Wa ya yi Kisa?
Wata ranar Lahadi wani mai kuɗi yana zaune da matarsa a
cikin gida. Sai matar ta tashi domin ta shiga damfami ta duba abincin da ta ɗora
bisa wuta. Ba ta yi mintuna biyar ba ta dawo. Amma sai ta tarar mijinta a mace.
An kashe shi! Ta yi kururuwa mutane suka taru. Kan a jima ‘yan sanda sun iso
cikin gidan.
‘Yan sandan nan suka tara illahirin masu aiki a gidan domin su yi musu tambayoyi. Matar ta ce, ita dai ta suna tare, amma sai ta shiga cikin damfami na misalin mintuna biyar. Mai gadi ya ce, shi dai yana nan bakin ƙofa bai je ko’ina ba, kuma babu wanda ya shigo. Mai tuƙin gidan ya ce, shi dai ya kai yara makaranta a lokacin da abin ya faru. Mai bayin fulawa ya ce, shi dai yana can bayan gida yana bayin fulawa lokacin da abin ya faru. ‘Yan sandan nan suka yi shiru, can sai ɗayansu ya ce:
“Ku kama wannan mai tuƙin.”
Wace hujja wannan ɗan sanda ya yi amfani da ita?
1 Comments
[…] karanta almara: […]
ReplyDeletePost your comment or ask a question.