Ticker

6/recent/ticker-posts

Waiwaye Adon Tafiya: Fadakarwa A Cikin Kagaggun Labaran Hausa

Na

Umar Aliyu Bunza

Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Waya: 07063532532, 08095750999
Ƙibďau: aliyubunzaumar@yahoo.com

Satumba, 2013

1.0 GABATARWA


Faďakarwa aba ce da ake samu a cikin kowane nau’i na adabin Hausa. Wannan ya sa lamarin faďakarwa ya kasance ruwan dare cikin adabin Hausa na baka da rubutacce.
Ƙagaggen labari wani nau’i ne na rubutaccen adabi da aka fara samarwa cikin Hausa bayan wanzuwar mulkin mallaka da kafa hukumomin inganta adabin Hausa. A zamanin rayuwar Hukumar Talifi ne aka fara samar da wannan nau’in adabi dalilin gasar da hukumar ta shirya a dukkanin faďin Arewacin Nijeriya. Tun daga wannan lokaci zuwa yau, Ƙagaggen labarin ya ci gaba da samun karƂuwa ga hukumomi da ďaiďaikun mutane har zuwa yau da ake jin akwai littattafan Ƙagaggun labaran Hausa sama da 3, 500 (Malumfashi, 2010). Littattafan da aka samar sun kasance wata hanya muhimmiya don samar da nishaďi da gargaďi da faďakarwa da koyar da al’umma dabarun rayuwa da sauransu. Ganin wannan matsayi da Ƙagaggen labari ya samu na zamansa komai da ruwanka a al’amurran yau da kullum na rayuwar al’umma, ya sa na shiga cikin wasu littattafai domin kalato darussan faďakarwa da marubutan suka gina a cikin rubuce –rubucensu. Duk da yake Ƙagaggen labari ne ginshiƘin maƘalar, na kauce wa duba tarihin Ƙagaggen labarin da nau’o’insa ba don komai ba sai don ganin masana da manazarta (Yahaya, 1988 da Mukhtar, 2004 da Malumfashi, 2006, 2009, 2010, 2011 da Bakura, 2011 da Adamu, 2013 da Aminu, 2013 da sauransu) sun yi rubuce-rubuce kan wannan.

2.0 MA’ANAR FAƊAKARWA


Kalmar faďakarwa kalma ce da ke nufin jan hankali da wayar da kan jama’a kan wani abu mai alfanu gare su. A cewar, Usman (2008), faďakarwa hanya ce ta waye wa mutane kai kan wasu al’amurra da yake ganin suna da alfanu gare su. Shi kuma Gusau (2008), a bayaninsa kan turƘen faďakarwa ya nuna cewa, a kodayaushe wannan jigo na faďakarwa yakan yi ƘoƘari ne ya sanar da mutane wasu abubuwa sababbi da suke aukuwa a rayuwar yau da gobe. A taƘaice, faďakarwa hanya ce ta ilmantar da mutane ko yi musu nasiha da tunatar da su don jan hankalinsu kan wani abu muhimmi na rayuwarsu.

3.0 FAƊAKARWA A WASU ƘAGAGGUN LABARAN HAUSA


Ƙagaggen labarin Hausa wata hanya ce da mutanen da Allah ya ba hikimar rubutu suke amfani da ita don isar da saƘonni daban-daban na rayuwar yau da kullum a cikinta. Marubuta litattafan suna shigowa da faďakarwar ce wasu lokuta a matsayin Ƙaramin jigo ta fuskar nasiha ko ilmantarwa ko tunatarwa don kyautata wani abu na rayuwar al’umma da kuma nasarar warware babban jigon littafinsu. Kodayake, marubutan ba a fili suke nuna faďakarwa suke yi ba, to sai dai ga wanda ya karanta gaƂar faďakarwar zai ji wani abu na tunatarwa ko nasiha ko ilmantarwa ya shiga rayuwarsa. Akwai littattafan Ƙagaggun labaran Hausa masu yawa da aka rubuta kan jigogi mabambanta, amma kuma ta ƘoƘarin warwarar jigo, sai marubuci ya shigo da wani batu na faďakar da al’umma kan ďaya daga cikin fuskokin faďakarwa guda uku.

3.1 FAƊAKARWA TA FUSKAR NASIHA


Nasiha na nufin kyakkyawar shawara (Ƙamusun Hausa, 2006: 357). Shi kuma Yahaya (2004), ya nuna kalmar nasiha na nufin luraswa ko shawara. Idan aka dubi waďannan ma’anonin ana iya cewa, kalmar na iya ďaukar ma’anar shawarar da aka ba mutum ta amfani da kalmomin rarrashi don jan hankalinsa zuwa ga wani abu da ake son ya kula don amfanin rayuwarsa. Akwai wasu litattafan Ƙagaggun labaran Hausa da ke ďauke da irin wannan faďakarwa ta nasiha a cikinsu. Ga misali, a littafin Shaihu Umar wanda Abubakar Tafawa Ɓalewa ya rubuta marubucin ya yi amfani da wasu kalamai da suke zama faďakarwa ga al’umma ta bakin wata tauraruwar littafin a lokacin da ta kai Shaihu Umar riƘo a wajen wata mata. Ga yadda ya kawo bayanin;
‘Amina, ina so mu yi ban kwana da ke yanzu domin ina so zan tashi tun kafin a kira sallah. To, sai fa ki ďauki hanƘuri, kin san halin yaron, kullum abin da ya ke so ya yi in ba a bar shi ba sai ya yi kuka, amma idan ana barinsa ya yi abin da ya so a gaba ba zai ji daďi ba. Ya kamata ki riƘa kwaƂonsa ko yaushe, kada kuwa ki kula da cewa ai wannan yaro ba nawa ba ne, wallahi da ni da ke duk ďaya ne, tun da yake Allah ya haďa mu, kuma a kan amana mu ke zaune’ (shafi na 18).

