Ticker

6/recent/ticker-posts

Isa Rasco Dangoma: Ayyukansa A Duniyar Adabin Hausa

Na

Dr. Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Lambar Waya: 07063532532
Ƙibďau: aliyubunzaumar@yahoo.com

www.amsoshi.com

Tsakure


Aikin samar da rubutaccen adabin Hausa wata hikima ce da Allah ya ba waďansu mutane cikin bayinsa. Wasu cikin marubutan sun yi fice, an ji su har ana nazarin ayyukansu a ilmance wasu kuma ba su sami wannan gatancin ba. Isa Rasco Dangoma na cikin marubuta da ba a san da ayyukansu ba a fagen ilimi duk da yawan rubuce-rubucensa da ya fara daga shekarar 1994. Daga wannan shekarar zuwa yau, ya samar da waƘoƘi da Ƙagaggun labarai da fim masu yawa, amma ba a sami wani da ya yi nazari kan adabin nasa ba. Ba shakka, adabin nasa na buƘatar nazari domin a fito da hikimomin da ke ciki, ya kuma bi sahun takwarorinsa. Manufata a wannan maƘala ita ce sharar fage a nazarin adabin Isa Rasco Dangoma.

Gabatarwa


Nazarin rayuwa da adabin wani mutum abu ne da manazarta suka daďe suna yi. Manazarta da yawa (Ɗangambo, 2002 da Usman, 2008 da Maiyama, 2008 da Malumfashi, 2009 da Adamu, 2009 da Bunza, 2009, da Bunza, 2012 da da Isah, 2013 da Bunza, 2014 da sauransu) sun yi ayyuka kan adabin ďaiďaikun mutane. Wannan ya nuna aiki kan wani adabi da adabinsa abu ne mai muhimmanci. Isa Rasco Dangoma wani matashi ne mai shekaru 41 da Allah ya yi wa hikimar shirya rubutaccen adabi. Ya rubuta waƘoƘin Hausa da Ƙagaggun labarai masu yawa, ya kuma shirya finafinan Hausa. Adabinsa ya kasance kan fannonin rayuwa masu yawa kamar faďakarwa da kishi da soyayya da siyasa da sauransu. Duk da yawan ayyukan adabin Hausa da Isa Rasco ya rubuta a iya ƘoƘarina ban ci karo da wani aikin bincike ko nazari da aka yi kansa ba bale a san da shi a ilmance. Na rubuta wannan maƘalar ce domin nazarin adabin nasa a taƘaice. Na taƘaita maƘalar kan tarihinsa da rabe-raben adabinsa da nazarin wasu ayyukan nasa a taƘaice domin yin haka ya kasance somin-taƂi, kuma sharar fage don ci gaba da nazarin taskar adabin nasa. Ba shakka ci gaba da nazarin zai ba da damar fito da hikimarsa da kuma ganin irin tasa basirar. Haka kuma nazarin zai Ƙara faďaďa binciken da ake yi na adabin Hausa.

2.1 TaƘaitaccen Tarihin Isa Rasco Dangoma


Sunansa na yanka shi ne Isa. Sunan mahaifinsa Abdullahi Dangoma.An fi sanin sa da Isa Rasco Dangoma. Ya sami laƘabin ‘Rasco a makarantar boko. An haifi Isa Rasco a shekarar 1975 a wani gari da ake kira Dangoma. Dangoma wani Ƙaramin gari ne da ke cikin Ƙaramar Hukumar Mulki ta Kalgo cikin Jihar Kebbi, Nijeriya. Garin yana gabas ga titi a bisa hanyar Bunza kafin isa wani gari mai suna Sabon Birni. A cewar, Bunza (2016), garin Dangoma yana da tarihi. Na farko a garin ne wani Buzu ya fara ya da zango da littafin ‘Jawahirul Ma’ani’ na tafsirin AlƘur’ani mai girma. .
Lokacin da Isa yake Ƙaramin yaro mahaifinsa ya sa shi makarantar allo ta Malam Muhammadu Dangoma. A wannan makaranta ya sauke AlƘur’ani mai girma kuma ya fara shiga cikin littattafan sani na fiƘihu da hadisai kamar Ƙawa’idi da Ahalari da Arba’una Nawwawi da Majamu’ul Baharaini da sauransu.
Bayan makarantar allo, an sa Isa Rasco makarantar firamare a garinsu na Dangoma (Dangoma Model Primary School). Bayan da ya kammala sai ya wuce ta gaba da Firamare a Government Secondary School, Gwandu (GSS Gwandu) daga shekarar 1989 zuwa 1994. A wannan shekara ce (1994) ya fara gabatar da adabinsa da wata waƘar Hausa ta Madahu mai suna ‘Ɗan Aminatu’ inda ya yi yabo ga Manzon Allah (S A W).
Isa Rasco ya yi karatu a makarantar Kimiyya da Ƙere-Ƙere, (Birnin Kebbi Polytechnic) inda ya kammala a shekarar 1997. A nan ya sami takardar shaidar kammala Ƙaramar Diploma ta ND a Sashen Sanin Yanayin Ruwa Da Ƙasa (Soil and Water ConserƂation). A shekarar 2006 ya sake komawa makarantar ya yi babbar Diploma (HND) ya kammala a 2007 a wannan fannin da ya karƂi takardar shaida ta Ƙaramar Diploma.
A gwagwarmayar rayuwa, Isa ya fara aiki bayan kammala Diplomarsa a wani Kamfanin Ɗab’i mai suna Mubel Printing Press da ke Birnin Kebbi a shekarar 1999. Shiga wannan kamfani sai Allah ya sa ya zama Ƙwararre a aikin na ďab’i (Rubutu a Injimin Rubutu). Da yake tun lokacin da yake matashi ya zan yana sha’awar aikin jarida, da karatun Ƙagaggun labarai, sai ya yi amfani da damarsa ta aikin kamfanin na ďab’i ya fitar da littafin Ƙagaggen labari na farko mai suna ‘WasiƘa Abin Ado Ga Masoya’. Tun daga wannan lokaci Isa Rasco ya ci gaba da zurfafa ga rubuce-rubuce na waƘoƘi da littattafai da kuma shiga harkar samar da fim yana kuma samun yabo da godiya ga wasu masu karanta adabin nasa.

