Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Ƙarya Da Gaskiya: Nazarin Waɗansu Waƙoƙin Littafin Specimens Of Hausa

Daga

Umar Aliyu Bunza
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
07063532532, 08095750999

2014

1.0 Gabatarwa

Littafin Specimens Of Hausa Literature littafi ne da wani fitaccen ɗan leƙen asirin nan na Mishan, mai suna Charles Henry Robinson ya wallafa a shekarar 1896. Robinson Baingile ne da ƙungiyar Church Missionary Society ta tura zuwa ƙasar Hausa, a ƙarƙashin wata ƙaramar ƙungiya mai suna ƙungiyar Hausa, da aka kafa a shekarar 1891. Manufar kafa wannan ƙungiya ita ce, domin ta turo wasu jamiai zuwa ƙasar Hausa saboda tattara bayanai kan rayuwar Hausawa don shimfiɗa ayyukan yaɗa addinin Kirista.


A shekarar 1891 Robinson ya shigo ƙasar Hausa bayan da ya koyi magana da Hausa a ƙasar Tunisiya. Bayan Robinson ya shigo ƙasar Hausa sai ya sami damar yawata wasu manyan biranen Hausawa irin Kano da Zariya da wasu sassan biranen inda ya sami wasu rubutattun waƙoƙin Hausa da zuben rubutu na tarihin masarautar Zazzau ya yi amfani da su ya samar da littafin nasa. Waƙoƙin cikin littafin shida ne, kuma rubuce cikin Ajamin Hausa kan jigon addinin Musulunci. Robinson ya nuna wasu malaman ƙasar Hausa uku ne (Muhammadu Na Birnin Gwari da Limamin Ceɗiya da kuma Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo) suka wallafa waƙoƙin. Kowane malami Robinson ya jingina masa biyu daga cikin waƙoƙin.
Idan aka dubi yanayin waƙoƙin musamman ta fuskar jigo da zubin baituka, za a ga cewa, waƙoƙin sun yi kama ƙwarai da na malaman ƙasar Hausa na wancan lokaci na kafin mulkin mallaka. Ta wata fuska kuma, idan aka yi nazarin waƙoƙin aka kuma kwatanta su da na malaman, za a ga akwai illolin da za su kore rubuta waƙoƙin ga malaman da marubucin littafin ya kawo su a matsayin marubutan su.
Manufar wannan maƙala ita ce, nazarin waɗannan waƙoƙi ta fuskar tarihin adabin Hausa domin fito da illolin da ke raunana gaskiyar dangantakar malaman da waƙoƙin cikin littafin. Na fara da bayanin ƙunshiyar littafin da zubi da tsarin waƙoƙinsa sai kuma nazarin illolin danganta waƙoƙin ga waɗannan sanannun malamai.

2.1 Taƙaitaccen Bayanin ƙunshiyar Littafin Specimens Of Hausa Literature


Specimens Of Hausa Literature littafi ne da Charles Henry Robinson ya wallafa da nufin musanya abin da J. F. Schon ya gabatar a littafinsa na Magana Hausa na cewa shi ne na farko da ya fara samar da rubutu a harshen Hausa (Robinson, 1896). ƙunshiyar littafin Specimens Of Hausa Literature ta haɗa rubutattun waƙoƙin Hausa guda shida waɗanda Robinson ya danganta rubuta su ga wasu malaman ƙasar Hausa sanannu guda uku, sai kuma labari ɗaya wanda ya kawo a ƙarshen littafin. Kowane ɗaya daga cikin waƙoƙin da labarin an rubuta shi ne cikin Ajamin Hausa kafin daga baya Robinson ya juya su zuwa rubutun Hausar boko da kuma fassara cikin Ingilishi. Wannan ya sa littafin nasa yake ɗauke da ɓangarori guda biyu mabambanta.
A ɓangaren farko, tsarin rubutun boko ne na waƙoƙin da labarin wanda shi ne rubutun Robinson wanda ya yi na juya rubutun Ajamin na asali. Shi kuma ɓangare na biyu, shi ne rubutun Ajamin Hausa wanda shi ne rubutun asali na ƙunshiyar littafin. Dukkan waƙoƙin ba ko ɗaya da ke da wani suna da aka ba ta ko a farko, ko a cikin ta, ko kuma a ƙarshe.
Bayan aikin Robinson na tattara waƙoƙin da zuben da kuma juya su daga rubutun Ajamin Hausa zuwa rubutun boko, ya kuma yi sharhin ƙunshiyar baitocin kowace waƙa da kuma ƙunshiyar labarin daidai gwargwadonsa. Wannan ya sa sharhin nasa yake ƙunshe da shaci-faɗi masu yawa da ya haɗa har da kawo sunan wani malami a matsayin marubuci da faɗar jigon waƙa da sauransu.

