NA


ASHIRU USMAN GABASAWA
ADM.NO:1110106129


KUNDIN BINCIKEN NEMAN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA)
WANDA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN
NIJERIYA JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO.


SATUMBA, 2016


BABI NA UKU
TSARIN GUDANAR DA BINCIKE3.0 Shimfiďa


Wannan aiki an yi amfani da muhimman hanyoyin gudanar da
bincike da aka amince da su, a tsarin gudanar da bincike irin wannan. Kashi na farko na waďanda ake aiki a kan su, su ne ‘yan siyasar jam’iyyu da magoya bayansu, sai Ƃangare na biyu masu goyon bayan jam’iyyunsu tare da sojojin baka. Hakan ya haifar da amfani da waďannan hanyoyi kamar haka:

3.1 Wuraren da Bincike ya Shafa


Harshen Hausa shi ne harshen hulďa a arewacin Najeriya tun zamanin turawan mulkin mallaka. Harshen ya daďe yana taka rawa matsayin ya fi yawan jama’a da samun gatan kayayyakin karatu da amfani da shi wajen koyarwa a makarantu da amfani da shi a gidajen rediyo na ciki da wajen Ƙasar nan. Bugu da Ƙari an daďe ana gudanar ayyukan gwamnati a majalisun dokokin jahohi na arewacin Ƙasar nan da shi. Wannan ne ya sa dole ‘yan siyasa daje neman shugabacin jama’a gudanar da yaƘin neman zaƂensu a cikin harshen. Bayan tasirin harshen akwai kuma yawan al’umma masu jefa Ƙuri’a daga jahohi sha tara (19) na arewacin Ƙasar nan baya ga Hausawa da suka watsu a kowanne saƘo da kungu na Ƙasar. Ko a jahohin da ba Hausawa ba ne gaba ďaya a arewacin Najeriya, harshen Hausa ya kasance shi ne harshen hulďa a tsakaninsu al’ummomin, domin kyautatuwar jagoranci na wani muhimmin makami ne na samar da ci gaban al’umma a Ƙasar, musamman a arewacinta.
Kamar yadda taken bincikenmu ya nuna muhallin da za a gudanar da aikin, wato Arewacin Najeriya mai ďauke da jahohi goma sha tara (19) wanda a cikinsu yankin da ake kira Ƙasar Hausa yake shimfiďe. Don Ƙara sannin inda aikin ya gaba yana da kyau mu kawo wuraren daa ake cewa Ƙasar Hausa a arewacin Najeriya, da ke binciken ya Ƙunshi Hausa ne da Hausawa na Arewacin Ƙasar nan kan irin Karin harshen ‘yan siyasa wurin. Ƙasar Hausa gungun Ƙasashe ne daban-daban da suka kasance ƘarƘashin sarkuna daban-daban waďanda ke Ƙunshi mutanen da suka babbanta ta fuskoki da dama Harshe kawi da suke amfani da shi ya haďa su. A arewacin Najeriya wuraren da suka zama cikin Ƙasashen Hausawa su ne Daura da Kano da Rano da Zamfara da Kebbi da Katsina da Zazau da
Gobir da Garin Gabas waďannan Ƙasashe ne da akaa fara samun Hausawan asali haka kuma, daga nan ne al’adun Hausawa suka fara samuwa suke yaďuwa Ƙabilu da garuruwa waďanda suke da’awar Hauawa ne ayau (Adamu 1978: 1-2).
Sakamakon rarraba jahohi ne waďannan garuruwa na sama suka kasance a cikin wasu jahohi na Arewa ke nan.
Daura da Katsina = Katsina
Rano da Kano = Kano
Zamfara = Zamfara
Gobir = Sakkwato
Zazzau = Kaduna
Garin Gabas = Jigawa

Sakamakon wannan bayani daga masana da yadda taken aikin mu ya nuna waďanna wurare sune muhallin gudanar da binciken mu tunda ya
Ƙunshi Hausa ne da Hausawa kawai.

3.2 Adadin Bayanan da Aka Tattara


A wannan Ƃangare za mu duba yawan irin maganganun da ‘yan siyayar arewacin Najeriya aka samu nasarar tattarawa a yayin gudanar da wannan bincike wajen amfani da aro da ƘirƘira a cikin kalmomi ko kalami da jimloli ko sashin jimla don cimma burinsu da yaďa manufarsu da tallata gwanayensu na siyasa a wannan rukini.
Yawan kalaman ‘yan siyasar da wannana bincike ya iya samowa a wuraren da aka samu damar ziyarta na arewacin Ƙasar nan, an raba su zuwa gida uku kashina na ďaya waďanda aka faďaďa ma’anar Kalmar asali, kashi na biyu kuma wanda aka ƘirƘira daga kalmomin asali, kashi na ukun kuma wanda aka sarrafa kalmomin aro. A kashi na ďaya wato wana aka faďaďa ma’anar Kalmar asali muna da guda goma (10), a kashi na biyu da aka kira ƘirƘira daga kalmomin asali akwai guda goma sha takwas (18), kashi na ukun kuma mai laƘabin sarrafa kalmomin aro na guda ashirin da ďaya (21). Adadin wuraren da aka fara amfani da su a arewacin Najeriya ya shafi jahohin Kano da Sakkwato da Zamfara da Jigawa, wato a inda aka fara amfani da su kafin su watsu zuwa sauran jahohin arewa gaba ďaya ko ma
Ƙasar gaba ďaya.