Idan aka yi nazarin wannan zance da idon basira, za a ga cewa nasiha ce uwar Shaihu Umar ke yi wa Amina, amma yana Ƙunshe da abin da yake faďakar da mutane dangane da halin yara da kuma yadda ya kamata a kula da tarbiyyarsu. Kowane yaro ba ya son a hana shi abin da ya sa a gabansa, to sai dai kuma hana shi, shi ne alheri gare shi da al’umma. Dalili kuwa shi ne, yaro bai san abin da yake daidai da wanda ba daidai ba a lokacin yarintarsa. Idan aka ce a bar yaro kan abin da yake so, to bayan girmansa zai iya zama fitina ga al’umma domin zai tashi ba shi da tarbiyya tagari musamman ta fuskar tarbiyyar jiki kan ayyukan wahala. Ke nan wannan gaƂar littafin faďakarwa ce ga mai karatu kan yadda ya kamata a yi tattalin yara da renon su don su tashi nagari cikin al’umma. Wannan kuwa haƘƘi ne na kowa da kowa, ba wai sai iyayen yaro kawai ba kamar yadda uwar Shaihu Umar ta nuna wa Amina.
Shi ma littafin Tura Ta Kai Bango wanda Sulaiman Ibrahim Katsina ya rubuta an yi amfani da wasu bayanai da suke kasancewa faďakarwa ga mai karanta littafin. Marubuci littafin ya shigo da irin wannan faďakarwa ta bakin wani tauraronsa mai suna malam Maigafaka inda ya kawo cewa,
‘A yau malam Maigafaka yana karanta wa almajiransa wani hadisi na manzon Allah ne yana cewa, ‘Alamar munafiki uku ce: Idan ya yi magana sai ya faďi Ƙarya, in an ba shi amana sai ya ci, in kuma ya yi alƘawari ba zai cika ba. Amma mu a yau mutane ba su ďauki Ƙarya a bakin komai ba. Sai ka iske babban mutum, ko ma malami yana ta zuba Ƙarya. Ko ya yi alƘawarin yin abu, ya Ƙi yi.’ (shafi na 25)

A nan marubucin na ƘoƘari ne ya faďakar da jama’a hadisin Annabi (S A W) da ya yi magana kan alamomi ko siffofin munafiki. Ya kawo alamomi uku; Ƙarya da cin amana da kuma saƂa alkawari. Shigo da wannan batu wani ƘoƘari ne na faďakar da duk wanda ya karanta littafin don ya kiyaye daga faďawa cikin waďannan alamomin.

A wani wurin marubucin ya Ƙara faďakarwa ta bakin malamin da wani hadisi da ya kawo kamar haka;

‘Wani bai taƂa cin wani abu mai amfani ba, da ya zarce abin da ya yi aiki da hannunsa ya samu.’ Malamin ya ce, ‘Wannan hadisai ya nuna muna cewa, kowanne mutum, abin da ke tabbata mafi amfani gare shi shi ne abin da shi ya yi aiki da hannunsa ya samu, ba wai wani ya je ya nemo, kai kuwa kana kwance ka amsa ka ci ba.’ (shafi na 25-26)

A wannan wuri faďakarwa ce marubucin ke yi wa wanda ya karanta littafin don ya san irin abin da ya fi alheri ga rayuwarsa. A nan ya kawo bayanin abin da zai kasance mai kishin kai da tashi ya nemi abin kansa ba wai ya zama ci-ma-kwance ba, sai wani ya samo ya ba shi.
A wata gaƂa ta littafin marubucin ya ja hankalin mai karatu kan wani hadisi da ya kawo wasu abubuwa da ke nisantar da mai aikata su daga rahamar Allah da sa shi cikin azabarSa. Ga yadda ya kawo wannan bayani ta bakin malam Maigafaka,

‘....Mutum uku Allah ba zai yi musu magana ranar Ƙiyama ba, ba zai yi musu duban rahama ba, kuma ba zai tsarkake su ba balle ya sa su a aljanna, kuma suna da azaba mai tsanani. Su ne mutumin da ke da ruwa mai yawa baƘo ya zo mai wucewa ya hana shi. Sai wanda ya yi mubaya’a don a ba shi kuďi ba don tsare haƘƘin Allah ba, in ba shi ba kuma ba zai jefa Ƙuri’arsa ba a inda ba a ba shi kuďin ba. Sai na uku shi ne wanda ya yi wa wani mutum Ƙarya ga kayansa don ya cuce shi.’ (shafi na 26).