3.1 Waƙoƙin Cikin Littafin Specimens Of Hausa Literature


Waƙoƙin littafin Specimens Of Hausa Literature waƙoƙi ne guda shida, kuma duka kan jigon addinin Musulunci. Robinson ya shirya waƙoƙin ta hanyar ba su lambobi na ‘ABCD’ na Hausa.

3.1.1 Zubin Waƙoƙin


An shirya waƙoƙin wannan littafi kan tsarin ƙwar biyu, sai dai akwai bambanci a yawan baitukan waƙoƙin da kuma tsarin ƙafiya.
Waƙa ta farko mai lamba ‘A’ an shirya ta cikin baituka 85 kuma a kan tsarin ƙwar biyu. Babu wani tsayayyen tsari a ƙafiyar wannan waƙa. Ga wasu kaɗan cikin baitukan waƙar;
Bismi na fara da yerdan maisama ka yi taimako a gareni zan tabba kokari.
Zanchen kiyama babu maikara nata sai ko ka che ka yi gargodonka na kokari.
Rana ya ki kuka da ruri maiyawa rana da ba cheto kudinsa dubu dari.
Duk ya uwana duk ku zo mu ji waatsi kulu musulmi ba rua alkafiri.

Waƙa ta biyu mai lamba ‘B’ an kawo baituka 174 nata, kuma bisa tsarin ƙwar biyu. Ita wannan waƙa ba ta da wani tsayayyen zubin tsari a ƙafiya. Ga wasu kaɗan cikin baitukan waƙar;
Bismi allahi farkon kalmata allahu akbar subhan allahi
Allahu la allah illa allahu muhammadu rasulu abin kamna
Jabaru wahidi sarki allah ubangijinmu maiyo maigobi
Allah ubangijinmu ni ki roko komi ni ki bida da bukatata
Allah shi tsarkaki mamu aikimu shi bamu hankali da basiratas

Ita kuma waƙa ta uku ‘C’ an kawo ta ne ɗauke da baituka 55 a kan tsarin ƙwar biyu. Babbar ƙafiyar wannan waƙa ita ce gaɓar sautin ‘ya’ da take ƙarshen kowane baiti. Ga kaɗan daga cikin baitukan waƙar;
Ya rabbi dan bawa laifi na barra domin ka tsarshani ga zanba dunia.
Zanbata da ta ruski masugudu nata balatana gurgu makafo dunia.
Ita kama mallamai berri ni jahili ya rabbi tarshan kadda ta kan mani dunia.
Ni ban sani ba bida ni kaina en samasa kowa yi aiki ba sani ya sunkwia.
Ita waƙa ta huɗu ‘D’ tana rubuce cikin baituka 101 kan tsarin ƙwar biyu. Ta fuskar zubin ƙafiyar waƙa, wannan waƙa ba ta kan wani tsari tsayayye na ƙafiya. Ga kaɗan daga cikin su;
Bismi allahi farawa na karatu suna ni na allah dakanan fara aiki
Ya allah rabbi ka bamu gamu katerta muna zikir muna addua muna sallati
Ya allah ya khaliku ya arziki bai ma’abudu ya rabbana sarki sarota
Waƙa ta biyar ‘E’ tana cikin baituka 52 kan tsarin ƙwar biyu, amma ba kan wani tsarin ƙafiya ba. Ga kaɗan daga cikin baitukan waƙar;

Mu godi ubangiji sarki sarota da ya aiko muhammadu dan amina
Muna zuba essallati bisa fiyaiyi da umatan muhammadu ya fi kowa
Ku sorara jama’a alkadirawa hallinmu da ankazana sai mu tuba
Ita kuma waƙa ta shida mai lamba ‘F’ tana da baituka 255, kuma kan tsarin ƙwar biyu da kuma daidaitacciyar ƙafiyar gaɓar sautin ‘wa’ a ƙarshen kowane baiti. Ga wasu baitukan waƙar;
Mu godi jalla sarki maiiyawa ta’ala jalla maiiyawa da kowa
Muna kuma yin sallati bisa muhammad da ali da sahibi da jama’u annabawa
Da tabii tabiina da waliau da malaku muna kuma salmawa
Fa baia shikawa sallatu da salmawa ku sorara jama’a alkadirawa