3.1 Isa Rasco Dangoma Da Rayuwar Adabin Hausa


Isa Rasco Dangoma mutum ne da Allah ya ba hikimar sarrafa tunaninsa a rubuce domin isar da saƘo ga al’umma. Wannan ya sa ya yi rubuce-rubuce masu yawa. Shi kansa rubuce-rubucen nasa sun yi tasiri sosai ga ci gaban rayuwarsa. Da rubuce-rubuce Isa ya san mutane masu yawa, su ma suka san shi. Ta wannan hanya ya gina gidansa, ya sayi mota. A halin yanzu, adabi ya kasance sana’a gare shi, kuma yana ďaya daga cikin hanyoyin rayuwarsa. Adabin nasa ana iya kasa su gida uku: waƘa da Ƙagaggen labari da kuma fim.

3.1.1 WaƘa


Isa Rasco ya rubuta waƘoƘin Hausa masu yawa daga shekarar 1994 lokacin da ya fara waƘarsa mai suna Ɗan Aminatu. WaƘar Ɗan Aminatu waƘa ce ta madahu wadda ya yabi Manzon Allah (S A W) a cikinta. Ya rubuta waƘar bisa tsarin ‘yar Ƙwar huďu, kuma cikin baituka 40. Babbar Ƙafiyar wannan waƘa ita ce gaƂar kalmar ‘ba’ da ke zowa a Ƙarshen kowane baiti. Dan a tambaye shi dalilinsa na fara waƘar Madahu. Ya nuna cewa, bai san wani tsayayyen dalili ba domin yana yaro ya rubuta ta. Abin da kawai yake cewa, shi ne shi Musulmi ne mai son Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Tun bayan wannan waƘa, Isa ya ci gaba da rubuta waƘoƘi kan fannonin rayuwa daban-daban. A hirar da na yi da shi ya nuna cewa, ya rubuta waƘoƘi sama da ďari biyu tsakanin na madahu da siyasa da yabo da aure da kuma ilmantarwa. Ga wasu kaďan daga cikin waƘoƘin nasa:

Ɗan Aminatu, Manzo Muhammad, Sayyadil Anbiyyah, Nana Aisha, Sayyadi Abubakar, Dan Khaďďab (Umar), Ɗan Attanna, Sayyadi Ali, ‘Yar Manzona Fatima, YaƘin Uhudu Nana Khadijat, Ya Muhammadu Manzon Allah (SAW), You Are Prophet (Saw), Sayyadi Hamza Zakin Allah, Uwar Mummunai A’isha, Mu Yo Soyayya, Tafi Tafiya Za Ni Yi
Kofi-Kofi, Ehl Lallai Soyayya, Sahibata, Sahibina, Uwar Gida Ran Gida, Naf Studio. Mu Ne Fa Ɗaliban, Tsadar Rayuwa, Duniya Ho! , Illar Talla, Bangar Siyasa, Mu Yo Ilmi, Kishin Ƙasa, Dogara Da Kai, An Sa Ta Lalle (Ɗan Alhaji), Auren Soyayya, Auren Sunnah A Yau An Ka Ɗaura, Aure Yau Fa An Ka Ɗaure, Arzika Zaki Ango, Zayyanu Da Zainab Auren Sunnah, Atiku Ya Share Ga Amarya, Matar Mutun Kabarinsa, Rangwaďa Amarya Yau Ranar, ‘Yan Uwa Da Masoya, Marhaban Marhaban (Ɗakin Gari), Ɗan Baiwa, An Haďe An Zamo Ɗaya, PDP Sak (Ɗakingari), CPC Ce Muke Shiga (CPC).

