Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Hausar Masu K’wallon K’afa A Cikin Garin Sakkwato

DAGA
Muhammad Mustapha Umar


Department of Nigerian Languages


Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto


Email: mustaphahausa@yahoo.com GSM: 08065466400


DA
Musa Shehu


Department of Nigerian Languages


Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto


Email: msyauri@yahoo.com GSM: 07031319454TSAKURE


Wannan bincike ya shafi karin harshen rukunin masu ƙwallon ƙafa a cikin garin Sakkwato. Wato binciken za a gudanar da shi ne don ƙoƙarin gano ainihin yanayin samuwar sauyi a sanadiyar zamantakewa, wanda ya haifar da Hausar masu sha’awar tamola. Domin tabbatar da samuwar wannan Hausar da ta sha bamban da ta wasu rukunan jama’a, za a yi amfani da kalmomi da sassan jimla, waďanda suka fi armashi da karƂuwa a idon magoya bayan ‘yan wasa ko kulob-kulob. Hanyoyin cim ma wannan ƙuduri sun haďa da: Ziyarar kai tsaye a filayen buga ƙwallon ƙafa da kuma gidajen kallon ƙwallo daban-daban da ke a cikin garin Sakkwato, domin ji kai tsaye daga bakin masu amfani da wannan Hausar, da kuma samun damar tattaunawa da su, domin tattara bayanai. Haka kuma, binciken ya gano cewa masu harkar ƙwallon ƙafa sun ƙware sosai wajen amfani da salon ƙirƙira sababbin kalmomi, ta hanyar faďaďa ma’anar kalmomin Hausa, da kuma Hausantar da kalmomin Ingilishi tare da sarrafa su ta yadda za su dace da tsarin Hausa mai mayar da ďan wani nata.

1.0 GABATARWA


Karin harshen rukuni ya samu ne sanadiyar bambancin aji ko matsayi ko jinsi ko muƙami ko kuma sana’a da ake samun a cikin zamantakewar al’umma. Kuma ƙarƙashin wannan kashi na karin harshe ake samun nau’o’i da dama, musamman abin da ya shafi Hausar rukunin jama’a masu ƙwallon ƙafa, mai matsayin wasa wadda ƙungiyoyi biyu masu ‘yan wasa goma sha ďaya (11) kowannensu, ke ƙoƙarin buga wani abu da aka yi da tsumma ko roba ko fata domin samun nasarar cin ƙwallo ko jefa ta a cikin gola. Ana gudanar da wasar tamola ko tawayya a filin buga ƙwallon ƙafa, tare da kulawar alƙalan wasa bisa wasu sharuďďa da ke yi wa ‘yan ƙwallon jagoranci. Kowace ƙungiya tana da masu horar da ‘yan wasa da kuma magoya bayansu. Da gangan na ƙi kawo tarihin ƙwallon ƙafa.

Farfajiyar binciken za ta tsaya ne a kan hanyoyi biyu da aka fi amfani da wannan karin harshe, wato duba yanayin samuwar Hausar masu buga ƙwallon ƙafa, yayin da suke wasar motsa jiki a filayen buga wasanni daban-daban, da kuma masu kallon ƙwallon ƙafa, yayin da suke kallon wasannin ƙwallo na cikin gida da na ƙasashen waje, musamman a gidajen kallon wasanni na kuďi, da kuma dandalin tattaunawarsu inda suke tabka muhawarori. Akwai kuma, dandalin zaman ma’abota wasanni da za a riƙa ziyara, domin jin hirar da suke yi, musamman bayan an dawo daga buga wasa, ko kuma bayan kammala kallon wata wasar kulob-kulob na ƙasashen ƙetare. Akasari a waďannan lokuta ake samun zafafar gardandami, da sharhi ko a dawa a kan yadda wasanni suka kaya, wanda ta haka ne ake samun samuwar kalmomi da dama da ake dangantakawa da masu ƙwallon ƙafa.

2.0 MATSAYIN ƘWALLON ƘAFA GA AL’UMMAR HAUSAWA


Ƙwallon ƙafa na ďaya daga cikin manyan wasanni da suka samu karƂuwa a duniya. Wannan dalili ne ya sa ake samun yara da manya na mayar da hankali wajen bugawa domin motsa jini ko kallonta ta talabijin domin nishaďi. Tsananin tasirin ƙwallon ƙafa ga masu sha’awarta ya haifar musu matuƙar shagala sosai, da kuma samun wasu Hausawa na amsa sunayen wasu ‘yan ƙwallo na cikin gida da ma na ƙasashen waje a matsayin laƙabinsu. Saboda haka, a wannan sashe za mu duba irin yadda Hausawan garin Sakkwato ke kallon ƙwallon ƙafa, ko mu duba irin matsayin da suka bata a wannan lokaci da muke ciki. Sai dai ya kamata mu san cewa; kamar yadda ake samun masu sha’awar ƙwallon ƙafa a cikin al’umma, haka ake samun ďimbin masu tsananin ƙiyayya da ita.

Ƙwallon ƙafa wata babbar hanya ce da mutane ke amfani da ita wajen motsa jikinsu, domin samun ingantacciyar lafiya da jin garau. A yau al’ummar garin Sakkwato sun ďauki yin ƙwallon ƙafa ko buga ta a matsayin nau’in atisaye. Saboda haka, wannan ne ya sa ake samun nau’o’in mutane masu buga ƙwallon ƙafa domin motsa jini kawai. Misali ana samun rukunin mutane masu ƙiba, ko babban ciki na rungumar wasar ƙwallo don kawai rage jikinsu. Ta wannan wasar sukan sami nasarar zubar da kitsen da ke tattare a jikinsu. Haka kuma, wasu daga cikinsu suna yin wasar ne domin samun ƙarfin jiki da kuzari. Domin likitoci sun ba da fatawar cewa; gudanar da wasar ƙwallon ƙafa ko zagayen filin ƙwallo ko kuma yawaita atisaye ko gudu, sukan taimaki jiki samun isassar lafiya da taimaka wa jiki ƙarin inganci.