3.1.2 Jigon Waƙoƙin


Jigo shi ne manufar ko maƙasudi yin wani abu, ko ƙaga wani abu, ko tsara yin wani abu (Bunza, 2009). Waƙoƙin littafin Specimens Of Hausa Literature an shirya su bisa jigon addinin Musulunci ta hanyar wa’azi da gargaɗi da faɗakarwa. Ga misali waƙa ta farko jigonta shi ne wa’azi. An fara nuna jigon a baiti na 5 inda aka ce;
Duk ya uwana ku zo mu ji waatsi kulu musilmi ba rua alkafiri.
Tun daga wannan baiti marubucin ya ci gaba da wa’azi kan abubuwa daban-daban. Ita kuma waƙa ta 2 jigonta shi ne gargaɗi da faɗakarwa. Ya yi gargaɗin a baituka daban-daban. Ga misali,
Chiuta da jahili kanwa kai nai ko gobara ba yita don bannai
Ku yan uwa ku jinni ku saurara ku ber yawan dumi ku ji kalmata
Shi do guda guda ta tsiri mai domi ba angamusu atara ba
Shi wanda ke bida aljanna tas kun san ba shi kullata da dunia ba

Sauran waƙoƙin littafin duka kan irin wannan jigon aka shirya su. Idan aka dubi waɗannan waƙoƙi za a ga cewa, sun yi kama da waƙoƙin malaman masu jihadi musamman ta fuskar jigo da zubin baituka da kuma salo.

4.0 Tsakanin ƙarya Da Gaskiya A Waƙoƙin Littafin Specimens Of Hausa Literature


Duk da yake waƙoƙin wannan littafin sun yi kama da na malamai magabata irin su Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo da almajiransa da wasu da suka gabace su, akwai wasu muhimman abubuwa da za a iya lura da su masu nuna raunin gaskiyar jingina waƙoƙin ga waɗannan sanannun malamai na wancan lokaci. Muhimman abubuwan da aka duba masu nuna raunin da’awar dangantakar waƙoƙin da malaman sun haɗa da sunan waƙa, sunan mawallafi da lokacin rubuta waƙa (ramzi) da kuma ƙafiya.

4.1 Sunan Waƙa


A tsarin rubutattar waƙa musamman ta Hausa, suna muhimmin abu ne domin shi ne farkon abin da ake amfani da shi don gane saƙon waƙa. Kowace waƙar Hausa akan raɗa mata suna domin sauƙaƙa fahimtar ta da kuma jigonta kai tsaye. Marubuta waƙoƙi a ƙasar Hausa sun kasance suna ba kowace waƙa suna, wani lokaci har su ambaci sunan waƙar cikin baitukanta.
A ƙasar Hausa, tarihi ya nuna an fara samun waƙoƙi cikin Hausa tun a wajajen ƙarni na 17. Daga cikin malaman da aka kawo sunayensu akwai Sheikh Ahmad Tila wanda ya rubuta waƙar Jamuyah da Shi’ir Hausa. Akwai kuma Sheikh Abdulƙadir Tafa wanda ya rubuta waƙar Tarih El-Sudan. Sauran malaman sun haɗa da malam Wali Ɗanmasani an nuna shi ya rubuta waƙa mai suna Daliyya, da Nuniya da Waƙar Taba. Shi kuma Wali Ɗanmarina ya rubuta waƙar Sharhin Ishiriniyar Shehu Alfazazi
da Shi’a’ir Ruba. A
ƙarni na 18 nan aka sami Malam Muhammadu Na Birnin Gwari ya rubuta waƙoƙi kamar Waƙar Billahi Arumu da Waƙar Dumbula da Waƙar Kankandiro da sauransu. Malam Shi’itu Ɗan Abdurrahman ya rubuta Waƙar Tuba (Jimiyya) da Waƙar Wawiya (Yahaya, 1988).
Zamanin masu jihadi, malamai sun rubuta waƙoƙi masu yawa. Shaihu Usmanu shi kaɗai ya rubuta waƙoƙi da suka kai guda 25. Daga cikin su akwai Gargaɗi Ga Jama’ar Musulmi da Taulafin Sidi Abdulƙadir da Salati Guzurin Mumini A Lahira da Gargaɗi Da Tsoratarwa da Ma’ama’are da sauransu. Abdullahin Gwandu ya rubuta waƙoƙi 8. Cikin su akwai kamar Tunatarwa Ga Zuwan Mutuwa da Wa’azu Ga Sarkin Gobir Bawa da Tsarin Mulki na Musulunci da sauransu. Shi kuma Muhammadu Bello ya rubuta waƙar Hausa ɗaya mai suna ‘Yan Jihadi. Idan aka dubi kundin Sa’id (1978) za a ga cewa ya tattaro sunayen wasu malamai na wancan lokaci da waƙoƙinsu da ba su kasa 90 ba, kuma kowace waƙa tana da sunan da aka raɗa mata.
Idan aka dubi waɗannan misalai, sun nuna, waƙoƙin malaman ƙasar Hausa da suka rayu kafin zuwan Robinson kowace da sunan da ake kiran ta da shi.
Robinson ya danganta Waƙoƙin Littafin Specimens Of Hausa literature ga malamai uku kamar haka: Muhammadu Na Birnin Gwari da malam Halilu (wanda ya ce shi ne limamin wani gari Ceɗiya) da Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo. Duk da yake waƙoƙin ya jingina rubuta su ga malaman, amma ba ko ɗaya da aka ambaci sunanta ko a farko, ko kuma cikin baitukan waƙa. A maimakon suna sai aka ba kowace waƙa lamba wanda yake nuni ne kawai kan tsarin waƙoƙin daga ta farko zuwa ta ƙarshe. Ga misali,
A
Bismi na fara da yerdan maisama ka yi taimako a gareni zan tabba kokari.
Zanchen kiyama babu maikara nata sai ko ka che ka yi gargodonka na kokari.
Rana ya ki kuka da ruri maiyawa rana da ba cheto kudinsa dubu dari.
Duk ya uwana duk ku zo mu ji waatsi kulu musulmi ba rua alkafiri.