3.1.2 Rubutaccen Ƙagaggen Labari

Rubutaccen Ƙagaggen labari wani faďaďďen labari ne, watau labari ne na zube wanda ake rubutawa da yake bayani game da mutum da yanayin zamantakewa, tare da kawo wani abu da yake faruwa a rayuwar al’umma. Haka ma abin yana iya kasancewa ko bai faru ba, amma ana hasashen faruwarsa (Bunza, 2011). Shi wannan nau’in rubutaccen adabin Hausa an fara samar da shi ne daga shekarar 1933. Adabin ya bunƘasa a tsakanin shekarar 1984-2010 lokacin da aka Ƙiyasta akwai littattafai sama da 3,500 (Malumfashi, 2010). Daga wannan lokaci 1984 –yau matasa masu yawa sun yi rubuce-rubucen Ƙagaggen labarin Hausa kan fannonin rayuwa masu yawa aka kuma sami masu nazari da suka ba adabin nasu sunaye daban-daban. An kira rubuce-rubucen adabin da sunaye kamar Adabin Kasuwar Kano da Littattafan Soyayya da Adabin Hausa Na Zamani da Hadisan ‘Yan Kano da Rayayyen Adabin Hausa (Malumfashi, 2002 da Adamu, 2013). Isa Rasco ya kasance ďaya daga cikin matasan da suka samar da wani Ƃangare na wannan adabi.
Isa ya fara rubuta Ƙagaggen labari ne da wani littafi mai suna ‘WasiƘa Abin Ado ga Masoya’ a shekarar 1999. Shi wannan littafi ne da ke kan jigon soyayya da yadda ake samun shigar soyayya tsakanin ‘ya’yan talakawa da ‘ya’yan masu kuďi. Ya rubuta littafin ne saboda a daidai wannan lokaci ne lamarin soyayya ya fara shiga rayuwarsa. Ya fara karanta littattafan soyayya da aka rubuta. Tun daga wannan lokaci Isa Rasco ya ci gaba da rubuta littattafan Ƙagaggun labarai inda zuwa yau ya rubuta littattafai masu yawa waďanda kuma aka buga su a maďaba’arsa mai suna Nabila Printing Press, Birnin Kebbi. Ga jerin littattafan nasa:
WasiƘa Abin Ado Ga Masoya 1 Da 2 (1999)
Gayun Zamani Ga Gida Ga Naira (2001)
Balkisu Koka-Kola (2002)
Maza Allurar Guba 1 Da 2 (2002)
Shafin Zuciya (2002)
Komai Saurin Narba Tana Barin Talata Ta Wuce (2005)
Zama Da Kishiya Riba Ce
‘Yar Ƙwalisa 1 Da 2 (2001)
AlƘawari Da Macce Aikin Banza 1 Da 2 (2008)
Hattara Ɗan Tsako Shaho Na Kallon Ka (2008)
Ɗan Duniya HayaƘin Taba 1 Da 2 (2013)
Ƙarya Linzamin Shaiďan. Da dai Sauransu.

3.1.3 Fim

Fim wani Ƃangare ne daga kafar sadarwa ta lantarki wadda take samar da gani da ji da motsi, domin amfanin mutane masu yawa. (Gidan Daboni da Yakasai, 2004). Fim wani nau’in wasa ne da ake shirya wasu abubuwa na yanayin rayuwa a aiwatar da su zahiran, kamar dai wasan kwaikwayo. Tarihi ya nuna an fara samar da fim na Hausa a tsakanin shekarar 1980-1984 a garin Kano lokacin da wasu Ƙungiyoyi suka fara aiwatar da shi. A wannan lokaci ne wata Ƙungiyar wasan kwaikwayo mai suna Gyaranya ta samar da wasu finafinai biyu; ďaya ya Ƙunshi sigar fim na Ƙasar Sin na faďace-faďace. Ɗaya kuma sigar fim irin na Ƙasar Indiya na yadda suke rawa da waƘa (Chamo, 2004). Al’amarin fim na Hausa ya ci gaba ya bunƘasa daga shekarar 1999 lokacin da marubuta matasa da dama suka mai da hankali ga shirya finafinai da aiwatar da su (Malumfashi, 2002). Wannan ya sa aka sami finafinan Hausa masu yawa kan jigogin rayuwa daban-daban.
Isa Rasco Dangoma ya kasance ďaya daga cikin marubutan Hausa da suka taka rawa ga samuwar fina-finai ko bayan rubuce-rubucen da suka ci gaba da aiwatarwa. Isa ya kasance yana shirya fina-finansa ne ba tare da amfani da juya wani littafinsa zuwa fim kamar yadda wasu marubuta suke yi ba. Ya fara shiga harkar fim ne a shekarar 2004 lokacin da ya samu fitar da wani fim mai suna ‘Baya Da Ƙura’. A halin yanzu ma yana kan shirya wani fim mai suna ‘Bokon Zamani’. Dukkan fina-finan nasa yana shirya su ne tsakanin garuruwan Birnin Kabi da Kalgo zuwa Kamba. A waďannan garuruwa yake samun yawancin taurarin fina-finansa, ya Ƙara da wasu daga Kano kamar Ahmed Tagge. Kowane fim nasa ya warware jigonsa cikin kaset na CD guda ďaya. A kamfaninsa mai suna Rasco Fim Production da ke Birnin Kebbi yake tsara su tare da haďin guiwar Tagge Production Kano. Waďannan su ne fina-finan da ya fitar zuwa yau. Ga finafinan kamar haka:
Baya Da Ƙura
Bokon Zamani

4.1 Rabe-Raben Jigogin Adabin Isa Rasco


Jigo shi ne manufar ko maƘasudi yin wani abu, ko Ƙaga wani abu, ko tsara yin wani abu (Bunza, 2009). Isa Rasco ya rubuta ayyukan adabinsa da manufar isar da wasu saƘonni daban-daban ga al’umma. Jigogin na adabin nasa sun haďa da soyayya da yabo da madahu da siyasa da aure da faďakarwa da kishi tsakanin mata da sauransu. A nan za a raba ayyukan nasa ta fuskar jigoginsu.