Ƙwallon ƙafa a yau ta zama wata hanya da ake neman abincin kai wa ga bakin salati. Saboda mutane da dama sun riƙi ƙwallon ƙafa a matsayin sana’ar zamani, wadda ake iya dogaro da ita domin biya wa kai buƙatu na yau da kullum. Kamar kowace sana’a ita ma ƙwallon ƙafa sai an saka jari da kuma ƙwazo da himma wajen koyon dabaru wasar, tun daga mataki na ƙasa. Wannan ya sa ake samun ‘yan wasa da dama da ke ďaukar horo na musamman, a makarantun koyon ƙwallon ƙafa da ake samu a wasu ƙasashe na duniya. A taƙaice, babban abin da ya sa mutane ke tururuwa cikin harkar wasannin ƙwallon ƙafa, shi ne ana samun kuďaďe masu ďimbin yawa ta wannan hanya. A yau ‘yan ƙwallon ƙafa na ďaya daga cikin masu kuďin duniya, kamar dai yadda hasashe ya nuna.

A yau siyasar duniya ta taimaka ainun wajen bunƙasa sana’ar buga ƙwallo, domin akwai babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya da aka kafa domin haďa kan al’ummomin duniya. Aikin wannan ƙungiya shi ne alhakin kula da harkokin wasannin duniya. Wannan ya samar da tsarin gasar wasannin ƙwallon ƙafa, wanda ke farawa tun daga matakin cikin gida, da matakin nahiya har zuwa ga matakin duniya. Misali kowace ƙasa tana da ‘yan wasa masu wakiltarta, kuma gwamnatin ƙasar ita ke kula da albashin kowane ďan wasa, tare da lafiyarsa. Akwai kuma kulob-kulob da ke sayen ‘yan wasa domin samun nasarar lashe gasar da suke fafatawa. Sayen ‘yan wasa yana da matsayi tun daga matakin ƙasa zuwa nahiyoyi daban daban. Kuma kowane kulob shi ke biyan ďan wasa albashi da alawus-alawus da sauransu.

Wasar ƙwallon ƙafa na ďaya daga cikin manyan wasanni masu kawo sada zumunci tsakanin al’umma. Ana amfani da wasar ne wajen haďa kan ƙabilu daban-daban na duniya, musamman saboda bambancin wurin zama, ko harshe, ko addini ko al’ada ko sauran hanyoyin zamantakewar rayuwa. Misali, a da ƙasashe suna zaune cikin yaƙe-yaƙe da rashin zaman lafiya da matsananciyar gaba. Amma a yau wasar ƙwallo ta kasance hanyar sulhu da sasantawa tsakanin ƙabilun duniya. Saboda haka, muna iya cewa wasar ƙwallon ƙafa ta taimaka wajen rage ƙabilanci ko nuna wariyar launin fata, musamman saboda shirya wasannin sada zumunci, da kuma gasar cin kofin duniya da ta nahiyoyi daban-daban. Ga shi kuma hukumomin ƙwallon ƙafa sun tanadi hukunci daban-daban ga duk wanda aka sama da laifin aikata irin waďannan laifuka.

Idan kuma muka juya a Ƃangaren filayen buga wasanni za mu ga ‘yan wasar sukan fito daga ƙabilu, da addinai, da al’adu daban-daban, kuma abin ban sha’awa wasar kan Ƃatar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu har ana cewa suna zama abu ďaya. Misali, a kulob-kolob na ƙasashen waje da suka haďa ƙabilu daga ƙasashe mabambanta, za ga ka ‘yan wasa na rungumar juna, musamman bayan zura ƙwallo a raga, ba tare da nuna ƙyama ko wariyar launin fata. Su ma gidajen kallon ƙwallo mahaďa ce ta ƙabilu masu bambancin addinai daban-daban, amma saboda tarayyar goyon bayan wani kulob sai ka nemi bambance-bambancen da ke tsakanin ‘yan kallo ka rasa. Ko babu komi wasar ƙwallon ƙafa ta taimaka ainun ta wannan haujin.

Akwai Hausawan da suka ďauki ƙwallon ƙafa a matsayin abokiyar hira, domin takan taya al’umma hira ta hanyar rage lokaci ga masu bugawa ko masu kallon yadda take kayawa a cikin akwatunan talabijin. Haka kuma, muna iya cewa aba ce da ke ďebe wa ma’abota wasanni kewa. Sa’annan ƙwallon ƙafa ta zama sahun gaba wajen samar da shaƙatawa, musamman lokacin da rayuwa ke son hutu, bayan share dogon lokaci ana ayyuka barkatai. Wani abin armashi ga wasar ƙwallo shi ne ana samunta cikin kasakasan CD, da kuma cikin sigar wasannin gem da ake samu a kwamfuta da wasu wayoyin salula. A taƙaice, tagulla a wani ƙauli, ta taimaka wajen taya al’umma hira, musamman lokutan kaďaici, ko lokutan da babu ayyuka da yawa, kai ko lokutan da ake hutu da sauransu.

3.0 MATSAYIN GIDAJEN KALLON ƘWALLO A GARIN SAKKWATO


Gidajen kallon ƙwallo wurare ne da aka keƂe a cikin wani gida, ko shago ko kuma wani katafaren fili, domin gudanar da sana’ar watsa wasanni da ake biya kafin a kalla. Akasarin ƙwallayen da ake kallo a talabijin, ƙwallaye ne na ƙasashen waje, musamman ƙungiyoyin wasanni da ke Turai, da sauran ƙasashen duniya. Masu wannan sana’ar kan tanadi wuri, da wutar lantarki ko janareta, da manyan akwatunan talabijin, da tauraron ďan’adam ko dish, tare da sayen kati mai kawo dukkanin wasannin da ake buƙata.

Babban matsayin waďannan gidaje na kallon ƙwallo shi ne sana’ar zamani, wadda musamman ‘yan shekaru baya ake samun maƙudan kuďaďe a cikinta. Dalilin kiran ta sana’ar zamani bai wuce ganin daga baya ta kunno kai ba, kuma duk abubuwan da ta ƙumsa na zamani ne. Haka kuma, wannan sana’ar gidan kallon ƙwallo ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin garin Sakkwato, domin an sami yawaitar mutane cikin wannan sana’ar, sannan ana samun masu ƙanana sana’a’o’i suna caƂawa a duk lokacin da ake kallon ƙwallo. Misali, akwai masu sayar da ruwan sanyi, da rake, gasasshen nama, da ‘yan tireda, kai duk shagon da ke kusa da irin waďannan gidaje yakan sami ciniki, saboda yawan masu kallo. Kuma ana iya cewa wannan sana’ar ta rage zaman kashe wando, tare da samar da aikin dogaro da kai, musamman ga masu tsaro ko karƂar kuďi a gidajen kallon wasanni.
Akwai Ƃangaren jama’ar Sakkwato masu kallon ƙwallo saboda tana samar da nishaďi da annashuwa. Wato, akwai farin ciki tattare da ita, musamman idan wani abu ya faru na ban dariya, ko na burgewa, ko na al’ajabi ko kuma idan ƙungiyar da mutum ke goyon baya ta ci ƙwallo, ko ta yi nasara. Misali idan ana kallon ƙwallo a cikin unguwa, da zarar an ci wasa za ka ji kuwace-kuwace, da sowa da dare-dare masu nuna murna da jin daďi. A taƙaice, ma’abota kallon ƙwallo na haďuwa da raha da kwanciyar hankali, ko samun wadatar zucci a wasu lokuta.