Idan aka yi la’akari da wannan bayani za a ga cewa, faďakarwa ce ga mai karatu kan abubuwa uku da za su kai shi ga halaka; su ne hana baƘo ruwa tare da halin ba shi da sayar da mubayi’a sai kuma Ƙarya don yin cuta. A nan marubucin faďakarwa ce ya yi don wanda ya karanta ya hankalta ya tsare waďannan abubuwa domin ya kuƂutar da kansa daga shiga cikin mutanen da za su dauwama cikin azabar Allah.
Shi ma littafin Turmin Danya na Sulaiman Ibrahim Katsina marubucinsa ya yi amfani da wasu zantukan nasiha da ke zaman faďakarwa ga duk wanda ya karanta littafin. Ga misali, a shafi na 62, a lokacin da wani tauraron littafin mai suna Mukhtar yake tattaunawa da wasu jami’an kwastan abokan aikinsa, marubucin ya yi amfani da yawun bakinsa ya kawo wannan faďakarwar kamar haka,
‘Ai bai wuce cewa kowane rai mai ďanďanar mutuwa ne. Domin an ce, tun ran gini, tun ran zane. Hanyar da duk Allah ya Ƙaddara za ka mutu, to babu dabarar da za ta iya kare ka. Ko haka nan, ko rashin lafiya, ko haďari, tarnatsa, ko zubar ďaki, faďowa daga jirgin sama, ko doki, ko tuntuƂe ko a kai maka hari. Duk dai ta hanyar da Allah ya Ƙaddara, baka da magani. Saboda haka, ka ga da ka yi mutuwar matacce, gara ka yi ta mai rai. Da ka mutu a banza, tunda mutuwar za ka yi, to gara ka mutu a kan tsaron gaskiya. Ka ga in ka yi nasara, jama’a ta ji daďi, kuma Allah ya saka maka. In kuma ba ka yi nasara ba, wanda da wuya a ce baka samu nasarar ba, domin ko ba komi za ka wayarwa jama’a kai, to a lahira, ana sa ran Allah shi baka babban rabo-wataƘil ma irin ta waďanda suka yi shahada, don saboda kyakkyawar niyar da ka mutu da ita.

Idan aka yi la’akari da wannan gaƂar za a ga cewa, akwai faďakarwa ga duk wanda ya karanta wannan wurin. Abu na farko dai shi ne, mai karatu na Ƙaruwa da sanin mutuwa dole ce kan kowa, kuma kowane mutum yana mutuwa ne bisa ga sanadin da Allah ya tsara masa. Abu na biyu kuma shi ne, kowane mutum ya yi burin ya tsaya kan gaskiya, ya kuma mutu kan hanyar gaskiya domin ta hanyar gaskiya ce kaďai ake Ƙaruwa da mutum, kuma bayan mutuwa ya samu sakayya ta gari a wajen Ubangiji. Ke nan a nan marubucin na so ne mai karatu ya kasance mai tsoron Allah da kiyaye gaskiya a kan kowane lamari, kuma koyaushe.
Ita ma Habiba Muhammad a littafinta mai suna Rashin Rabo marubuciyar ta faďakar da al’umma ta fuskar nasiha kan wasu mata da suke ‘yan wuta tun a nan duniya. Ta yi wannan faďakarwa da wani hadisin Annabi (S A W) kamar haka;
‘....Annabi (S A W) ya ce akwai ’yan wuta iri biyu waďanda har yanzu ban gan su ba. Mata ma su sanye da tufafi amma kuma tsirara suke karkatattu ne da kuma masu karkatar da kawunansu. Kamar tozon rakumi, su ne ba za su shiga Aljanna ba, kuma ba za su ji kamshinta ba.’ (shafi na 6).

A wannan gaƂa nasiha ce ga jama’a, musamman mata kan haďarin da ke tattare da sa suturar da ba ta kare tsiraicinsu. Idan aka yi la’akari da kawo wannan hadisi marubuciyar na faďakar da mai karatu ne dangane da yadda ya dace mata su yi sutura mai kauri da Ƃoye sassan jikinsu. Rashin yin haka da sa sutura mai bayyana jikinsu alama ce ta ‘yan wuta.

3.2 FAƊAKARWA TA FUSKAR TUNATARWA


Tunatarwa kalma ce da tushenta shi ne kalmar ‘Tuna.’ A Ƙamusun Hausa (2006: 444), an nuna kalmar ‘Tuna’ na nufin komowar abin da aka mance a zuciya. Daga wannan ana iya cewa, kalmar tunatarwa a nan na nufin a faďakar da mutum don tunatar da shi kan wani abin da ya sani, amma ake ganin ya yi sakaci kansa ko kuma ya manta da shi don ya koma zuwa gare shi don alherinsa ko ya nisance shi don sharrin da ke tattare da shi. Akwai wasu litattafan Ƙagaggun labarai da ke ďauke da faďakarwa ta fuskar tunatarwa don masu karatu su amfana da abin da marubuta suke son su lurar da su kansa.
Littafin Ƙwaryar Ƙira wanda Yusuf Adamu da Ado Ahmad Gidan Dabino suka shirya a cikinsa an yi amfani da dabarar faďakar da mai karatu ta hanyar tunatar da shi kan wasu abubuwa muhimmai na rayuwa. Ga yadda aka kawo gaƂar labarin;
‘Wata daga cikin Ƙawayen amarya mai suna Zurfa’u ta kada baki ta ce. ‘To amarsu mu ma za mu tafi, amma kafin mu tafi, mu na da wata tsaraba da muka zo da ita za mu baki. ...Sulaiha ga wasu muhimman abubuwa da za su taimakawa rayuwar aurenku kamar haka: Na farko biyayya. Mace na samun mallakar mijinta ta hanyar biyayya. Kuma biyayya shi ne mace ta bi umurnin mijinta a cikin komai matuƘar bai yi umurni da saƂon Allah ba. Sai abu na biyu, watau haƘuri, domin shi haƘuri babban sinadari ne ga zamantakewar aure. HaƘuri nau’i uku ne, akwai tsakaninki da mijinki, haƘuri bisa biyayya ga umurnin mijinki, sai haƘuri bisa hanawa ga abin da yake yi. Sai abu na uku, sanin ya kamata, ƘoƘarin yadda za ki kyautata mijinki da faranta masa shi ne sanin makama. Sai abu na gaba kuma nah uďu watau zumunci. Kyautatawarki ga iyayen mijinki da ‘yan uwansa da danginsa shi ne ake kira zumunci.’ (shafi na 100-101).