4.1.1 Soyayya

Soyayya hanya ce ta nuna Ƙauna tsakanin mutane musamman tsakanin maza da mata. Soyayya ta kasance wani muhimmin jigo da marubutan adabin Hausa suka yi rubuce-rubuce da dama kansa. A irin wannan jigo ne ake nuna yadda mace ke son namiji ko namiji ke son mace. Haka kuma ta wannan hanya ake bayyana matsayin masoyi a zuciyar mai son sa. Ana bayyana wasu abubuwa da soyayya ke haifarwa masu kyau ko marasa kyau da kuma bayyana gurin da masoya suke da shi na yin aure. Rubuce –rubucen jigon soyayya sun taka rawa ga bunƘasa adabin Hausa da kuma taƂarƂarewar wasu sassan tarbiyyar al’ummar Hausawa.
Isa Rasco ya samar da wasu ayyukan adabi kan jigon soyayya waďanda a cikinsu ya faďi abubuwa da dama kan abin da yake hasashe kan soyayyar zamani. Ga wasu daga cikin adabinsa na soyayya:
WaƘoƘi
Mu Yo Soyayya
Tafi Tafiya Za Ni Yi
Kofi-Kofi
Eh! Lallai Soyayya
Sahibata, Sahibina
Uwar Gida Ran Gida
Muna Fa Ɗaliban
Tsabar Rayuwa

Littattafan Zube
WasiƘa Abin Ado Ga Masoya (1999)
Gayun Zamani Ga Gida Ga Naira (2001)
Balkisu Koka-Kola (2002)
Shafin Zuciya (2002)
Komai Saurin Narba Tana Barin Talata Ta Wuce (2005)
‘Yar Ƙwalisa Sarauniyar ‘Yan Mata

4.1.2 Madahu

Madahu jigo ne na yabon Annabi (S A W) ko sahabbansa ko iyalansa. Rubuce-rubucen madahu abu ne da aka daďe ana yi, musamman waƘoƘi. Marubuta waƘoƘin Hausa da dama sun rubuta waƘoƘi inda suka yabi waďannan fiyayyun mutane don nuna Ƙauna gare su. A waďannan waƘoƘi ana bayyana gudummuwar da waďannan mutane suka ba da wajen ci gaban addinin Musulunci ta fuskar jihadi da karantarwa. Daga baya an sami wasu masu madahu da suke yi kan waliyyai da shaihunnai da wasu magabata malamai.
Isa ya shiga cikin waďannan marubuta da suka yi madahu ga Annabi (S A W) da wasu sahabbansa kamar Abubakar da Umar da Aliyu da kuma iyalan gidan Annabi (S A W) kamar Khadija da A’isha da Fatima (A S) da sauransu.Ya nuna ya yi waďannan waƘoƘi ne domin neman lada ga Ubangiji ba don wani abin duniya ba. Ya kai wasu kaset-kaset guda shida na wasu waƘoƘin nasa na madahu a gidan Radiyon Jihar Kebbi inda ake sa su don watsawa ga jama’a. Ga wasu daga cikin waďannan waƘoƘin.

Ɗan Aminatu
Manzo Muhammad
Ya Muhammadu Manzon Allah (SAW)
You Are Prophet (SAW)
Sayyadil Anbiyyah
Nana Khadijat
Nana A’isha
Uwar Mummunai A’isha
Sayyadi Abubakar
Ɗan Khaďďab (Umar)
Sayyadi Ali
‘Yar Manzona Fatima
YaƘin Uhudu
Sayyadi Hamza Zakin Allah

4.1.3 Yabo

Yabo na ďaya daga cikin muhimman jigogin da aka yi rubuce-rubucen Hausa kan su.Yabo na nufin faďar wata kalma mai daďi game da wani wadda idan ya ji ta zai ji daďi, ta kuma sa mutane su so shi, su kuma Ƙara ganin girmansa. A wannan jigo ne marubuci kan kawo wasu muhimman abubuwan gwarzanta mutum domin daďaďa masa rai da kuma jan ra’ayin mutane don su so shi. Ire-iren abubuwan da ake yaba mutum da su yawanci sun haďa da hali na gari da riƘon addini da taimakonsa da kyauta da ilimi da sauransu.
Daga cikin adabin Isa Rasco akwai waƘoƘin da ya shirya kan wannan jigo. Su waďannan waƘoƘi, Isa ya rubuta su ne bisa nufin yaba wasu mutane da yake jin sun cancanci ya yaba su saboda arzikinsu da kuma yadda suke sarrafa shi ko kuma saboda mulkinsu da sauransu. Ga kaďan daga cikin waďannan waƘoƘi nasa:
Ɗan Bauran Gwandu (SadiƘ Marafa)
Kabiru Kamba Zakin Fama
Chairman Ciyamomi (Hannu ba ka da tsoro)
Duk Jama’ar Kalgo (Ali Diggi)
Ibrahim Basaura Sadauki (Chairman Jega)
Mazan Jiran Maza (Hannu Ba ka da tsoro)
Chairman Maiyama Zakin Fama (UU)
Sarkin Gwandu (Iliyasu Bashar)
MagayaƘin Kebbi

