Shimfiďa: Babban gine ne majingina a guri na ‘ya’yaye uba.
Darajar uba,
Falalar uba,
Martabar uba,
Darajar uba.
Amshi: Babban gine ne majinginar ‘ya’ya uba,
Inuwa ta huce zufa ga ‘ya’ya sai uba,
Ya Halilu Allah Rahimi ya Ubangiji,
Na taho ina horowa ka yi mani agaji,
A cikin yabo na uba ka sa kada in gaji,
Ka nufe ni in faďi martabar darajar uba.
Farko uba shi yake zuwa samowa,
Managarci ya mai tarbiya ta zamo uwa,
Ya ba ta kula da ďawainiya babu cutuwa,
Su yi zuriya managarciya sanadin uba.
Duk ďawainiya da tufatuwa na wuyan uba,
Gun kwanciya babu lafiya duka sai uba,
Ci da sha da kare haƘi uwa na gurin uba,
Da tarairaya ga kyauta yi duka sai uba.
Zuria’a da ta zaka duk tana wuyan uba,
Daga haihuwa ya zuwa cikar ka a gun uba,
Namiji a sa shi a kasuwa babu ja’iba,
Ita mace a kai ta gidan miji aikin uba.
Ya Mudabbiru kai ka yi ni ďa a gurin uba,
ďa a ji yawan shekare na zamo uba,
Ina Ƙarami na zamo maraya ba uba,
In na tsinci ayoyi ďari duk a kan uba.
Na ga samuwa da tarairaya a idon uba,
‘Yan uwan uba sun tarairaye mu gaban uba,
Dangin uba da abokanai ban bar su ba,
Komai na ke so za na yi tun da ga uba.
Babban gine ne majinginar ‘ya’ya uba
Marashin uba ya shiga ga babbar ja’iba,
Sirrin gida za ya tone in har ba uba,
Matan gida za su wargaje dan ba uba,
‘Ya’yan gida za su tarwatse tin da ba uba.
Tarbiyar ďiya ta yi tasgaro tin da ba uba,
Babu mai kwaƂa babu masu tsawa ba uba,
Mata da ke a gidan miji dan rashin uba,
Zagin su kullum ake ta yi dan rashin uba.
Ka gano uwa na galauniya dan rashin uba,
Ko’ina suna yawon bara dan rashin uba,
Wasu goye wasu a kafaďa marashin uba,
Allazi wahidun ku ba mu dan ba uba.
Ko karatukan ‘yan yara babu da ba uba,
Sai bibiyar juji marayu maras uba,
Boko karatu na zamani babu ba uba,
In kai rashin Uba babban rashi mai ja’iba.
Darajar mace fa a rayuwa na gurin uba,
Gatan mace fa a rayuwa na gurin uba,
Auren mace ba a yin sa sai in ga uba,
Ko gidan miji in ta Ƃaci komo gurin uba.
Wasu sunka ce wanda ya riƘe namiji uba,
Zai mace maraya inji su ‘yan malafar uba,
Ƙalubale ga martanin darajar uba,
Darajar mutum ba ta samuwa sai ga uba.
Wasu sunka ce rigar Ƙashi namiji uba,
Wasu suka ce bolar Ƙaya namiji uba,
Wasu suka ce babu ya shi namiji uba,
Wasu suka ce babu tabbaci ga namiji uba.
Ƙalubale fa ida tana a gurin uba,
Ƙalubale daraja tana a gurin uba,
Ƙalubale falala tana gurin uba,
Ƙalubale martaba tana ga namiji uba.
Babban gine ne majinginar ‘ya’ya uba,
Inuwa ta huce zufa ga ‘ya’ya sai uba,
Mafakar asirai maigida gata uba,
Marashinka za ya ga rayuwar Ƙuna uba.
WaƘar wacce na yi ta kan darajar uba,
Rabbi in da lada ka kai wa Ladan farin uba,
ďan Abubakar mai inkiya Ladan uba,
Alan Kano ne yake faďin falalar uba.
Babban gine ne majinginar ‘ya’ya uba,
In ka ga dara ďiya na daras su sun yi rawarsu ne da bazar uba,
In ka gano uwa na rawarta ta yi rawarta ne da bazar uba,
Idan ka gano ďiya sun takure sun takure dan rashin uba,
Idan ka gano uwa ta takure ta kuďuďďuke ta kuďuďďuke dan rashin uba.
- Home-icon
- Al'ada
- _Maguzawa
- _Zamantakewa
- _Abinci
- _Magunguna
- _Sana'o'i
- _Gine-Gine
- _Tufafi
- _Bukukuwa
- _Addini
- ADABI
- _Azanci
- __Karin Magana
- __Kacici-Kacici
- _Waƙoƙi
- __Waƙoƙin Baka
- ___Na Gargajiya
- ___Na Mawaƙa
- __Rubutattun Waƙoƙi
- __Waƙoƙin Zamani
- _Zube
- __Almara
- _Wasan Kwaikwayo
- __Finafinai
- HARSHE
- _Ƙirar Sauti
- _Tsarin Sauti
- _Ƙirar Kalma
- _Ginin Jimla
- _Ilimin Ma'ana
- _Walwalar Harshe
- _Fassara
- _Ƙa'idojin Rubutu
- _Kimiyya da Fasaha
- BIDIYOYI
- HOTUNA
- EDUCATION
- _Courses
- Humanities
- _Poems
- _Linguistics
- _Literature
- _History
- SOCIAL SCIENCE
- _Theories
- _Sociology
- _Psychology
- _Economics
- _Philosophy
- _Political Science
- SCIENCES
- _Agriculture
- _Crypto
- _Health
- _ICT
- _Mathematics
- Jokes
3 Comments
[…] Duba wak’ar Ala […]
ReplyDelete[…] Karanta wak’ar Ala: […]
ReplyDelete[…] Karanta wannan […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.