (2) Hira,
tattaunawa ko musayar ra’ayi (hira ko tattaunawa/ chat). (3) Bincike a intanet (bincike/ search).
(4) Aika saƘonni ko wasiƘu (imel/ email). (5) Yaďa bayanai a intanet (bulog/ blogging). Bayan
nazari sosai an fitar da keƂaƂƂun kalmomin intanet na Hausa da ke ciki.

3.1 Bitar Hanyoyin Amfanin Intanet Don BunƘasa Tattalin Arziki


A yau, hanyoyin amfani da intanet suna da yawa. A Ƙasashen da suka ci gaba irin na
Nahiyar Turai da Asiya, ana amfani da intanet wajen gudanar da sha’anin kasuwanci (saye da
sayarwa); da neman ilimi (nazari da bincike) da kula da tsaro na ciki da waje da tattaunawa da
hira da musayar ra’ayi da kula da kiyon lafiya da dai harkoki da dama da suka shafi ci gaban
rayuwa na yau da kullum. Don haka har yanzu ana ci gaba da inganta hanyoyin cin gajiyar
fasahar intanet.
Wannan muƘala ta fito da amfanin da ake iya samu ta amfani da intanet domin ya zama
jigon tattaunawa da kuma ba da Ƙwarin guiwa domin inganta samar da keƂaƂƂun kalmomin
intanet na Hausa. Kodayake intanet ba ta daďe da samun wajen zama a Nijeriya ba, duk da haka
Ƙiyason Ƙididdigar da Internet Live Stats (a shafin www.InternetLiveStats.com) ya gabatar a
shekarar 2014 ya nuna cewa kimanin kashi 37.59% suna iya amfani da intanet a Nijeriya.
Wannan Ƙididdiga ta haďa dukkan al’ummomin da ke Ƙasar Nijeriya ciki kuwa har da al’ummar
Hausawa. Kodayake ba a tantance adadin Hausawa masu amfani da intanet ba, duk da haka
dagewa ga samar da wadatattun keƂaƂƂun kalmomin intanet na Hausa zai ba Hausa damar shiga
cikin sha’anin intanet sosai. Yin haka kuma shi zai Ƙara kawo gajiyar intanet kusa ga al’ummar
Hausawa.
A taƘaice dai intanet ita ce babbar hanyar sadarwa a duniya baki ďaya. Matsayinta ya
zarce a kwatanta shi da duk wata hanya ta sadarwa a yau, musamman ta la’akari da yadda
sha’anin intanet yake daďa samun karƂuwa a duniya. Ƙididdigar da shafin Internet Live Stats
(www.InternetLiveStats.com) ya gabatar a shekarar 2014 ya nuna cewa kimanin kashi 40.4% na
al’ummar duniya ke iya amfani da intanet, idan aka kwatanta shi da kashi 18% da ke amfani da
intanet a shekarar 2006, wannan ba Ƙaramin cigaba ba ne, kuma yana nuna irin karƂuwar da
intanet take daďa samu a faďin duniya. A dalilin haka intanet ta kasance babbar hanyar sadarwa
mafi sauƘi da kuma sauri. Shi ya sa Turawa suka riƘe ta a matsayin makamin ‘shirin game
duniya’ (globalization) ta hanyar amfani da harshen Ingilishi, kamar yadda aka bayyana a baya.
Wannan muƘala ba ta Ƙi aminta da wannan bayani ba ne, sai tana hasashen cewa Hausa tana da
gudummuwar da za ita bayarwa domin ta amfana kuma a amfana da ita a kan intanet. Bugu da
Ƙari, wannan shi ne dalilin da ya sa intanet ta kutsa cikin kowane sha’ani na rayuwa na yau da
kullum. Ga wasu bayanai da misalai na wasu hanyoyi da ake iya cin gajiyar intanet. Wasu
hanyoyin an daďe da fara cin amfaninsu, wasu kuwa yanzu aka fara, wasu kuma ci gabanmu bai
kai gare su ba tukuna, amma dai mu je zuwa.

