DAGA
DANO BALARABE BUNZA
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA
JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO.
Email:danobunza@yahoo.com
Phone No: 07035141980.
Maris 2014
Tsakure
Tarihi muhimmin abu ne da kowace al’umma ke bugun gaba da shi domin sanin
tushenta. Duk al’ummar da ba ta san tarihinta ba, babu abin da za ta yi bugun
gaba da shi balle ta faɗi. Haka kuma akwai abubuwan tarihi da ke faruwa na waɗansu
abubuwan ban mamaki da ban tausayi da ma na takaici. Ba wannan kaɗai ba akan
sami waɗansu abubuwan tarihi da ke ɗauke da ban dariya da kuma ban tausayi.
Ganin haka ya sa takardar ta hango dangane da nason tarihi a cikin wasu waƙoƙin
Malam Maharazu Barmu Kwasare da ke ɗauke da abubuwan da suka faru a lokacin da
yake raye, keɓance a cikin garin Sakkwato da kewaye. Takardar ta yi bayanin
nason tarihin da ke cikin ‘‘Waƙar Masallaci’’ da ‘‘Waƙar Jinni Sago’’ da ‘‘Waƙar
Ɓauna’’ da kuma ‘‘Waƙar Wutar Kasuwa’’ da aka yi a kasuwar Sakkwato a wannan
lokaci. Tana ɗaya daga cikin manyan gobarar da aka yi a wannan lokaci. Idan ba
domin taskace wannan tarihi da Maharazu ya yi ba da ba a sami jin waɗannan
abubuwa da suka faru ba. Ta hanyar samun nason tarihi a cikin waƙoƙin Maharazu
Kwasare sai aka sami labarin abubuwan da suka gabata tun lokaci mai tsawon
gaske da ya wuce. Baicin wannan taskace tarihi da Malam Maharazu Barmu ya yi
ba, da ba a sami ko ɗaya daga cikin abubuwan nan huɗu da takardar ta kawo ba.
Ba shakka ba za a san abubuwan da suka faru ba sai ta hanyar samun tarihinsu.
Samun tarihin ba zai yiwu ba face ta hanyar rubutu da kuma jin su daga bakin waɗanda
aka yi abin lokacin da suke da hankalin kiyaye abin da ya gudana. ƙaramin yaro
ba ya iya kiyaye wasu abubuwan tarihi da suka faru lokacin da yake raye. Sai
dai ya dace a san cewa, ba kowane mutum ke iya kiyaye abubuwan da suka faru da
daɗewa ba balle ya ba da tarihinsu. Duk da haka, akwai wasu da Allah ya yi wa
baiwar kiyaye tarihin abubuwan da suka faru a zamanin da ya wuce. Ta la’akari
da wannan ne ya sanya aka fito da wannan batu na nason tarihi a cikin waƙoƙin
Malam Maharazu Barmu Kwasare. Akwai waƙoƙinsa da dama da ke ƙunshe da tarihin
abubuwan da suka faru a lokacin da yake raye. Sanin abubuwan da suka faru a
lokacin da yake raye na da muhimmancin gaske, domin ba a cika samun tarihin
abubuwan da suka faru fiye da shekara hamsin da suka wuce daga bakunan mutane
da yawa ba face idan suna rubuce. Akwai abubuwan tarihi a cikin waƙoƙin wannan
bawan Allah da za su haska wa na baya domin sanin abubuwan da suka faru a
zamanin da ba su zo duniya ba. Takardar za ta dubi nason tarihi a cikin ‘‘Waƙar
Masallaci” da ta “Jinni Sago” da ta “Ɓauna” da kuma ta “Wutar Kassuwa”. Ba waƙoƙin
da ke ɗauke da tarihi ba ke nan a cikin waƙoƙinsa, sai dai su ne takardar ta zaɓi
ta yi tsokaci a kansu. Wani abin ban sha’awa na tarihi shi ne, yakan taimaka wa
jama’a sanin abin da ya faru ga al’ummar da ta gabace su, ta yadda za su
tausaya kan abubuwa masu muni ko na sharri da suka faru gare su. Wannan
takardar za ta dubi abubuwa kamar haka:
2.0 Wane
ne Malam Maharazu Barmu Kwasare?
