Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarbiya A Cikin Adabin Hausa: Tsokaci Daga Karin Magana

Daga

Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
aliyubunzaumar@yahoo.com
07063532532, 08095750999

August, 2011

1.0 GABATARWA

A cikin adabin Hausa, karin magana fage ne babba da ya shafi kowane ɓangare na rayuwar alumma tun daga zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu. Ganin irin wannan yanayi na karin magana na zaman sa komai da ruwanka a alamurran jamaa na yau da kullum, ya sanya wannan maƙala ta nutsa a cikin karuruwan maganar Hausa domin ta zaƙulo wasu da take ganin ana amfani da su domin gyaran tarbiya da kuma kyautata halayyar alumma. Duk da yake karin magana ne zuciyar maƙalar, an kauce wa duba maanar karin magana da nau’o’insa ba don komai ba sai don ganin masana da manazarta (Koko, 1989 da Yunusa, 1989 da Bagaye, 1992 da Birniwa, 2005 da Bada 2007 da Bada da Mode, 2007 da Nahuche, 2008 da Usman, 2005 da Hassan, 2009 da Mahuta, 2002 da Bunza, 2006 da sauransu) duk sun yi rubuce-rubuce kan wannan. Don haka wannan maƙalar ta fara da duba tarbiya.

2.1 MA’ANAR TARBIYA


Tarbiya na ɗaya daga cikin kalmomin harshen Larabci da suka shigo harshen Hausa tun zamani mai tsawo. Kalmar na nufin tattalin mutum da koyar da shi yanayin rayuwa na gari da zai tashi da ƙima, ya amfani kansa da al’ummarsa. A cewar Sa’id (2006) tarbiya ita ce koyar da hali na gari. Shi kuma Gusau (1999) ya kawo cewa tarbiya wata hanya ce ta kyautata rayuwar ɗan Adam da shiryar da shi ya zuwa halaye da ɗabi’u masu kyau da nagarta. Ta yin haka zai sa ya tashi da ƙima da kwarjini da ganin mutuncin abokan zamansa, sa’annan ya riƙa ba kowa hakkinsa daidai yadda ya kamata gwargwadon hali. Shehu (2011) shi kuma ya kawo cewa tarbiya ita ce aza wani mutum bisa wata hanya da zai koyi wani abu wanda zai amfane shi a rayuwarsa da ma sauran jama’arsa baki ɗaya. A cewar Bunza (2002) tarbiya tana nufin samun kyakkyawan horo ga mutum ya zama masanin kyawawan abubuwa na ɗabi’un hulɗa da jama’a da ladabi, da biyayya, da kamun kai, da kasancewa mai jin kunya da kyakkyawan maƙasudi.
Ta la’akari da waɗannan ma’anoni za a iya cewa, tarbiya ta shafi gina mutum a bisa halayen da al’ummarsa ta aminta da su na kunya da ƙwazo da ladabi da biyayya da girmama na gaba da kishin kai da riƙe iyali da taimakon juna da haɗin kai da son aikata alheri da nisantar kwaɗayi da rowa da sauransu.

3.1 KARIN MAGANA MASU KYAUTATA TARBIYYA


Kasancewar karin magana fage babba da ya taɓa kowane ɓangare na rayuwar al’umma ya sanya sau da yawa akan yi amfani da wani karin magana domin kyautata halayyar wani ko wasu mutane. Akan yi haka ne ta hanyar jeho wani karin magana da ke nuna gargaɗi ko faɗakarwa ko hannun kai mai sanda ga wani da ya karkata daga wata halayya ta gari da al’umma ta yarda da ita a zamantakewar yau da kullum. Akwai fannonin rayuwa da dama da ake amfani da karin magana domin kyautata halayyyar mutane. Ga wasu daga ciki da kuma karuruwan maganar da ake amfani da su.

