Ticker

6/recent/ticker-posts

HAUSAR ‘YAN SIYASA A AREWACIN NIJERIYA (BABI NA BIYU)

KUNDIN BINCIKEN NEMAN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) WANDA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO.

NA

ASHIRU USMAN GABASAWA
ADM.NO:1110106129

SATUMBA, 2016


BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0 Shimfiɗa


Hausawa kan ce “waiwaye adon tafiya, kuma daga na gaba ake gane zurfin ruwa” saboda haka wannan aiki ya yi waiwaye da bitar ayyukan da masana da manazarta da malamai suka yi masu alaƙa ta kusa da ta nesa da wannan aiki ta fuskoki da dama komai kankantarsu domin samun tudun dafawa.

2.1 Bita a Kan Aro da ƙirƙira


Imam (2009) ya wallafa littafi mai suna “Asalin Aro, Ma’anarsa Da Ire-Irensa” ciki ya kawo asalin aro daga Larabci da yadda Hausa ta mai da ita a yau sannan ya kawo rabe-raben aro da mahimmancin sa ga harshen aro da ire-iren misalan aro daga Larabci da Turanci da Azbinanci da Fulatanci da Nupanci da Barbanci da Faransanci da sauran su zuwa cikin harshen Hausa. Akwai alaƙa ta kusa da littafin Imam wajen bayyana asalin kalmar aro da ire-irensa da rabe-rabe tare da kawo misalan aro daga wasu harsunan duniya zuwa Hausa. Sun bambanta da wannan aiki da zai kalli aro da ƙirƙira a karin harshen yan siyasa na Arewacin Najeriya.
Giro (2012) ya yi bincike a kan ire-iren aron kalmomin da ke cikin littafin Mace Mutum a kan harsunan Ingilishi da Larabci wanda
mawallafiyar tai amfani da su a ƙoƙarinta na isar da sakon littafin, bayan kawo maanar aro da ire-irensa daga masana da dama sai ya tsara kalmomin ta yin laakari da irin aron da Hausa ta yiwo a Larabci da kuma ɗaya ɓangaren wato Ingilishi sannan daga baya kuma ya kawo kalmomin aron a littafin na Larabci da akai amfani da su da Ingilishi da kuma tsofaffin kalmomin Hausa a ƙarshe ya gama da kammalawa da manazarta. Akwai alaƙa domin sun yi canjaras ta fuskar aron kalmomi duk da yake aikina zai kalli aro da ƙirƙira a cikin kalaman yan siyasa na Arewacin Najeriya.

Besse (2015) ya gudanar da bincike kan “Dangantakar Harshe Da Siyasa A Sakkwato.” Bayan gabatarwa a sashi na farko a na biyun ne ya shiga kawo ma’anar harshe daga masana da alaƙarsu da siyasa da irin tagomashin da ya samu. Sai kuma ya ba da irin nasarar da yan siyasa a garin Sakkwato ke samu a dalilin harshe. Akwai dangantaka tsakanin aikina da na Besse ta laakari da yadda ya gudanar da bincikensa ne a kan abin da ya shafi siyasa da harshe amma kuma sun sha banban saboda aikina zai yi nazarin nauin karin harshen ‘yan siyasa na Arewacin Najeriya.
Aliyu (2007) ya gudanar da bincike mai taken “Kalmomin Aro Na Zamani A Hausa”. Ya kawo yadda zamani ke sauyawa wanda hakan ke haifar da baƙin abubuwa a harshe wanda ba a san su ba. Daga nan sai aikin ya mayar da hankali kan baƙin kalmomi ɓangaren kimiyya da fasaha da suka ƙara yawan samuwar wadatattun kalmomi a Hausa da ake amfani da su kai tsaye ko saɓanin hakan. Tabbas akwai dangantaka makusanciya ta fuskoki mabanbanta, musamman idan aka yi magana a kan aron kalmomin zamani a Hausa.
Yakasai (2005) Bayan gabatarwa da bayyana ra’ayin masana
dangane da aro a cikin harshe tare da kawo ma’anar da suka bayar irin su Fishman (1972) da Trudgill (1974) da Hymes (1974) dangane da aro cikin harshe. A kashi na biyu ya kawo amfanin da ƙirƙira ke kawo wa da cewa dukkanin kalmomin aro suna inganta kalmomin harshe da kuma ƙirƙira na kawo hikima a harshen aro sai ya yi ƙoƙarin fassara abubuwa sababbi cikin faɗaɗa maanar. Ya kuma bayyana samuwar sababbin kalmomi waɗanda alummar wannan wurin ke amfani da su a jamaa. Misali
• Wanki – mai nufin maguɗin jarabawa
• B.Z – mai nufin bazawara
ƙwaro mai nufin mai ƙwazo
• Presido – mai nufin shugaba

Babu shakka akwai alaƙa dangane da faɗaɗa maanar kalmomin da ake da su a cikin harshe da ƙirƙirar sababbi domin sadarwa a cikin jamia da garin Sakkwato. Sun sha bamban da wannan aiki ne da ya kalli nauin karin harshen yan siyasa na Arewacin Najeriya baki ɗaya kan aro da ƙirƙira a cikin kalami ko kalmomi.
Bature (2002) ya gabatar da maƙala mai taken Nazari Kan ƙirƙirar Sababbin Kalmomi A Hausa. Da farko ya kalli hanyoyin ƙirƙirar kalmomi daban-daban da suka dace da kalmomin Larabci zuwa Hausa da kuma Turanci. A nan ya kasa aikin zuwa gida biyu sashi na ɗaya ya yi bayanin mahimmancin binciken da dalili samuwar sababbin kalmomi, a ɓangare na biyu kuwa sai ya kalli hanyoyin ƙirƙirar sabuwar kalma tare da amfani da kalmomin Hausa na asali ko na aro da yadda ake hausance su a Hausa har su koma kamar sabuwar kalma, daga ƙarshe ya naɗe da yadda Hausa ke sarrafa kalmomin aro zuwa azuzuwan kalmomi ya yin da aikatan Hausa yafi ɗaukar kaso mai yawa na kalmomin aro. Binciken Bature na da alaƙa da wannan aiki ta ƙut-da- ƙut sakamakon ɓangaroren da ya taɓo a cikin aikinsa ya yin da aikina ke kallon aro da ƙirƙira a cikin kalamai ko kalmomin fannu ko jimloli a Hausar yan siyasar Arewacin Najeriya.
Salihi (1998) ya gudanar da bincike mai taken “Baƙin Kalmomi Da
Gamin Gambiza Daga Turanci Zuwa Hausa A Cikin Rubutattun ƙagaggun Labarai. Ya kawo maanar baƙin kalmomi da samuwar su tare da ire-iren aro haɗi da gamin gambiza da kalmomin ƙirƙirarru sannan a cikin aikin ya kawo misalansa cikin ƙagaggun labarai da dama ƙarshe ya kammala da shawarwari tare da manazarta. An samu alaƙa sosai tsakanin ayyukan, sai dai sun banbanta ne ta fuskar keɓe farfajiyar binciken sa a cikin ƙagaggun labarai sabanin wannan aro da ƙirƙira a karin harshen yan siyasar Arewacin Najeriya.
'Dantumbishi (ba shekara) ya wallafa maƙala mai taken Neologism
In Hausa: Its Relevence And Development”. Ta ƙunshi irin bunƙasar da ƙirƙirar kalmomi ke haifarwa a harshen Hausa musamman wanda aka samar sakamakon cuɗanya da Larabawa da Turawa tun ƙarni na tara zuwa na sha biyu (9th 12th centuary) tare da faɗaɗa maanar wannan kalmomi da muka aro a garesu. Ya duba ɓangaren ƙirƙira da samar da wata kalma daga cikin wata da wanda muke canzawa maana ta asali daga harshen aro sai ya mayar da hankali kan ƙirƙirar sababbin kalmomi daga Turanci da Larabci inda yake ganin an gaza a nazarin bangaren. Akwai dangantaka da aikin [antunbishi dangane da ƙirƙira da mahimmancin ta a Hausa a lokacin cuɗanya da Larabawa da Turawa sai dai mu aikin mu zai ba ƙarfi ne kan abin da ya shafi Hausar Hausawa yan siyasa.
Abba (2013) ya gababtar da maƙala mai take Coinage And Neologism In Kano Politics ya kawo kaɗan daga tarihin shahararrun yan siyasar Kano na farko har kawo wannan zamani kan yadda suke bunƙasa harshen Hausa wajan yin aro da ƙirƙira a ƙoƙarin neman goyon bayan jamiyyun su dan sukai ga nasara a cikin yaƙin neman zaɓen jahar Kano. Ya kawo kalmomin na nan kusa (2011) ƙadan irin su wujuwuju da dawodawo tare da wanda aka faɗaɗa maanar su zuwa wata daban, misali hannun jaririrai da goro ɗan ujile da sauransu. Babu ko shakka akwai alaƙa mai nauyi da aikin Abba kan yadda ya dubi aro da ƙirƙira tare da faɗaɗa maanar wata jimla a cikin bayanan yan siyasar Kano, wannan aiki ya banbanta da na sa domin ya yi duba izuwa aro da ƙirƙirar kalami ko kalmomin fannu a cikin bayanin yan siyasar Arewacin Najeriya ba jaha kaɗai ba.
Busa (2013) ya gudanar da bincike mai taken “Hausa Loans Words In Gbagyi”. Bayan kawo taswirar wannan al’ummar cikin ƙasar nan sai ya ba da dalili cewa sakamakon cuɗanyar su da Hausawa ya saka su aro na dole daga harshen Hausa ta ɓangarori irin su ilimin gundarin sauti (phonetics) da ilimin tsarin sauti (phonology) da kuma wadatuwar kalmomi (lexicology). Ya yi nazarin irin kalmomin da suka aro zuwa cikin harshen na su na Gbagyi ya kawo kalmomin walwalar harshe cikin aron su da sunayen mutane da kasuwanci da dabbobi da tsirrrai da sassan jikin mutum da launi da sutura da sauransu. Misali:

GBAGYI HAUSA
Gbada Agwada
Kawa Akawu
Yira Inna
Batule Bature
Fali Fari
Ciloma Ciroma
Baluba Abarba
Bunsulu Bunsuru
Kamar yadda muka ambata a sama aikin Busa bincike ne kan yadda harshen Gbagyi ya yi aro daga Hausa saɓanin wannan da zai duba yadda Hausa ke amfani da aro wajen samar da Hausar yan siyasa.
Dambo (2013) ya gabatar da maƙala mai taken ƙirƙirarrun Kalmomin Hausa: Ina Makomarsu? Bayan gabatarwa da waiwaye kan irin hanyoyii da ake bi wajan ƙirƙirar kalmomi a harshe daga masana ya yi ƙoƙarin kawo shawarwari domin kafa wata hukuma ko cibiya da za ta taskance wannan ƙirƙirarrun kalmomin a isar da su cikin alumma domin bunƙasa harshen Hausa da inganta sadarwa a ƙarshe ya naɗe da kawo manazarta. Tabbas hanyoyin da ya nuna da ke taimakawa wajan samar da sababbin kalmomi za su ƙara wa aikinmu haske sosai, musamman ta fuskar ƙirƙira da ta shafe mu kai tsaye.
Abbas da Umar (2016) Sun gabatar da maƙala mai taken Harshe Da Siyasar Canji A Arewacin Najeriya. Bayan kawo mahimmancin harshe da siyasa a rayuwar alumma sai aikin ya yi duba irin tasirin harshen Hausa cikin jamaa da jamiyyar adawa wajen kawo canjin gwamnati a yaƙin neman zaɓen da bayan babban zaɓen shekara ta 2015 a Arewacin Najeriya, binciken ya gudana kan rain nazarin kalami a kimiyyar harshe. Akwai alaƙa da aikin Abbas da Umar dangane da muhallin da aka gudanar da binciken Arewacin Najeriya da da rukunin ‘yan siyasa tare da mahimmancin harshe, sun sha banban da wannan aiki kan ra’in nazarin kalami a kimiyyar harshe wajen yaƙin neman zaɓe ya yin da wannan aikin ke kallon aro da ƙirƙira a cikin zantukan yan siyasa.