Bayanan da ke wannan gaƂa suna kasancewa faďakarwa ta hanyar tunatarwa ga duk wanda ya karanta kan matakan kyautata zaman aure, musamman ga ‘ya’ya mata. A bayanin an kawo biyayya da haƘuri da zumunci waďanda dukkaninsu muhimmai ne kuma sanannu ga mata wajen kyautata zaman aurensu. A nan marubucin na faďakar da mata ne kan su riƘe waďannan abubuwan, su yi aiki da su domin kyautata zaman aurensu da kuma mallakar mazajensu.
A cikin littafin In Da So Da Ƙauna na Ado Ahmad Gidan Dabino nan ma marubucin ya faďakar da mai karatu kan wasu al’amurran da yake son a kula da su domin samun dacewa, musamman a halin zamantakewar aure. Ga yadda ya kawo faďakarwar tashi;
‘To ma’abota soyayya, kun ga yadda ake riƘe alƘawarin soyayya da hannu biyu, ba irin yadda kuke yi ba, idan yarinya ce ta sami wani mai hannu da shuni sai ta watsar da talaka, haka idan saurayi ne ya sami wata kyakkyawa sai ya watsar da ta farko, ‘yan’uwana matasa a bar neman kyau ko kuďi a nemi na gari.’(shafi na 80).

A wannan wurin marubuci littafin ya yi faďakarwa ta hanyar tunatar da mutane kan yadda masoya ya kamata su riƘe alƘawarin soyayyar aure a tsakaninsu. Haka kuma ya faďakar da mai karatu kan ya kiyaye ga zaƂen matar aure kan cancanta ba don kallon kuďi ko kyau ba. Da wannan mai karatu ya amfana dangane da yadda soyayyar aure tsakanin namiji da mace ya kamata ta kasance.
A wani shafi marubucin ya Ƙara faďakar da mai karatu kan illar aurar da yarinya kan tilas da irin abin da auren tilas ke kawo wa al’umma. Ga yadda ya kawo batun nasa;
‘Ka ga auren tilas ba Ƙaramar illa ba ce, domin yawancin ‘yan matan da suka shiga bariki, suke kuma iskanci, auran dole ne sanadiyyarsa. Su kuma iyayenmu saboda rashin tunanin abin da zai je ya zo sai su ƘeƘasa Ƙasa su ce sai wanda suke so za a bai wa. Ai yanzu zamani ya canja, wanda yarinya take so a ba ta shi kawai ka sami zaman lafiya....’(shafi na 81).

Idan aka yi la’akari da wannan bayanin za a ga kasancewarsa faďakarwa ta fuskar tunatarwa ga duk wanda ya karanta shi kan illar auren tilas ga yarinya. Auren tilas ke sa wasu mata shiga bariki da yawon iskanci. Ke nan marubucin na faďakar da mai karatu ne kan a riƘa aurar da yarinya ga wanda take so tun da zamani ya kawo haka. Yin wannan zai sa a sami zaman lafiya cikin al’umma da kuma rage yawan lalacewar yara mata da ake fama da shi a yau.
Shi ma littafi Zama Da Kishiya Riba Ce na Isah Rasco Dangoma marubucin ya yi amfani da hikimarsa ya faďakar da mai karatu wasu abubuwa da yake son ya kiyaye don kyautata zaman iyalinsa a koyaushe. Ya yi wannan faďakarwa ta bakin jarumar littafin mai suna Hajaru inda mijinta Dr. Haliru ya tambaye ta abubuwan da ya dace mutum ya kiyaye idan ya yi amarya. Ita kuma Hajaru ta zayyana wasu abubuwa da suke zaman faďakarwa ga wanda ya karanta littafin kamar haka:
‘Ya kira amarya da uwargida a falonsa ko kuma idan bashidafalo, to ya kira su a dakin uwargida domin yayi musu huduba. Ya nuna musu duk matsayinsu daya don haka duk wadda ke son ta zauna tare dashi to ta zauna da abukiyarta lafiya. Amma kada ka kirasu dakin amarya saboda uwargida na ganin kamar ka walakantata, kada ka yarda ka nunawa Amarya cewa uwargida banza ce gareka, idan kayi haka to ka haddasa fitina tsakaninsu. Saboda ita amarya ba zata sake ganin uwargida da darajja ba. (shafi 49).

Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa, wata muhimmiyar faďakarwa ce ta hanyar tunatarwa ga mai karatu kan yadda ya dace ya shirya iyalinsa don samun zaman lafiya. Waďannan abubuwa sun haďa da bayyana wa matansa matsayinsu ďaya da kare mutuncin uwar gida da ba ta girma ta hanyar kiran matan a ďakinta don huďuba. Ke nan kula da waďannan abubuwa da aiki da su zai iya zama wata kafa ta samun zaman lafiya a cikin iyalin mutum. Wannan tunatarwa ce marubucin ya yi a kaikaice ga mai karatu. A wani wuri a cikin littafin marubucin ya Ƙara yin faďakarwar inda ya kawo cewa;

‘Kada ka nuna banbanci ga ‘ya’yansu ma’ana ka nuna ga wanda kakeso fiye da wani. Ta wajen sutura duk kayi musu kala daya. Bawai ina nufin ka sayawa wadansu yadi dan Madina suko wadancan ka saya musu gisna ko miro wannan yana daya daga cikin abinda ke hadda fitina.’ (shafi na 49).

A nan marubucin ya faďakar da mai karatu ta hanyar tunatarwa kan yadda ya kamata ya daidaita iyalinsa musamman ta gefen ‘ya’ya. Ya nuna rashin daidaita soyayya ga ďiyan kishiyoyi wata babbar matsala ce da ke haddasa fitina a cikin iyalin mutum. Wannan faďakarwa ce ga mai karatu don ya san yadda zai yi mu’amala da yaransa, musamman idan ya zan yaran ba uwa ďaya suke ba.
Ya Ƙara faďakar da mai karatu kan abin da ya rataya a wuyansa na yin adalci a tsakanin matansa ta bakin Hajaru. Ya ce,
‘‘Babbar magana a wajen kwana ka raba daidai, kada ka rinka doguwar hira ga kwanan wata idan kwanan waccan yazo ka dawo da wuri ka tuna da Allah da ya halicceka kayi adalci.’’ (shafi na 50).

A wannan bayani za a ga cewa faďakarwa ce ta hanyar tunatarwa ga mai karatu dangane da yadda ya kamata mai gida wanda ke da fiye da mata ďaya zai yi dangane da rabon kwana a tsakanin matansa inda aka nuna ya raba daidai. Haka kuma an faďakar da mai karatu yin adalci da ya kamata ya yi dangane da lokacin kowace mace. Wannan zai sa mai karatu, musamman mai mata fiye da ďaya ya samu haske dangane da wani abu da zai kawo zaman lafiya a gidansa.
Har ila yau, marubucin ya Ƙara kawo wani abu da zai faďakar da mai karatu dangane da zamantakewarsa da iyalinsa don samun zama na gari mai lumana. Misali,

‘‘...Ka karantar da su ilimin jin tsoron Allah, kuma ka umurcesu da suji tsoron Allah ba wai suji tsoronkaba. Saboda idan sukaji tsoron Allah to tsoronka tilas ne garesu.’’ (shafi na 50).

A wannan wuri marubucin ya tunatar da mai karatu ne kan alhakin da ya rataya ga wuyansa na karantar da matansa ilimin addini da horon su da jin tsoron Allah. Karantar da mata addini shi ne mataki na farko na cusa musu tsoron Allah wanda kuma idan ya samu zai sa su yi biyayya ga miji don biyayya gare shi a inda ba saƂon Allah ba tilas ce domin biyayya ce ga Allah. A nan marubucin na son mai karatu ya hankalta da wannan ne, ya kuma yi aiki da shi don samun zaman lafiya cikin iyalinsa.
A cikin littafin Turmin Danya, marubucin ya shigo da wani bayani da ke zaman faďakarwa ga mai karatu ta bakin tauraronsa Mukhtar lokacin da yake lurar da wani abokinsa Kirista mai suna Ishaya. Ga yadda ya kawo batun;
‘Ji nan Ishaya, ko da yake addininmu ya banbanta, amma ni cikin nawa addinin akwai rashin jin tsoron kowa banda Allah. Wanda duk kake zaton zai iya yi maka wani abu, shi ma bai iya yi ma kansa maganin kome. Yadda bai iya kare kansa daga talauci, to haka baya iya kare kansa daga rashin lafiya ko mutuwa.’ ‘Ai muma addininmu, haka ya ce.’ (shafi na 64).

A nan marubucin na ƘoƘari ne ya tunatar da mai karatu cewa, a tsarin addini, ba a jin tsoron kowa sai Allah kaďai. Haka kuma ba wani mutum da ke da iko na cutar da wani domin shi kansa bai mallaki iya yi wa kansa maganin komai a rayuwa ba. Ga wanda ya karanta wannan littafi a daidai wannan wurin musamman mai Ƙarancin ilimin addini zai amfana da sanin Allah ne kaďai abin tsoro da neman biyan buƘata a koyaushe.