Malam Maharazu fitaccen marubucin waƙa ne kuma sananne a zamaninsa. A lokacin
da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya (1988) ya rubuta littafinsa mai suna ‘Hausa A
Rubuce:Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa’, ya kawo sunan Maharazu cikin
marubuta waƙoƙin jihar Sakkwato kuma shi ne na goma sha biyu a ciki.
Ba wannan kaɗai ba, Malam Maharazu ya faɗi ko shi wane ne a cikin wasu baitocin
waƙoƙinsa. Ga abin da ya ce a cikin waƙarsa ta masallaci:
Tammat daɗa Barmu ya cika wanga littafi,
Sunansa Maharazu halshenai da Hausanci.
Garinsu Kwasare nasbatai guda biyu ta,
Abbun Fulatiyyi Ummu haƙiƙa Gobarci.
Idan aka dubi baitocin da ke sama na cikin “Waƙar Masallaci”, za a fahimci
sunan marubucin da kuma harshen da yake amfani da shi. A baiti na biyu kuma, ya
kawo sunan garinsa da faɗar cewa yana da aslai iri biyu, inda ya ce mahaifinsa
Bafulatani ne, ita kuma mahaifiyar Bagobira ce. Duk inda aka sami mutum ya faɗi
sunansa da na garinsu kuma bai tsaya nan ba ya haɗa har da aslainsa, to ana iya
cewa ya bayyana kansa da yadda ake iya gane ko shi wane ne.
Bayan wannan kuma Malam Maharazu ya ƙara wa mai karatun waƙoƙinsa haske game da
shi kansa a cikin “Waƙar Ta’aziyar Malam Babi”. Ga abin da ya ce:
Tammat daɗa waƙa ta cika,
Daga Barmu Maharazu sha’iri.
Birnin Kwasare nan yaf fita,
Wani mai yawo almajiri.
Allah sarki! Dubi yadda Malam Maharazu ke ba da bayanin yadda ake iya gane shi
a cikin waƙa kamar yana kallo ana kallon sa. A baiti na sama ya faɗi sunansa
tare da bayanin cewa shi fa marubucin waƙa ne. Bayan wannan ya ƙara bayanin
cewa Kwasare ne garinsa na haihuwa, kuma yawo yake yi na kasuwanci. Bugu da ƙari
kuma almajiri ne mai neman ilmin addinin Musulunci. Ta hanyar wannan bayani za
a tabbatar da akwai bayani cikakke ga duk mai neman ya san shi.
3.0
Ma’anar Kalmar Tarihi da Naso
Kalmar tarihi ba kalma ce mai rikitarwa ba ta fuskar ma’ana. Kalma ce da ke ɗauke
da tsayayyar ma’ana da ke da sauƙin fahimta. A cikin ƙamusun Hausa na Jami’ar
Bayero ta Kano (2006), an ba da ma’anar kalmar gida biyu. Ma’anar farko cewa
aka yi, tarihi na nufin labarin abubuwan da suka wuce. Ma’ana ta biyu kuma,
cewa aka yi, fannin ilimi ne na al’amurran da suka faru a zamanin da ya wuce.
Kalmar tarihi da wannan takarda ke ƙoƙarin bayani ba ta wuce waɗannan ma’anoni
biyu da aka ambata ba, saboda labarin abubuwan da suka wuce ne takardar za ta
kawo.