3.1.1 HAƙURI


Haƙuri shi ne juriya ga wata wahala ko ɓacin rai. Irin wannan juriyar ta shafi ɗaukar ɗawainiyar wani abu ko neman wani abu ko kuma jure rashin wani abu. Haƙuri na cikin matakan samun zaman lafiya da ci gaba a tsakanin al’umma. Idan haƙuri ya samu a zukatan jama’a sai a sami al’amurransu su tafi daidai ba tare da matsala ba. Rashin haƙuri shi ke sanya al’amurran jama’a su dagule, fitine-fitine su yawaita a tsakaninsu. Uwa-uba rashin haƙuri na haddasa taɓarɓarewar tarbiya gaba ɗayanta da kawo lalaci da sace-sace da sauransu. Domin samun al’umma ta gari, mai cikakkiyar tarbiyya ta ƙwarai, marashiya lalaci ya sanya ake ta ban haƙuri a koyaushe tsakanin jama’a ta hanyoyi daban-daban.
Karin magana na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su domin tabbatar da haƙuri a zukatan jama’a domin kyautata yanayin tarbiyyarsu. Akan zaɓi wani karin magana wanda ya dace da halin da ake ciki domin a ga an ba mutum haƙuri da halin da ya sami kansa. Karuruwan maganar Hausa da ake amfani da su don rarrashin mutane da sa su jure wani yanayin damuwa da suke ciki na da yawa. Ga wasu kaɗan daga cikinsu:
Haƙuri maganin zaman duniya
Mai haƙuri kan dafa dutse har ya sha romonsa
Komai ya ɓaci haƙuri ne babu
Bayan wuya sai daɗi
Mahaƙurici, mawadaci
Hushi silalin ɓarna
In an ciza a riƙa busawa
Wanda ya yi haƙuri da kunun maraice, ya kai ga tuwon dare
Mai ƙarami ke da babba in ya daure
Yau da gobe sai Allah.

3.1.2 HAƊIN KAI


Haɗin kai ɗaya ne daga cikin abubuwan da ake koya tarbiyya da su. Shi haɗin kai abu ne muhimmi a cikin al’umma. Da haɗin kai ne mutane ke nasarar aikata wani abu wanda ba ya aikatuwa ga mutum ɗaya, ko su kammala wani aiki mai wahala a cin ƙanƙanin lokaci. Da haɗin kai a cikin zamantakewa ake samun ci gaba da kariyar mutuncin juna da ɗorewar zaman lafiya da tsaro da sauransu. Kowace al’umma na son ta ga jama’arta na da haɗin kai domin samar mata ci gaba a koyaushe. Wannan ya sanya al’ummar Hausawa ke ta kiran mutanenta kan su haɗa kansu a koyaushe domin ɗorewar girmanta da ƙimarta.
Akan yi amfani da karin magana a lokuta da dama idan ana son a jawo hankalin jama’a ga haɗa kai domin cin nasarar wani abu ko ɗorewar wani al’amari. Kaɗan daga karuruwan maganar da ake amfani da su don wannan su ne:
Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka
Akuyar da ta ware ita kura kan ci
ƙarfin yawa ya fi ƙarfin giwa
Haɗin kai ya fi haɗin gida
Hannu da yawa maganin ƙazamar miya
Gayya mai gama aiki
Aiki mutum guda ya raina
Sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga

3.1.3 TSARO


Tsaro na ɗaya daga cikin matakan kyautata tarbiyyar al’umma. Tsaro shi ne fakon wani abu na kaya ko mutunci ta hanyar sa ido domin gudun gushewarsa ko zubewarsa ba tare da son ran wanda ke da shi ba. Tsaro abu ne muhimmi a cikin kowace al’umma. Idan aka sami tsaro a cikn zamantakewa, kowa ya kula da abin da yake nasa da na ɗan uwansa, aka hana salwantan abin wani, sai a sami zamantakewa mai nagarta. Haka idan aka sami tsaro ya inganta, sai a wayi gari sace-sace su taƙaita domin malalaci kamar ɓarawo ba zai sami faraga ta yin sata ba. Da zarar al’umma ta rasa tsaro a cikinta, sai al’amurra su lalace, sace-sace su yawaita domin sakaci ya shige ta.
Kari magana na daga cikin hanyoyin da ake farfaganda ga al’umma su zan masu tsaro ga kayakinsu da muhallinsu. Ga wasu cikin karuruwan maganar:
Kula da kaya ya fi ban cigiya
Taya Allah kiyo, ya fi Allah na nan
Kula da kaya ya fi Allah na nan
Hankali da kaya ya fi ban cigiya
Idan kana ruwa, kada ka zagi kada
Mutunci madara ne, in ya zube shi ke nan
Kar ka sake ruwa su ci ka a wankin kalwa