B
Bismi allahi farkon kalmata allahu akbar subhan allahi
Allahu la allah illa allahu muhammadu rasulu abin kamna
Jabaru wahidi sarki allah ubangijinmu maiyo maigobi
Allah ubangijinmu ni ki roko komi ni ki bida da bukatata
Allah shi tsarkaki mamu aikimu shi bamu hankali da basiratas

C
Ya rabbi dan bawa laifi na barra domin ka tsarshani ga zanba dunia.
Zanbata da ta ruski masugudu nata balatana gurgu makafo dunia.
Ita kama mallamai berri ni jahili ya rabbi tarshan kadda ta kan mani dunia.
Ni ban sani ba bida ni kaina en samasa kowa yi aiki ba sani ya sunkwia.
Idan aka yi la’akari da haruffan ‘‘A, B, C’’ za a ga cewa, suna waƙiltar jerin waƙoƙin ne kawai, amma ba suna ba. Da malaman ne da aka danganta waƙoƙin gare su suka wallafa su, tilas a sami sunan da suka raɗa wa kowace waƙa domin wannan tsari ne sananne a rubuce-rubucensu. Ke nan rashin raɗa wa ko ɗaya daga cikin waƙoƙin suna naƙasu ne ga gaskiyar kasancewar waƙoƙin na waɗannan malamai da aka jingina su gare su.

4.2 Sunan Mawallafi


Malamai marubuta waƙoƙin Hausa sau da yawa akan tsinci sunayensu a wajajen baitukan ƙarshe na waƙoƙinsu. Yawancin lokuta, malamin da ya rubuta waƙa yakan kawo sunansa cikin wasu baitukan waƙar, wani lokaci har ya nemi addu’a ga masu karatu. Wani lokaci kuma, akan sami wani cikin mabiyansa ya yi ƙari ga waƙar daga ƙarshe sai ya kawo sunan marubuci na asali, ya kuma haɗa da nasa. Irin wannan hikimar ta taimaka wajen sauƙaƙa gane waƙoƙin malamai daban-daban. Ga misali, a waƙar Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo mai suna ‘Kau Da Jita-Jita’ a baiti na 10 ya kawo sunansa a matsayin marubuci inda yake cewa;
Shehu yay yi ta kun jiya ‘yan uwana,
Don mu tuba mu bar abin nan haram na,
Kway yi tuba shi samu tsira ga ran nan,
Mu yi tuba ka ba mu tsira ga ran nan,
Don macecinmu Sayyidil-mursalina.

Shi ma Dikko Ɗan Bagine ya kawo sunansa a waƙarsa ta ‘Alamomin ƙarshen Duniya’ daga baitinsa na 60 zuwa na 61 inda ya ce;
Wane yai ta’alifin ga na ahiruz zamanu,
Muhammadu ɗan Hayyata fa na ahiruz zamani.

Idan ba ku san shi ku ce masa Dikko ɗan bagyane
Binu Salihi ɗan Geno Mallamin fannu.

Akwai wani malami mai suna Salihu Ɗan Zama shi ma yakan kawo sunansa a baitukan waƙoƙinsa. Ga misali, a waƙarsa mai suna ‘Jan Mari’ a baiti na 108 inda yake cewa;

Idan anka ce shin way yi waƙa ta gargaɗi,
Salihu ɗan Zama da Siddiƙu Abubakari.