Ita kuma kalmar naso da aka dube ta cikin ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ta
Kano cewa aka yi a dubi kalmar nasa. Ma’anar da aka ba kalmar nasa a shafi na
357 cewa aka yi, nasa na nufin wani abu a kan wani abu, misali rima ta nashe ɗaki
ko mai ya nashe a takarda. A taƙaice naso na nufin bayyanar wani abu cikin wani
abu ko a kansa. Wannan ne dalilin da ya sa aka yi amfani da kalmar naso domin a
tabbatar da cewa, akwai tarihi a cikin wasu waƙoƙin Malam Maharazu Barmu
Kwasare. Idan aka bi wannan takarda za a ga haka har ma a tabbatar da akwai
nason da aka ambata a cikin waƙoƙin malamin da aka ambata.
4.0
Nason Tarihi a Cikin Waƙoƙin Maharazu Barmu Kwasare
Akwai nason tarihi ƙwarai a cikin wasu waƙoƙin Malam Maharazu Barmu Kwasare
kamar yadda za a gani a cikin waƙoƙin da aka ambata. Labari ne na wasu abubuwa
da suka faru a zamani mai tsawo da ya wuce. Marubucin ya yi ƙoƙari ƙwarai wajen
kawo labarin abubuwan da suka faru da suka shafi wata al’ummar da wani bai sani
ba, kuma da ba zai taɓa sani ba face ta hanyar samun tarihi. Ga bayanin nason
tarihin da ake samu a cikin waƙoƙin da aka ambata a sama:
4.1
Nason Tarihi a Cikin Waƙar Masallaci
A wannan ɓangare za a yi tsokaci a kan yadda tarihi ya yi naso a cikin
rubutattun waƙoƙin Hausa, Musamman daga “Waƙar Masallaci ta Malam Maharazu
Baemu Kwasare. Abin da ya faru shi ne, a shekarun baya wajajen 1967-70 da aka
sami ɓarkewar yakin basasa a Nijeriya, hankula sun tashi matuƙar gaske har abin
ya kai kowa na tare da fargaba a cikin rayuwarsa. A daidai wannan lokaci ne aka
sami wata ranar juma’a da jama’a suka taru a masallacin Sakrin Musulmi Bello ɗan
Shehu, Liman na saman mimbari yana huɗuba, sai aka ji wasu yara uku masu
harbe-harben tsuntsaye da roba/danƙo suka iso masallaci. Da isowar su sai aka
ci sa’a akwai wasu tsuntsaye da ake kira hazbiya manya da ƙanana suna shiga da
fita cikin masallaci. Da yaran suka ga tsuntsayen sai hankulansu suka koma gare
su suka kasa la’akari da taron jama’an da ke wurin. Daga nan sai yaran suka ci
gaba da kiran sunan juna tare da ba juna ƙa’idar yadda za a harbi tsuntsayen,
ga shi kuma ana cikin tsoro da firgitar yaƙin basasan da ke gudana a wannan
lokaci. Sunan da ake kiran yaƙin shi ne ‘Yaƙin Ojukwu ɗan tawaye’. A wannan
lokaci ne Inyamurai suka himmatu da sai an raba ƙasar Nijeriya an bas u nasu
kaso. Daga nan sai yaran suka rinƙa kiran juna don lurar da juna yadda za a yi
harbin. Ana sane da cewa kowane masallaci na da ƙofofi a kusurwa uku wato ta
yamma da ta kudu da kuma ta ɓangaren arewa. Kuma ko za a yi su da yawa ne, haka
za a yi su. Kuma aka ci sa’a yaran uku ne sai suka yi tsarin cewa kowa ya tare
kusurwa ɗaya, sai ji jama’ar da ke ciki da wajen masallaci ke yi yaran na cewa
“Tare waccan ƙofa duk wanda ya fito ka harbe shi, ni kuma zan tare nan in
babbansu ya fito in harbe. Kai ko wane tsare duk wanda ya biyo ka harbe. Jin
haka ke da wuya sai hankulan waɗanda ke cikin masallaci suka motse har da
Liman. Nan da nan aka yi ciri kowa ya yi ta kansa ta hanyar in baka gudu ba ni
wuri. Liman bai daure ya tsaya ba bale mabiyansa. Haka kuma an dace Malam
Maharazu na cikin wannan masallaci lokacin da abin ya faru. Da aka ƙare wannan
al’amari ne sai ya ɗauki alƙalaminsa ya ba da labarin abubuwan da suka faru
gwargwadon hali. Ga wasu baitoci da ke tabbatar da nason tarihi a cikin waƙar
masallaci da Maharazu ya rubuta.