3.1.4 TSORATARWA


Tsoratarwa a nan na nufin kwaɓe mutum ga aikata wani abu wanda ake jin sakamakonsa na da aibi ga rayuwa. Irin wannan aiki ya haɗa duk abin da ake ganin ko jin sharri ne, kuma abin da zai je ya dawo ba zai yi daɗi ba. Koyaushe mutane ƙoƙari suke yi, su yi hani ga aikata duk wani abu da tarbiyyar al’umma ba ta yarda da aikata shi ba kai tsaye. Akan yi irin wannan hanin ta fuskoki da dama da suka haɗa da wa’azi da ba da shawara da jeho wani karin magana da zai zama hannunka mai sanda kai tsaye. Ga wasu karuruwan magana da ake jehowa:
Wanda bai ji bari ba, ya ji hoho
In kunne ya ji, jiki ya tsira
Jiki magayi
In gemun ɗan uwanka ya kama da wuta, sa ma naka ruwa
Gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah
In kana cin ƙasa, tsoraci ta suri
A riƙa sara ana dubin bakin gatari

3.1.5 KAME BAKI/HARSHE


Baki abin magana! Duk da irin fa’idar da ke ga bakin mutum, adabin Bahaushe sai da ya yi horo da kame shi. Ba shakka, baki abu ne muhimmi. Da baki ne mutum ke bayyana kansa a san shi a san cinikinsa. Duk mutumin da ke da baki, ya fi sauƙin mu’amala da mutane a fahimce shi. Hasali ma, duk yawancin mu’amalar mutane ta cinikayya da neman ilimi da addini da siyasa da neman abinci da sauransu ta baki ake yin su a sauƙaƙe. Mai baki ake sanyawa gaba domin isar da saƙon al’umma na kyautata tarbiyyar jama’a da kuma kyautata musu. Duk da irin wannan fa’idar ta baki, sai da aka shigo cikin adabi domin jan kunnen jama’a don su san yadda za su yi amfani da bakinsu a wajen maganganunsu na yau da gobe. Akwai karuruwan magana masu yawa da ke nuna haɗarin baki a wasu lokuta. Ga wasu cikinsu:
Bakinka ƙanin ƙafarka
Baki ke yanka wuya
Shegen mutum, bakinsa
Ga bakin wawa akan ji magana
Halshen mutum, zakinsa
In ka ga baki da tsawo na mai gardama ne
Maganar duniya iyawa ce, in ka ji ta kama bakinka
Kurum ta raba ka da kowa

3.1.6 RENO


Reno shi ne koyarwa. Koyarwa kuwa ta shafi kowane yanayi na rayuwa ta yadda za ta tashi mai nagarta, kuma da sabo da abin da ta koya. A halin tarbiyya, ba yara kaɗai ake reno ba, ana renon kowane mutum a kan abin da ake son ya koya ya tashi da shi a rayuwarsa. Duk da haka, yawanci yara ne aka fi mai da hankali a rene su ga wani abu domin su ne ake ganin sassan jikinsu ba su yi ƙarfi ba, kuma su ne ake kallo a matsayin manyan gobe. Ana renon kowane yaro ne da gwargwadon wani abu na tarbiyya da ake son ya taso da shi tun yana ƙarami wanda ya haɗa da sana’a da zamantakewa domin ya zama ya saba da shi ta yadda idan ya girma ba ya jin wahala, kuma a wannan lokacin zai amfani kansa da al’ummarsa. Akwai wasu karuruwan magana da ke nuna yadda ya fi dacewa da a kula da yara ta fuskar renon su domin a gaba a ci amfaninsu, ko su amfanin kansu. Ga wasu daga cikin karuruwan maganar:
Geza tana ɗanya ake tanƙwarar ta
Gini tun yana ɗanye ake masa zane
Ka ƙi naka duniya ta so shi
Da safe-safe ake kama fara
Kyawon ɗan ƙwarai ya gadi ubanai
Gadon gida alali ga raggo
Albasa ba ta yi halin ruwa ba