4.1.4 Kishi

Kishi na nufin rashin jituwa da nuna Ƙyashi wanda matan da ke auren mutum ďaya ke yi wa juna (CNHN, 2006). Shi kuma Bakura (2014) ya bayyana ma’anar kishi da cewa tsananin son da mace ke yi wa mijinta ko neman keƂancewa zuwa ga mijinta ko wanda take son ta aura, da take nuna Ƙauna, da kyakkyawar fata gare shi, tare kuma da nuna Ƙiyayyarta ga duk wata da take son sa da aure ko kuma shi yake son ta da aure. Kishi wani abu ne sananne a rayuwar matan Hausawa wanda wannan ya sa ake kiran sa kumallon mata. Da wuya a sami wata mace da ke son kishiya bale ta goyu bayan mijinta ya Ƙara aure.
Marubuta adabin Hausa da dama sun yi rubuce-rubuce kan lamarin kishi. Wasu sun kalle shi a matsayin mugun abu. Wasu kuma sun kale shi a matsayin abin dole ga mata. Akwai waďanda kuma suka yi rubutu don daidaita zaman kiyoshi da sauransu.
Isa Rasco ya kasance ďaya daga cikin marubutan da adabinsu kan kishi shi ne na ƘoƘarin gyara a zaman kishiyoyi. Littafinsa na Zama Da Kishiya Riba Ce ya tabbatar da mace ba ta son kishiya domin tsoron yanayin zaman da ake yi maras aminci. A wannan littafi Isa ya nuna akwai hanyoyin kyautata zaman kishi har mata su zama ‘yan uwa. Wannan littafi shi ne kaďai adabinsa kan jigon kishi

4.1.5 Siyasa

Siyasa ita ce tafiyar da al’amuran jama’a ta hanyar neman ra’ayinsu (CNHN, 2006). Siyasa ƘoƘari ne na kafa ko ďabbaƘa wani abu, ko kuma neman rusa wani abu, ko neman samar wa wani abu ‘yanci, ko matsayi, ko kuma tallata wani abu ya samu shiga da karƂuwa da kafa gwamnati domin tafiyar da lamarin mulkin jama’a kan wanda suka zaƂar wa kansu.
Al’amarin siyasa ya kutsa cikin al’amurran rayuwa mutane na yau da kullum da yawa. Neman matsayi a gwamnati ko kafa gwmanati abu ne da koyaushe yake buƘatar marubuta adabi musamman mawaƘa domin farfaganda da kuma watsa manufar jam’iyya ko ďan takara cikin zukatan mutane. Marubuta waƘa a fagen siyasa suna cikin masu tallata ďan siyasa, su kai shi inda Ƙafafunsa ko hotonsa bai riga ya isa ba. Wannan ya sa kowace jam’iyya da kuma kowane ďan takara suke amfani da mawaƘa a matsayin wata kafa ta watsa manufofinsu da kuma mai da martani ga wanda ke suka ko Ƙalubalantar su.
Isa Rasco ya taka rawa wajen rubuta waƘoƘin siyasa. Ya rubuta waƘoƘi don tallata wasu jam’iyyu da wasu ‘yan takara musamman na jihar Kebbi bias ga nemansa da aka yi ya rubuta, wasu kuma don ra’ayinsa ga ďan siyasa. Dukkan waƘoƘin yakan rubuta su, ya kuma rera su da kansa, wani lokaci tare da masu amsa masa. Ga wasu cikin waƘoƘinsa na siyasa.
An Haďe an Zamo Ɗaya
PDP Sak (Ɗakin Gari)
CPC Ce Muke Shiga (CPC)
A Kasa A Tsare (CPC)
Buhari Mazan Fama (CPC)
Kainuwa Dashen Allah (Ɗakin Gari)
Ɗan Tsiron Da Allah Ke So (Shatima)
Nasamu 2 Terms (Nasamu)
7 Point Agenda
Sakkwatawa Muna Murna (Alu Wamakko)
Sauyin Zamani
2007 Nasamu
2011 CPC
ANPP Muke Shiga (ANPP)
Ibrahim Bande Jarumi (Ɗan Majalisa)
Yanzu Kebbi Ta LeƘo Ta Koma (Ɗakin Gari)

4.1.6 Aure

Aure na nufin halartaccen zaman tare tsakanin namiji da mace da aka shirya bisa hanyar da al’umma ta amince da ita. Aure ya kasance jigo muhimmi da ya kawo samuwar wasu ayyukan adabin Hausa masu yawa. Marubuta da dama sun yi rubutu kan lamarin aure. Wannan kuwa ya shafi ko dai taya murna ko kuma hannunka mai sanda kan wasu matsalolin aure. Ta wannan hanya wasu marubuta ke watsa shawarwari kan yadda ya kamata ma’aurata su zauna don samun natsuwa da kyakkyawar rayuwa a tsakaninsu. Wasu marubuta kuma a cikin rubutu suke bayyana wa ma’aurata haƘƘoƘin da suka rataya kan su. Mata sau da yawa cikin adabi sukan tsinci bayanan da ke nuna musu matsayinsu na masu kula da gida da bayyana ayyukan tafiyar da gida da kula da miji da tsabta da sauransu. Shi ma namiji ana bayyana masa haƘƘoƘin kula da matarsa da kawo abinci da sauransu. A yau rubuce-rubuce kan jigon aure musamman waƘa sun zama wata hanyar rayuwa ga wasu da ke da hikimar wanda har akan gayyace su daga gari zuwa gari a ďauki ďawainiyarsu, a kuma biya su.
Isa Rasco ya rubuta adabi kan jigon aure musamman waƘoƘi. A cewarsa, yana rubuta waƘoƘin aure ne idan wani cikin ma’aurata ya buƘace shi da yin haka. Ya rubuta waƘoƘin aure masu yawa. Ga kaďan daga cikinsu.