Yau shekara uku tashin hankali da yawa,
Gida da daji balle masallaci.
Haɗari da haufi da ru’uba sun game mu duka,
Tsoro da shakka akwai su gare mu Ajamanci.
Wa in khazarta bi shai’in la ta’ammana,
Tsoro akwai shi ƙwarai ku jiya masallaci.
Ana gudun mutuwa gaba can a faɗa wata,
Ko mai cewa a bar tsoro masallaci.
Idan aka dubi baitin farko za a ga cewa an yi shekara uku ana gwabza yaƙin
basasar Nijeriya, daga 1967-1970 kuma marubucin ya ƙara da cewa duk tsawon
wannan lokaci babu kwanciyar hankali sai tashin sa a gida da ma daji balle a
masallaci. Manufa a nan ita ce a ba jama’a labarin cewa, an sami tashin hankali
sosai a wannan masallacin Juma’a. A baitoci biyu da ke biye marubucin na nuna
irin tashin hankalin da aka samu a wannan ranar, har ya nuna cewa ana ƙoƙarin
guje ma wata mutuwa sai kwatsam aka faɗa cikin wata daban. Ma’ana, dukkan
jama’ar da ke wannan wuri sun watse da gudu don tsoron kada a mutu, sai aka
sami wasu sun halaka ƙwarai sanadiyar wannan ciri da mutane suka yi.
Bayan haka za a ƙara samun nason tarihi a cikin baitoci masu zuwa da ke ƙara
tabbatar da samuwar tarihi a cikin waƙar masallaci. Ga baitocin nan zuwa a ƙasa
kamar haka:
Wurin kiran salla an taushe sautukka,
Sabadda tsoron aduwayye masallaci.
Allah shi fisshe mu khaufi don munajati,
Duk ko’ina balle matsalat masallaci.
Ai in ana haka na san ana tawaye,
Wani ƙila sai ya yi bauli masallaci.
Ga malfuna, ga rawunna ga kubuttayye,
Duka an bar su da darduma masallaci.
An bar agoginne da hulluna ƙubbe,
Ɗan tazbaha yai dubu zangu masallaci.
An karkashe jalluna an bar gafakkinne,
Ga sanduna ga akwamayye masallaci.
Wasu hailala suka yi wasu maula wasu ko Tijjani,
Wasu sunka ɗora kira masallaci.
Wasu ko suna kalima wasu ga su kwance ƙasa,
An turmuje su ana taki masallaci.
Wasu sun fake nan ga ginoni suna nishi,
Mutuwassu ta zaka sunka aza masallaci.
Wasu ko suna farfari har sunka hau gina,
Har ba su dubin tsawon ginam masallaci.
Inda wurin idi na bi na ga da ta fi haka,
Cikin gari aka wa tsuwwa batun zucci.
A bar dawaki da basukurai da raƙumma,
Wurin gudu a baro hwanda da motoci.
Wani ko shiga tai gidan kulli a ji shi ɗaka,
In maigida ya ishe shi su kama ɓotoci.
Yara guda uku na su sunka cuce mu,
‘Yan akhiraz zamani na ba su gijibirci.
Idan aka kwantar da hankali aka dubi baitocin da ke sama za a tarad da tarihi
ne marubucin ke bayarwa na abin da ya faru a maslalacin Jumu’a na Sarkin
Musulmi Muhammadu Bello ɗan Shehu. Baitocin ba su buƙatar wani ƙarin bayani
domin bayanin da suke ɗauke da shi a fili yake. Don haka, faɗar da aka yi cewa
akwai nason tarihi a cikin waƙar masallaci da Maharazu Barmu ya yi, ba faɗa ne
ba kurum domin an taki dahir.