3.1.7 WADATAR ZUCI


Wadatar zuci wani muhimmin makami ne na kyautata tarbiyyar al’umma. A duk lokacin da mutane suka kasance masu wadatar zuci, to sai kishin kai ya shige su, ya zan ba su hassadar abin da ke hannun wani. Dukkan mutumin da Allah ya ba wadatar zuci, ya yi dace domin zai zan mai natsuwa da kwanciyar rai a koyaushe. Haka a duk lokacin da wadatar zuci ya bazu a zukatan jama’a, to lumana da zaman lafiya za su samu a tsakaninsu. Haka lalaci irin na sace-sace da ƙyashi da jiye wa juna za su ragu sosai in har ma ba su gushe ba gaba ɗaaya.
A koyaushe shugabanni da masana a cikin kowace al’umma suna iya ƙoƙarinsu domin faɗakar da mutane su zama masu wadatar zuci da abin da Allah ya hore musu domin kauce wa faɗawa a wata muguwar hanyar da za ta ɓata tarbiyyarsu, ta fitar da su daga mutane na gari.
Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su domin dasa wadatar zuci a zukatan mutane akwai har da karuruwan magana da yawa. Kaɗan daga cikinsu su ne:
Guntun gatarinka ya fi sari ka ba ni
Zakaranka raƙuminka
In ba ki da gashin wance, kar ki yi kitson wance
ƙwai a baka ya fi zabuwa a daji
Abu ga hannu shi ne abu
In ruwanka ba su isar ka wanka, sai ka yi alwala ka tashi
Bar ganin girman kuka, bagaruwa ta fit a
Kowa ya rena kaɗan, ya dangana babu
Zafin nema ba ya kawo samu
Abin aro ba ya ado

3.1.8 KISHIN KAI


Kishin kai wani muhimmin batu ne na kyatata tarbiyya a zamantakewar al’umma. Da kishin kai ne kowane mutum kan zama namijin tsaye ya nemi abin korewa bakinsa ƙuda, ya biya buƙatun rayuwarsa, ya kare mutuncin kansa, ya kuma hana kansa zama ci-ma-kwance. Mai kishin kai ne ke zama mutum na gari a cikn al’umma har ya kawo mata ci gaba. Idan kowane mutum ya zama mai kishin kai, sai al’umma ta zama saliha domin kowa ya san abin da ke gabansa na neman rufa wa kansa asiri. Rashin kishin kai shi ke sa mutum ya lalace, zuciyarsa ta mutu, ya zama ci-ma-kwance har ya kai ga sace-sace. Da zarar al’umma ta zan da irin waɗannan mutane, to yanayin zamantakewarta zai gurɓata domin samun ɓara-gurbi marasa tarbiyya. Gudun irin wannan ke sanya al’umma shige da fice domin samar da hanyoyin kasuwanci daban-daban da za su kawo maslaha ga wannan matsala.
A cikin karuruwan maganganun Hausa akwai batutuwa da dama da ke ishara ga mutum ya zama mai kishin kansa domin tsirar da mutuncinsa. Ga wasu daga ciki:
Yaro bari rena ƙafarka don ganin motar dabe
Yaro riƙe ungulunka shamuwa baƙuwa ce
In don na ɗan uwa biɗi naka
Zomo ba ya kamuwa daga kwance
Wanda ya fi ka a filin gona, fi shi ga sa taki
Allah na taimakon wanda ya taimaki kansa
Babu maraya sai raggo

3.1.9 LADABI DA BIYAYYA


Ladabi da biyayya kalmomi ne da ke tafiya tare a fagen tarbiyya. Da wuya a sami ɗaya a rayuwa a rasa ɗaya. Kusan wannan ne mataki na farko na hasashen tarbiyya kyakkyawa a rayuwar mutum. Ladabi da biyayya sun haɗa biyar umurni da nisantar hani da kiyaye girman na gaba da mutunta doka da oda da kiyaye haƙƙin dukkan abokin mu’amala. Yawanci, an fi duban wannan daga na ƙasa zuwa ga na sama, sai dai ya wuce nan kawai domin har akan sami akasin haka, idan akwai kula doka da oda. Idan al’umma ta kasance mai cike da ladabi da biyayya, sai a sami wanzuwar zaman lafiya da ganin girman juna ta yadda kowa zai san haƙƙoƙin da suke kansa. Idan aka rasa ladabi da biyayya a al’umma, sai al’amurranta sun rincaɓe, a wayi gari ba mai mutunta wani balle tunanin ci gaba. Da wannan sai kowa ya zan gaban kansa kawai, sai al’umma ta lalace domin ba wanda ake sauraro, balle ya tsawata. Gudun haka ya sanya ake ta ƙoƙarin bin matakai daban-daban domin samar da wanzuwar ladabi da biyayya a cikin al’umma.
Kasancewar karin magana fage wanda ya taɓa kowane ɓangare na rayuwar al’umma, nan ma ya tanadi wani abu kan wannan. Ga wasu da ke nuni ga wannan batu:
Bin na gaba bin Allah
Duƙa wa wada bai hana tashi da girma
Matar na tuba ba ta rasa miji
To, ta raba ka da kowa
Yi na yi, bari na bari, ta raba ka da kowa