An Sa Ta Lalle (Ɗan Alhaji)
Auren Soyayya
Auren Sunnah A yau Anka Ɗaura
Aure Yau Fa An Ka Ɗaure
Arzika Zaki Ango
Zayyanu da Zainab Auren Sunnah
Atiku Ya Share Ga Amarya
Matar Mutun Kabarinsa
Rangwaďa Amarya Yau Ranar
‘Yan uwa da Masoya

4.1.7 Faďakarwa

Faďakarwa na nufin tunatar da mutane da fahimtar da su wani abu muhimmi da zai taimaki rayuwarsa ta hanyoyi masu yawa. Usman (2008), ya nuna cewa, faďakarwa hanya ce ta waye wa mutane kai kan wasu al’amurra da yake ganin suna da alfanu gare su. Ana yin haka ne don nuna wa mutane muhimmancin wani abu domin su jiƂinci aikata shi saboda muhimmancinsa. Wani lokaci ana faďakar da mutane illar wani abu domin su nisantar da kansu daga gare shi. Lamarin faďakarwa abu ne muhimmi da ya ja hankalin marubuta suka yi rubuce-rubuce kansa. Marubuta da dama sun yi rubuce-rubucen faďakarwa kan kyautata tarbiyya da gyaran al’umma kamar illar jahilci da shaye-shaye da zaman banza da talla da kuma muhimmancin ilimi.
Isa Rasco ya bi sahun wasu marubuta inda ya rubuta adabi domin faďakar da mutane wasu muhimman abubuwa da suka jiƂinci kyautata rayuwar Hausawa da ci gabanta. Ga wasu ayyukan adabinsa na faďakarwa.

WaƘa
Illar Talla
Bangar Siyasa
Mu Yo Ilmi
Kishin Ƙasa
Dogara Da Kai

Littattafan Zube
Maza Allurar Guba (2002)
Alkawari Da MacceAikin Banza (2008)
Hattara Ɗan Tsako Shaho Na Kallon Ka (2008)
Ɗan Duniya HayaƘin Taba (2013)
Ƙarya Linzamin Shaiďan

Fim
Baya Da Ƙura
Bokon Zamani (Bai riga ya fito ba)
5.1 TaƘaitaccen Bayanin Wasu Ayyukan Adabin Isa Rasco
Da yake an ga ayyukan adabin Isa Rasco, a nan nake son in yi bayani taƘaice kan Ƙumshiyar wasu ayyukan adabin nasa. Na zaƂi littafi ďaya mai suna Zama Da Kishiya Riba Ce da kuma fim ďaya na Muhimmancin Ilimi.

5.1.1 Zama Da Kishiya Riba Ce

Zama da Kishiya Riba Ce littafi ne da aka shirya kan jigon kishi. Yadda labarin yake shi ne, wani mutum ne mai suna Dr. Halliru ya auri wata Ba’indiya mai suna Mirsiyya. Dr. Halliru ďan wani hamshaƘin mai kuďi ne a garin Kano. Ubansa ya rasu ya bar masa dukiya mai yawa. Ita kuma Mirsiyya can farko Kirista ce ana kiran ta Bolgat. Da ta Musulunta sai iyayenta suka kore ta ta koma garin New York da zama. A can New York shi kuma Dr. Haliru yake a wannan lokaci yana karatu.
Wata rana ya je wani hotel mai suna New York Hotel sai ya haďu da wannan mata, kuma ya ji yana son ta. Ya je ya yi mata magana, aka yi dace suka daidaita maganar aure. Suka je wajen wani Ƙanin babanta wanda yake Musulmi ne aka canza mata suna daga Bolgat zuwa Mirsiyya. Daga nan bayan wata biyar aka ďaura musu aure. Suka ci gaba da zama har lokacin da ya Ƙare karatu ya ďauko ta suka koma Kano da zama. A nan suka ci gaba da zama cikin daula har tsawon shekaru goma sha ďaya. Tsawon wannan lokaci ba abin da ke damun su illa rashin haihuwa.
Ana nan wata rana Dr. Halliru ya fita yawo da yamma sai ya haďu da wasu ‘yan mata biyu; ďaya ana kiran ta Hajaru, ďaya kuma Lanti. Da ganin waďannan ‘yan mata sai ya ji yana son Hajaru. Bai tsaya ba ya je wajen su ya gaisa da su, ya kuma nuna soyayyarsa ga Hajaru har ya ďauke su da mota ya kai su inda za su je. Hajaru ta amince, ta kuma nemi ya je wurin iyayenta. Dr. Halliru ya aika magabatansa aka shirya maganar aure aka kuma sa lokaci. Wannan ya sa Dr. Halliru da Hajaru suka ci gaba da soyayya. Duk wannan abu bai gaya wa Mirsiyya ba.
Wata rana ya shigo gida sai ya sami Mirsiyya cikin damuwa.Ya tambaye ta ba ta ce komai ba. Daga nan ya gabatar mata da maganar Ƙara aure ita kuma ta nuna rashin yardarta. Ga yadda suka yi kan maganar:
‘A gaskiya ina ganin ya fi kyau na karo mata mugani ko Allah zai ci da mu…’
Ita kuma ta ba shi amsa da cewa;
‘Ba za ni yarda da kishiya ba har iyakar raina. Kuma komai ya faru tsakanina da kai to kai ne ka jawo shi. Ka kuma tuna na bar iyayena, na bar daula, na bar kasarmu don kawai in aure ka in yi maka biyayya. Shi ne ya sanya ni barin kasarmu da duk dangina. Amma ga shi kana son ka yi mini sakiyar da ba ruwa’ (shafi na 29).