3.3 FAƊAKARWA TA FUSKAR ILMANTARWA


Ilmantarwa hanya ce ta karantar da mutane da fahimtar da su wani abu muhimmi da zai taimaki rayuwarsa ta hanyoyi masu yawa. Marubuta littattafan Ƙagaggun labaran Hausa na amfani da hikimarsu ta rubutu don karantar da mutane abubuwa daban-daban na rayuwa ta hanyar shigo da wata gaƂar labari da za ta faďakar da mai karatu lokacin karatunsa.
A littafin ZaƂi Naka na Munir Muhammad Katsina an yi amfani da wasu kalmomi da suke zaman faďakarwa don ilmantarwa ga al’umma inda marubucin ya yi amfani da yawun wani shaihin malamin addini da ya buďa layar da aka sa wa wata mata a ƘarƘashin filo, bayan ya karanta layar sai ya ce,
‘To, ni a kan matsayina na malamin addini ba ďa ďibbu ba, ban san wani batu ba na cewa ana iya rubuta ayoyin AlƘur’ani a sha ko a yi laya da su ba, saboda a kashe ko a haukatar da mutum ba.’ (shafi na 20).

Idan aka yi la’akari da wannan wuri za a ga cewa, bayanan da ke ciki na faďakar da wanda ya karanta da ilmantar da shi dalilin saukar da AlƘur’ani mai tsarki shi ne karanta shi ake yi, ba wai amfani da shi don halakar da wani mutum ba ta hanyar laya ko sha ba. Haka kuma an faďakar da mai karatu cewa, amfani da AlƘur’ani don halakarwa aiki ne na malaman tsibbu, ba na malaman addini ba. Ke nan a kaikaice marubucin na jan hankalin mutane ne da ilmantar da su don su nisanci amfani da ayoyin AlƘur’ani don cutar da kowane mutum don ba kan haka Allah ya saukar da shi ba.

A wani wuri marubucin ya Ƙara faďakar da al’umma ta hanyar ilmantar das u matsayin AlƘur’ani ta bakin shaihin malami inda ya ce,
‘Ni dai iyakar abin da na sani game da Ƙur’ani shi ne Allah ya aiko da shi ga jama’a don ya zamo jagora ga rayuwar Ɗan adam a nan duniya. An hore mu, mu riƘa karanta shi a kullum, mu san fassararsa da manufarsa, kuma mu yi aiki da abin da muka fahinta. Amma ban ji an ce a yi magani da surorinsa ko ayoyinsa ba wajen hallaka wani ba. Saboda haka, ki tashi ki tafi gida. Ki dogara ga Allah, kada ki ji tsoron komai don ba abin da zai same ki matuƘar kina da gaskiya.’ (shafi na 20).

Bayanan da ke wannan wuri na ilmantar da duk wanda ya karanta game da dalilin saukar da AlƘur’ani mai girma a duniya da kuma horon da Allah Maďaukakin Sarki ya yi game da amfani da AlƘur’ani. Wannan dalilin kuwa shi ne AlƘur’ani ya kasance jagora ga dukkan rayuwar ďan Adam. Daga cikin horo da aka yi wa ‘yan Adam ga lamarin Ƙur’ani shi ne su karanta shi, su san ma’anoninsa, sannan su yi aiki da abin da suka fahimta. A nan marubucin na faďakar da mutane ne su tsaya ga AlƘur’ani inda Allah ya umurta, kada su wuce wuri suna sarrafa ayoyinsa da sunan halaka wani mutum. Haka kuma ya nuna duk wanda ya dogara ga Allah, ya tsaya ga gaskiya ba wani abu da zai same shi.
A cikin littafin Ƙwaryar Ƙira marubucin ya kawo wani bayani na ilmantar da mai karatu kan abin da ya kamata duk wanda aka kawo wa amarya ya aikata a darenta na farko don dacewa da sunnar Annabi (S A W) da samun albarka da kariya daga sharrin shaiďan a cikin aurensa. Ga yadda aka kawo wannan batu kamar haka;
‘Shi kuwa ango Muzaffar bayan da suka yi sallama da Ƙawayen amarya sai abokansa suka raka shi har Ƙofar gida. Har sun yi sallama sai wani daga cikin abokansa da ake kira da Shamsu Ashago ya ce. ‘Ango Kar ka manta da sallah raka’a biyu da za ku yi kai da amarya. Sai kuma ka dafa kanta ka ce, ya Allah ina roƘonka alherinta da alherin da ka halicceta da shi. Sannan ina neman tsari daga sharrinta da sharrin da ka halicceta da shi....’ (shafi na 101).

A nan akwai abubuwa biyu muhimmai da ake faďakar da mai karatu kansu a kaikaice. Na farko shi ne, ilmantar da ango da amarya su yi sallah raka’a biyu a daren farko. Na biyu, ango ya dafa kan amarya ya yi addu’a ga Allah don neman albarkarta da neman kariya ga sharrinta. Ke nan marubucin a wannan wuri yana faďakarwa ne kan abu na farko da ya kamata ma’aurata su aikata a daren farko na aurensu.
Ita ma marubuciyar littafin Rashin Rabo, a nata ƘoƘari na faďakar da al’umma ta yi amfani da yawun bakin wata tauraruwar littafin mai suna Yusra don ilmantar da mutane dangane da abin da Allah ya ce game da suturar mace Musulma da kuma yadda ya kamata mata Musulmi su fita. Misali;
‘Hijab shi ne mace ta suturce jikinta daga maza da ba muharramanta ba kamar yadda Allah maďaukakin sarki ya ce: ‘Kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi kuma su yi lullubi da mayafinsu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su bayyana adonsu sai ga mazan su, ko iyayensu, ko iyayen mazan su, ko ‘ya’yansu, ko ‘yan uwanku na jini muharramanku.’ (shafi na 5).