Idan aka yi la’akari da ma’anar kalmar tarihi da aka yi bayani a sama, kuma aka
dubi wasu baitoci da marubucin ya kawo kan abubuwan da suka faru a masallaci za
a tabbatar da akwai nason tarihin a ciki.
Kalmar aduwayye asali kalmar Larabci ce wato, aduwi mai nufin maƙiyi. Shi kuma
Malam Maharazu sai ya kira su aduwayye domin nuna yawansu wato maƙiya (masu
yawa). Kalmar kubuttayye na nufin takalman roba rufaffi irin waɗanda Fulani ke
amfani da su musamman lokacin da suke kiwon dabbobinsu a daji. Zangu kuma
kalmar Zabarmanci ce da ke nufin ɗari ɗaya. A nan Malam Maharazu na gaya wa mai
karatun waƙar cewa, a lokacin da jama’a suka firgita har cazbin da ke
hannayensu ba su yi dauriyar riƙewa ba, sun yar a ƙasa. A taƙaice, zangu kalmar
Zabarmanci ce mai nufi ɗari ɗaya na lissafi. Kalmar gafakkinne kuma jam’i ne na
sunan gafakka da ake ratayewa a jikin masallaci ko a kira ta jakar sanya Alƙur’ani.
Akwamayye ma jam’in akwama ne. Masu sayar da agogo na amfani da ƙananan
akwatinne na roba da suke saka hajarsu a ciki. Haka masu sayar da ‘yan kunne da
sarƙa na da abubuwan da suke saka hajarsu a ciki masu gilashi, haka ma masu
tallar turare. Abubuwan da suke saka hajarsu a ciki lokacin da suke talla su
ake kira akwamayye. Kalmar kulli na nufin kulle ko tsarin da ake yi wa matan
aure a cikin gidajen aurensu. Ma’ana gidan kulle ko gidan da matan aure ba su
fita sai tare da lalurar da shari’a ta aminta da ita. Kalmar ‘yan akhiruz
zamani kuma Larabci ne mai nufi yaran ƙarshen zamani.
4.2
Nason Tarihi A Cikin “Waƙar Jinni Sago”
Sago na da sunaye da ake kiran sa da su da suka danganci ɓangaren da ke kiran
sa hakan. Waɗansu na kiran sa sago, wasu kuma su kira shi bakangizo. Haka kuma
waɗansu na kiran sa zunni ko masharuwa. Kalmar jinni da marubucin ya laƙa masa
kalmar Larabci ce da ke nufin aljani, wanda yake ya fi dangantaka da aljannu ta
wajen sifofi da wurin zama. Labarin sago ya faru ne a wata unguwa da ke cikin
garin Sakkwato mai suna Rungumi. Ga al’adar masharuwa, ya fi zama cikin rami
irin na matattar rijiya ko wadda ba ta riga ta mutu ba. Abin sani game da sago
shi ne, idan akwai shi a cikin rijiya, ba za a sami isasshen ruwa cikin ta ba.
A wancan lokaci rijiyar na buƙatar gyara, waɗansu mutane suka shiga cikin
rijiyar aka yi rashin sa’a muguntar sagon ta tashi. Mutum biyar suka shiga
cikin rijiyar domin gyarar rijiyar sai suka haɗu da ajalinsu a wannan lokaci .
Tarihi ya nuna cewa, da mutanen biyar suka mutu a cikin rijiyar, sai mutum na
shida ya shiga don ya fito da su wanda shi ma bayan kwana ɗaya Allah ya yi masa
rasuwa. Hausawa dai sun ce waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi. Ga abin da
marubucin waƙar ya faɗa a wasu baitoci:
Batutuwa ba mu bin su irin na ashararu,
Mu dai tsarin Allah muka so ga jinni sago.
