Header Ads Widget

Request to place your ads here.

Kanu

6/random/ticker-posts

Kayan Kid’a: Banga, Kotso Kuru/Kuwaru

 

Na


Abbas Musa
Nuhu Ibrahim Bayawa
Shu’aibu Murtala Abdullahi


 

Gabatarwa


Buga abubuwan da aka yi musamman don bugawa da busa abubuwan da aka yi don busawa shi ake kira kiďa. A Ƃangaren nazarin adabin Hausa nazarin waƘa abu ne mai matuƘar faďi kamar filin sukuwa wanda sai ingarman doki zai iya sukuwa a cikinsa haka nazarin waƘa a yau da jiya.
ƘarƘashin nazarin waƘa ta baka nazarinta ba zai tafi yadda ya dace ba sai da dubin yanayi da yadda ake yin kiďa da saƘon da kiďan ke isarwa don cimma nasarar makiďin. A wannan aiki namu za mu dubi kayan kiďan Hausa ne guda uku da ake bugawa wato:
1. Kotso
2. Banga
3. Kuru/kuwaru
A wannan aikin za mu bayyana yadda ake haďa kayan kiďan da kuma abubuwan da ake buƘata don kayan kiďan da kuma sautin da suke bayarwa da waďanda ake kaďawa kayan kiďan da makaďan da ke amfani da kayan kiďan da za mu bayyana.
Kiďa shi ne samar da wani sauti na musamman ta hanyar goga wani abu ko busa shi ko grgiza shi ko buga shi ko ƘyanƘyasa shi kuma ya zamanto sautin da aka samar yana da manufa (Dumfawa, 2016).
Zaruk da wasu (1987) sun bayyana ma’anar kiďa da cewa: “Kiďa yana nufin wanzar da daddaďan amo daga abubuwan bugawa ko na gogawa ko na busawa ko kuma na girgizawa.” Misalin abubuwan bugawa shi ne kalangu, na gogawa kuma shi ne kamar goge, na busawa kuma sun haďa da sarewa, sai na girgizawa kuma kamar kacakaura.

Kashe-kashen Kiďa


Masana sun karkasa kiďa zuwa gida uku kamar haka:
1. Jinjina
2. Ƙirya/take
3. Ƙira

Jinjina
Ita ce inda makaďi zai kiďa abin kiďansa da ďayan manufa kamar haka:
a. Sanarwa: shi ne inda makaďi ya zo wurin da zai yi kiďansa don ya sanar da maigida cewa ga shi ya zo.
b. Gayyata: yana nufin inda makaďi zai rinƘa kiďa don jawo hankalin yara cewa za shi wasa, wato dai yana gayyatar mutane zuwa inda zai yi wasa.

Ƙirya/take
Shi ne kiďan da yake ďauke da wata magana. Take yana samar da abubuwa guda biyu kamar haka:
a. Samar da magana
b. Samar da karin waƘa

Ƙira
Shi ne kiďan da bai ďauke da wata magana amma yana tafiya da karin waƘa.

Dalilin Yin Kiďa


Daga cikin dalilan da ke sa a yi kiďa sun haďa da:
1. Nishaďi
2. Karin waƘa
3. Sadarwa
4. Mayar da martani
5. Zuga, kamar yadda Dumfawa (2016) ya ce ta kasu gida uku:
i. Zuga kumburau
ii. Zuga ingizau
iii. Zuga ta kariya

Amfanin Kiďa ga Bahaushe


Kiďa yana da amfani ga Bahaushe kamar yadda yake da amfani ga sauran al’ummomin duniya. Daga cikin amfanin kiďa ga Bahaushe akwai:
1. Bahaushe yana samun nishaďi ga kiďa. Duk lokacin da ake kiďa Bahaushe na samun nishaďi ta hanyar sauraro ko rawa.
2. Bahaushe na amfani da kiďa wajen sanarwa. Misali idan sarki na son tara jama’a zai bayar da umurni a buga wani abin kiďi kamar a lokacin Ramadan ko lokacin yaƘi kokuma ayarin fatake ko gun farauta a daji da sauransu.
3. Bahaushe yana amfani da kiďa don samar da karin waƘa.
4. Bahaushe yana amfani da kiďa wajen bautar iskoki. Misali a wajen girka da bori.

Su wa Ake wa Kiďa?


Bahaushe yana kiďa wa rukunin jama’a kamar haka:
1. Sarakuna
2. Maluma
3. Sana’in Hausawa
4. Sauran jama’a

Kayan Kiďan Bahaushe


Bahaushe yana amfani da kayayyaki daban-daban wajen kiďa. Masana sun bayyana nau’o’in kayan kiďa zuwa gida huďu kamar haka:
1. Kayan kaďawa, sun haďa da:
a. Banga
b. Duma
c. Dundufa
d. Ganga
e. Kalangu
f. Kuru/kuwaru
g. Kotso
h. Jauje
2. Kayan Busawa, sun haďa da
a. Algaita
b. Kakaki
c. Fare
d. Ƙaho
e. Kobira
f. Zilli
g. Sarewa
3. Kayan girgizawa/ƘyanƘyasawa, sun haďa da:
a. Kacakaura
b. Kwamsa
c. Caki
d. Ruwan gatari
e. Shantu
f. Caki
4. Kayan izga, sun haďa da:
a. Garaya
b. Goga
c. Gurmi
d. Kukuma
e. Kuntugi
f. Molo