2.2 Bita a Kan Hausar Rukuni


Harshen Hausa yana da faɗi da yalwa ta yadda har ya kai ga samar da kare-karensa masu damar gaske. Haka kuma, wannan yalwar tasa ita ce ta kai ga haifar da nau’o’in Hausa daban-daban (Yakasai 2012:109). Shi karin harshe na rukuni wani ɓangare ne na karin harshe da ya danganci wasu mutane masu halayyar zamantakewa da kuma hanyoyin sarrafa harshe iri guda, yanayin zamantakewar suke amfani da shi (Fagge, 1982).
Yakasai (2012) a cikin littafinsa ya kawo “Danagantakar Harshe Da Rukunin Jama’a”. Wanda ya yi tsokaci kan yanayi da tsarin rukunin jama’a tare da dangantakar harshe da rukunin jama’a sannan sai ya kawo nau’o’in Hausar kasuwanci da Hausar sarakuna da Hausar mawaƙa da Hausar malamai da Hausar dattijai da Hausar samari da yan mata da Hausar matan aure da Hausar gidan magajiya da ta wurin zaman makoki a ƙarshe ya kawo naɗewa cikin babin. Yakasai bai kai ga taɓo lamarin da muke son gudanar da bincike akai ba wato Hausar ‘yan siyasa.
Fagge (2004) ya bayyana yadda ake samun sauye-sauye ta hanyar saye da ƙirƙira a cikin harshe wanda ya haifar da ire-iren karin harshen Hausa na rukuni. Ya yi bayani a kan rukunoni da dama waɗanda suka danganci masu sanaoi mabanbanta da sabgogin rayuwa na yau da kullum. Da yake aikin Fagge ya kunshi Hausar rukuni daban-daban duk da yake ayyukanmu suna da kama, saboda sun taɓo abin da ya danganci Hausar yan siyasa, amma sun yi hannun riga da juna musamman ganin nawa aikin ya shafi nauin karin harshen yan siyasa na arewacin Najeriya a matsayin binciken neman digiri wanda zai kasance mai yalwa fiye da gudunmawar marubuci da ya fi ba da ƙarfi a cikin garin Kano.
Zailani (2012) ya gudanar da bincike mai take “Hausar Kan Titi”. Bayan gabatarwarsa sai ya kawo ma’anar kan titi da mutanen kan titi da sana’o’in su daga nan kuma sai ya shiga cikin aikin gadan-gadan inda ya yi ta kawo misalan nau’o’in Hausar kan titi kamar Hausar ‘yan tasi da Hausar ‘yan giya da Hausar ‘yan kodin da ‘yan sholisho da ‘yan wiwi da irin yadda suke sadarwa tsakanin su ya kuma faɗi mahimmanci harshe wajen sadarwa har da Hausar masu maganin gargajiya da jami’an tsaro a kan titi.
Garba (2010) ya gudanar da bincike mai taken “Hausar Gidan Rediyon BBC”. Bayan kawo tarihin kafuwar gidan rediyon na BBC da samun sashe na watsa labaru cikin harshen Hausa, ya karkata akalar aikin na sa zuwa irin yadda suke ya da labarai ta hanyar kawo irin jimlolin su cikin Hausa amma kuma a tsinci Turanci nan da can da fassarar da sukewa labarai na Turanci zuwa Hausa ya naɗe aikin da kammalawa da manazarta.
Yakasai (2003) ya gabatar da maƙala taken Sadarwa Tsakani Maza Da Mata: Nazarin Dagantakar Harshe Da Daidatuwar Jinsi. Bayan gabatarwa ya duba dalilin da ya sa mata ba sa magana kamar maza tare da kawo maanar daidatuwar jinsi sannan ya yi ƙoƙarin fahimtar alaƙa tsakanin harsuna daga nan sai ya kalli ayyukan masana domin nuna yadda suka gudanar da bincike kan irin na sa aikin yanayin tsare-tsaren Harshe har ma akwai inda akai magana akan harshe da jinsi a Hausa an kammala da shawarwari da manazarta.
Yakasai (2013) ya gabatar da maƙala mai taken Adon Harshe A
Fagen Dimokaraɗiyya A Kano”. Ya kawo ma’anar harshe da adon harshe tare da dimokaraɗiyya. Sai ya ya kawo jerin kafafen ya ɗa labarun da ‘yan siyasa ke amfani da su wajen sadarwa tsakanin su da juna. Daga nan, ya mayar da hankali wajen misalai na daga kalmomi da bayanan ‘yan siyasar Kano domin fito da abin da yake magana akai wato yadda suke adonta harshe cikin kalamansu ya kammala aikin da manazarta. Akwai alaƙa ta ƙut-da-ƙut da aikin Yakasai da ya yi magana a kan adon harshe a rukunin yan siyasar Kano. Ayyukanmu sun sha bamban saboda kamar yadda taken aikin ya nuna zai fi mayar da hankali ne kan samuwar Hausar ‘yan siyasa na Areawcin Najeriya ta amfani da dabarun aro da ƙirƙira.
Ayyukan da suka gabata da wannan nazari ya duba sun ƙara wa wannan aiki haske kasancewar akwai alaƙa da ke tsakani ta kusa da ta nesa. Don haka dukkan ayyukan sun bayar da babbar gudunmawa ga wannan bincike.

2.3 Naɗewa


Aikace-aikace da aka yi bitarsu su ne waɗanda wannan aikin ya ci karo da su yayin gudanar da binciken wanda suke da alaƙa ta kusa ko ta nesa. Kamar yadda bayanai suka gabata akwai kare-karen harshe da dama kuma waɗansu suna kama da juna, wannan alaƙa da ke tsakanin wadannan kare-karen harshe ya sa waɗansu mutane kan ɗauka cewa karin harshen waɗannan mutanen yana dai-dai da na waɗancan. Amma abin da ya kamata a fahimta a nan akwai yan bambance-bambance a tsakaninsu musamman wajen tsara alƙiblar wannan aiki mai taken “Hausar ‘Yan Siyasa A
Arewacin Najeriya”.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.