Idan aka dubi waɗannan misalai sun nuna ƙarara ana cin karo da sunayen malamai a cikin waƙoƙinsu kamar yadda sunan Shaihu da Dikko Bagaye da Salihu ɗan Zama suka fito cikin wasu waƙoƙinsu.
Waƙoƙi shida na littafin Specimens Of Hausa Literature, Robinson ya ce malaman ƙasar Hausa uku ne suka rubuta su. Biyu daga cikin waƙoƙin masu lamba ‘A’ da ‘C’ ya kawo sunan malam Liman Ceɗiya a matsayin marubucinsu. Su kuma waƙoƙi masu lamba ‘B’ da ‘D’ ya nuna Malam Muhammadu Na Birnin Gwari ya rubuta su. Sauran waƙoƙin biyu masu lamba ‘E’ da ‘F’ ya kawo sunan Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo a matsayin marubucinsu.
Ko da yake sunayen waɗannan malamai Robinson ya kawo, za a ga cewa, babu wata hujja ƙwaƙƙwara da ya yi amfani da ita wajen kawo sunayen waɗannan malamai. Idan aka koma cikin baitukan waƙoƙin za ga cewa, akwai wasu baituka da ke nuna ba ko ɗaya daga cikin waɗannan malamai da ke da alhaki ga rubuta waƙoƙin.
Waƙa ta farko da ke cikin littafin mai lambar ‘A’ da ta uku ‘C’ Robinson ya kawo cewa Liman Ceɗiya ne ya rubuta su. A cewarsa, Ceɗiya wani gari ne da ke tsakanin garin Kano da garin Bauchi inda kuma nan ne malamin ya rasu a wajajen shekarar 1866. Ya nuna waƙa ta farko ‘A’ waƙa ce ta jana’iza, kuma ta kasance wadda malaman ƙasar Hausa ke yawan karantawa a wajen bizne mamata. (Robinson, 1896).
Abin lura a nan shi ne, waƙa ta farko ‘A’ Robinson bai kawo ta duka ba bale wajen nazari a dubi wajajen ƙarshen baitocin waƙar ko a ga inda malamin ya kawo sunansa a matsayin marubucinta. Wannan na nuna akwai alamar Robinson ya yi haka ne domin a kasa gane gaskiyar marubucin ta, sai kawai ya jingina ta ga Liman Ceɗiya.
Wani abu da ya ƙara tabbatar da matsala ga kawo sunan wannan malami (Liman Ceɗiya) da aka jingina wa waƙoƙin shi ne, a waƙa ta farko ‘A’ Robinson bai kawo cikakken sunan wannan malami ba sai a sharhinsa na waƙa ta uku mai lamba ‘C’. A wannan waƙa ya nuna marubuci waƙar mai suna Halilu shi ne Liman Ceɗiya wanda ya rubuta waƙa ta farko. Haƙiƙa sunan marubuci wannan waƙa ta uku shi ne Halilu domin sunan ya fito a baiti na 43-44 kamar haka:
Waƙa ga ɗan bawa Halilu fa ya yi ta Almajiri gun shaihu ni fa Sanusiya.
Dangin uwa tasa du suna Allahuwa Dangin uba nasa Rimatawa kun jiya.
Ko da yake a wannan baiti marubucin ya ambaci sunansa, to sai dai bai danganta kansa da garin Ceɗiya ba ko limanci. Ya ambaci dangin uwarsa suna ‘Lahuwa’, su kuma dangin ubansa suna Rimatawa. Haka kuma ya nuna shi almajirin mazhabar Sanusiyya ne wadda ba ta watsu a ƙasar Hausa ba har zuwa yau. Ke nan wannan na nuna Robinson ne kawai ya danganta marubucin da cewa shi ne Liman Ceɗiya. Wannan na nuna Robinson ya kawo sunan ne bisa son ransa, ba don wata hujja tsayayya ba.
Wani abu da na yi na ƙoƙarin nemo tushen waɗannan waƙoƙi da Robinson ya ce marubucin su ya rayu har wajajen shekarar 1866 kusan huduwar Turawa a ƙasar Hausa shi ne duba wasu kundayen da aka wallafa. Na duba wasu littattafai da kundaye da aka bari kan tarihin adabin Hausa, amma kuma ban ci karo da wata waƙa mai alaƙa da wannan mutumin ba. Na duba kundin digiri na biyu na Bello Sa’id mai take ‘Gudunmawar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa’ (1978). Na kuma duba littafi mai suna Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa (1988) na marigayi Ibrahim Yaro Yahaya.
Shi kuma Malam Muhammadu Na Birnin Gwari Robinson ya jingina masa rubuta waƙa mai lamba ‘B’ da ‘D’. A cewar Robinson, Birnin Gwari wani gari ne da ke tsakanin garin Kano da garin Bida (Robinson, 1896).
Ta fuskar tarihin adabin Hausa an nuna Muhammdu Na Birnin Gwari ya rayu ne a wajajen ƙarni na 18. Yahaya, (1988) ya nuna an haifi Malam Muhammadu na Birnin Gwari a shekarar 1758 a garin Katsina. Daga baya mahaifansa suka tashi daga Katsina suka koma wani gari mai suna Sabon Ɗan Halima kusa da Tsohuwar Gwari a ƙasar Birnin Gwari.
Idan aka koma cikin waƙa ta biyu mai lamba ‘B’ akwai baituka biyu na 76 da 77 da suke nuna ba malam Muhammadu na Birnin Gwari ya rubuta waƙar ba domin marubucin ta ya rayu har bayan zamanin mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello wanda ya rasu a shekarar 1837. Ga yadda baitukan suka zo;
Duba ga Bello in don mulki na Wa ya yi tasu nan sararin Sudan.
Ya mulke ta bai rage ƙwaya ba Shina kira da addinin gaske.
Idan aka yi la’akari da abin da ke cikin waɗannan baituka na kawo lamarin mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello a ƙasar Sudan (ƙasar Hausa), ya nuna Muhammadu na Birnin Gwari ba shi ya rubuta wannan waƙa ba. Shi Muhammadu na Birnin Gwari ba a nuna an ji ɗuriyar rayuwarsa a zamanin masu jihadi ba. Haka kuma ba a sami wata ƙwaƙƙwarar madogara da ta tabbatar da rayuwarsa har bayan mulkin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ba. Wannan ya tabbatar da cewa, Robinson ya jingina mashi waƙoƙin biyu ne kawai domin bai yi rayuwa a zamanin Shaihu ba bale Muhammadu Bello.
Su kuma waƙoƙi biyu na ƙarshen littafin, waƙa ta biyar mai lamba ‘E’ da waƙa ta shida mai lamba ‘F’ Robinson ya nuna Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo ne ya rubuta su (Robinson, 1896). Ko da yake Robinson ya ambaci sunan Shaihu Usmanu a matsayin marubuci waƙoƙin, to sai dai akwai abubuwan da suka kore rubuta waƙoƙin ga Shaihu.
Abu na farko shi ne, sunan da yake a cikin waƙa ta 5 ‘E’ wanda aka kawo a ƙarshe bayan baitukan waƙar shi ne ‘Ramla ɗan Yusuf’ wanda da Larabci aka rubuta ‘Ismul mukatib Ramla bin Yusuf.’ Wannan suna da aka tsinta a ƙarshen wannan waƙa ya tabbatar da cewa, Shaihu ba ya da hannu a cikin waƙar domin cikin muƙarrabansa ba mai wannan sunan. Abin da ma Sa’id (1978) ya nuna shi ne Shaihu, Abdullahin Gwandu yake ba waƙa ya duba, kuma ba inda aka nuna ya taɓa ba kowa waƙa ya duba masa in bayan shi.
Wani abu kuma shi ne, ita wannan waƙa ( mai lamba E) ba wani wuri da sunan Shaihu Usmanu ya shigo a cikinta, kuma ba ramzin da za a iya a yi amfani da shi domin tantance zamanin da aka yi waƙar ko zamanin rayuwar Shaihu ne.

4.3 Lokacin Rubuta Waƙa/Ramzi


Lokacin rubuta waƙa (ramzi) muhimmin abu ne da ke taimakawa wajen nazarin dangantakar waƙa da marubuci. Shi lokacin rubuta waƙa ko ramzi a Larabce, lissafi ne da ke nuna shekarar da aka rubuta waƙa ta amfani da haruffan Larabci. Kowane baƙi na Larabci yana da wata daraja da aka ba shi a alƙalamin lissafi. Duk waƙar Hausa da ke da ramzi, shi ake amfani da shi ga sanin zamanin da aka rubuta ta. Da ramzi ake amfani a auna zamanin rayuwar malami da waƙa don tabbatar masa da ita, ko kuma kore masa ita.
Malamai da yawa a ƙasar Hausa sukan sa ramzi a cikin waƙoƙinsu domin nuna shekarar da suka rubuta waƙa. Duk waƙar da ke ɗauke da ramzi shi ake amfani da shi domin sauƙaƙe gano lokacin da aka rubuta ta. Ramzi na taimaka wa mai nazari gano dangantakar waƙa da marubucinta ta fuskar zamanin rayuwarsa. Akwai irin wannan lokacin rubuta waƙa (ramzi) cikin waƙoƙin masu jihadi da yawa. Ga misali, a waƙar Shaihu mai suna Daliyya akwai ramzi a baitinta na 63. Ga yadda baitin yake;

Bisa shekarar ƙASSHIN da FAJJIN don ku ji,
Hijirar fiyayye Annabinmu Muhammadi.

Ita ma Asma’u ‘yar Shaihu waƙarta mai suna ‘Dalilan Samuwar Allah’ ta shigo da ramzi a baitinta na 35 kamar haka;
Ramzi na hijira tai fiyayye HASHRA’U,
Mun roƙi alheri ga Allah Shi ɗaya.