3.2 Kasuwanci A Kan Intanet (internet banking)


Wannan wani muhimmin Ƃangare ne da ya samu kulawa sosai a intanet. Intanet ta
kasance wani babban dandali ko cibiyar kasuwanci ta duniya a yau. Wannan Ƃangare na cin
gajiyar intanet shi ake kira ‘e-commerce’ a Ingilishi. Ayo da wasu (2011) sun bayyana cewa:
E-commerce is the use of internet for marketing, identification,
payment and delivery of goods and services. Through the ecommerce
technology consumers haƂe the ability to bank, invest,
purchase, distribute, communicate, eplore, and research from
Ƃirtually anywhere, anytime where there is internet Access.

Fassara:
Kasuwanci a kan intanet shi ne amfani da kafar sadarwa ta intanet
domin saye ko sayarwa ko tallata haja ko biyan kuďaďe kamar na
sufurin kayayyaki duk a kan intanet. Haka kuma masu amfani da
hanyar kasuwanci a kan intanet suna da damar yin hulďa da banki
da yin dillanci da saka hannun jari da gudanar da bincike kan hajoji
a ko’ina suke a duniya kuma a kowane lokaci matuƘar suna da
damar amfani da intanet.

https://www.amsoshi.com/2017/09/27/jagora-ga-amfani-da-intanet-don-bunkasa-harshen-hausa/

Wannan bayanin ya nuna cewa ana iya cin gajiyar intanet ta hanyar gudanar da
kasuwanci ba tare da an ďauki lokaci zuwa kasuwa ko kantuna ba. Mai amfani da intanet zai iya
yin zaune a gidansa ya yi cinikin duk abin da yake buƘata, ya biya kuďi, kuma a kawo masa abin
da ya saya har Ƙofar gidansa. Ƙasashen nahiyar Turai da dama sun daďe da fara morewa irin
wannan ci gaban. Kodayake dai wannan ci gaban babban baƘo ne a Ƙasar Nijeriya. A halin
yanzu wannan hanyar kasuwancin ta fara samun kulawa a Ƙasar nan. Ayo da wasu (2011) sun
tabbatar da cewa a Nijeriya akwai shafuka aƘalla guda huďu waďanda suke ba da damar amfani
da wannan kafar ta kasuwanci. Alal misali akwai shafuka kamar: www.234world.com da
www.ďtaples.net da www.booksng.com da www.oderbay.com. Kodayake wannan bincike ya yi
ƘoƘarin ziyartar waďannan shafuka, amma abin ya ci tura. Saboda haka wannan bicike ya kawo
wasu shafuka waďanda ake iya gudanar da hulďar kasuwanci ta intanet da su. Ga shafukan kamar
haka: www.konga.com da www.jumia.com.ng. Duk da kasancewar irin wannan ci gaban yana
kusa da al’ummar Hausawa, hakan bai sa Hausa ta yi wani abin a-zo-a-gani ba ta wannan
Ƃangaren na kasuwanci a kan intanet. Saboda haka wannan bincike yana kira ga manyan ‘yan
kasuwa na Ƙasar Hausa, musamman waďanda suka mallaki manyan kantuna, da su dubi yiwuwar
shiga sha’anin kasuwanci na intanet.
Sha’anin kasuwanci a intanet ba nan kaďai ya tsaya ba. Ayo da wsu (2011) sun bayyana
cewa, ta amfani da intanet ana iya gudanar da wasu harkokin kasuwanci daban-daban, kamar
biyan kuďaďe ta intanet (e-payment) da hulďa da banki da intanet (e-banking) da kuma yin
rinjista ta intanet (e-registration). Ga Ƙarin bayani a kan kowace hanya daga cikinsu:

3.2.1 Biyan Kuďaďe Ta Intanet (e-payment)


Kenny, (2003) ya bayyana cewa intanet ta kawo sauƘi Ƙwarai ga harkar biyan kuďi a
wannan zamani. Misali, a halin yanzu ana iya biyan kuďin haraji na gwamnati; ko biyan kuďaďen
amfani kamar na hotel da kuďin lantarki na PHCN da kuďin haya; ko biyan kuďin tikitin jirgin
sama da wasu kamfanoni duk a kan intanet. Bayanan da wannan muƘala ta samu daga shafin
www.firs.goƂ.ng (2013) sun bayyana cewa, mai amfani da intanet zai iya shiga wannan shafin
domin biyan kuďinsa na haraji. Wannan adireshi na shafi Federal Inland ReƂenue Service (FIRS)
ne wato Hukumar Tara Kuďaďen Shiga na cikin Ƙasa. Bayanin ya nuna cewa tun daga farko sai
an ziyarci ofishin FIRS an yi rijista da su. Bayan ka yi rijista, za su ba ka lambar da za ka riƘa
yin amfani da ita duk lokacin biyan kuďin haraji. Wannan lamba ita ake kira Taď Identification
Number (TIN) da Ingilshi, mun ari sunanta muka fassara shi da Lambar Tantance Biyan Haraji.
Daga nan sai ka ziyarci shafin nasu mai adireshin da muka kawo a sama domin ci gaba da biyan
kuďinka na haraji kan intanet.
Mai amfani da intanet zai iya ziyartar shafin hotel ko na wani kamfani da yake haya da su
domin biyan kuďin hayarsa. Alal misali, mai bincike ya ci karo da wani bayani a shafin
www.tolet.com.ng (2013) kan yadda mai amdani da intanet zai iya biyan kuďinsa na haya a kan
intanet. Kodayake wannan kamfani yana samar da gidajen haya ne ga mazauna garin Abuja da
Lagos kawai, saboda haka sai mazauna waďannan garuruwa ne za su iya more wannan damar ta
biyan kuďin haya a kan intanet. Bayanin ya farad a cewa, tun daga farko sai an yi rijista da
wannan kamfani a shafinsu na intanet. Bayan an yi rijista, ana iya shiga shafinsu domin dudduba
gidajen haya waďanda ke ƘarƘashin kulawarsu a wannan lokaci. Idan ka samu gidan da ya yi
daidai da ra’ayinka da kuďinka, sai ka zaƂe shi domin ganin dukkan bayanansa. Idan bayanan
sun yi maka daidai, sai ka wuce shafin da za ka biya kuďin hayar. Kurbalija (2010) ya yi Ƙarin
haske a kan irin wannan hulďa, ya bayyana cewa irin waďannan shafuka suna karƂar biyan
kuďaďe ta amfani da MasterCard da kuma ƂisaCard, kuma a shafukan nasu za ka shigar da
lambar katinka ta MasterCard ko ƂisaCard da kuma sauran bayananka na banki. Daga nan za su
tuntuƂi bankinka domin tantance bayananka. Idan komai ya yi daidai, za su cire daidai kuďin da
ya kamata su cire. Daga nan sai a ba ka damar ka gurza shafin a matsayin rasitinka. Duk wannan
je-ka-ka-dawo ba zai wuce cin minti biyar ba in dai akwai kyakkyawan sabis na intanet.
Bugu da Ƙari, ana iya biyan kuďin sufuri na jirgin sama a kan intanet. Harkar sufuri ta
jirgin sama ita ce ta fi kowacce bunƘasa a sha’anin sufuri a nan Nijeriya. Kamfanonin sufurin
jirgin sama kamar Air Nigeria da Airik Air da Dana Air duk sun mallaki shafukan kansu a
intanet. Alal misali, mai tafiya zai iya ziyartar shafin kowane ďaya daga cikin shafukan
waďannan kamfanoni domin biyan kuďin tikitinsa. Alal misali, bayanan da mai bincike ya ci
karo da su a shafin www.arikair.com (2013) sun bayyana cewa ana iya biyan kuďin tikiti na jirgi
zuwa inda ake so a cikin Nijeriya a kan intanet. Idan aka shiga wannan shafin, a shafin farko ne
mai amfani da intanet zai zaƂi Ƙasar da yake. Idan aka zaƂi Nijeriya, sai shafinsu na Nijeriya ya
buďe. A cikin wannan shafi ne za a zaƂi lokacin da ake buƘatar tafiya da sauran bayanai. Daga
nan za a je shafin da za a biya kuďin jirgi. A wannan shafin ne za a buƘaci mai amfani da intanet
ya ba da lambar katinsa na MasterCard ko ƂisaCard da kuma lambar sirri. Daga nan za su
tuntuƂi bankinka domin tantance sahihancin bayanan da ka bayar. Idan komai ya yi daidai, za su
cire daidai kuďinsu. Shi kenan an kammala hadahadar, sai a ba ka dama ka fitar da takardar
tikitinka. Shi kenan an kammala biyan kuďin jirgi. Ita ma dai wannan hulďa ba za ta wuce cin
minti biyar ba idan akwai kwakkyawan sabis na intanet.
Abin lura a nan shi ne duk waďannan hulďoďi ko hadahadar kasuwanci ta intanet ba za ta
wuce cin minti biyar ba idan akwai kwakkyawan sabis na intanet. Kenan an taƘaita wa mutane
ďawainiyar tafiya shaguna ko kantuna ko bankuna ko wasu ofisoshin domin biyan kuďaďe na ireiren
waďannan huldoďi da muka ambata a sama. A nan, wannan muƘala tana ganin cewa idan
aka samar da wani Ƃangare na waďannan shafuka cikin harshen Hausa zai Ƙara bunƘasa cigaban
tattalin arzikin al’ummar Hausawa da kuma haƂaka harshen Hausa. kodayake wannan kaďai ba
zai yiwu ba sai ďalibai da manazarta da kuma masana Hausa sun ba da ta su gudummuwa wajen
bunƘasa keƂaƂƂun kalmomin intanet na Hausa. Sannan su kuma Ƙwararrun masu gina na’urorin
kwamfuta da intanet (software engineers and web programmers) su iya yin wani abu a harshen
Hausa. Kenan dai, har yanzu Hausa ba ta kai ga wannan matsayi na yin kasuwanci a kan intanet
ba.