3.1.10 HORO DA ALHERI DA HANI GA SHARRI


Alheri da sharri (mugunta) kalmomi ne biyu masu ban hannun riga; ɗaya a gabas, ɗaya kuma a yamma. Alheri ne abin da kowane mutum ke son a yi masa, kuma shi ne akasarin mutane suke son aikatawa. Alheri ya shafi magana ta ƙwarai da aikata wani aiki na gari daga sassan jiki kamar kyauta da sadaka da aikin gayya da sauransu. A zamantakewa, da alheri ake ɗaukar girma kamar yadda a dalilin sharri girma ke zubewa. Ta yin alheri ƙarami kan doke babba har a ji shi (ƙarami), a girmama shi har ya zan ana karɓar ban maganarsa. A duk lokacin da jama’a suka kasance masu aikata alheri tsakaninsu, kuma suka nuna ƙin junansu da sharri, to akwai alamun kyakkyawar tarbiyya ke nan tsakaninsu.
Fagen karin magana bai bar alheri a baya ba, ya shigo da shi domin ƙoƙarin tsima jama’a kansa don gyara tarbiyyarsu. Ga wasu karuruwan magana masu nuni ga fa’idar alheri:
Aje alheri bayanka, ka tsince shi gabanka
Alheri ɗakin hutuwa
Alheri danƙo ne ba ya faɗuwa ƙasa banza
Da alheri aka ɗaukar girma
Abin da mutum ya shuka shi zai girba
Mai gina ramin mugunta, gina shi gajere
Alheri ba ya da kaɗan

3.1.11 RIƙON GASKIYA DA BARIN ƙARYA


Gaskiya da ƙarya a koyaushe ba su zama tare a wuri ɗaya. Gaskiya ce koyaushe son kowa ga kowane al’amari. Ba wani al’amari da zai tsayu da ƙafafunsa, ya kuma ɗore face sai idan kan gaskiya ake tafiyar da shi. Komai raunin al’amari idan dai kan gaskiya ake tafiyar da shi, to komai daɗewa rauninsa zai tafi, ƙarfi ya shige shi. Haka kuma duk yadda al’amari ya tashi sama, ya cika ya batse idan dai kan ƙarya ake tafiyar da shi, yau da gobe zai rushe, wata rana sai ya zan kamar ba a yi shi ba. Ganin ƙimar gaskiya a cikin kowane al’amari ya sa koyaushe ake ta ƙoƙarin raya ta a cikn zukatan mutane. Idan mutane suka tarbiyantu da gaskiya, ta ginu a zukatansu, to an sami al’umma mai nagarta ke nan. Idan kuwa aka sami irin wannan al’umma, to tabbas zamantakewarsu za ta yi daidai, ta inganta, a sami ci gaba mai ɗorewa a cikinsu domin an kawar da mai rosa su, ƙarya ke nan.
A cikin karuruwan maganar Hausa akwai masu ishara da kiyaye gaskiya domin samun al’umma ta gari. Ga wasu kaɗan daga ciki:
Gaskiya nagartar namiji
Ciki da gaskiya, wuƙa ba ta huda shi
Zancen gaskiya a yi shi da wando
Gaskiya ina laifinki
Daga ƙin gaskiya sai ɓata
Gaskiya ba ta neman ado
ƙarya mugun guzuri
Faɗin gaskiya sai namiji
ƙarya mugunyar magana
Gaskiya dokin ƙarfe
Ramin ƙarya gajere ne
A yi yau, a yi gobe sai gaskiya
Gemu babu gaskiya, ko na bunsuru ya fi shi

3.1.12 ZAMAN LAFIYA


Zaman lafiya ne ƙololuwar abin da ake son wanzuwar sa a cikn al’umma. Zaman lafiya shi ne wanzuwar lumana da kwanciyar hankali wanda ke samuwa ta samuwar ingantacciyar tarbiya a tsakanin jama’a. A duk lokacin da al’umma ta sami wanzuwar zaman lafiya, kuma ya ɗore, za ta sami dama da sukunin inganta dukkan wani abin da zai kai ta ga ci gaba na ji da faɗi. Rashin zaman lafiya shi ke sanya al’umma ta rikice ta ruɗe ta rasa inda za ta kama domin inganta al’amurranta. Wannan ya sanya a koyaushe ake ta kiran jama’a da su kasance masu son zaman lafiya da wanzar da shi.
Karin magana bai yi ƙasa a guiwa ba ga kiran al’umma ta zan mai son zaman lafiya a koyaushe, a kuma kowane hali. Dubi waɗannan karuruwan magana:
Zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki
Zama lafiya ya fi faɗa
Fitina kwana take yi, Allah ya la’anci mai tashe ta
Maso faɗa wawa
Fitina na kawo tsiya