4.0 ABUBUWAN DA KE HAIFAR DA HAUSAR MASU ƘWALLON ƘAFA


Haďuwar al’umma wuri ďaya, na cikin muhimman abubuwan da suka haifar da Hausar masu ƙwallon ƙafa, musamman saboda bambancin ƙabila ko addini. Wannan ya sa dole uwar na ƙi, ake samun karin harshen buroka a tsakanin masu buga ƙwallo ko masu kallonta a akwatunan talabijin. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne a sami ƙirƙirar sabbin kalmomi, waďanda sai wanda ke cikin rukunin ma’abota wasar ƙwallon ƙafa, ke iya fahimtar abin da ake nufi.

Adawa na nufin kushewa ko jin zafin wani da wani samu. Adawa na faruwa a wasar ƙwallon ƙafa yayin da aka ce ƙungiyoyi biyu sun haďu, saboda wasar sada zumunci, a yayin wata takara ko gasar lashe wani kofi ko kyauta. A irin wannan yanayi kowane sashe yana tsananin adawa da ďan’uwansu, domin kowa ya fi da son ya sami galaba. Su ma masu kallo ko goyon bayan ƙungiyoyin suna tsananin adawa da junansu, domin kowa ya fi son ƙungiyar da yake so ta yi nasara. A fagen masu ƙwallon ƙafa adawa na iya ďaukar zuwa kallon ƙwallon abokanin hamayya, da fatar ganin yadda za a lalla sa su. A taƙaice, wani lokaci akan dace a ci abokanin adawa, a yayin wata rana akan sami akasin haka, kuma wannan adawa ta taimaka wajen samar da Hausar masu ƙwallon ƙafa.

A Ƃangaren masu kallon wasanni, an fi samun adawa tsakanin magoya bayan babban kulob, musamman mai riƙe da kambu, ko kuma a tsakanin manyan ƙwararrun kulob-kulob, waďanda kowane daga cikinsu zakara ne, kuma yakan yi adawar ganin abokin hamayyar sa ya yi nasara komi zamanta ƙarama. A ko’ina ana samun wannan adawa, sai dai tafi ƙarfi a wasannin Turai, inda ake samun ma’abota goyon bayansu a garin Sakkwato. Tsananin adawa yayin kallo ƙwallo na haifar da sabbin kalmomi da ake dangantawa da masu ƙwallon ƙafa. Misali a ƙasar Ispaniya ana samun adawa tsakanin Real Madrid da Barcelona, a Ingila akwai adawa tsakani Manchester United da Arsenal, ko tsakanin Manchester United da Manchester City, sai a ƙasar Italiya inda ake samu adawa tsakanin A.C Milan da Inter Milan da sauran.

Tsokana na nufin jawo magana, ko yin wani abu da zai jawo hankalin wani, da zimmar Ƃata masa rai ko don tsokanarsa wasa. Sai dai, tsokana a nan tafi shafuwar yinta don nuna adawa. Masu kallon ƙwallon na amfani da wasu kalmomi don ci wa ‘yan adawa rai, ko don kawai a Ƃata musu rai, musamman idan ba su ke ci ba. Saboda haka, ta wannan hanya ce ake samun ƙirƙira kalmomi, waďanda suke samuwa sanadiyar wannan tsokana da ake yi tsakanin masu kallon ƙwallon ƙafa.

Yadda tsokana ke kasancewa a gidajen kallon ƙwallo kan faru ne, lokacin da ake lallasa wani kulob, ko kuma kulob yana wasa amma cin ƙwallo bai samu ba. A irin wannan lokaci ne tsokana ke kutsowa. Misali idan ana cikin wasa, sai aka ga wani daga cikin gwarzayen ‘yan wasa ya rage motsi ko taka leda, sai ka ji abokan adawa na cewa ruwa na malala, ko su yi ta faďin a shigo da wane, ko da yana cikin wasar. Idan kuma ana son a ba da tsoro ko tsokana ga abokan adawa, to duk lokacin kyamara da nuno layin ‘yan wasan da ba a saba, wato masu jiran canji ko ta kwana, sai ka ji ana cewa; benci na hayaƙi, ko kuma idan wani ďan wasa ya ji rauni, ko wanda ya yi likya-likya har ya nemi a yi canjinsa. A irin wannan lokaci za ka ji abokan adawa na cewa “sai ya ishe ta”. A taƙaice, haka waďannan kalmomi ko jimloli ke samuwa har su sami gindin zama a tsakanin rukunin jama’a ma’abota wasannin ƙwallon ƙafa.

Idan muka lura da kyau za mu ga dalilan adawa da tsokana suna cikin muhimman abubuwan da suka samar da Hausar masu ƙwallon ƙafa. Sai dai, sun bar baya da ƙura, musamman a shekarun baya da aka fi samun faďace-faďace da tashin hankali, waďanda ke haifar da samun raunuka da jikkitar wasu, kai wani lokaci har hasarar rayuka ake samu. Saboda kawai an ci ƙungiyar da wasu ke goyon baya, musamman idan an nuna musu adawa ko tsananiin tsokana, ko riƙa yi musu sowa ko dariya a kan rashin nasarar da suka yi. Wannan dalili ya sa a farko-farkon buga ƙwallon ƙafa da kallonta ake gayyatar jami’an tsaro, domin rage faďa tsakanin masu ƙwallon ƙafa, amma da tafiya ta yi tafiya an sami wayewar kai da fahimtar juna, inda a yau an rage samun tashin-tashina a gidaje kallon ƙwallo da filayen da ake buga wasanni.