3.2.3 Hulďa da Banki ta Intanet (mobile banking)


Kenny, (2003) ya bayyana cewa intanet ta kawo sabuwar hanyar tu’ammali da kuďi a
wannan zamani da muke cike. A yau mai amfani da intanet zai iya zamansa a gida, ya kuma biya
buƘatarsa ta mu’amala da kuďi tsakaninsa da banki ba tare da ya Ƃata lokacinsa zuwa bankin ba.
Mai amfani da intanet zai iya biyan kuďin cinikin da ya yi a kan intanet, kuma a kawo masa hajar
da ya saya har Ƙofar gidansa. Haka kuma, zai iya tura kuďi zuwa asusun wani a kan intanet. Zai
iya biyan kuďaďe kamar kuďin makaranta ko kuďin hotel a kan intanet. Babbar kasawar wannan
hanya ita ce rashin damar iya riƘe kuďi tsabarsu a hannu. Domin samun mafita ga wannan
kasawar, sai wasu bankuna suka buďe cibiyoyin gudanar da hulďar banki ta intanet (e-banking
centers). Waďannan tamkar harabar gudanar da hulďar banki ce, sai dai waďannan babu
ma’aikata a cikinsu. Da shigarka cikin ďakin za ka tarar da manyan injuna na ATM biyu ko uku
ko fiye da kuma kyamara (abin ďaukar hoto) a cikinsu. Amfanin kyamarar shi ne domin kiyaye
tsaro na masu shige da fice a cikin harabar. Na’urar ATM ita ce take ciro maka kuďi daga
asusunka na banki. Haka kuma za ka iya saka kuďi cikin asusunka ta wannan ATM. Za ka iya
tura kuďi zuwa asusun wani ta wannan ATM. Sauran hanyoyin amfani da ATM su ne biyan
kuďin lantarki na PHCN da sayen katin waya. Bayan wannan kuma, cigaban intanet ya kawo
cewa yanzu mai amfani da intanet zai iya yin hulďa ta banki ko’ina yake, matuƘar dai yana da
wayar salula ko tabileti (irin ipad da palmtop) wadda ke iya shiga intanet, sannan yana da sabis
na shiga intanet a na’urarsa. Wannan cigaba zai iya inganta tattalin arziki, domin an rega wa
jama’a wahalar kai-da-kawo zuwa banki ko ďakin ATM. Haka kuma, idan aka Ƙara bunƘasa
wannan hanya ta kai ga katse tankiyar da ke tsakaninta da harsunan Nijeriya, ba Ƙaramin sauƘi
cigaba za a samu ba. Alal misali, idan aka fassara hanyar hulďa da intanet ta na’urorin hannu
(mobile banking) zuwa harshen Hausa, ai ka ga da farko dole a tuntuƂi ďalibai da masana Hausa
domin yin wannan aiki; na biyu Hausa za ta Ƙara martaba kuma darajarta ta ďaukaka a kan
intanet.