Jin wannan magana ta sa Dr. Haliru ya ji tsoron gabatar da maganar aurensa ga Mirsiyya. Ana nan wata rana sai wata mata mai suna Malka mai haja ta je talla wajen Mirsiyya. Suna cikin magana sai Malka ta gaya mata cewa, mijinta na nan yana maganar aure har ma an yi kusan sa amarya lalle. Wannan magana ta tayar da hankalin Mirsiyya, ta shiga damuwa sosai.
Bayan an ďaura auren Dr. Halliru da Hajaru da kuma tarewar amarya ďakinta, sai Mirsiyya ta shiga kishi. Bayan wani lokaci zaman nasu ya yi kyau saboda Hajaru na ba Mirsiyya girmanta da kuma kare mutuncinta koyaushe. Haka zaman ya ci gaba har su duka suka haihu. Hajaru ce ta fara haihuwa aka raďa wa yaro suna Mas’ud. Ita kuma Mirsiyya bayan wata shida ta haihu aka sa wa yaro suna Fahad. Yaran suka tashi suna son juna, iyayen nasu suka zauna lafiya.

5.1.2 Baya Da Ƙura

Baya Da Ƙura fim ne da Isa Rasco ya shirya A Rasco Fim Production Birnin Kebbi a ƘarƘashin umurnin Ahmad Tagge. An shirya wannan fim ne kan jigon faďakarwa kan muhimmancin ilimi da kuma illar talla ga ďiya mace. Yadda wannan fim ya gudana shi ne wasu mata ne kishiyoyi su biyu. Ɗaya sunanta Rashida, ďaya kuma Hauwa’u. Ita Rashida ita ce uwar gida tana da ‘ya’ya uku duka mata. Ita kuma Hauwa’u (Amarya) tana da ďiya ďaya.
Uwargida Rashida babban burinta shi ne yaranta su sami ilimin addini da na boko. Wannan ya sa kowace rana takan tabbatar da yaran sun tafi makaranta ko da kuwa tana da wani abu da take son su yi mata. Da wannan tsari na karatu akoyaushe yaran nata suka taso har suka girma.
Amarya ita kuma babban abin da ta sa gaba shi ne ‘yarta ta nemi kuďi ta tara kaya domin aurenta. Wannan ya sa kowace rana sai ta shirya wa yarinyar wani abu da za ta je talla a kasuwa ko tasha ko filin wasa. Duk lokacin da uwargida ta ja kunnenta kan yadda take hana ďiyarta zuwa makaranta da aza mata talla, sai ta yi cikin ta da faďa tana faďin ita ba za ta bari su yi kunyar ‘yan wari ba. A tashi aure ba su aje komai ba sai tarin takardun banza da biro. Haka ita kuma wannan yarinya ta ci gaba da rayuwarta.
Wata rana yarinyar ta fita talla a gareji wurin kanikawa sai ta sami wani saurayi mai suna A- Sa- Ni- A- Layi. Bayan da ya kira ta suka gaisa, sai ya saye dukkan abarbar da take ďauke da ita kan kuďi naira dubu da ďari biyar. Daga nan ya yi mata alƘawalin duk lokacin da ta biyo zai saye mata sana’arta don ba ya son ganin ta tana wahala. Sannu-sannu yarinya ta ci gaba da zuwa har ya ja ta ďakinsa har ya kai ya yi mata ciki. Da ciki ya bayyana amarya ta yi da –na- sani da baƘin cikin ďora ďiyarta ga tallace-tallace.