3.3 Hanyoyin Tattara Bayanai


Wannan aiki an yi amfani da muhimman hanyoyin gudanar da
bincike da aka amince da su, a tsarin gudanar da bincike irin wannan. Kashi na farko na waďanda ake aiki a kan su, su ne ‘yan siyayar na Arewaci Najeriya. Hakan ya haifar da amfani da waďannan hanyoyi kamar haka:
3.3.1 Hira/Tattaunawa
An gudanar da hira da tattaunawa dam asana masu hulďa da kuma masu harkoki da suka danganci rukunin jama’ar da ake aiki akai musamman sojojin baka da suka fi taka muhimmiya rawa wajan samar da waďannan kalamai a rukunin, wasu an gana da su ta ido na ganin ido wasu kuma ta hanyar waya domin neman Ƙarin bayani a kana abin da ya shige mana duhu. Ga jerin sunayen waďanda aka yi hira da su:
1. Ali Baba Agama Lafiya Fagge, a ofishinsa da ke Fagge layin bola ranar 2 da 3 ga watan Afrilu, 2016 (Asabar da Lahadi)
2. [an Bilki Kwamanda, a ofishin Ali Baba dake Fagge layin bola ranar 9 da 10 ga watan Afrilu, 2016 (Asabar da Lahadi).
3. Aminu Black Gwale, a jan bulo gidan Sani Dawaki Gabasawa ranar ranar 16 da 17 ga watan Yuli, 2016 (Asabar da Lahadi).
4. Abdulrashid Sani Dawaki, magatakardan jam’iyyar APC na Ƙaramar hukumar Gabasawa a duk lokacin da ake neman Ƙarin bayanin abin da ya shige duhu.
5. Hajiya Binta Sayyadi a ofishin Ali Baba da ke Fagge layin bola ranar
9 ga Afrilu 2016 (Asabar).

3.3.2 Lura ta kai-Tsaye
An Ƙara samun tattara bayanai ta hanyar kura da irin yadda sojojin bakan nan da ‘yan siyasa suke gabatar da wani bayani a filin yaƘin neman zaƂe ko a wata hira da ake yi da su a kafafen yaďa labaru, an lura da yadda abubuwan da suke gudana kai tsaye na daga jama’ar wannan rukuni.
3.3.3 Karanta Wallafaffun Ayyuka
An yi amfani da bayanan da aka samo ta hanyar karance-karance daga littattafai da mujallu ko maƘalu da kundaye da aka samu a ďakunan karatu.

3.3.4 Kafar Yaďa Labarai
An tattara bayanai masu yawa ta hanyar sauraren zantukan ‘yan siyasa a rediyo da talabijin, kafin zaƂuka da bayan zaƂuka daga 1999 zuwa 2016 a jahohin arewan Ƙasar. Haka an kalli kalmomi wasu mawaƘan siyasa suka yi amfani da su a wannnan rukuni da suka shafi aikin mu, bugu da Ƙari mai binciken ya yi amfani da masaniyar da yake da ita na wasu kalmomi dan kasncewarsa Bahaushe kuma mazaunin wani yanki na
Areawcin Ƙasar nan.

3.4 Yadda Aka Tatatro Bayanai


An tattaro bayanai ta hanyar zuwa da kai wuraren da aka gudanar da binciken, wato jahohin Kano da Sakkwato da Zamfara da Jigawa an samu wasu kuma ta hanyar bayan na ziyarci wuraren da aka ambata daga baya aka samu saƘonus.
Haka kuma an tattara bayanai ta amfani da wallafaffun ayyuka a ďakin karatu wajen gudanar da wannan binciken, daga ciki akwai ďakin karatu da ke jami’ar Usmanu [anfodio a Sakkwato da na jami’ar Bayero da ke Kano. An duba kundayen bincike na neman digiri tun da na ďaya har zuwa digiri na uku waďanda suke da alaƘa da ta kusa da nesa da wannan aiki da amfani littafai da mujallu da Ƙasidu dam asana daban-daban suka rubuta musamman waďanda suke da nasaba da wannan aiki.
Sannan anyi amfani kafar sadarwa ta intanet wajen tattaro bayanai masu alaƘa da aikin mu.

3.5 Yadda Aka Sarrafa Bayanai


Ra’in da za a yi mafani da shi don sarrafa bayanai shi ne wassafawa, ta hanyar yin amfani da hanyoyi uku fitattu da ke kawo bayanai dalla-dalla, kuma a cikin jadawali.

3.5.1 Kalma ko Kalami

A cikin wannan tsarin jadawalin ƘarƘashen kalma ko kalami za a samar da irin kalmomin da kalamai na ‘yan siyasa da suke amfani da su a rukunin su na ‘yan siyasa tsakaninsu da juna kai tsaye. A taƘaice wannan sashe ya Ƙumshi Hausar ‘yan siyasa da za a nazarta.

3.5.2 Ma’ana ta Asali
A ƘarƘashin wannan jadawali ne kuma za a faďI asalin Kalmar ko kalamin don nuna inda ta samo asali Bahausheya ce ko ƘirƘirar ta akai ko a’a faďaďa ma’anar akai a wannan rukuni na ‘yan siyasa . Wannan ma’ana ta asali tana nufin ma’anar da kowa na iya fahimta ko wadda ake amfani da ita yau da kullum.

3.5.3 Sabuwar Ma’ana
A ƘarƘashin wannan kuma za a kowa sabuwar ma’anar da wannan rukuni na ‘yan siyasa suke amfani da ita wadda ta babbanta da ma’ana ta asali da kuma yadda aka saba amfani da ita a cikin sadarwa ta yau da kullum.

3.6 Naďewa


A cikin wannan babi mai taken tsarin gudanar da bincike an duba adadin bayanan da aka tattara da hanyoyin tattara su da kuma yadda aka yadda aka tattaro bayanan da yadda aka sarrafa su a cikin wannan aikin na mu.

 

ci gaba da karatu

https://www.amsoshi.com/2017/07/08/hausar-yan-siyasa-a-arewacin-nijeriya-babi-na-biyu/