Kawo wannan bayani wani ƘoƘari ne na faďakar da al’umma ta fuskar ilmantar da su bisa ga abin da wannan aya ta tabbatar kan suturar mace Musulma. A nan marubuciyar ta faďakar da mai karatu kan abin da ake nufi da hijabi a addinin Musulunci da kuma irin mutane da shari’a ta yarje wa mace Musulma ta kawar da hijabinta da bayyana adonta gare su kamar iyaye, da kakanni, da mazajen aure, da ďiya da kuma ‘yan uwa muharramai.
Shi Sulaiman Ibrahim Katsina a littafinsa na Turmin Danya ya yi irin wannan faďakarwa don ilmantar da mutane matsayin AlƘur’ani mai tsarki da tasirin addu’a ga wanda ya dogara ga Allah. Misali;

‘‘Alhaji Ɗantalle baka ganin shi yasin yake yi ma yanka kamar yadda ka ce. Bayan kuwa Allah yana cewa AlƘur’ani rahama ne, ya ya mutum zai yi anfani da wata aya ko sura wajen mugun abu. Har y ace, bata biyan bukata sai an yi mata yanka. Ka ga wannan nau’i ne na shirka. Saboda haka, ka ga in mun roƘi Allah, to zai fi taimakon mu fiye da shi. Tunda shi ya kauce hanya.’’ (shafi na 75).

Idan aka dubi wannan bayani za a ga cewa, wani abu ne na ilmantar da al’umma ta hanyar faďakar da su kan matsayin AlƘur’ani mai girma na kasancewarsa rahama ba abin da ake amfani da ayoyinsa ba don wani mugun aiki, balle dogara ga cewa, akwai aya ko surar AlƘur’ani da biyan buƘatarta ya dogara ga sadaukar da wani abu gare ta. Haka kuma ya tabbatar da yarda da haka shirka ne zahiri. Marubucin ya Ƙara faďakar da jama’a cewa, Ba abin da ya fi ga Musulmi illa addu’a kan kowace matsala da ke barazana ga rayuwarsa.

Shi ma littafin Mallakin Zuciyata marubincinsa ya kawo irin wannan ilmantarwa ta bakin Malam Kalla da ya yi wa kakarsa kan fa’idar kowane nau’in ilimi na Arabiyya da boko. Misali;

‘‘Kakar ta ce, ‘‘Ai ilmin karatun Allah ake nufi ba na bokon banza ba.’’ ‘‘Lura, ai kowane iri amfani gare shi, in dai zai yi ma mutum amfani
cikin rayuwarsa. Kuma a makarantar bokon ma ana koya musu salla,
wanka, da alwalla da kuma tauhidi. Har ma da Larabci’’ (shafi na 20)

A daidai wannan sakin layi akwai ilmantar da mai karatu fa’idar neman kowane irin ilimi da kuma makarantar boko. Mai karatu idan ya karanta wannan wuri zai san irin abubuwan da ake koyar da yara a makarantun boko waďanda ke da alaƘa da addinin Musulunci irin Sallah da wankan sunnah da Alwalla da tauhidi da harshen Larabci. Ke nan wannan faďakarwa ce ta fuskar ilimi ga mai karatu, musamman wanda bai san abubuwan da ake koyar da yara na addinin Musulunci a makarantun boko ba.
Balkisu Ahmad Funtuwa a littafinta mai suna Duniya Rawar ‘Yan Mata 1 ta kawo irin wannan faďakarwa ta fuskar ilmi kan abubuwan da suka kamata a kula da su wajen amincewa da mutumin da za a ba wata mata aure. Misali;
.....Idan ba ta manta ba malaminsu na islamiyya yace
masu wanda ya halatta a baiwa aure sune baligin da ya
malaki addininsa, kyawawan ďabi’u, sana’ar da zai iya
riƘe iyali sai mahalli, to me kuma zata nema wajen halifa? (shafi na 5-6)

Bayanan da ke wannan wuri suna ilmantarwa ne cewa, mutum wanda ya fi dacewa a ba mace aure shi ne baligi mai addini, mai halaye na gari, kuma wanda ke da wata sana’a da zai kula da iyalinsa. Ke nan marubuciyar a wannan wuri ta faďakar da jama’a ne kan mataki na farko muhimmi da ya dace a kula da shi wajen ba namiji mata aure. Wannan kuwa bai shafi tarin dukiya ko muƘami ba.

4.0 KAMMALAWA


Idan aka kalli bayanan da suka gabata da misalan da aka tsakuro daga littattafan da aka yi amfani da su, sun nuna lamarin Ƙagaggen labarin Hausa ya wuce abin da aka fi zato gare shi na nishaďantarwa kawai. Misalan sun tabbatar da ana tsintar dami a kala ta inda ake samun wasu bayanai masu faďakar da mai karatu ta hanyar nasiha ko tunatarwa ko kuma ilmantarwa kan abin da zai taimaki rayuwarsa duniya da lahira.
Wani abu da binciken ya ci karo da shi cikin littattafan shi ne yadda aka karkasa faďakarwa gida uku wanda marubutan suka yi amfani da shi don jan hankalin masu karatu da wayar musu da kai kan abubuwa daban-daban. Wannan na nuna cewa, bincike a littattafan Ƙagaggun labaran Hausa zai ba da dama ga hango Ƙarin wasu muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar Hausawa ta kowane gafe.
Daga Ƙarshe, binciken na fatan wannan ya zama dalilin buďe wata kafa muhimmiya ta ci gaba da bincike don gano wasu muhimman abubuwan ilmantarwa da ke Ƙunshe cikin Ƙagaggun littattafan.