Mutum biyat Jalla Yay yi kira cikin sa’a,
Guda hukuncin Ilahi Rabbana ga sago.
Na shidda wannan da yaz zo don shi tsamo su,
Wan shekare yab bi su bayan gamo da sago.
Allah shi gafarta musu don uban Bello
Shi sauƙaƙe musu barzahu kan sago.
Za a fahimci bakangizo/sago ya yi sanadiyar rasa rayukan wasu mutum shida a
sanadiyar shigan da suka yi a cikin rijiyar da yake ciki. Mutuwarsu tabbas ce
domin har roƙa musu Allah aka yi don samun sauƙin zama cikin kabari. Ba tare da
wannan waƙa ba wata rana za a wayi gari a rasa labarin wannan abu da ya faru ko
kuma waɗanda suka san wannan labari. A gaba sai marubucin ya kawo sunan wurin
da wannan abu ya faru. Ga abin da ya ce:
Shiyya ta Rungumi can marina wajen kwalta,
Jabbaru yaƙ ƙaddaro musu waƙi’a ga sago.
Samun rubuce-rubuce irin waɗannan na tabbatar da nason tarihi a cikin waƙa.
Idan aka ce nason wani abu, ana nufin akwai abin ko da ba a zo da shi baki ɗaya
ba. Kuma an sami haka domin tabbatar da abin da ake magana a kai.
4.3
Nason Tarihi a Cikin “Waƙar Ɓauna”
Yadda aka sami nason tarihi a cikin waƙoƙin da aka ambata a sama haka ma akwai
shi a cikin “Waƙar Ɓauna”. Ɓauna ba dabbar gida ba ce, dabbar daji ce. Tana da
kama da saniya sai dai ba saniya ba ce. Abin da ke tabbatar da ta yi kama da
saniya kuma ba dabbar gida ba ce shi ne kirarin da ake yi mata na cewa: Ɓauna
saniyar sake, kuma ba saniyar uban kowa ba.
Ga al’adar namun daji yakan sami fita cikin ‘yan’uwa, daga nan sai ya faɗa wani
wuri da bai saba da shi ba sai ya ruɗe hankalinsa ya tashi daga nan sai ya
canza mugunta ta shiga. Haka ne ta faru ga bajinin ɓauna da ya fita garge, sai
dai ba a tabbatar da daga ina ya fito ba. Ɓaunan ya biyo ta wasu ƙauyukan garin
Sakkwato ne. ƙauyukan sun haɗa da Gidan aiki da Mauɗawa da Lemi da Gulbi da
Gidan Inda da Gelgel da Bokaye da ƙaurare da sauran ƙauyuka da yawa. Ga wasu
baitoci da ke ɗauke da nason tarihi a cikin “Waƙar Ɓauna” kamar haka:
Ɗiya tat tashi tac ce inna kura,
Da tatc tcinkai su ba tashi ga ɓauna.
Sai taz zaburo duk tak kiɗe su,
Tay yo yamma nan aka gane ɓauna.
Durbawa da taz zaka tay yi gulbi,
Tay yi kafau ana kuwwa ga ɓauna.
Wani yaz zaburo har yab buge ta,
Sai tas sa ƙafo tah hude wanna.
Wani yaz zaburo sai sunka sarƙe
Taɗ ɗauke shi sai bisa kanta ɓauna.
Tana yawo da shi abu babu kyawo,
Tak kashe shi tal lashe shi ɓauna.
Sakkwato anka kai su wurin tiyata,
Likkita, gudansu an ce babu wanna.
Wasu sun ce akwai shi batunsu zak kyau,
Ya tcere ma sharfiyya ta ɓauna.
Basansan da taz zaka tag ga jaki,
Tam murje shi nan taf fara ɓauna.
Tam milke shi yam mutu babu wawa,
Yaro yag ganat tak koro wanna.