Yadda Ake Koyon Kiďa


Kiďa a matsayin sana’a ana koyon sa kamar yadda ake koyon kowace irin sana’a a duniya ba kawai tsakar dare mutum kan tasarwa sana’ar ba, lallai makaďi ya koya ko dai daga wani ko kuma ya fara koyo daga karan kansa har ya Ƙware.
Waďansu sukan koyi kiďa ta fara koyon yadda ake buga ďan kuntuku da kanzaki wanda tun suna bugawa ana cewa ga yadda za su yi da baki har su Ƙware.
Bayanin Yadda Ake Yin Wasu Kayan Kiďa
1. Kotso: Abin kiďa ne na Bahaushe kuma kotso ya yi kama da kalangu sai dai shi baki ďaya ke gare shi, kuma da hannu ake buga shi. Sarakuna ake buga wa shi. Daga cikin makaďan da suka yi suna a Ƙasar Hausa wajen buga kotso sun haďa da:
i. makaďa Ibrahim Tubale Narambaďa
ii. Alhaji Sa’idu Faru
iii. Alhaji Musa ďanƘwairo
Yadda ake kotso kuwa shi ne, ana yin kotso da itacen Ƙirya ko gawo ko kaďanya ko kolo. Da farko za a fafare cikin itace a daidaita tsayinsa a fitar da bakunansa biyu na sama da na Ƙasa. Daga nan sai a sami fatar damo ko guza a rufe bakin saman a yi masa Ƙangu a ďaure da tsarkiya. Za a manna wa fatar saman naƘe kana a ďaura zare mai Ƙara amo da diri kuma akwai huďar da ake yi da ake liƘonta da saƘar zuma kuma ana yi masa maratayi ta yadda za a rataya shi a kafaďa. Kotso a siffa siriri ne bai kai girman kalangu ba. ya yi kama da banga sai dai bai kai tsayi da girmanta ba.
Abubuwan da suka haďa kotso su ne:
i. Fata
ii. Nake
iii. Itace
iv. Zaiga
v. Kambu
vi. Maďauki
2. Banga: Kayan kiďan sarauta ce sannan ‘yar Ƙarama ce tana da rawani a gefenta. Tana da kawara a gefenta. Dumfawa (2016) ya ce idan makaďi zai buga ta cikin riga yake saka ta saboda ba a son a ga bayanta. Da hannu ake buga ta sannan sauti ďaya kawai take samarwa wato mai tashi. Sai dai Gusau (2016) ya ce ana yi mata maratayi har ma a rataya ta ga kafaďa.
Abubuwan da suka haďa banga su ne:
i. Fata
ii. Itace ko gwangwani
iii. Tsirkiya
iv. Awara
v. Kambu
vi. Nake
vii. Ƙiriniya
viii. Ido
3. Kuru/kuwaru: kayan kiďan Bahaushe ce ana kaďawa sarakuna ita da kuma manoma. Amma galibi an fi kaďa wa manoma ita. kuma ana kiďa shi ga maguzawa masu wasan bauta. Idan za a yi wa manoma akan cire nake, idan kuma za a yi wa sarki sai a sanya shi sannan yana da maratayi. Makaďan da suka shahara a Ƙasar Hausa da kiďan kuwa su ne:
1. Jibo Magajin Kuwaru
2. Abubuakar Akwara Sabon Birni
3. Abu ďankurma Maru
Abubuwan da ke haďa kuwaru/kuru su ne:
i. Fatar akuya
ii. Itace
iii. Zare
iv. Nake
v. Tsarkiya
vi. Maratayi

Naďewa


A wannan aiki mun dubi ma’anar kiďa bayan gabatarwa, da kuma kashe-kashen kiďa. Sannan an dubi dalilin yin kiďa da amfanin kiďa ga Bahaushe sannan mun bayyana rukunin mutanen da ake wa kiďa bayanin kayan kiďan Bahaushe da yadda ake koyon kiďa sai kuma bayanin yadda ake yin wasu kayan kiďa wato kotso da banga da kuma kuwaru/kuru.

Duba wak'ar Ala

https://www.amsoshi.com/2017/07/10/aminu-ladan-alan-waka-uba/

Manazarta


Dumfawa, A. A. (2016). Laccar aji ta ALH 404, Sashen Harusnan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Gara, C. Y. (1991). Sana’o’in gargajiya a Ƙasar Hausa. Ibadan: Baraka Press and Publishers ltd
Gusau, S. M. (2016). Ƙamusun kayan kiďan Hausa. Kano: Century Research and Publishin Limited, Nigeria.
Zarruk da wasu (1987). Sabuwar hanyar nazarin Hausa don Ƙananan makarantun sakandare littafi na biyu.

Post a comment

1 Comments

Rubuta tsokaci.