6.1 Kammalawa


Idan aka yi nazarin abin da ya gabata a wannan maƘala za a ga cewa, Isa Rasco Dangoma ya kasance ďaya daga cikin matasan zamani da suka ba da gudummuwa kan ci gaban adabin Hausa. Ya yi rubutu a dukkan fannoni uku (waƘa da zube da wasan kwaikwayo) na adabin Hausa. Da yake an taƘaita nazarin adabin nasa, an yi haka ne domin nazarin ya zama shimfiďa ga fito da shi da kuma matashiya ga ci gaba da nazarin taskar adabinsa.
MaƘalar ta gano cewa, akwai ďimbin abubuwan nazari a fannin harshe da al’ada da ma cuďeďeniyar adabi cikin adabin Isa Rasco Dangoma. An lura akwai salon sarrafa harshe da aron kalmomi da tasirin karin magana da baƘar magana da kirari masu yawa cikin adabin nasa. Wannan na buƘatar faďaďa nazarin adabin nasa ga manazarta da ďalibban ilimi domin fito da waďannan abubuwa.
Wani abu kuma shi ne, lura da aka yi cewa, Isa Rasco Dangoma bai karanci Hausa a matakin gaba da sakandare ba bale ya san tsare-tsaren rubutun Hausa. Don haka ci gaba da nazarin zai ba da damar jawo shi kusa ga masana don kyautata aikin adabinsa, ya ďora shi bisa Ƙa’idodjin rubutun Hausa don inganta shi. Da haka sai y azan an kyautata tunaninsa da rubutunsa don a gudu tare, a tsira tare.
Daga Ƙarshe maƘalar na tabbatar da cewa, ba shakka idan aka ci gaba da nazarin adabin Isa Rasco Dangoma za a tsinto muhimman abubuwan da suke Ƙunshe cikin hikimar da Allah ya yi masa ta rubuta adabin Hausa. Don haka akwai buƘatar manazarta su san da haka, su kuma sa wannan cikin tunaninsu.

 

karanta wani:

https://www.amsoshi.com/2017/07/09/family-life-education-foundation-human-social-security/

Manazarta


Abdullahi, A. M. (1998), Abubakar Imam: Nazarin Tubali Da Ginuwar Ayyukansa Na Adabi. Kundin Digiri Na Ukku, Kano: Jami’ar Bayero.

Adamu, Y. M. (2013), Ruwan Saman Marubuta A Ƙasar hausa: Daga Damunar 1980 Zuwa Yau. Cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture the 1st National Conference. Centre for the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University,

Ahmad, A. A. (2009), Rupert Moutrie East: Gudummuwarsa Ga Adabin Hausa Da Kuma Sharhi Kan Ayyukansa. Kundin Digiri Na Uku, Kano: Jami’ar Bayero.

Bakura, A. R. (2014), Kishi A Ƙasar Hausa. Kaduna: Garkuwa Media Services.

Bunza, A. M. (2009), Narambaďa. Lagos: Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.

Bunza, D. B. (2012), Nazarin Diwanin Malam Maharazu Barmo Kwasare. Kundin digiri na biyu, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Bunza, A. M. (2014), In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka (Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo). Cairo: Elkods Printing House.

Chamo, I. Y. (2004), Tasirin Al’adun Turawa A Cikin Finafinan Hausa. Cikin Hausa Home Ƃideos: Technology, Economy and Society. Kano: Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa Tare da Haďin Guiwar Adamu Joji Publishers.

Dangoma, I. R. (ba shekara), Zama Da Kishiya Riba Ce. B/Kebbi, Kebbi State: Nabila Printing Press, Rafin Atiku Beside NULGE Office.

Ɗangambo, H. A. (2002), Gaskiya Da Almara Cikin Littafin Ganďoki Na Walin Katsina Alhaji Bello Kagara. Cikin Algaita Journal Of Current Research in Hausa Studies Ƃol. 2, No. 1. Kano: Jami’ar Bayero.

Gidan Dabino, A. A. da Yakasai, B. M. (2004), Matsaloli Da Nasarorin Masu Shirya Finafinan Hausa Musamman Na Kano. Cikin Hausa Home Ƃideos: Technology, Economy and Society. Kano: Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa Tare da Haďin Guiwar Adamu Joji Publishers.

Isah, Z. (2013), Gudummuwar MawaƘan Hausa Ga Ci Gaban Arewacin Nijeriya: Nazarin WaƘar ‘AJANDA’ Ta Haruna Aliyu Ningi. Cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture the 1st National Conference. Kano: Centre for the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University.

Malumfashi, A. I. (2010), Hausa Literature At 50: The Interface Of Tradition, Arab and Colonial Heritages, Takardar da aka gabatar a taron cikar Nijeriya shekaru 50. Jami’ar Port Hacourt, Nijeriya.

Malumfashi, I. (2009), Adabin Abubakar Imam. Sakkwato. Garkuwa Media Services.

Malumfashi, I. A. M. (2002), Adabi Da Bidiyon Kasuwar Kano A bisa Faifai: TaƘaitaccen Tsokaci. Presented at taron Ƙara wa juna sani kan sabon Tafiyar Adabin Hausa, Cibiyar Nazarin Hausa, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Malumfashi, I. A. M. (2006), Ginuwar Ƙagaggun Labaran Hausa: Ƙarin Haske. Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Ƃol. 1 No. 1. Kano: Jami’ar Bayero.

Malumfashi, I. A. M. (2011), Ta’aziyyar Adabin Kasuwar Kano. Cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture The Siďth Hausa International Conference, Centre for the Study of Nigerian Languages, Kano: Bayero University.

Mukhtar, I. (2004), Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai. Kano. Adamu Joji Publishers.

Usman, B. B. (2008), Hikamar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000) Da waƘoƘinsa. Kundin Digiri na Uku, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce : Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC.
Yahya, A. B. (1997), Jigon Nazarin WaƘa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Post a Comment

3 Comments

Post your comment or ask a question.