Sauran waƙoƙin malaman da dama suna ɗauke da ramzi a cikin su. Idan aka yi la’akari da ramzin za a ga cewa, ya fayyace lokacin da malami ya rubuta waƙarsa, ko kuma idan lokacin bai yi daidai da zamanin rayuwar malamin ba, sai a kore masa waƙar.
A cikin littafin Specimens Of Hausa Literature waƙa ɗaya ta shida ‘F’ wadda Robinson ya kawo sunan Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo a matsayin marubucinta ke ɗauke da lokacin rubuta ta (ramzi) a baiti na 255. Ga yadda baitin yake;
Kanawa fa na yi waƙar nan na wa’azi Nurayshu ramzu hijira babu wawa.

Idan aka ɗauki darajar baƙaƙen ramzin (Nuraysh) za a ga sun fito kamar haka;
N=50
R=200
Y=10
Sh=1000

Da wannan idan aka haɗa lissafin waɗannan baƙaƙe za su ba da shekarar 1260 ta hijra wadda take daidai da 1843 miladiyya. Daga wannan lissafi ya nuna ke nan, kowane malami ne ya rubuta wannan waƙar, to ya rayu har zuwa wannan lokaci. Shi kuma Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo da aka danganta wa rubuta waƙar tarihi ya nuna ya rasu a shekarar 1817 (Sa’id, 1978). Daga wannan ƙididdiga an tabbatar da cewa, ko da aka samar da wannan waƙa har Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rasu. Abin da lokacin ya nuna, an rubuta waƙar ne a zamanin Sarkin Musulmi Ali Babba ɗan Muhammadu Bello wanda ya yi mulki a tsakanin 1842-1859. Ke nan wannan ramzi ya kore wannan waƙa ga Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo.

4.4 ƙafiya /Amsa-Amo


ƙafiya na nufin tsarin gaɓar sautin da marubucin waƙa ke ƙare kowane baiti na waƙarsa da shi (Dunfawa, 2003). A tsarin zubin rubutattun waƙoƙin Hausa akwai ƙafiya iri 4 waɗanda kan ɗaya daga cikin su ake rubuta waƙoƙin Hausa. ƙafiya na fito da kaifin basirar malami da kuma zurfin hikimarsa da fasaharsa ta rubuta waƙa. Duk waƙar da aka rubuta ba kan wani tsari na ƙafiya ba, wannan yana nuna rashin gwanewa da ƙarancin hikima da fasahar marubuci.
Malaman ƙasar Hausa Allah ya ba su kaifin basira da fasahar rubuta waƙa bisa wani tsari na ƙafiya, musamman daidaita babbar ƙafiya. Wannan yana da alaƙa da tsarin waƙoƙin Larabci da suka aro fasaharsu. Ga misali, waƙoƙin Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo suna kan wani tsari na ƙafiya. Misali, waƙar ‘Taulafin Sidi Abdulƙadiri’ tana da tsayayyen tsarin babbar ƙafiya gaɓar kalmar ‘ri’ a ƙarshen kowane baiti. Ga misali:
A mu gode zucci da zahiri,
Bisa samun Abdul-ƙadiri.

A mu gode Allah ‘yan uwa,
Bisa tsarin Abdul-ƙadiri.

Ita ma waƙar ‘Salati Guzurin Mumini A Lahira’ babbar ƙafiyarta ita ce ‘tu’. Ga misali:
Mu gode mai salamu da yai salatu,
Da yaf fare mu yac ce mui salatu.

Salatu nai da taslimi su duma,
Ga Ahmadu shugabanmu mu yo salatu.

Sauran malamai irin su Abdullahin Gwandu da Muhammadu Bello da Asma’u ‘yar Shaihu da Maryam ‘yar Shaihu da Giɗaɗo ɗan Laima da Dikko ɗan Bagaye da Salihu ɗan Zama da Mallam Darho da sauran su duka kan wani tsari na ƙafiya suke rubuta waƙoƙinsu.
Idan aka dubi waƙoƙin littafin Specimens Of Hausa Literature za a ga cewa, waƙa ta 3 mai lamba ‘C’ da Robinson ya jingina wa Liman Ceɗiya da ta 6 mai lamba ‘F’ wadda Robinson ya ce Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo ya rubuta ta, su kaɗai ke kan tsarin daidaiton babbar ƙafiyar gaɓar sauti. Sauran waƙoƙin 4, ba ko ɗaya da ke kan wani tsari na ƙafiya. Su kuma waɗannan waƙoƙin biyu, kowace na da naƙasu mai ƙarfi dangane da malami da aka jingina wa rubuta ta. Waƙa ta 3, sunan Halilu ya zo a baitinta na 76-77 a matsayin wanda ya rubuta ta. Shi kuma bai alaƙanta kansa da garin Ceɗiya ba, bale limanci saɓanin abin da Robinson ya ce. Ita kuma waƙa ta 6, ramzinta ya kore wa Shaihu Usmanu rubuta ta. Rashin daidaitaccen tsarin ƙafiya ya nuna cewa, malaman da aka ayyana sunayensu a matsayin marubuta waƙoƙin shida, ba su ne suka rubuta su ba domin babu hikima ga tsarin ƙafiyar waƙoƙin guda huɗu.