4.1 KAMMALAWA


Daga abin da aka gabatar a sama, ana iya ganin cewa, karin maganar Hausa ya wuce zancen raha da nishaɗi kawai, ya haɗa har da kyautata tarbiya da zamantakewar al’umma. Ba wannan kaɗai ba, karin maganar Hausa ya taɓa dukkan sauran al’amurran al’umma na kasuwanci da kiyon lafiya da sauransu. An taƙaita maƙalar ce ga tarbiya kawai. A ɓangaren tarbiya ma, an taƙaita nazari kan waɗannan fannonin da aka nuna misalai ba don suke nan ba. Misalan karuruwan maganar da aka kawo ma, ba su kaɗai ake iya samu ba, sai dai an kawo su ne domin nuna misalai kawai domin haskakawa ga masu sha’awar ɗorawa nan gaba.

5.1 MANAZARTA


Bada, B. D. (2007), ‘The Role of Hausa Karin Mgana in Conflict Pre
vention, Management and Resolution’ Maƙalar da aka gabatar a taron ƙasa na ƙarawa juna sani kan nazarin Hausa, Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bada, B. D. da Mode M. A. (2007), The Role of Hausa Pro
verbs in Accidents Control in Nothern Nigeria’ Maƙalar da aka gabatar a taron ƙasa na ƙarawa juna sani kan nazarin Hausa, Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Bagaye, Y. I. (1992), ‘Nazarin Karin Magana Mai Labari’ Kundin Digiri Na Farko. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Birniwa, H. A. (2005), ‘Tsintar Dame A Kala: Matsayin Karin Magana a Cikin Waƙoƙin Siyasa’ Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies. Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Bunza, A. M. (2002), Yaƙi Da Rashin Tarbiya, Lalaci, Cin Hanci Da Karɓar Rashawa Cikin Waƙoƙin alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace. Ibrash Islamic Publications Centre Ltd., Lagos

Bunza, A. M. (2006), Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Limited, Lagos.
Bunza, A. M. (2006), ‘Cultural Shortcomings in Hausa Popular Proɓerbs’ Maƙalar da Aka Gabatar a Taron ƙasa da ƙasa, Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, Osun.

Ɗanyaya, B. M. (2007), Karin Maganar Hausawa. Makarantar Hausa No. 1 Ubandoma Road (Sabon Titi), Sakkwato.
Gusau, S. M. (1984), Tarbiyya A ƙasar Hausa Jiya Da Yau’’ Maƙalar Da Aka Gabatar A Taron ƙaddamar Da ƙungiyar Hausa, Jami’ar Sakkwato.

Gusau, S. M. (1999), ‘Tarbiyya a Idon Bahaushe’ Journal of Hausa Studies

Hassan, H. (2009), ‘Nazarin Karin Magana Da Suke Nuna Rarrashi’ Harshe 3. Journal of African Languages. Department of Nigeria and African Languages, Ahmadu Bello University, Zaria

Koko, H. S. (1989), ‘Karin Magana A Hannun Mata A garin Sakkwato’ Kundin Digiri Na Farko, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Ka’oje, U. I. (2006), ‘Tarbiyya a ƙagaggun Labaran Hausa: Nazari Kan ‘Ya’yan Hutu na malama Bilkisu Funtuwa’ Kundin Digiri Na Farko, jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Mahuta, G. A. (2002), ‘ The Status of Women in Hausa Pro
verbs’ Studies in Hausa language, literature And Culture The Fifth Hausa International Conference. Centre For The Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Nahuche, M. I. (2008), ‘Karin Maganar Hausa A Rubuce’ Kundin Digri Na Biyu, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Sa’id, B. (2006), ƙamusun Hausa. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Shehu, M. (2011), ‘Ci Gaban Mai Ginan Rijiya: Illolin Zamani Kan Tarbiyyar Hausawa’ takardar Da Aka Gabatar A Taron ƙara Wa Juna Sani, Sashen Koyar Da harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Usman, U. K. (2002), ‘Women in Hausa Pro
verbs.’ Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies. Nigeriana Languages Department, Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto.

Yunusa, Y. (1989), Hausa A Dunƙule.
Triumph, Kano.

www.amsoshi.com

Post a Comment

2 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.