3.3 Samar Da Ayyukan Yi


Manyika, da Roďburgh, (2011) suna da ra’ayin cewa intanet a yau ta kasance wata babbar
kasuwa mai samar da ayyukan yi ga jama’a. Aikin yi shi ne wani abu da mutum zai yi domin a
biya shi ladar aikinsa. A yau, akwai nau’o’in ayyuka daban-daban da ake aiwatarwa ko dai a kan
intanet ko kuma waďanda suka danganci intanet domin samun abin hannu. Morton (2006) ya
bayyana cewa daga cikin ayyukan da ake aiwatarwa a kan intanet akwai talla kan intanet (online
advertisement) da kula da kafar shiga intanet (network administration) da tsarawa da gina
shafukan intanet (web design) da kuma kula da intanet da hanyar sadarwa ta intanet (network
and web administration). Duk waďannan sababbin ayyukan yi ne da intanet ta kawo. Haka kuma,
Aliego da Aliogor (2010) sun bayyana cewa akwai harkokin tallace-tallace da intanet ta kawo
(online advertisement). Alal misali, ana tallata gurabun neman aiki na ma’aikatu da kamfunna a
kan intanet, ana kuma tallata kowace irin haja a kan intanet. Yanzu haka akwai shafuka dabandaban
da suka shahara a kan samar da bayanai na gurabun ayyukan yi a ko’ina a duniya. Misalan
waďannan shafuka su ne: www.jobberman.com (a Ƙasar Nijeriya) da www.careerbuilder.com (a
Ƙasar Amurka) da www.naukri.com (a Ƙasar Indiya). Bayan wannan, akwai wani samfurin talla a
kan intanet (online advertisement) wanda yake *****
A lura cewa waďannan hanyoyi na bunƘasa tattalin arziki da intanet ta kawo, an yi musu
bugun ďiyan kaďanya ne, saboda dukkansu a halin yanzu ba wanda ake aiwatarwa ƘarƘashin
Ƙwarewa da harshen Hausa. Wato ďaliban Hausa sai sun falka daga bacci sun rungumi karatun
wasu abubuwa game da kwamfuta da yawaita amfani da kwamfuta da sa kai cikin al’amurran
intanet sannan za su iya cin moriyar waďannan hanyoyi na bunƘasa tattalin arziki. Ya kamata
ďalibai su sani cewa, dukkan waďannan hanyoyi na samar da ayyukan yi masu tsoka ga ďimbin
mutune waďanda galibinsu ba Hausawa ba ne, ba ďaliban Hausa ba ne, sannan ba Hausa suke yi
wa aiki ba; saboda haka ayyukan da suke yi ba zai taimaka ga bunƘasa tattalin arzikin Hausawa
ba, ballantana a yi maganar haƂaka Hausa ko yayata ta.

4.1 Ƙalailace Bincike


A yau, amfani da intanet ya zarce duba imel (email) ko fezbuk (Facebook) ko was’af
(WhatsApp) Tuwita (Tweeter) da link’in (LinkedIn) da instagaram (Instagram) da sauran
shafukan sadarwa na walwala a kan intanet. Hanyoyi da aka tattauna kansu a cikin wannan
muƘala na bunƘasa tattalin arziki da suka haďa da hulďa da banki kan intanet (internet banking)
da kasuwanci kan intanet (e-commerce) da talla kan intanet (online advertisement) da kula da
kafar shiga intanet (network administration) da tsarawa da gina shafukan intanet (web design) da
kuma kula da shafukan intanet (web administration) duk hanyoyi ne na cin gajiyar intanet kuma
masu amfani. Ana iya amfani da kowace daga cikin waďannan hanyoyi kai tsaye ta amfani da
kwamfuta ko kuma wayar salula ko na’urar hannu (tabileti). Babban abin sha’awa game da
intanet shi ne ďauke wa mai amfani da ita wahalar tattaki zuwa biyan wasu daga cikin buƘatunsa
waďanda ake iya aiwatarwa ta amfani da intanet. Alal misali, intanet ta ďauke wa mai amfani da
ita yawon zuwa wasu shaguna da kantuna; intanet ta ďauke wa mai amfani da ita wahalar yawon
neman jaridu da mujallu; intanet ta sauƘaƘa wa mai amfani da ita ďawainiyar zuwa biyan kuďin
jirgi ko na lantarki ko na haya; intanet ta taimaka wajen samar wa wasu jama’a ayyukan yi;
intanet ta rage wa mai amfani da ita ďawainiyar yawon neman aiki, ga su nan dai. Waďannan duk
suna daga cikin cigaban da intanet ta kawo ta fuskar bunƘasa tattalin arziki; duk da yake dai ba a
fara damawa da Hausa a kan wasu Ƃangarori na cin gajiyar intanet, fatar wannan muƘala ita ce
zaburar da ďaliban Hausa da Hausawa domin su tashi tsaye su samar wa Hausa ‘yanci ta samu
mallakar wasu muhimman Ƃangarori na intanet. Wannan zai samu ne kaďai idan an waiwaya an
bunƘasa samuwar keƂaƂƂun kalmomin intanet da sha’anin kwamfuta da na ginin sofwayasofwaya
cikin harshen Hausa.

https://www.amsoshi.com/2017/08/22/duniyata-kashi-na-farko/

5.1 Shawarwari


Ta la’akari da bayanan da aka gabatar da abubuwan da suka biyo baya, wannan muƘalar
tana ganin cewa samun wadatattun keƂaƂƂun kalmomin intanet na Hausa zai taimaka wajen Ƙara
kawo gajiya ta intanet kusa ga al’ummar Hausawa. A kan haka, wannan muƘalar take ba da
shawarwari kamar haka:

1. Tsamo keƂaƂƂun kalmomi da taskace su wani jan aiki ne da yake buƘatar Ƙwarewa tare da
samun tallafi. Da farko dai dole malamai da hukumomin jami’a sun shiga ciki. Saboda haka
sai hukumomi da ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni sun ba da gudummuwa ƘwaƘƘwara
wajen ci gaba da bunƘasa taskace keƂaƂƂun kalmomi a sha’anin intanet.

2. Ya kamata attajirai da ‘yan kasuwarmu su yi nazari kan irin ďimbin ribar da ke cikin saka jari
a sha’anin sadarwar kwamfuta. Dalili kuwa shi ne, Ƙididdigar 2013 ta Forbes a shafin
www.forbes.com ta lisafo Mr. Bill Gates a matsayin ďaya daga cikin manyan masu kuďi na
duniya. Haka kuma a jerin masu kuďi ‘yan Ƙasa da shekaru 40 waďanda suka yi fice a
duniya, akwai mutane goma waďanda dukkaninsu suna tafiyar da harkokinsu ko dai a kan
sha’anin kwamfuta ko intanet ko kuma sadarwa ta zamani ne. Wannan yana nuna irin ribar
da ke cikin Ƃangaren kasuwanci na kwamfuta ko sha’anin intanet. Saboda haka ake ba da
shawara ga ‘yan kasuwa da su dubi yuwuwar saka jari a wannan Ƃangare.

3. Ya kamata Hausa Language Board (Hukumar Kula da Harshen Hausa) ta Ƙara tashi tsaye
domin tabbatar da daidaito a ƘoƘarin samar da keƂaƂƂun kalmomi a Hausa.

4. Masana da manazarta da ďalibai masu nazarin Hausa a kowane mataki su taimaka a bunƘasa
ire-iren wannan bincike. A Ƙara ƘoƘari domin tsamo wasu ďaruruwan keƂaƂƂun kalmomin
intanet na Hausa waďanda wannan bincike bai kawo ba. Yin haka zai Ƙara ďaga matsayin
harshen Hausa a sha’anin intanet da kwamfuta.

5. Ya kamata Hausawa su shiga cikin sha’anin nazarin fannin kwamfuta, su yi ruwa, su yi tsaki
a dukkan Ƃangarorinta.


6.0 Kammalawa


A wannan Ƙarni da muke ciki (Ƙarni na ashirin da ďaya), intanet ta riga ta shiga gaban
kowace hanyar sadarwa ta wannan zamani. A kan haka, wannan muƘala ta kammala da cewa
Hausa tana da haske a sha’anin intanet. Sai dai akwai Ƙalubale ga ďalibai da manazarta wannan
harshe, matuƘar suna son harshen ya ci gaba da haskakawa a duniya, dole ďalibai da manazarta
Hausa su dage wajen koyon amfani da kwamfuta da kuma intanet. Sannan su tashi tsaye a dama
da su a Ƃangaren amfani da intanet. Daga Ƙarshe, muƘalar tana kira ga ďalibai da manazarta
Hausa da su Ƙara ƘoƘari wajen amfani da intanet wajen taskace sahihan bayanai domin bunƘasa
bincike da nazarin harshen Hausa.