Suna ta gudu ƙwarai yaf faɗa rame,
Samun rijiya yab bauɗe ɓauna.
Idan aka kula daga baitin farko har zuwa na ƙarshe labarin ɓauna ne ake bayarwa
game da karon battan ƙarfen da wasu mutane suka yi da shi. Ba tare da ƙoƙarin
marubucin ba da wannan tarihi ya salwanta.
4.4 Nasan Tarihi a cikin “Waƙar Wutar Kassuwa”.
Akwai waƙoƙi da dama da ke ɗauke da tarihi a cikin waƙoƙin Malam Maharazu Barnu
Kwasare. “Waƙar Wutar Kasuwa” na ɗaya daga cikinsu. Wannan gobarar ta faru a
cikin kasuwar garin Sakkwato a wani lokaci mai tsawo da ya wuce. Marubucin ya
kawo wasu baitoci da ke ɗauke da bayanin gobarar da ta faru a kasuwar . Ga wasu
baitoci da ke ɗauke da tarihin wutar da aka yi kamar haka:
Almalikul Mulki Sarki Karimun,
Alwahidun Jalla Sarki Hakimun,
Alƙadirun Rabbu Sarki Azimun,
Alwasi’um huwa Sarki Rahimun,
Shi yan nufa gobarak kassuwa.
Wannann baiti na ɗauke da tarihin cewa wutar da ake maganar an yi gaskiya ce
kuma, Allah ne ya ƙaddaro faruwar ta ba kowa ba. Wannan na nuna imanin da
al’umma ke da ga abubuwan da Allah ke jarrabar su da shi kuma komi na da
sanadin faruwarsa sai dai, mayar da komi wajen Allah ya fi. Marubucin ya ci
gaba da kawo tarihin wannan gobara a inda ya ce:
Sakkwato an yi wuta ta ci mali,
Ta ƙone kayan halal da halali,
Ta ƙone kayan rikitta na Mali,
Allah kaɗai shi fa Yas san misali,
Abin nan da yab babbake kassuwa.
Wannan baiti na ɗauke da tarihin gobarar da aka yi cikin kasuwar Sakkawato,
wanda ba ƙarya a ciki. Haka a layi na biyu na baitin, marubucin ya ba da
labarin cewa, gobarar ta ƙone kayyayyaki iri-iri inda ta ƙone kayan haram da
halal baki ɗaya. Bai tsaya nan ba sai da ya kawo cewa gobarar ta ƙone har da
kayan rikici da ke cikin kasuwar a layi na uku na baitin. A layi na huɗu da na
biyar kuma, maruubucin na ba da tarihin cewa ba wanda ya san iyakar hasarar da
aka yi sai Allah kaɗai, na kayan da suka ƙone. Haka kuma akwai wasu baitoci
biyu da ke ƙara ba da nason tarihi a cikin waƙar wutar kassuwa. Ga su nan:
Zancen wuta wagga har nesa ya kai,
Kurmi, ƙasar Bauci har Bidda ya kai,
A Adar, ƙasar Borno har Da’ifa ya kai,
Misra, ƙasar Jidda har Makka ya kai,
Duk an ji aikin wutak kassuwa..
A nan marubucin na ba da bayanin cewa, labarin gobarar kasuwar Sakkwato da aka
yi ya kai wurare da yawa kuma masu tsananin nisa, kamar Kurmi da Bauci da Bidda
da Adar da Borno da Da’ifa da Misra da Jidda har da Makka. Faruwar wannan ya
tabbatar da nason tarihi a cikin waƙar kasuwa.
A baiti na biyu kuma, ga abin da Barmu ya faɗa:
ƙasar Hausa duk yalla ya zo,
Mallam Wazirimmu ko yalla ya zo,
Marafan garin namu Sakkwato ya zo,
Sarkin Musulmimu labudda ya zo,
Dubin kufan gabarak kassuwa.