Nishaďi wani abu da ke faruwa cikin zukatan al’umma, ta hanyar nishaďi mutum ke iya bayyanar da abin da ke cikin zuciyarsa, musamman na farinciki, tare da yin fara’a. Saboda haka, dangantakar nishaďi da wasar ƙwallon ƙafa wata alaƙa ce da ke bayyana Ƃaro-Ƃaro lokacin aka sami abubuwan burgewa ko na taka leda kamar haka; yin yanka gwanin ban sha’awa, tare da yin wani sitayil, ko zura ƙwallo ta amfani da salon da zai ƙayatar, ko yin fasin ko riƙa raba ƙwallo yadda ya kamata. Duk waďannan suna sa a sami nishaďi da jin daďi, musamman masu kallo kan tashi tsaye suna kuwa, suna murna, kai wani lokaci har da zage-zage don nuna jaruntaka da dai sauransu. Su ma ‘yan kallo kan ba junansu dariya saboda faruwar wani abu cikin wasar da ake kallo. A taƙaice, ƙwallon ƙafa tana samar da nishatantarwa a cikin al’umma a garin Sakkwato, musamman a tsakanin masu sha’awar wasanni.

6.0 MATSAYIN HAUSAR MASU ƘWALLON ƘAFA GA DAIDAITACCIYAR HAUSA


Hausar masu ƙwallon ƙafa karin harshen Hausa na rukuni ne, kuma karin harshen Hausa na rukuni mataki ne na biyu cikin rabe-raben karin harshen Hausa. Dalilin mu a nan shi ne, Hausar masu ƙwallon ƙafa yanayi ne na samar da sababbin kalmomi da sarrafa harshe wanda ya bambanta da yadda wasu rukunoni na al’umma ke amfani da harshen Hausa, sai dai kamar kullum ana samun fahimta tsakaninsu.

Matsayin Hausar masu ƙwallon ƙafa a cikin harshen Hausa, shi ne karin harshe ne da wasu keƂaƂƂun rukunin jama’a ke amfani da shi a cikin al’ummar Hausawa. Wannan karin harshe ne da ya samu sanadiyar zamani, kuma tuni ya sami gindin zama a cikin harshen Hausa, saboda kasancewar wasu rukunin jama’a na riƙa jefa ire-iren kalmomi ko jimlolin ƙwallon ƙafa, musamman yayin da ake magana ko zantawa. Har ila yau, wannan karin harshe ya ba da gudummuwa wajen bunƙasa harshen Hausa, wato dai Hausar masu ƙwallon ƙafa ta taimaka wajen haƂaka Hausa, musamman saboda sauye-sauyen da ta haddasa a cikin Hausa. A taƙaice, muna iya cewa harshen Hausa ya amfana ta Hausar masu ƙwallon ƙafa, ta fuskar ƙari da aka samu na nau’in Hausar rukuni, da haƂakar kalmomi da jimlolin Hausa da dama.

Kamar yadda harshe ke yaďuwa, haka shi ma wannan karin harshe na Hausar masu ƙwallon ƙafa ke yaďuwa. Saboda haka, Hausar kan fara ne daga mutum ďaya zuwa biyu ko fiye, a musamman filayen da ake buga ƙwallo ko gidajen kallon ƙwallo da ke birjik a cikin garin Sakkwato. Yaďuwa a nan kan kasance ta daga mutum zuwa mutum ko daga rukunin jama’a zuwa wani rukuni. A mafi yawan lokuta, an fi ďaukar Hausar tare da yaďa ta a wuraren buga ƙwallo, ko wuraren da ake hidimar kallonta har zuwa mahaďar matasa ko majalisarsu.

Kamar yadda aka al’adanta, matasa kan zauna a majalisu inda suke hirar ƙwallon ƙafa, musamman a lokutan kakannin wasannin duniya. Ta haka irin waďannan kalmomi da jimloli ke game ko’ina gwargwadon hali, musamman a muhallan bincikenmu. Tamkar karin harshen Sakkwatanci Hausar masu ƙwallon ƙafa ta game saƙo da lungu cikin garin Sakkwato.

7.0 HAUSAR MASU ƘWALLON ƘAFA A CIKIN GARIN SAKKWATO


Hausar masu ƙwallon ƙafa Hausa ce da ake samu a tsakanin matasa a filayen buga ƙwallon ƙafa, wato wuri ne da ake kira filin wasa, inda ake buga ƙwallo a matsayin motsa jiki. Yayin gudanar da wannan wasa ake samun yawan amfani da salon magana, wanda ya jiƂinci yanayin wasar ƙwallon ƙafa. Misali riƙa ambatar sunayen da suka shafi ƙwallo, da fili, da ‘yan wasa da sauran yanaye-yanayen yadda ake gudanar da wasar. A Ƃangaren gidajen kallon ƙwallo kuwa, ana iya cewa wuri ne da aka shirya domin kallon ƙwallo, wadda ake bugawa kai tsaye, ko wadda aka riga aka kammala. A nan ma, lokacin kallon ƙwallo ake samu ma’abota kallo na jefa kalmomi ko jimloli, waďanda ke dacewa da yanayin yadda ‘yan wasa ke taka leda a cikin talabijin, ko sharhi irin na ďan kallo ko bayan fage.

Wannan Hausar masu ƙwallon ƙafa da ake amfani da ita a cikin garin Sakkwato ana iya cewa ta haďa da: Hausar masu ƙwallon ƙafa wadda ake yi tare da fahimtarta a cikin gari na yankin Sakkwato. Wato duk wanda ya fito daga wani yanki ba zai fahimci akasarin wainar da ake toyawa ba. Akwai kuma, Hausar gama-gari wadda ake samu a ko’ina a cikin Hausawa. Saboda mafi yawan waďannan kalmomin ƙwallon ƙafa na gama-gari an karƂe su ne daga harshen Ingilishi, don a yi amfani da su kai tsaye a cikin harshen Hausa. Sannan ana samun ƙago ko gano hanyar sarrafa harshe ko samar da Hausar da za ta dace da rukunin masu sha’awar ƙwallon ƙafa. Sai dai ana samun tarayya ta fuskar wannan ƙirƙira, inda ake samun amfani da wannan Hausar tsakanin masu ƙwallon ƙafa da ke zaune a wurare mabambanta a cikin ƙasar Hausa.