karanta wani

https://www.amsoshi.com/2017/07/20/zama-da-madaukin-kanwa-ke-sa-farin-kai-nason-bakin-aladu-cikin-aladun-auren-hausawa/

5.0 Kammalawa


Idan aka yi la’akari da abin da maƙalar ta tattara a kansa, za a ga cewa waƙoƙin littafin Specimen Of Hausa Literature na ƙunshe da illolin da ke kore dangantakar malaman da waƙoƙin da marubuci littafin ya kawo a matsayin waɗanda suka wallafa su. Akwai yiyuwar ya yi haka ne kawai saboda jin irin gudummuwar da wasu malamai na ƙasar Hausa irin su Muhammadu na Birnin Gwari da Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo suka bayar a fagen adabin Hausa. Haka kuma yana iya yin haka don ƙoƙarinsa na ya kai wa jami’an ƙungiyarsa ta CMS wani abu da zai tabbatar da zurfin ilimin Hausawa don a yi nazarin yadda a ilmance za a yaɗa addinin Kirista cikin ƙasar Hausa. Haka ya sa bai yi dogon bincike game da waƙoƙin malaman ƙasar Hausa ba, bale ya ga irin tsare-tsarensu don ya yi amfani da su ga nashi waƙoƙin ba. Wannan maƙala ta taimaka ga ƙoƙarin da wasu manazarta ke yi na taskace haƙiƙanin waƙoƙin malaman ƙasar Hausa da kuma kore waƙoƙin da ba nasu ba ne waɗanda jingina musu su kawai aka yi. Daga ƙarshe za a ga maƙalar ta fito da wasu muhimman abubuwa waɗanda da su ne ake iya kore waɗannan waƙoƙi ga malaman uku.

Manazarta


Ade-Ajayi J. F. (1970), Journal of the Re
v. James Frederick Schon and Mr. Samuel Crowther who accompanied the Expedition up the Niger in 1841.Second Edition. Frank Cass & co. Ltd., London.

Aliyu, S. A. (2000), ‘‘Christian Missionaries and Hausa Literature in Nigeria, 1840-1890: A Critical E
valuation.’’ A Cikin Mujallar Kano Studies NewSeries vol.1, No. 1, Jami’ar Bayero, Kano.

Baldi, S. (1977), Systematic Hausa Bibliography. Istituto Italo-Africano. Collana in Studi Africani.

Bakura, A. R. (2011), Gudummuwar Turawa Wajen Samuwa Da Ginuwar Adabin Hausa. Kundin Digiri Na Uku, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bunza, A. M. (2009), Narambaɗa. Ibrash Islamic Publications Centre Ltd., Lagos.

Bunza, U. A. (2013), Bauta Da Aikin Hajji Da Tasirinsu Ga Ginuwar Wani Ɓangare Na Adabin Hausa. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa na farko da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano ta shirya daga ranar 14-16 ga Janairu, 2013.
Crampton, E. P. T. (1976), Christianity In Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria.

Dunfawa, A. A. (2003), Ma’aunin Waƙa. Garkuwa Publishers, Sokoto.

Gada, A. M. ( 2010 ), A Short History Of Early Islamic Schorlarship in Hausaland. Department of Islamic Studies, UDU, Sokoto.

Mani, A. (1966), Zuwan Turawa Nijeriya Ta Arewa. NNPC, Zaria.

Niɓen, C. R. (1955), Labarin Nijeriya. NORLA, Zaria.

Robinson, C. H. (1896), Specimens of Hausa literature. University Press, Cambridge.

Robinson, C. H. (1897), Hausa or 1500 Miles. London.

Robinson, C. H. (1900), Nigeria Our Latest Protectorate. Negro Uniɓersities Press, New York.

Robinson, C. H. (1915), History Of Christian Missions. Public Library, Kansas City, Mo.

Sa’id, B. (1978), Gudunmuwar Masu Jihadi Kan Adabin Hausa. Kundin digiri na biyu, juzu’i na biyu.Kwalejin Jami’ar Bayero, Kano. Jami’ar Ahmadu Bello.

Sani, A. B. (2008), Some Reflections of British Intelligence Operatiɓes in Northern Nigeria, C: 1820’s -1920’s. A cikin Mujallar Taguwa Journal of Humanity No.1 ɓol. Katsina State University.

Skinner, N. (1980), An Anthology of Hausa Literature. Zariya NNPC.

Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC, Zaria.

www.amsoshi.com

Post a Comment

2 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.