7.0 Manazarta


Aliego, J. E. da Aliogor, O. (2010). Total Free Browsing and Simple Ways to Make Money
Online. Enugu: De Joe Publication and Communication Limited.
Almajir, T. S. 2008. Hausa da Sadarwar Intanet. Harsunan Nijeriya, Vol. ďďI. CSNL - BUK,
Kano, Nigeria.
Amfani, A. H. 2007. “Globalization and Documentation of Nigerian Languages.” Paper
presented at the 21st Conference of Linguistics Association of Nigeria (LAN), University
of Uyo, Akwa Ibom State, Nigeria.
Ayo, C. K., Adewoye. J. O. and Oni, A. A. 2011. “Business – to – Consumer E-Commerce in
Nigeria: Prospects and Challenges.” cikin African Journal of Business Management. Vol.
5 (13). Pp. 5109 – 5117. A shafin http://www.academicjournals.org/AJBM DOI:10.5897
AJBM10.822
Becker, S., et al 2010. Opportunity for All: How the American Public Benefits from Internet
Access at U.S. Libraries. Washington, DC: Institute of Museum and Library Services. A
shafin http://www.tascha.washington.edu/usimpact.
Crystal, D. 2001. Language and the Internet. Cambridge: Cambridge University Press.
Illingworth, Ƃ. (ed.) 1996. Oxford Dictionary of Computing. New York: Oxford University
Press.
Kenny, C. 2003. “The Internet and Economic Growth in Less-developed Countries: A Case of
Managing Eďpectations?” a cikin Oxford Development Studies, Vol. 31, No. 1. Oxford:
International Development Centre. ISSN 1360-0818 print/ISSN 1469-9966
online/03/010099-15. DOI: 10.1080/136008103200004721.
Manyika, J. da Roďburgh, C. 2011. The Great Transformer: The Impact of the Internet on
Economic Growth and Prosperity. London and San Francisco: McKinsey Global
Institute.
Morton, F. S. 2006. “Consumer Benefit from Use of the Internet.” cikin Adam, B. J., Josh, L.
and Scott, S. (editoci). InnoƂation Policy and the Economy, Volume 6. available at:
http://www.nber.org/books/jaff06-1; http://www.nber.org/chapters/c0205
Muhammad, ď. 2004. “Hausa a Duniyar Yau: Tasirin Game Duniya Kan Harshen Hausa”. Cikin
Yalwa, L. ď. da wasu editoci (2011). Studies in Hausa Language Literature and Culture
– Proceedings of the Sixth Hausa International Conference – Center for the Study of
Nigerian Languages, Bayero University, Kano, 15th
– 17th December 2004. Zaria:
Ahmadu Bello University Press Limited.
Mwangi, J. 2014. “Open for Business? the Economic Impact of Internet Openness” daga shafin
http://www.dalberg.com ranar 1 ga watan Maris 2016.
Rumšiene. G. 2004. “Development of Internet English: Alternative Leďis, Syntax and
Morphology.” cikin KALBU STUDIJOS No. 6. ISSN 1648-2824.
SYBEX;. 2000. Dictionary of Networking. Sybex; – Alameda, CA. a shafin
http://www.sybex;.com.
Tsangarwa, A. M. 2006. Kwamfuta a SauƘaƘe. Kano: Dandalin Fagge.
Ureigho, R. J., Oroke, G. U. da Ekruyota, G. O. 2006. “The Impact of Internet Usage: A case
study of Delta State (Nigeria) Tertiary Institutions” cikin Scientific Research and Essay
Vol. 1 (2), Pp. 054 – 056. a shafin http://www.academicjournals.org/SRE.
Williams, C. da Strusani, D. 2014. Ƃalue of ConnectiƂity: Economic and Social Benefits of
Expanding Internet Access. Deloitte, London: The Creative Studio.
Manazarta ta shafukan intanet
http://www.wikipedia.org
www.jobberman.com
www.careerbuilder.com
da www.naukri.com
www.arikair.com
www.tolet.com.ng
www.firs.goƂ.ng
www.konga.com
www.jumia.com.ng
www.InternetLiveStats.com