7.1 HAUSAR MASU BUGA ƘWALLON ƘAFA


Hausar masu buga ƙwallon ƙafa Hausa ce wadda masu buga ƙwallon ƙafa kan yi amfani da wannan karin harshe, yayin da suke hidimar buga ƙwallo a filayen wasanni daban-daban. Ko kafin fara wasa, lokacin da ake shirye-shiryen farawa za ka iske matasan na hasashen yadda za su motsa jikinsu, ko bayan an kammala ta, inda ake samun sharhi na yadda wasar ta gudana, da kuma shirya wa wasa ta gaba lokutan tirenin. Wani lokaci ma idan ana zaune a majalisa akan riƙa hirar yadda wasar yau ko ta wani lokaci ta kaya, tare da fashin baƙin matsaloli da nasarorin da aka samu, da ƙoƙarin fito da hanyoyin gyara ko na ci gaba da farar anniyya.

Abin ban sha’awa da wannan Hausar masu buga ƙwallon ƙafa shi ne, suna amfani da ita a cikin harkokinsu na al’amurran rayuwa, sai dai ba kowa zai fahimci ma’anar ire-iren waďannan kalmomi ba, sai wanda ke cikin rukunin masu abu. Sai dai ya kamata a san cewa, ana samun jama’a masu sha’awar zuwa kallon masu buga ƙwallon ƙafa a filayen wasa, domin ďebe wa ido ƙeya.

7.2 HAUSAR MASU KALLON ƘWALLON ƘAFA


Wannan sashe ya ƙumshi tsokaci ne kan Hausar masu kallon ƙwallon ƙafa, yadda take samuwa da yadda ake sarrafa ta a gidajen kallon ƙafa, ko majalisun samari daban-daban da ke cikin garin Sakkwato. Wannan karin harshe yana samuwa ne kafin a fara kallon wasa, inda kowane mai goyon baya zai tofa albarkacin bakinsa a kan yadda wasar za ta kasance. Sai dai, idan an fara kallon wasar, lokaci ne da ake samun tsananin adawa, nuna goyon baya, da riƙa jefa kalaman tsokana ko na wasa kai, musamman idan ana kan nasara. Sai babban lokacin gardandami bayan an gama kallon wasar, wanda ke haifar da hirar ƙwallo a duk inda aka ga gungun matasa. Irin wannan lokaci ne magoya bayan ƙungiyoyin da suka fafata ke bayyana ra’ayoyinsu a kan rashin adalcin da aka yi wa wani Ƃangare, ko nuna jin daďi ko rashin jin daďin yadda ƙwallon ta kaya.

Ita ma wannan Hausar masu kallon ƙwallon ƙafa kamar takwararta da ake yi a filin buga ƙwallo, ana samun ma’abota kallon wasar ƙwallon ƙafa na tsarma ta a cikin maganganunsu na yau da kullum, musamman idan sun haďu da junansu. Sai dai shi ko duk wanda bai tu’ammuli da harkar kallon ƙwallon ƙafa ba zai fahimci wainar da ake toyawa ba, balantana ma har ya kama tasha. A taƙaice, ga muhimman kalaman Hausar masu kallon ƙwallon ƙafa, kamar yadda aka kalato a bakunan ma’abota kallon wasanni, da waďanda aka ci karo da su a gidajen kallon ƙwallo a cikin garin Sakkwato.

JADAWALI MAI NUNA HAUSAR MASU ƘWALLON ƘAFA A CIKIN GARIN SAKKWATO


Lamba Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa Ma’anarta
1 Wacce ku ci mu Ramuwar zura ƙwallo ta nan take, bayan an fara zura wa gefen da ya rama ƙwallo
2 Ƙyare ko wasiƙa ko saƙo Ingantaccen kurosin, ko bugun sama da zai kai ga wanda ake so ya karƂa
3 Katanga Jeruwar ‘yan wasa, a matsayin kariya ga gola ko mai tsaron gida, idan za a buga firikik
4 Mai kan jaki/ tururuwa Ruud van Nistelrooy lokacin da yana buga wa ƙungiyar Manchester United
5 Ya sa kai ďan wasa ya ja ƙwallo da gudu
6 Akwai ƙura Nuni ne a kan fafatawar manyan ƙungiyoyin ƙwallo
7 Osi Zura wa ďan wasa ƙwallo ta ƙarƙashin ƙafafunsa
8 Suka Buga ƙwallo da cikin faruttan ƙafa
9 Kora Kai wa abokan karawa hari na ba zata
10 Kwante Ragowar ƙwallo da aka jinkirta bugawa
11 Yau akwai zama Akwai kallon ƙwallo ke nan
12 Záárìyáá Sunan da ake yi wa Gerrad Pique ďan wasar Barcelona
13 Kullu yaumin hasara Sunan da aka riƙa yi wa Real Madrid tlokacin da suka rage kuzari
14 Ga ci ga yanka Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da ke ƙasar Ispaniya
15 Kanikawa Ƙungiyar wasar ƙwallon ƙafa ta Chelsea da ke ƙasar Ingila
16 Cehwane Sayen sabbin ‘yan wasa
17 Agogo Ɗan wasa ya zagaya da ƙwallo
18 Ya yi mai taggo da wando Obahed, ko jallabiyya ko a yanke mutum ta sama, ta hanyar buga ƙwallo ta tsallake kansa
19 Ɗan na farce Messi ďan wasan Barcelona
20 Jahili ne Ɗan wasan da bai iya ba
21 Kare shi, ko tashi da shi Mai tsaron gida ya hana wucewa
22 Ya buga mai su Wasa da ƙafafu, ko yin wala-wala da su, bayan ďan wasa na riƙe da ƙwallo a tsakiyar ƙafafunsa, don kawai ya samu yanke wani, ko wucewa da ƙwallo ba tare da wata tangarďa ba
23 Ja shara Ɗan wasa ya ja ƙwallo daga tsakiya yana yankan abokan takara
24 Sun ba da ƙwaya Sun ba ri an cinye su, ta hanyar karƂar maki uku daga gare su.
25 Ku biďi ƙwaďďo ‘Yan wasa su nemi cin gwal
26 Ku biďi tsaro A yi difendin gem, a buga ƙwallo tare da tsare gida, kuma ba a damu a je a zura ƙwallo ba
27 Ruhe Lokacin da wani Ɗan wasa ya yi shot, ko ya buga ƙwallo da ƙarfi don neman gwal
28 Ana tare Masu kallon ƙwallo su yi tarayyar kulob wajen goyon baya, ko a sami haďin guiwar goyon baya tsakanin ƙungiyoyi biyu mabambanta. Misali, Barcelona da ke Ispaniya suna abota da Manchester United da ke Ingila. Su kuma Real Madrid na Ispaniya suna abota da ‘yan Arsenal da ke Ingila
29 Dodon raga Ronaldo na Brazil
30 Gyado Ronaldo ko Ronaldinho ‘yan wasar ƙasar Brazil, ana yi musu wannan suna ne saboda fitowar haƙoransu na sama
31 A ci gaba da gashi A ci gaba da matsa lamba, ko lallasa abokan fafatawa
32 Kahirrai masu kurus Ƙungiyar Barcelona, wanda bajensu ked a ratsin kurus
33 Ba a tare Idan Ɗan wasa ya zura ƙwallo a raga, sai ya yi alamar kurus don nuna jin daďinsa, a nan masu goyon bayansu kan ce ba a tare.
34 Ɗan sarauniyar Ingila Wayne Rooney ko Ɗan wasan ƙungiyar Manchester United
35 Golan duniya Iker Casillas golan ƙungiyar Real Madrid.
36 A ruhe ƙohwa Idan an ci wani kulob, kuma magoyon bayansa suna fita kafin a gama, ko a bushe.
37 Sai ya ishe ta Ɗan wasa ya nemi a sauya shi, saboda gajiya ko samun rauni.
38 Za a coke baya Za a ďinke Ƃara ko giƂin da kulob ke fuskanta a wani Ƃangare yayin da ake buga wasa.
39 Ya tunhwaye ta, ya ishe ta Cin ƙwallo bayan gola ya yi amai.
40 Ta ďanyace Ramuwar cin ƙwallo da za ta sauya galaban wani Ƃangare zuwa matakin daidai kafin a tashi daga wasa.
41 Ya yi odiye ko ya ci gida ‘Yeskwaba Ɗan wasa ya zura ƙwallo ragarsu bias kuskure
42 Kawo Tsakiyar filin wasa, inda ake ďora ƙwallo idan za a fara wasa ko idan an ci ƙwallo
43 Yaji Sunan da ake yi wa Pepe ďan wasar Real Madrid
44 Ɓarawon gola A bar ďan wasa shi kaďai cikin gidan da ba nasu ba, sannan a bashi ƙwallo
45 Ku ja layi A tsare gida a hana kowa wucewa zura ƙwallo
46 Ya riƙe shi Wani ďan wasa ya hana abokin karawarsu shaƙat ko samun walwala a cikin wasa
47 Ga Mesin nan bayanku, ko ga Ronaldo nan bayanku. Ma’abota kallon ƙwallo kan tsokani junansu, musamman kafin buga ƙwallon adawa tsakanin Real Madrid da Barcelona
48 Gidauniya Cin gwal mai yawan adadin gaƂoƂin sunan wani kulob

JADAWALI MAI NUNA HAUSAR MASU ƘWALLON ƘAFA TA GAMA-GARI


Lamba Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa Ma’anarta
1. Turoyin Jifar ƙwallo da hannu
2. Kwánàà Bugun gefe
3. Fyanariti Bugun daga kai sai mai tsaron gida ko gola.
4. Gola Mai tsaron gida, ko raga, ko inda ake cin ƙwallo
5. Kohi Kofi ko kyautar da ake ba ƙungiyar da ta yi nasarar lashe wata gasa
6. Gwal Zura ƙwallo cikin raga
7. Fawul Laifi ko saƂa ƙa’idar a wasar ƙwallon ƙafa
8. Ofsayid Shiga gidan abokan karawa ba bisa tsari ba. Wato ďan wasa ya kasance ba tare da kowa ba, ko ya wuce wanda suke tare sannan a bashi ƙwallo, satar fage
9. Firikik Bugun kyauta da ake ba waďanda aka yi wa sharri ko ƙeta
10. Yalokad Katin jan kunne ko na kashedi da ake ba wanda ya yi laifi a cikin wasa
11. Difendin gem Buga ƙwallo tare da tsare gida, kuma ba a damu a je a zura ƙwallo ba
12. Akuro Cirawa sama a buga ƙwallo ta baya, wanda zai sa mutum ya faďi rairan
13. Hedin ko sa kai Nusar ƙwallon sama da gaban goshi, ko bugu-da-kai
14. Obahed Jallabiyya ko a yanke mutum ta sama, ta hanyar buga ƙwallo ta tsallake kansa
15. Kurosin Buga ƙwallo sama a gidan abokan karawa, da zimmar ta kai ga ďan wasan gefenku
16. Lasiman/lasman Mataimakin alƙalin wasa, mai ďaga tuta idan wani abu ya faru a cikin fili
17. Ya yi firi Ɗan wasa riƙe da ƙwallo daga shi sai gola ko mai tsaron gida
18. Ya kashe gwal Ya kasa zura ƙwallo cikin raga
19. Tirenin Horar da ‘yan wasa, ko koyon ƙwallo, ta hanyar motsa jiki
20. Kwata-fainal Wasar kusa da wadda ke kusa da ƙarshe
21. Sami-fainal Wasar kusa da ƙarshe
22. Fainal Wasar ƙarshe
23. Koc Mai horar da ‘yan wasa
24. Kaftin Shugaban ‘yan wasa
25. Difenda Ɗan wasan baya
26. Sitiraika Mai kai hari
27. Tim Ƙungiyar ‘yan wasa
28. Jassi/Jesi Rigar ‘yan wasa
29. Fasin Le
30. Fasin-fasin Yin yawo da hankalin ďan wasa ta hanyar hana shi karƂar ƙwallo
31. Rezin Riƙa buga ƙwallo sama da saman ƙafa ko ƙafa biyu bayan ana tsaye wuri ďaya. Ko hikimar sarrafa ƙwallo
32. Ongwal Ɗan wasa ya zura ƙwallo gidansu da kuskure
33. Duro Kunnen doki ko canjarar, wato ba wanda ya cinye wani, ko a ce kowa ya samu maki ďaya maimakon maki uku da ake ba kulob guda da ya yi galaba a kan ďan’uwansa
34. Tiri Point Maki uku
35. Basa Ƙungiyar Barcelona da ke Ispaniya.
36. Riyal Ƙungiyar Real Madrid da ke Ispaniya.
37. Manyu Ƙungiyar Manchester United da ke Ingila.
38. Fagi Mai horar da ƙungiyar Manchester United da ke ƙasar Ingila.
39. Tebur Jerin sunayen ƙungiyoyin ƙwallo da sakamakon gasa mai nuna kulob ďin da ke kan gaba da maki.
40. Lokal camfiyon Ƙungiyar da ba ta ďaukar kofi.

41. Wolbes Ɗan ƙwallon duniya mai riƙe da lamban girma ta shekara
42. Laliga Gasar cin kofi tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙasar Ispaniya
43. Firimiya Gasar cin kofi tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙasar Ingila
44. Siri’a Gasar cin kofi tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙasar Italiya
45. Ralageshon, sun tsunduma Rage darajar kulob daga babban mataki na gasa zuwa ƙaramin mataki, don ya kasa samun wani kaso na maki da ake buƙata
46. Camfiyon lig Gasar cin kofin zakarun Turai
47. ‘Yan ralageshon, ko sabbin yara Ɗaukaka darajar kulob daga ƙaramin mataki na gasa zuwa babban mataki, bayan kulob ya samun wani kaso na maki da ake buƙata
48. Fifa Taƙaitaccen sunan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya
49. General Gatuso Sunan da ake yi wa tsohon ďan wasar A.C Milan Gennaro Ivan Gattuso
50. Timba ko ya sha timba Buga ƙwallo ta daki gimshiƙan da ke riƙe da ragar gola, ba tare da ta shiga raga ba.
51. Hawa tebur, mun hau tebur Ƙungiyar da ta wuce kowa da yawan maki, ko hawa matsayi na farko da yawan maki
52. Kowa na nan, babu injuri Dukkanin ‘yan wasa suna cikinn ƙoshin lafiya, babu wanda ya ji rauni.
53. Ya hange gola Cin ƙwallo ta sama
54. An kai shi injuri Ɗan wasa ya yi raunin da zai hana shi buga ƙwallo na wani lokaci

JADAWALI MAI NUNA HAUSAR MASU ƘWALLON ƘAFA TA HAƊIN GAMBIZA (TA CIKIN GARIN SAKKWATO DA TA GAMA-GARI)


Lamba Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa Ma’anarta
1 Homa Ragar gola ko cin gwal
2 ‘Yan madara, ko madara, ko ‘yan babban gida Ƙungiyar wasar Real Madrid da ke ƙasar Ispaniya
3 Samba Iya raba ƙwallo daki-daki, tare da yanka
4 Ƙungiyar tsofaffi/ sanet Ƙungiyar wasar ƙwallon ƙafa ta A.C Milan da ke ƙasar Italiya
5 Kohi haram Ƙungiyar wasar ƙwallon ƙafa ta Arsenal da ke ƙasar Ingila
6 Sun ba da gari Lokacin da wata ƙungiyar wasa suka kasa kamo abokan adawarsu bayan sun ba su ratar maki
7 An wanke mai kashi, ko an yi mai tsalki Yi wa ďan wasa osi, ko zura wa ďan wasa ƙwallo ta ƙarƙashin ƙafafunsa
8 Ya je sayen kayan miya An yanke shi
9 Ya kashe mu, ko ya kashe gwal Ya kasa cin ƙwallo, bayan ya sami damar zura ta a raga
10 An yi muna PDP An yi rashin adalci ko an nuna son kai
11 Sun ji matsi Gana wa wata ƙungiyar ƙwallo azaba, ta hanyar yanka, da kai matsanantan hari, da shan timba
12 Ya hauta Ɗan wasa ya taki ƙwallo ya juya da ita
13 Kare shi, ko tashi da shi Mai tsaron gida ya hana wucewa
14 Ya auna shi, ko ya gwada shi Ɗan wasa ya kwarari gola ya fito, sai ya nemi cin ƙwallo daga nesa
15 Gida, ko gida muke Filin wasar ƙungiyar da ake goyon baya ake buga wasar
16 Waje muke, ko gidansu Ƙungiyar da ake goyon baya ta ziyarci filin abokan karawarta
17 Gida da daji, ko gida da waje, ko mun yi musu gida da daji An cinye abokan karawa gidansu, da gidan ƙungiyar da ta lallasa su
18 Bai da kai Ɗan wasan da ba ya sa kai ya doki ƙwallon sama
19 Ku zo mu tafi Ɗan wasa ya ja ƙwallo ya zura da gudu a bi shi
20 Ya ƙare Ɗan wasa ya gaji, ko kuzarinsa ya rage.
21 A sawo Messi, ko Ronaldo Tsokanar abokan takara lokacin wani Ɗan wasa yana ciki, amma bai aikin da ya saba yi ba
22 Igwai, ko sarki Henry lokacin da yana bugawa ƙungiyar Arsenal
23 Zuzu ko sarki Zidane lokacin da yana bugawa ƙungiyar Real Madrid
24 Ƙwallo ba ta sonmu A cinye ƙungiyar da ďan kallo ke goyon baya.
25 ‘Yan wasanmu ba su nan Wasu sun sami raunin da zai hana su buga ƙwallo.
26 Ya yi caca Buga ƙwallo daga nesa, don gwada sa’a, ko kutsawa cikin abokan fafatawa masu yawa, don ƙoƙarin wucewa da ƙwallo.
27 Ya sa shi talla A yi wa ďan wasa yankan walaƙanci har ‘yan jarida su riƙa nuna shi yayin share fage ko filin tallace-tallace
28 Ya aika shi/bodi Ruďin ďan wasa, musamman idan ana riƙe da ƙwallo za a yi kamar a yi dama da ya tafi, sai a yi gefen hagu.
29 Zan neme ka Alwashin samun nasara daga magoya bayan kulob-kulob a wata wasa da za a fafata.
30 Bushi Amfani da alƙalin wasa ke yi da mabusa wajen ba da umurni a cikin wasa
31 An bushe An tashi ko an kammala wasa
32 Hari Abokan karawa su ja ƙwallo da gudu rufe da ido, suna neman gwal
33 Le Ɗan wasa ya ba ďan gidansu ƙwallo, ba tare da abokin karawa ya karƂe ba
34 Sa ido Zuwa kallon ƙwallon abokanin adawa domin ganin yadda wasarsu za ta kaya
35 Ya hange Ɗan wasa ya yi ritaya daga buga ƙwallo ƙafa.
36 Yanka Hikima ko dabarar wuce ďan wasa da ƙwallo ba tare da ya karƂe ba
37 Ga ci ga yanka An cinye abokanin karawa, sannan an taka musu leda
38 Mamaya A mamayi abokan karawa, tun ba su shirya ba a buga firikik ko ƙwallo
39 Na saye Ɗan wasa ya shirya karƂar ƙwallon sama, musamma wadda za a tare da gaba
40 Ya yi kwáánáá Ɗan wasa ya rage kuzarin wasa kamar da.
41 Ya yi amai Gola ya kama ƙwallo ya saki, saboda ba ta kamuwa, sabili da zafin shot ko bugu

Waďannan jadawalai uku suna ďauke da wasu daga cikin kalmomi ko yankin jimla ko jimloli da ke haďuwa su samar da Hausar masu ƙwallon ƙafa a cikin garin Sakkwato. Ita wannan Hausar ta ƙumshi Hausar gama-gari wadda ake iya samu a mafi yawan garuruwan ƙasar Hausa, da kuma Hausa Basakkwaciya wadda ake amfani da ita a cikin garin Sakkwato kawai. Sai haďin gambizar Hausar masu ƙwallon ƙafa wadda ake hasashen ana amfani da ita a garin Sakkwato da wasu garuruwan ƙasar Hausa. Sai dai idan muka lura da kyau, za mu fahimci cewa wannan Hausar ta samu ne ta hanyar aron kalmomin harshen Ingilishi, ta hanyar yi musu kwaskwarima domin dacewa da tsarin harshen Hausa. Kuma waďannan kalmommin aro na ƙwallon ƙafa suna aiki cikin bambance-bambancen karin harshe tamkar yadda kalmomin asali ke fuskantar rabe-rabe, saboda kawai bambancin wurin zaman majiya harshe. Sannan kuma akan yi amfani da salon ƙirƙira ta hanyar ƙirƙira daga kalmomin asali ko hikimar faďaďa ma’anar kalmomin aro domin fassara abubuwa sababbi waďanda suka shafi ƙwallon ƙafa. Haka kuma, akasarin Hausar ta masu buga ƙwallon ƙafa, ita ce mataki na farko kafin samuwar Hausar masu kallon ƙwallon ƙafa. A taƙaice, an sami tasirin Hausar masu buga ƙwallon ƙafa a kan ta masu kallonta, saboda mafi yawan masu buga ƙwallon suna kallon ƙwallayen da ake nunawa, na musamman ƙasashen waje.

8.0 KAMMALAWA


Binciken da aka gudanar gudummuwa ce a kan karin harshen Hausar masu ƙwallon ƙafa a cikin garin Sakkwato. Bayanan da suka gabata sun nuna cewa akasarin masu buga ƙwallon ƙafa a garin Sakkwato, suna kallon ƙwallo a gidajen kallon ƙwallo, sannan ana samun waďanda ba su buga ƙwallo a filayen wasanni, kuma ba su zuwa kallon ƙwallo a filayen buga ta, amma sai ga su suna zuwa gidayen kallon ƙwallo. Saboda haka, muna iya cewa ana samun masu zuwa kallon ƙwallo saboda yayi, wai an ce lokacin abu a yi shi. Wayewar kai ya taimaka wajen rage faďace-faďace a tsakanin masu sha’awar bugawa ko kallon ƙwallon ƙafa, musamman kasancewar waďanda suka fi kowane mataki na cikin al’umma runguwar wannan yayin ƙwallon ƙafa matasa ne, kuma samari maza. Daga ƙarshe, muna fatar wannan maƙala ta buďe sabon babin gudanar da zuzzurfan bincike game da asalin Hausar masu ƙwallon ƙafa da abin da ya shafi dangantakarta da Hausar wasu wasanni na daban, tare da duba bambancin karin harshe sosai a cikin Hausar masu ƙwallon ƙafa.

Duba wata makala

https://www.amsoshi.com/2017/07/25/al%c6%99alami-ya-fi-takobi-nazarin-kaifin-al%c6%99alamin-malam-saadu-zungur-a-fagen-dagar-siyasar-nijeriya/

MANAZARTA


Bature, A. 1995. “Nazari kan Ƙirƙirar Sababbin Kalmomi a Hausa”, Babban Taron Ƙara wa Juna Sani na Biyar (5) kan Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa. Kano: Jami’ar Bayero.

Ɗantumbishi, M.A. 2003. A Study of Hausa Slang in Kano Metropolis: A Sociolinguistic Approach. Unpublished PhD Thesis, Sakkwato: Usmanu Ɗanfodiyo University.

Ɗantumbishi, M.A. 2004. “Harshe, Al’umma da Kuma Zamananci”: Takardar Ƙara wa Juna Ilimi da Aka Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Fage, U.U. 2002. Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Garba, S.A. 2010. Hausa a Gidan Rediyon BBC. Kundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Jamai’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Ƙaraye, M. 2003. Sabbin Kalmomi: Ingilishi Zuwa Hausa (Littafi na Ɗaya), Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.

Sa’id, B. (Ed.). 2006. Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sani, M.A.Z. 2003. Alfiyyar Mu’azu Sani 3: Karorin Harshen Hausa a Waƙe. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Sirajo, I. 2001. Hausar Kasuwanci: Yanayin Ƙirƙirar Sababbin Kalmomi a Kasuwar Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Farko. Sakkwato: Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Skinner, N. 1965. Ƙamus Na Turanci Da Hausa-English, Hausa Illustrated Dictionary (Babban Jagora Ga Turanci). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Ltd.

Umar, M.M. 2005. Kasuwanci da Muhimmancinsa ga Al’ummar Hausawa. Kundin Digiri na Ɗaya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Umar, M.M. 2012. Nazarin Saƙon G.S.M a Wayar Salular Hausawa. Kundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Jamai’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yakasai, S.A 2005. “Aro da Ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a da Kuma Garin Sakkwato”: Maƙalar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Yakasai, S.A 2007. “Dangantakar Harshe Da Al’umma: Nazarin Halaye Da Ɗabi’un Magana a Al’ummar Hausawa”: Maƙalar Da Aka Gabatar a Sashen Harsunan Asiya da na Afrika. Beijing: Jami’ar Koyon Harsunan Waje.

Yakasai, S.A 2010. “Dangantakar Harshe Da Muhallin Magana: Nazarin Kan Matakan Magana a Tsakanin Al’ummar Hausawa”. In Harsunan Nijeriya. Centre For The Study of Nigerian Languages, Bayero University Kano: Volume XXII, Pp. 78-84.

Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services.

Yule, G. 1985. The Study of Language: An Introduction. Australia: Cambridge University Press.

Post a Comment

1 Comments

Rubuta tsokaci.