Ticker

6/recent/ticker-posts

Alu Sarkin Yamma Ɗan Barade Jikan Umaru

Jagora: Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ɗan Barade Jikan Umaru.
Yara: Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ɗan Barade Jikan Umaru.
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.


Jagora: Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara: Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa.

Jagora: Gwamna mai faɗa da cikawa,
Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: Ka rai babban kada,
Uban Lamiɗo.
Yara: Kwaj ja da kai,
Ka karya mai tsara,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: Ka rai babban kada,
Uban Lamiɗo.

Yara: Kwaj ja da kai,
Ka karya mai tsara,
Ɗan Barade jikan Umar,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkawato.

Jagora: Gwamnan da yah hi kowa aiki,
Yara: Birni da ƙauce,
An ce ka ka yi ɗa.

Jagora: Gwamnan da yah hi kowa aiki,
Yara: Birni da ƙauce,
An ce ka ka yi ɗa.

Jaora: Don ka yi gwamna,
Ka ba she haushi.
Yara: Ka bar su wane,
Sai korar fage.

Jaora: Don ka yi gwamna,
Ka ba she haushi.
Yara: Ka bar su wane,
Sai korar fage.

Jagora: 2007 ka yi gwamna,
2008 ma ya yi gwamna,
2011 ta danno,
Yara: Kai za a baiwa,
Gwamnan Sakkwato.

Jagora: Aliyu,
Yara: Kai za a baiwa,
Gwamnan Sakkwato,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu Gwamnan Sakkwato.

Jagora: Ya Rabbana, ya kama ma dawa,
Yara: Rabbana ya kama ma.

Jagora: Aliyu Rabbana ya kama ma dawa,
Yara: Rabbana ya kama ma,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara: Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa.
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: Da birbiri da jemage,
Bana sun tura gar,
Biɗan wauta,
Wani na kun san shi,
Yara: Mai Rodu ɗan tsiya,
Mai tsintsiya,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Haji Aliyu gwamnan Sakkwato,
Ɗan Barade jikan Umaru.

Jagora: Ɗan Barade jikan Umaru,
Aha Ɗan Barade jikan Umaru.
Yara: Ya Rabbana ya kama ma kwarai,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Haji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: In ka ga alfijir ya ɓullo,
Rana kaɗan ka ɓullo wa ciki.
Yara: Ai hannu ba za ya karekke ta ba,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu Sakwato.

Jagora: Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara: Birni da ƙauye an ce ka yi ɗa,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: In ka ga alfijir ya ɓullo,
Rana kaɗan ka ɓullowa ciki,
Aradu ko ta ɓullo,
Yara: Hannu ba za ya karekke ta ba,
Ɗan Barade jikan Umaru,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: Gwamna mai faɗa da cikawa,
Yara: Birni da ƙauye,
An ce ka yi ɗa.
Ɗan Barade jikan Umar,
Hajji Aliyu gwamnan Sakkwato.

Jagora: Toron giwa Alu uban tafiya,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Gwamna Alu uban tafiya,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Aliyu uban tafiya,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Mu bugti tamburran gwamna,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Aliyu ag gwamna,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adalci ne,
Ɗan Barade Wamakko,
Ali Sarkin Yamma.

Jagora: Gwamna Aliyu yai aiki,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Gwamna Aliyu yau aiki,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Gwamna Aliyu ya gyara,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Birni da ƙauye yai aiki,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Ya saki kaya,
A ba talakkawa,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: wasu shaggu,
Sai su ɓoye kayansu,
Yara: Duk saboda sarkin Yamma.

Jagora: Shaggu da su da matansu,
Yara: Duk saboda sarkin Yamma,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adalci ne,
Ɗan Baraden Wamakko,
Ali Sarkin Yamma.

Jagora: Allah shi maka jagora,
Yara: Ya Wahabu.

Jagora: Ya sa ka gama lafiya cikin mulkin,
Yara: Ya wahhabu shi nir roƙa.

Jagora: Gwamna Aliyu mai daraja,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Gwamna Aliyu mai daraja,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Sakkwato mun samu,
Gwamna mai ilimi,
Yara: Ɗan Barade kai ɗai ka iyawa.

Jagora: Mun ɗeɓe zamarke,
Mun ka sa gwaiba.
Yara: In tai ɗiyanta sai mun ƙoshi.

Jagora: Kai munahukin Allan nan,
Da yai yi makircin,
Yara: To fa gwamna ya rantse,
Bai barin shi,
Sai ya ɗaurai,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adali ne,
Ɗan Baraden Wamakko,
Ali Sarkin Yamma.

Jagora: Wane munahukin Allah,
Yara: ɗan Ubayyu,
ɗan shi’a ne,
Riƙa ƙwarai gwamna,
Mai gaskiya da adalci ne,
Ɗan Baraden Wamakko,
Ali sarkin Yamma.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.