Gobarar da aka yi a kasuwar Sakkwato daɗɗaɗen abu ne da tarihinta ke da wuyar
samu in ba a rubuce ba domin lokaci ya yi tsawo. Ko za a sami waɗanda suka san
wannan abu da ya faru zai yiwu ba su iya tuna abin sosai bale ma mafi yawa sun
zan babu. Wannan baiti da ke sama na ba da tarihin waɗansu manyan mutane da
suka tafi wurin da aka yi gobarar domin gani da idonsu tare da yi wa waɗanda
abin ya shafa jaje. Sarakunan ƙasar Hausa Kamar Wazirin Sakkwato da Marafan
Sakkwato har da Sarkin Musulmin wannan lokaci ya je dubin ɓarnar da wutar ta yi
domin yi wa waɗanda abin ya rutsa da su jaje. Idan tarihi aka nema aka kai ga
abubuwan da ke cikin waɗannan waƙoƙi da aka ambata ba shakka an sami abin riƙawa
dangane da nason tarihi a cikin rubutacciyar waƙa, musamman waƙoƙin Malam
Maharazu Barmu Kwasare. Duk waɗannan abubuwan tarihi sun faru ne lokacin mulkin
Sarkin Musulmi Abubakar na Uku. A taƙaice abubuwan sun faru cikin shekarar
1970s saboda Malam Maharazu ya rasu a 1979 farkon jamhurya ta biyu. Abubuwa ne
da aka ji labarin faruwarsu wasu cikin Sakkwato wasu kuma har a ƙasa baki ɗaya.
Misali gobarar da aka yi har kasuwar Sakkwato ta ƙone a wannan lokaci..
5.0
Kammalawa
Tarihin muhimmin abu ne da ke taimaka ma al’umma gano abubuwan da suka faru tun
lokaci mai tsawo da ya wuce. Daga cikin taskokin adana tarihi akwai rubutattun
waƙoƙin Hausa da sauransu. Ta yin amfani da rubutattun waƙoƙin Hausa ana samun
tarihin abubuwa daban-daban da suka faru da idan ba ta hanyarsu ba, da wuya bai
salwanta ba. Nason tarihin da aka samu a cikin “Waƙar Masallaci” da ta “Jinni
Sago” da ta “Ɓauna” da kuma “Waƙar Wutar Kassuwa” da sauransu nasara ce aka yi
domin Maharazu ya kundace su da sai an nema a rasa. Da yake wannan takarda na
matsayin zakaran gwajin dafi ne kafin waɗansu su biyo bayanta. Haka kuma duk
wanda ya nazarci wannan takarda, zai tabbatar da tana ƙunshe da tarihin wasu
abubuwa da suka faru tun lokaci mai tsawo da ya gabata. Kar mu manta, ta hanyar
tarihin ne ake fahimtar abubuwa da yawa da suka gabata.
Manazarta
Bunza D. B. (2012), Nazarin Diwanin Malam Maharazu Barmu Kwasare, Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya, Sakkwato. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ɗangambo A (1980), Hausa Wa’azi Verse From Ca 1800-1970, ‘A Critical Study of
Form, Content, Language and Style’, Kundin Digiri Na Uku, Jami’ar London.
Ɗangambo A (2007), Ɗaurayar Gadon Feɗe Waƙa. Zaria: Amana Publishers Ltd.
Usman B. B. (2008), ‘Hikimar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr.) Umaru
Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000) da Waƙoƙinsa’. Kundin digiri na uku,
Sakkwato Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahaya I. Y. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa, Zaria
NNPC.
Yahya A. B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna Fisbas Media Service.
Yahya A. B. (2001), Salo Asirin Waƙa, Kaduna Fisbas Media Service.
Yahaya I. Y. (1992), Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Ibadan,
University Press Ltd.
Zarruk R. M. (1986) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don ƙananan Makarantun
Sakandare. Ibadan University Press Ltd.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.