 

Wannan zai burge ku:

https://www.amsoshi.com/2017/07/17/nazarin-hada-hadar-kudi-tattalin-arzikin-hausawa-duba-ga-wasu-littattafan-kagaggun-labaran-hausa/

5.1 MANAZARTA


Adamu, Y. M. (2013), Ruwan Saman Marubuta A Ƙasar Hausa: Daga Damunar 1980 Zuwa Yau. MaƘalar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani na farko da Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Bayare Kano ta shirya daga ranar 14-16 ga watan janairu- 2013.

Adamu, Y. M. da Gidan Dabino, A. A. (2010), Ƙwaryar Ƙira. Adamu Joji Publishers Suite 1B, No 123, Mangwarori Street Sabon Titi Mandawari, Kano City.

Ahmad, A. A. (2009), Rupert Moutrie East: Gudummuwarsa Ga Adabin Hausa Da Kuma Sharhi Kan Ayyukansa. Kundin Digiri Na Uku, Jami’ar Bayero, Kano

Aminu, N. (2013), Malami A Mahangar Marubuta Adabin Zamani: Nazari daga Littattafan Gasar Rubutu Ta 1933. Takardar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani, ƘarƘashin Sashen harsunan Nijeriya, Tsangayar Fasaha Da Nazarin Addinin Musulunic, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sokoto, Ranar Alhamis 28 Ga Watan Fabrairu, 2013

Bakura, A. R. (2011), Gudummuwar Turawa Wajen Samuwa Da Ginuwar Adabin Hausa. Kundin Digiri Na Uku, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

Dangoma, I. R. (ba shekara), Zama Da Kishiya Riba Ce. Nabila Printing Press, Rafin Atiku Beside NULGE Office, B/Kebbi, Kebbi State.

Gidan Dabino, A. A. (1990), In Da So Da Ƙauna.

Gusau, S. M. (2008), WaƘoƘin Baka A Ƙasar Hausa Yanaye-yanayensu Da Sigoginsu. Benchmark Publishers Limited, Kano-Nigeria.

Katsina, M. M. (1982), ZaƂi Naka. Gaskiya Corporation Ltd, Zaria.
Katsina, S. I. (1980), Mallakin Zuciyata. NNPC, Zaria.
Katsina, S. I. (1982), Turmin Danya. Gaskiya Corporation Ltd, Zaria.
Katsina, S. I. (2010), Tura Ta Kai Bango. NNPC, Zaria.
Malumfashi, I. (2009), Adabin Abubakar Imam. Sakkwato. Garkuwa Media Services.
Malumfashi, A. I. (2010), Hausa Literature At 50: The Interface Of Tradition, Arab and Colonial Heritages, Takardar da aka gabatar a taron cikar Nijeriya shekaru 50. Jami’ar Port Hacourt, Nijeriya.

Malumfashi, I. A. M. (2006), Ginuwar Ƙagaggun Labaran Hausa: Ƙarin Haske. Cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, Ƃol. 1 No. Jami’ar Bayero, Kano

Malumfashi, I. A. M. (2011), Ta’aziyyar Adabin Kasuwar Kano. Cikin Studies in Hausa Language, Literature and Culture The Siďth Hausa International Conference, Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Malumfashi, I. A. M. Da Aliyah Ahmed, A. (2006), ‘‘Colonial Legacy and Writing Competitions in the DeƂelopment of The Hausa NoƂels’’Cikin The NoƂel Tradition in Northern Nigeria. Proceedings of The 4th Conference on Literature in Northern Nigeria, Department of English
Muhammad, H. B. (2011), Rashin Rabo.

Muhammad, M. S. Da Ahmad, I. M. (2013), Gudummuwar Marubuta Littattafan Hausa Wajen Wayar Da Kai Ta Fuskar Siyasa: Tsokaci A Kan Littafin Tura Ta Kai Bango. Takardar da aka gabatar a taron Ƙara wa juna sani na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayare Kano. 14-16 ga Junairu, 2013.

Mukhtar, I. (2004), Jagoran Nazarin Ƙagaggun Labarai. Kano. Adamu Joji Publishers.

Usman, B. B. (2008), Hikamar Magabata: Nazari A Kan Rayuwar Malam (Dr) Umaru Nassarawa Wazirin Gwandu (1916-2000) Da WaƘoƘinsa. Kundin Digiri na Uku, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Tafawa Ɓalewa, A. (1966), Shaihu Umar. NNPC, Zaria.
Yahaya, A. B. (2004): Jigon Nasiha A Rubutattun WaƘoƘin Hausa. A cikin Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, No 3, Ƃol. 1, Department of Nigerian Languages Series IƂ. September, 2004.
Yahaya, Y. I. (1988), Hausa A Rubuce : Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. NNPC, Zaria.
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments