Citation: Anas Sa’idu Muhammad (2017). Tantance Awon Baka A Matanin Waƙoƙin Makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon Birni. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 5. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660
TANTANCE AWON BAKA A MATANIN WAƘOƘIN
MAKAƊA SA’IDU MAIDAJI SABON BIRNI
Anas
Sa’idu Muhammad
Abstract
The analysis in the repertoires of Hausa oral songs context, progressiɓely has derived the enthusiasm of
researchers due to the logical manifestations embedded in the compositional teɗts. However, the reɓiew of literature in
this study uncovered very limited studies were conducted on structural analysis goɓerning the performances
and stanza flow in Hausa oral song’s composition. Thus,
this study utilizes the theoretical premise of Waƙar
Baka Bahaushiya (WBB) to depict the context of performance and the stanza flow embedded in the textual repertoires of
Makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon
Birni. The method applied in this study is qualitative in nature and the analysis is subjective to the postmodernist
narrative discourse
interpretation technique. The findings indicated that Makaɗa Maidaji has the solid
power to competently filter his message to the audience as he adorns WBB
theoretical stanza patterning of
+lead+chorus+encoding+increase+corollary+-reaction/mutational response+song’s
base+rhythm. Moreoɓer, the findings showcase the singer’s structural
performances are heavily guided by the WBB theoretical edicts of stanza
construction in terms of clause structures, simple, compound, complex, and compound-complex sentences in the
enjambment and run-on patterns of rising+extreme-high+fused+ falling+end-stopped.
Key words: awon baka, awon ɗiya, awon rerawa,
matanin Makaɗa Maidaji, waƙar baka Bahaushiya (WBB)
1.0 GABATARWA
Duk da dai
Abdulƙadir
(1981) da Muhammad (1981) da Abba da Zulyadaini (2003) da kuma Finnegan (2012)
sun yi hasashen cewa hanya ɗaya mafi muhimmanci wajen fahimtar yare ko al’umma ita ce ta
kallon awon baka. Amman kawo yanzu, nazarin awon baka na ɗaya daga cikin muhimman
fanni wanda da yawan manazarta suka bar babban giɓi a kai. Bisa fahimtar sauran manazarta, awo a fasahar baka
na bayyana aikin fasihi wajen dangantakar da ke tsakanin matani da ma’ana da
kuma manufar saƙo ta amfani da salo mai gamsarwa (Gusau, 2014; King,
1967).Yiyuwar hakan ya sa Gusau (2003a) ya ayyana lallaimatani a waƙar
baka a kowane “ɗan waƙa mai nazari zai iya kula da yadda makaɗi yake ƙulla
carbin tunaninsa da saƙa kalmomi donisar da saƙonni cikin jimloli” (sh.
33-34). Shi kuwa Satatima (2009) ganin yake yi ana“fayyace ɗan waƙa a
matsayinsa na ƙunshiyar saƙo ko manufar waƙa da ke auna yadda makaɗi ke shirya tunaninsa wajen ƙulla
kalmomi su bayar da saƙon da yake burin isarwa ga al’umma” (sh. 127-128). Yayin da
kuma Muhammad (2012) ke kallon awonbaka da“hanyar da makaɗi kan bi ya jera tunaninsa,
tare da shirya shi domin ya isar da saƙonsa ga mai sauraro ta
amfani da ɗiyan waƙa waɗanda suke tamkar rassa irin
na itaciya da ake fara hawowa daga gindi a sauka ta kansa (Muhammad, 2012, sh.
147). Ke nan awon baka:
Fage ne na
nazarin waƙar baka da ya shafi yadda makaɗi yake shirya waƙa a cikin zubin ɗiya da dabarun karin murya
inda ake duba tsarin saɗara da adadin ɗiyan waƙa da tsarin rerawa da karin murya da amsa-amon kari da
sauransu (Gusau, 2003, sh.32).
Domin haka,
za a iya ayyanar da kowace al’umma da lokacin da ta soma nazarin awon baka a
cikin fasaharta ta asali gwargwadon wayewarta da ci gabanta da saduwarta da
wasu baƙin
al’ummu.A waƙoƙin baka na Hausa, akan tsara ɗiya waɗanda ake amfani da su a gina waƙa (Abdulƙadir, 1975; Gusau, 2008). Domin kamar yadda aka bayyana makaɗa sukan yi amfani da zantuka ne su
sarƙa zaren tunaninsu a waƙa don jawo hankali da saka karsashi
da nuna zalaƙa tare da gwanincewar harshe (Gusau, 2002). Idan aka waiwayi ayyukan masana adabi irin su Muhammad (1981)
da Gusau (2001) da Schuh (2002) da Olatunji (2005) da Gusau (2011) za a tarar
sun nazarci hanyoyin awo da ma’auni da kuma tsari a waƙoƙin
baka na Turawa da na Yarbawa da na Hausawa ta hanyoyi mabambanta.Ke nan awon
baka hanya ce wadda ta ƙunshi karin murya ta fuskar hawa da saukada faɗuwar murya da amsa-amon
karida tsarin layuka a ɗiya na waƙoƙin baka. A taƙaice wannan bincike yi yi ƙoƙarin
amfani da dabarun nazarin awon baka daga ra’in WBB (Gusau, 2014) wajen ɗora matanin waƙoƙin
Makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon Birni[1]
bisa masakin tarke. Duba da haka, wannan bincike ya yi amfani da dabarun ra’in
Waƙar
Baka Bahaushiya (WBB) wajen fito da tsarin awon baka a waƙoƙin
Makaɗa Maidaji. Ke nan, sigar
wannan binciken ya shafi matanin waƙoƙin
Maidaji ne zalla bisa ra’in WBB inda yai ƙoƙarin
amsa waɗannan tambayoyi: (a) Ta wace
siga Makaɗa Maidaji
ke auna ɗa mai sauƙi a
matanin waƙoƙinsa? (b) Shin ko Makaɗa Maidaji kan tsarma awon ɗa mai tsauri da ke ƙunshe da harshen damo a
matanin waƙoƙinsa? (c) Wace fitacciyar sifa ce Makaɗa Maidaji ke amfani da ita
gina jimloli yayin rera waƙoƙinsa?
2.1 RA’IN WAƘAR BAKA BAHAUSHIYA (WBB)
Wani ɓangaren ra’in WBB ya fayyace
tunaninsa ne dangane da wanzuwar awon baka a matanin waƙoƙin
baka na Hausa. Dangane da awon baka, ra’in WBB ya fara kafa hujja ne da ayyukan
Burton (1954) da Richards (1976) da Burgess (1964)da Gray (1975) da Muhammad (1978) da King (1986)
da Schuh (2002) da Dunfawa (2003) inda yake kallon matanin waƙa
dangane da tsari da ma’auni da ƙirgar ma’ana da kuma gidan dara na kari waɗanda fasihi kan yi amfani da
su wajen isar da saƙo. Ra’in na nuni da sigar awon baka ta yadda fasihi ke nuna
gwanintarsa tare da zalaƙar harshensa wajen isar da rauji tare da amsa-amon kari a
cikin waƙoƙinsa.
Hakan kan ba mazarci damar fahimtar daidaituwar kari a gaɓar saɗarun ɗiya (Gusau, 2014).Ta haka ne
kuma ra’in WBB ya fito da hanyoyin awon baka a saɗarun ɗiyan waƙa ta lura da yadda ma’ana take hawa da sauka da yadda ake yi
mata takidi da ajewa da saukar-sauka (Gusau, 2001).Ra’in ya fayyace yadda tsarin tarbe da rakiyada karɓeɓɓeniyada bayayyeniyake
bayyana sigar dangantakar ɗiya a waƙoƙin bakana Hausa bisa manya da ƙananan saƙonnin
turke. Ta hake ne ra’in WBB ke ganin, ana iya rarrabe ɗa da ɗa a waƙar
baka ta maimaita rera gindin waƙa (a wajen makaɗi wanda = +ƙungiya +karɓi +Layi) ko sautin kiɗa(a wajen makaɗi wanda = –ƙungiya -karɓi -layi) ko tsarin rerawa. Domin hawa da sauka suna tabbatar
da saƙo da
makaɗa sukan cusa ba kara zube
yake ba. Ta duban waɗannan bayanai, ra’in WBB ya bayyana hanyoyi guda biyu waɗanda ake amfani da su wajen
fitar da awon baka da suka haɗa da:
Awon Baka na Ɗiyan Waƙa a WBB
Awon baka
na ɗiyan waƙa
kan fayyace matanin ma’ana ta hanyar fayyace ma’ana ne a ɗan waƙa
mai nazari zai fito da matakai waɗanda makaɗi yake bi ta kansu wajen tsara ɗa a waƙarsa. Waɗannan matakai sun haɗa da:
Hawa: Na nufin inda aka
fara furta ƙaramin saƙo; Jagora/Kaɗaita/Wakili.
Hauhawa: Na nufin inda aka ci
gaba da furta ƙaramin saƙo; Jagora/Kaɗaita/Wakili.
Sauka: Na nufin ƙarasa
furta ƙaramin
saƙo da
aka faro a hawa; ‘Y/Amshi+Layi, ko Kaɗaita –Layi.
Ajewa: Wuri ne da ake
numfasawa kan gaɓar ƙaramin saƙo; ‘Yan Amshi/Kaɗaita.
Saukar-Sauka: Wato
kacokan wurin da aka iyar da ƙarasa ƙaramin saƙo ‘Yan Amshi/Kaɗaita(Gusau, 2014).
Haka
zalika, awon baka na ɗiyan waƙa na tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da tantance ƙirgar ma’ana inda manazarci
zai iya duba yawan ƙananan saƙonni ne da aka zuba a ɗa, za a yi amfani da haruffan Abacada Ɗa,
b, c, d, e da sauransuɗ wajen ƙirga yawan ƙananan saƙonni da aka zuba a ɗa na waƙar baka. Sai kuma harafin Ɗɗɗ wajen nuna adadin layuka na gindin waƙa.
Awon Baka na Rerawa a WBB
Awon rerawa
kuwa “tsari ne inda makaɗi yake amfani da karin murya cikin rauji mai ma’ana ya furta
kalmomin da ya zuba a cikin waƙoƙinsa” (Gusau, 2003b, sh.183). Ra’in WBB na kallon
awon rerawa a matsayin hanyar da ake furta ƙwayoyin kalmomi cikin
jumloli da tsara su saɗara-saɗara a cikin ɗiya tare da samar da rauji mai inganci da ake shiryawa da
nufin isar da wani saƙo. Ra’in WBB ya fito da wasu dabaru waɗanda ake amfani da su wajen
fito da awon baka na rerawa. Ra’in ya ayyana waɗannan dabaru na rerawa waɗanda ake ganin da wahala makaɗa da mawaƙan baka na Hausa su zarce wannan ƙa’ida
ko da kuwa na kaɗaita ne ko kuma na ƙungiya ne. Ga yanayin
afkuwar kamar haka:
i) Rerawa ta + Jagora +
‘Y/Amshi/ (‘Y/Karɓi) + Ƙulli + Tarbe (Ƙari) -/+ Karɓeɓɓeniya (Rakiya) + Gindin Waƙa
-/+ Bayayyeniya + Kiɗa/Rauji.
ii) Rerawa ta + Jagora
–‘Y/Amshi - Ƙulli –Ƙari – Gindin Waƙa + Kiɗa/Rauji.
iii)Rerawa ta + Jagora +
‘Y/Amshi/ (‘Y/Karɓi) + Ƙulli + Ƙari + Karɓeɓɓeniya + Gindin Waƙa – Bayayyeniya + Kiɗa/Rauji.
iɓ) Rerawa ta + Jagora
-‘Y/Amshi - Ƙulli - Ƙari -Tarbe - Karɓaɓɓeniya (Rakiya ) + Gindin Waƙa + Kiɗa
(Gusau,
2002,sh. 44; Gusau, 2003a, sh. 40).
Kashi na farko ya ƙunshi, jagora
wanda ‘yan amshinsa suke ƙari da tarbe da
karɓeɓɓeniya ko rakiya kamar Makaɗa Maidaji da Makaɗa Musa Ɗanƙwairo da
Makaɗa Salihu
Jankiɗi da Makaɗa Ibrahim
Narambaɗa da
sauransu. Kashi na biyu ya ƙunshi jagora da
‘yan amshinsa masu yin karɓi ta maimaita gindin waƙa zalla kamar Makaɗa Mamman Shata
da Makaɗa Muhammadu
Gawo Filinge da Makaɗa Audu Karen Gusau da makamantansu. Kashi na uku
kuwa ya ƙunshi jagora da ‘yan amshinsa suna maimaita duk
abin da ya furta ne ba tare da yi masa ƙari ba,
kuma ba sa rera gindin waƙa domin waƙoƙinsu ba su da
gindin waƙa. Wato masu ɗauke da tasirin bayyayyeniya ke nan. Kashi na huɗu kuwa ya
haɗa da jagora
wanda babu mai yi masa amshi ko karɓi, sannan babu mai yi musu ƙari, ba tarbe ba rakiya sannan kuma babu karɓeɓɓeniya ballantana bayayyeniya amma suna amfani da sautin kiɗa. Ire-iren
waɗannan mawaƙa sun haɗa da Makaɗa Ɗanmaraya
Jos da Makaɗa Babangida Kakadawa da sauransu.
3.0 FAYYACE AWON BAKA NA ƊIYA AWAƘOƘIN MAKAƊA MAIDAJI
Duba da
ra’in WBB kamar yadda aka bayyana a baya, awon ɗa na iya zama mai sauƙi ko mai tsauri bisa
tafarkin nazari kamar haka:
3.1 AWON ƊA MAI SAUƘIA WAƘOƘIN MAKAƊA MAIDAJI
Shi ne
wanda zai ƙunshi ƙaramin saƙo ɗaya. Waƙoƙin Makaɗa Maidaji cunkushe suke da misalai,da suka shafi awon
bakadomin kuwa yana gina waƙoƙinsa cikin tsarin rerawa mai armashi kuma karɓaɓɓe. Waƙoƙi ne
da ke tattare da zalaƙar rerawa da gwanincewar harshe. Ga misalin tsarin ɗa mai sauƙi a
waƙar
Arzika ta noma ‘Sarki yai abin daka ya
huta’:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Baba mijin Shibo mijin Maryama,
Sauka A2
: Giwa maganin itacen daji,
Ɗ1 : Sarki yai abin daka ya huta,
Ɗ2 : Zaki ɗan Abubakar ɗan Buda.
(Muhammad,
2012, sh. 155)
Sannan a waƙar ‘kak ka yarda da raini uban Baraya’ ta
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris (1975-), Makaɗa Maidaji ya ƙara bayyana:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Ai ga ni na zaka Zazzau mu gai da sarki,
Sauka A2
: Ban ga Habiba ba kuma ban ga Mariya ba,
Saukar
Sauka A3 : Ai ko su Binta ba su da halin su daƙile
ni,
Ɗ1 : Kak ka yarda da raini uban Baraya,
Ɗ2 : Shehu Alhaji Allah ya taimaka ma.
(Muhammad,
2012, sh. 157)
Har wa yau
dai a waƙar ‘gagari gaba na Salihu’ ta Sarkin Gobir
na Sabon Birni, Alhaji Ummaru
ɗan Salihu (1957-1966),Makaɗa Maidaji ya ƙara fito da irin wannan batu:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Ga ni ina son ɓacin tcibilbila,
Sauka A2
: Zaman zauri ɗai nika
gudu,
Ajewa A3
: In zauri ya buwaya yanzu,
Saukar
sauka A4 : Ko ga itace zama takai,
Ɗ1 : Gagari gaba na Salihu,
Ɗ2 : Mainasara ɗan Durumbu,
Ɗ3 : Ɗan Hayatu magajin gidan Kada.
(Muhammad,
2012, sh. 155)
A waƙar ‘ya kwan yana aikin mota’ ta Sarkin
Tashar Motar Sabon Birni, Alhaji Idi ɗan Argiji, Makaɗa Maidaji ya isar da saƙo ta cikin kinaya tare da
nuna zalaƙar harshe, ya yi amfani da wannan dama ya faɗi yadda ya taro aradu da ka
domin ga shi yana so zai yi tafiya Zazzau ya amsa kiran Sarki amma babu
wadatattun kuɗi a wajensa
kuma ga shi da tarin yara masu yi masa amshi inda daga bisani sai sarkin tashar
motar garin Sabon Birni ya shiga tsakani. Ga kaɗan daga cikin abun da ya rera:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Ga ni ina shirin tahiya Zazzau,
A2
: Kuma ga ni ba ‘yan kuɗɗi,
Hauhawa A3
: Ina nuhin tahiya Zazzau,
A4
: Kuma ga ni ba ‘yan kuɗɗi,
Sauka A5
: Ga ni ina dibin mota ni ko suna kallo na,
A6
: ‘Yan Kamishon suna dibin mota,
A7
: Ni ko suna kallo na,
Ajewa A8
: Don sun gane ni da taron,
A9
: Yara zay yawa bayana,
Saukar
Sauka A10 : Har an yi jinga na tada,
A11
: Ba zan biyan kuɗɗi ba,
Ɗ1 : Ya kwan yana aikin mota,
Ɗ2 : Ɗan Argiji ɗan Shawai,
Ɗ3 : Sarkin tasha jikan Idi,
Ɗ4 : Jikan fulanin Ɓaure.
(Muhammad,
2012, sh. 156)
Ga kuma
wani misalin ɗa mai sauƙi
daga waƙar ‘Ya wuce tantama’ ta Alhaji Shu’aibu
inda Makaɗa Maidaji
ya bayyana cewa:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Ni da dai nas sauka Sabon Birni,
A2
: To na sauka ko han na kwan,
A3
: Na ishe yara na wata waƙa,
Hauhawa A4
: To ko yara kau ko ‘yan mata,
Sauka A5
: Sun ce wanda yas sai nama,
A6
: Ya ɗara wanda yas sai kihi,
A7
: To, wanda yas sai anta,
A8
: Ya ɗara wanda yas sai hanji,
A 9
: To, kuma wanda yas sai doya,
A 10
: Ya ɗara wanda yas sai gwaza,
Ajewa A11
: To, kuma wanda yas sai doki,
Saukar
Sauka A12 : Ya ɗara wanda yas sai jakki,
Ɗ1 : Ya wuce tantama,
Ɗ2 : Shi Alhaji Shu’aibu zamani nai ya kai.
(Muhammad,
2012, sh. 158)
A waƙar ‘Ɗan Sidi amshi sandar mulki ƙasatai’ ta Sarkin Buza, Alhaji
Muhammadu, Makaɗa Maidaji cewa ya yi:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Da na samu kurciya ko ko damisa ne,
A2
: Ko ko tattabara uwat tsuntsaye na samu,
A3
: Da na ba da saƙo,
Hauhawa A4
: Saƙon
da ba ni ba za ta zo ta kwana ba,
Sauka A5
: In tac ce gari da nisa in ba da taguwa,
A6
: In tac ce gari da yunwa in ba da gari,
A7
: In tac ce gari da ƙishirwa in ba da salka,
A8
: In tac ce gari da ɗari in ba da bargo,
Ajewa A9
: In taz zo tac ce matan Falgore ƙasatai,
Saukar
Sauka A10 : Ga darnin da yab bari ya koma katanga,
Ɗ1 : Ɗan Sidi amshi sandar mulki ƙasa
tai,
Ɗ2 : Mai Buza ɗan Hassan mai taro hannu.
(Muhammad,
2012, sh. 157)
3.2 AWON ƊA MAI TSAURI A WAƘOƘIN MAKAƊA MAIDAJI
Shi ne ɗa mai harshen damo wanda ya ƙunshi
ƙananan
saƙonni
biyu ko fiye da haka. Shaharar Makaɗa Maidaji a waƙar baka ta Hausa da
gwanincewarsa wajen saƙa tunani don isar da saƙo cikin rauji mai karsashi
ya ba shi damar watayawa cikin nishaɗi. Za a iya samun misalin ɗa mai tsauri a waƙar ‘Malam Alo na baraz zaki’ ta Alhaji Ali Marafa da ya ce:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Kura ba ta gasa da ɗan zaki,
Ajewa A2
: Azamarsu ba ta zama ɗai ba,
Sauka A3
: Don azamar su wane ‘yar gajera ta,
Saukar
Sauka A4 : Har yanzu ba ta yi tsawo ba,
Hawa B1
: Ko can da shirin hwaɗa Ali yat tasa,
Hauhawa B2
: Tun da ba a shira mai wuƙa ba,
Sauka B3
: Yanzu akwai wuƙa akwai mashi,
Saukar
Sauka B4 : Don an shirya mai makami,
Hawa C1
: Ko can dokin ƙwarai shi ka kama gudu,
Hauhawa C2
: Shi daɗe shina hamidanci,
Sauka C3
: Shi kuma dokin su wane sai biɗar tsaba,
Saukar
Sauka C4 : Tun ba a gwada mai ruwa ba,
Ɗ1 : Malam Alo na baraz zaki,
Ɗ2 : Jikan Kilo ɗan Marafa.
(Muhammad,
2012, sh. 159)
Sannan a waƙar ‘toya matsahwa baƙon
dole’ ta Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Salihu ɗan Umaru Shawai
(1945-1956). Wannan tana ɗaya daga cikin waƙoƙin da Maidaji ya ɗani (Gusau, 2015)
daga waƙoƙin yayansa Makaɗa Nadada. Makaɗa Nadada shi ne
makaɗin Sarki Salihu,
sai bayan rasuwar Sarki Salihu ne, Makaɗa Nadada ya koma harkar malanta, da ma yana da almajirai da
yakan koyar, sai ya bar waƙa. Sannan ne Makaɗa Maidaji ya zama
mawaƙin Masarautar Gobir ta Sabon Birni. Makaɗa Maidaji yana cewa cikin waƙar:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: An koma shiri na Ali na Gambai,
Hauhawa A2
: Motsin duniya ya tashi,
Sauka A3
: Sarki za shi tarben Gwamna,
Ajewa A4
: Ke mota je ki ɗauki Baba,
Saukar
Sauka A5 : Ki kai shi da lahiya don Allah,
Hawa B1
: Taron shawara ne yaz zo,
B2
: Mun yo rakkiya mun dawo,
Sauka B3
: An yit tambaya ba sarki,
Saukar
Sauka B4 : Ban san inda zai kwana ba,
Hawa C1
: Ni ban san inda zai kwana ba,
Hauhawa C2
: Ko birnin Kabbi ko Dutse,
Sauka C3
: Sarki bai tsaya dun nan ba,
Saukar
Sauka C4 : Amma
ya wuce sai Wurno,
Hawa D1
: In an kuma yin wani taro,
D2
: Ko ni mai kiɗi sai na zo,
Ajewa
D3 : Amma ban zuwa huntuna,
Sauka D4
: Sai an kuma ban wata riga,
Saukar
Sauka D5 : Sai
an kuma ban wani doki,
Ɗ1 : Toya
matsahwa baƙon dole,
Ɗ2 : Jikan
Sanda baban Yari.
(Muhammad,
2012, sh. 162)
A waƙar ‘na taho gai da babba gardaye’ wadda
Makaɗa Maidaji ya rera wa Alhaji Ɗansanda
Gangara, akwai inda yake cewa:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Na ishe tsamiya ta yi kyaun kunne,
Sauka A2
: Ga makiyaya da ko gittocinsu,
Ajewa A3
: Ga tumakinsu mai takin oda,
Saukar
Sauka A4 : Babu damar a sara sai dibi,
Hawa B1
: Ina manoman ga ‘yan takin oda,
Sauka B2
: Wanda ya iske gawo ya sare,
Saukar
Sauka B3 : Ya yi kashi ne da kainai ya tasa,
Hawa C1
: Ina makiyayan ga sun sukar mulki,
Sauka C2
: Wanda ya iske gawo ya sare
Saukar
Sauka C3 : Ya yi kashi da kainai ya tasa,
Hawa D1
: Shin ina Lawwali shi da Zaƙoli,
Ajewa D2
: Ku zo ku shaida wa babba gardaye,
Sauka D3
: Na taho in yi mai kukan yunwa,
Saukar
Sauka D4 : Yau gidajenmu ba sauran tsaba,
Ɗ1 : Na taho gai da babba gardaye,
Ɗ2 : Babba ɗan Inna mai gandun daji.
(Muhammad,
2012, sh. 161)
A waƙar ‘kai ab bahagon gulbi’ ta Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Muhammadu Bawa
(1975-2003) Makaɗa Maidaji Sabon Birni yana cewa:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: To, sai an yi kadankarma,
Sauka A2
: A san babba a san yaro,
Ajewa A3
: Kuma sai an yi karambatta,
Saukar
Sauka A4 : A san wane a san wane,
Hawa B1
: Ai ina da uba sulɗanin Gobir,
Hauhawa B2
: Wanda ka hisshe ni,
Sauka B3
: Ni ba ni gudun hitinar Gobir,
Saukar
Sauka B4 : Duw wada tat tashi,
Hawa C1
: Ai ga taronmu na Sakkwato,
Hauhawa C2
: Mun gama kaya ga hawan daba,
Sauka C3
: An shirya dawakayye,
Saukar
Sauka C4 : Amma babu kaman namu,
Hawa D1
: Doki ya hi dubu goma,
Hauhawa D2
: Raƙumi
ya hi dubu goma,
Sauka D3
: Duk an gamu an jera,
Saukar
Sauka D4 : Uban Shantali ya canye,
Ɗ1 : Kai ab bahagon gulbi,
Ɗ2 : Uban Shantali ɗan Mamman,
Ɗ3 : Ɗan Inna Kilo Sarki,
Ɗ4 : Uban Bunu da baraz zaki.
(Muhammad,
2012, sh. 160)
A waƙar ‘Sarkin Gandu ubangijin gutsun gawo’ wadda
aka rera wa Sarkin Gandu, Makaɗa Maidaji yana cewa:
Ma’ana Ƙirgar Ma’ana
Hawa A1
: Bara na iske masassaƙa suna ɗibar hwaru,
Hauhawa A2
: Su ko su ukku ne suna cajin hwaru,
Sauka A3
: Guda sai yac ce tsaya gabas ka yi saurare,
Ajewa A4
: Guda sai yac ce tsaya arewa ka yi saurare,
Saukar
Sauka A5 : Guda sai yac ce tsaya gabas ka yi saurare,
Hawa B1
: Tun ba su gama gardama ba ko sai ga Tsintau,
Sauka B3
: Su duka sun shirya shawara don su ɓace mai,
Saukar
Sauka B4 : Yac ce duk wanda yag gusa kau zai harbai,
Ɗ1 : Sarkin Gandu ubangijin gutsun gawo,
Ɗ2 : Iro mijin A’i gandu mai ɗakin Kande.
(Muhammad,
2012, sh. 160)
4.1 FAYYACE AWON BAKA NA RERAWA A WAƘOƘIN
MAKAƊA MAIDAJI
Rerawa
fitacciyar siga ce domin ana sadar da waƙar baka ne ta hanyar karin
murya cikin rauji. Makaɗa Maidaji na ɗaya daga cikin makaɗa da mawaƙan baka na Hausa masu rera waƙa a cikin ƙungiya
waɗanda ake yi wa ƙulli
da ƙari.
A wannan ƙungiya, Makaɗa Maidaji shi ne shugabanta, wato jagora, sannan yana da ‘yan
amshi. Yawanci yakan rera ɗa ɗaya ko biyu ko fiye da haka gwargwadon yadda ya tsara a waƙarsa
sannan masu yi masa amshi su furta sauran saɗaru. Wani abin tambaya game da wannan batu, yaya manazarta da
masana adabin Hausa suke kallon tsarin rerewa a waƙar
baka? Gusau (2003a) yana da ra’ayin rerawa wata “hanya ce wadda ake
furta kalmomi cikin jimloli da aka shirya a yanayi na waƙa
domin a isar da wasu saƙonni ga jama’a. Rerawa ke nan ta shafi furuci da fatar baki
inda ake fitar da ƙwayoyin sauti ta amfani da harshen da ake magana da shi cikin
rauji da ya shafi yanayin hawa da saukar murya ko faɗuwarta mai ma’ana” (Gusau,
2002, sh. 42). Waɗannan dabaru a matanin waƙoƙin
Makaɗa Maidaji Sabon Birni sun haɗa da:
4.1.1 AWON RERAWAR ƘULLI
Ƙulli dai shi ne fara furta ƙaramin
saƙo a ɗa daga bakin jagora ko da na
ƙungiya
ne ko kuma na kaɗaita ne. Ƙulli “wuri ne inda ake fara furta ƙaramin
saƙo a ɗan waƙa
wanda yakan ƙunshi saɗara ɗaya ko biyu ko ma fiye da haka” (Gusau, 2003a, sh.
38). Makaɗan kaɗaita idan suka fara ƙulla
waƙa,
babu mai yi masu karɓi, babu mai yi masu ƙari, sannan babu masu yi
masu tarbe, su da kansu suke yi wa waƙoƙinsu
takidi.Makaɗa Maidaji
na da wata alkintacciyar sifa dangane da yadda yake fara ƙulla
waƙarsa.
Mafi akasari, Makaɗa Maidaji, yakan fara ƙulla waƙarsa
ne da rera gindin waƙa, inda a mafi akasarin lokuta, yakan rera layin farko zuwa
na biyu ne na ɗa a gindin
waƙa
sannan masu yi masa amshi su ƙarasa sauran za a iya tabbatar da haka idan aka saurari ‘waƙar ‘kai ab bahagon gulbi’ da ta ‘Jikan Jari ginshiƙi’ da ta‘gagari gaba na
Salihu’da dai sauransu. Sannan, a wasu daga cikin waƙoƙinsa,
sukan zamanto ya fara ƙulla ɗa wanda ba shi ne gindin waƙarsa ba. Misali a waƙar ‘na Ali ɗan Bajini’ ta Sarkin
Gobir Alhaji Umaru Salihu (1957-1966), Makaɗa Maidaji ya fara ƙullin da:
Ƙulli : Na Ali ɗan Bajini,
:
Jikan Shekara ka gama lahiya,
:
Shi Nadabo ƙanin Buzuwa,
:
Sarki uban Shamaki ɗan
Kasau.
(Muhammad,
2012, sh. 165)
Sannan a
wata rerawa ta waƙar ‘Uban Na’Allah uban
Madauci’,ta Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris (1975-), Makaɗa Maidaji ya nuna fasaharsa
da balagarsa ta juya saƙonninsa cikin harshe mai zalaƙa da karsashi. Wato, yawanci
ɗiyan waƙoƙinsa
ba su dogara da junansu ba. Yakan iya ɗauko ɗa na farko ya kai tsakiya ko ƙarshe. Makaɗa Maidaji ya fara ƙulla
waƙar
ne ta hanyar rera saɗaru uku sannan masu yi masa amshi su karɓa masa da rera gindin waƙar:
Ƙulli : Alhaji
Mani ba shi ƙin kowa,
: Komi kac ce yanai
ma,
: Shehu bai iya
za’ida ba,
: Uban Na Allah uban Madauci,
: Shehu sannu da yau da gobe.
(Muhammad,
2012, sh. 167)
A waƙar ‘ya tara dame mai dama’ ta Alhaji Ɗanbawa,
Makaɗa Maidaji Sabon Birni ya
fara ne da ƙulli kamar haka:
Ƙulli : Ɗan Bawa Magajin Jimro,
: Na Badiga jikan Mana,
: Kai munka
sani gun ƙwazo,
: Ya tara
dame mai dama,
: Ɗan
Bawa ƙanen
mai gona.
(Muhammad,
2012, sh. 167)
4.1.2 AWON RERAWAR ƘARI
Ƙari na nufin ƙarasa
furta ƙaramin
saƙo a ɗa (‘Yan Amshi/ Kaɗaita), wato wuri ne inda
yakan ƙunshi
tarbe ko rakiya da gindin waƙa (Gusau, 2003a, sh. 3). Masu yi ma Makaɗa Maidaji amshi yawanci
sukan yi masa ƙari a waƙoƙinsa yayin da ya fara ƙulla waƙa.
Bari mu kalli waƙar ‘na yi mamakin
harkatai’ ta tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Alhaji Shehu
Aliyu Shagari, Makaɗa Maidaji da yaransa sun tsara waƙar
ne kamar haka:
Ƙulli : Shugaban ƙasa Allah kyauta mai,
Ƙari : Zaman
mutane na murna tai,
Gindin waƙa : Na
yi mamakin harkatai,
: Shehu mai daraja
Shagari.
(Muhammad,
2012, sh. 168)
Sannan a waƙar ‘ka buwayi maza sai na zo’ ta Garkuwan
Dutsi, Innar Gobir, Makaɗa Maidaji ya kawo wannan ɗan waƙar ne kamar haka:
Ƙulli : Kai nis sani ƙasas
Sabon Birni,
Ƙari : Tun da kai ka wa ‘ya’yana toshi,
Gindin waƙa : Ka buwayi maza sai na,
: Mu gai da Garkuwa na ɗan Gardaye.
(Muhammad,
2012, sh. 168)
Idan aka
kalli waƙar ‘Uban Makama uban Gardaye’ ta Sarkin
Gobir na Sabon Birni, Alhaji Muhammadu Bawa (1975-2003), Makaɗa Maidaji ya kawo wannan ɗa ne da:
Ƙulli
: Ina mazan suke?
Ƙari
: Sarkin Gobir ina mazan suke duk sun ƙare,
Gindin Waƙa : Uban Makama uban Gardaye,
: Bawa sannu da kwanan yaƙi.
(Muhammad,
2012, sh. 169)
4.1.3 AWON RERAWAR TARBE
Furuci ne
da ake tarbo abin da aka furta a ƙulli (‘Yan Amshi kawai),
wuri ne inda ‘yan amshi suke ƙarasa ma’ana ƙarama wadda jagora ya faro ta a ɓangarensa na ƙulli.
Ana yin wannan dabara ta tarbe a waƙoƙi waɗanda ake rerawa “ta hanyar
jagora da ‘yan amshinsa, amma ban da a waƙoƙi waɗanda makaɗi ba shi da ‘yan karɓi” (Gusau, 2014, sh. 38). A
waƙar ‘namijin daga uban Gardaye’ ta Sarkin
Gabas na Gwaranyo, Alhaji Umaru, Makaɗa Maidaji da yaransa sun kawo wannan ɗan waƙa ne
kamar haka:
Ƙulli : Ina ƙaunar
mai kama maciji,
Ƙari : In dai bai shaƙu da
ni ba,
Tarbe : Bari in kwanan mutum sun ƙare shi za ya kausai,
Gindin Waƙa :
Namijin daga uban Gardaye,
: Sarkin Gwaranyo.
(Muhammad,
2012, sh. 170)
Idan aka
kalli waƙar ‘Allah za ni roƙonka’ ta tsohon Gwaman Jihar Sakkwato, Alhaji Garba Nadama wanda
ya yi shugabanci jihar Sakkwato tsakanin shekarar (1981-1983) za a iya fitar da
wannan batu ta yadda Makaɗa Maidaji da yaransa suka tsara waƙar
kamar haka:
Ƙulli : Ko can duniya haka tag gada inji mai
tulu,
Ƙari : Ka san duniya daɗa,
Tarbe : Ba mai hurce
iyakatai,
Gindin Waƙa : Allah za ni roƙonka,
: In yi biyag gwamna mai girma.
(Muhammad,
2012, sh. 170)
Har wa yau,
a waƙar ‘dogo ɗan Abubakar na Malumfashi’ ta
Alhaji Abubakar Malumfashi, Makaɗa Maidaji cewa ya yi:
Ƙulli : Gidan Mamman nit taho kiɗi sai na gaisai,
Ƙari : Sai ga Audu ɗan Bala ga Musa
nan,
Tarbe : Komi nib biɗa ga yau sai an yo
min,
Gindin Waƙa : Dogo ɗan Abubakar na Malumfashi,
: Jikan Dabo ɗan Kilo Gwamron giwa.
(Muhammad,
2012, sh. 170)
Sannan a waƙar ‘harka da ilmi mukai’ ta Makaɗa Maidaji wadda ya yi don
nuna muhimmancin ilmi a tsakanin al’umma cewa ya yi:
Ƙulli : In dai mutum yaɓ ɓace,
: Maisai ga hanya mu kai,
Ƙari : In ko mutum yaƙ ƙiya,
Tarbe : Mu iza shi
bayan gida,
Gindin Waƙa : Harka da ilmi mu kai,
: Allah ya gyara mana,
: Mu gama da ban-gaskiya.
(Muhammad,
2012, sh. 171)
4.1.4 AWON RERAWAR RAKIYA/ KARƁEƁƁENIYA
Rakiya ko
karɓeɓɓeniya na nufin maimaita ƙari
da ‘yan amshi sukeyi wa jagora, wato wuri ne inda ‘yan amshi suke maimaita ƙarin
da suka yi wa jagora daga lokaci zuwa wani ɗan lokaci. Domin ita ma karɓeɓɓeniya furucin ƙari ne da nufin yi wa jagora
rakiya. Tarbe da rakiya da karɓeɓɓeniya duk ana yin su ne a waƙoƙin
da ake “rerawa ta hanyar ƙulli da ƙari daga jagora da ‘yan amshi” (Gusau, 2003, sh. 39; 2014,
sh. 19).Ke nan, idan aka kalli fasalin waƙoƙin
Makaɗa Maidaji, yakan yi amfani
da tsarin karɓeɓɓeniya cikin nishaɗi da walwala. Yakan nuna
fasaharsa ta naƙaltar kalmomi ta hanyar nuna godiya ko alhini ko tarihi da
sauran hanyoyin da suke ginshiƙan rayuwa.
Haka
zalika, idan an waiwayi wasu daga cikin waƙoƙinsa,
Makaɗa Maidaji kan aiwatar da karɓeɓɓeniya a taƙaice
domin faɗakarwa tare da fito da
nasabar wanda yake yi wa waƙa kamar a waƙar ‘ga ni na zaka murna
gare ka sarki gwarzo’ ta Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Muhammadu Bawa
(1975-2003).Domin fayyacewa, ga misali daga waƙar ‘kai ab bahagon gulbi’ ta Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji
Muhammadu Bawa (1975-2003), Makaɗa Maidaji ya fito da wannan tsari:
Ƙulli : Kai aj Jari da
Shawai,
Ƙari
: Alhaji kai a Ibrahima,
: Kai ne Mainasarar
mashi,
Tarbe : Ina wanda ka
tambaba,
Ƙulli
: Gohe ya buga tamburra,
Ƙari
: Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Gauɗe ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Tambai ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Yakuba ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Ibrahim ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Balarabe ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Jadi ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Jari Kada ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Shawai ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Salihu ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi.
Ƙulli
: Ummaru ya buga tamburra,
Karɓeɓɓeniya : Dum mun ji su ga tarihi,
Ƙulli
: ‘Yan Gatawa da Yakubawa,
Ƙari
: Kowane an sa shi ga tarihi,
: Haba sarki riƙe tarihin ga,
Tarbe : Da kowa ka biɗa jiddun,
Takidi + Ƙulli : Haba sarki riƙe tarihin ga,
: Da kowa ka biɗa jiddun,
Ƙari
: Kai kag gane mahwarinai,
Tarbe :Kuma ka san
wada yak ƙare,
Gindin Waƙa : Kai ab bahagon
gulbi,
: Uban Shantali ɗan Mamman,
: Ɗan'inna Kilo sarki,
: Uban Bunu da Baraz
Zaki.
(Muhammad,
2012, sh. 172)
Haka abun
yake idan idan aka kalli sauran nau’o’in waƙoƙin
Makaɗa Maidaji kamar waƙar ‘gaskiya da roƙon
Allah ba ka fasawa’da waƙar‘Uban na Allah uban Madauci’duk waɗanda ya rerawa Sarkin
Zazzau, Alhaji Shehu Idris (1975-).Har wa yau, za a iya kallon wani misali daga
waƙar ‘Iro na Bawa baƙon
dole’ wadda Makaɗa Maidaji yaiɗani daga Makaɗa Nadada ta Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Salihu Shawai
(1945-1956) inda ya kawo tsarin karɓeɓɓeniya ta:
Ƙulli : Ai koma shiri Magajin Mani,
Ƙari : Kogin duniya ya tashi.
Takidi
+ Ƙulli
: Haba koma shiri Magajin Mani,
Ƙari : Kogin duniya ya tashi.
Takidi
+ Ƙulli
: Kai dai koma shiri Magajin Mani,
Ƙari : Kogin duniya ya tashi.
Ƙulli : Ko wacce akwai dole Gobir,
Ƙari : Jagoran hwaɗa ya tashi.
Ƙulli : Jari da yai irin nashi ya yi,
Ƙari : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Almu da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Gohe da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Maso ɗan Danga da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Ko Baciri da yai irin nashi ya
yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Sobe da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Mayaƙi
da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Jangwarzo da yai irin nashi ya
yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Ɗangwamci
da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Ɗan
mai Jadi da yai irin nashi ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Ko Jari Kada da yai irin nashi
ya yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Ko Ummaru da yai irin nashi ya
yi,
Karɓeɓɓeniya : Bai ɗau shawarak kowa ba.
Ƙulli : Kai ba ka jan wani sarki,
Karɓeɓɓeniya : Tsoro ba ya jan wani kaɗo.
Takidi
+ Ƙulli
: Salihu ba ya jan wani sarki,
Karɓeɓɓeniya : Tsoro ba ya jan wani kaɗo.
Ƙulli : Kai ka ɗauki ragamar musulmi,
Ƙari : Wannan ba a hana ka na Malam,
Gindin
Waƙa
: Iro na Bawa baƙon dole,
:
Jikan na Sanda baban Yari.
(Muhammad,
2012, sh. 175)
4.1.5 AWON RERAWAR TAKIDI A WAƘOƘIN MAKAƊA MAIDAJI
Takidi
“tsari ne karɓaɓɓe a rera waƙoƙin
baka na Hausa, ta hanyar takidi makaɗi yake maimaita rera wani zubi na ɗa a waƙa”
(Gusau, 2003, sh. 44). Har wa yau, akwai nau’in takidi wanda ‘yan amshi suke yi
wa jagora rakiya wanda ake kira da ‘Takidin Karɓeɓɓeniya’. Ban da wannan kuma akwai takidi na ‘Bayayyeniya’ inda
‘yan amshi suke rera duk abin da jagora ya furta a layi-layi na ɗiyan waƙa.
Duk da yake:
Takidi ya
saɓa wa dokar furuci ko rubutu
na yau da kullum, makaɗa sukan yi takidi a layukan farko ko na tsakiya ko na ƙarshe
na ɗa a waƙar
baka. Wani lokaci akan yi takidi a rabin saɗara, kuma ana yi wa dukkan ɗa a waƙar baka takidi (Gusau, 2002, sh. 47).
Haka
zalika, idan aka kalli waƙar ‘kak ka ɗau reni’ wadda Makaɗa Maidaji ya rera wa Sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji
Ibrahim (1970-1975) a cikin waƙarya yi amfani da takidi ta sigar fito da tsarin rerawa ta
amfani da kalmomi a maimaice. Ga misali kamar haka:
Ƙulli : Zamanin akwai manya,
Ƙari : Tsuntsu ko da yaushe ba ya gudun Ɗantsara,
Taikidi
+ Ƙulli
: Zamanin akwai Jadi,
Ƙari : Jadi ko da yaushe ba ya gudun Ɗantsara,
Taikidi
+ Ƙulli
: Zamanin akwai manya,
Ƙari : Ai Kakanku bai yi ƙyamar
kakana ba.
Ƙulli : Mamman na gode,
Ƙari : Don albarkacin Durumbu magajin
Shawai.
Taikidi
+ Ƙulli
: Mamman na gode,
Ƙari : Allah dai ya ƙara
imani yai komi,
Taikidi
+ Ƙulli
: Dango na gode,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Allah dai ya ƙara imani yai komi,
Ƙulli : Dango ɗan Galadima,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Allah dai ya ƙara imani yai komi,
Ƙulli : Salihu Marahwa na gode,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Allah dai ya ƙara imani yai komi,
Taikidi
+ Ƙulli
: Garba na gode,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Allah dai ya ƙara imani yai komi,
Taikidi
+ Ƙulli
: Malam Garba na gode,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Allah dai ya ƙara imani yai komi.
Gindin
Waƙa
: Kak ka ɗau
reni,
:
Ɗandango
Durumbu ɗan Inna ɗan Shawai.
(Muhammad,
2012, sh. 187)
Duba da
haka, Makaɗa Maidaji
yana da wata alkintacciyar sifa wadda yake amfani da ita wajen rera waƙoƙinsa
ta hanyar amfani da takidi. Makaɗa Maidaji yana amfani da takidi a saɗarun farko ko na tsakiya ko
kuma a saɗarar ƙarshe.
Wani lokaci, Makaɗa Maidaji yakan yi takidi a rabin saɗara, kuma ya yi wa dukkan ɗa a waƙarsa
takidi. A waƙar Makaɗa Maidaji ta ‘harka da
ilmi mukai’ wadda ya rera domin tunatarwa tare da faɗakar da al’umma bisa
muhimmancin ilmi cewa ya yi:
Ƙulli : Tun dak Kaduna haz Zariya had da
manyan Kano,
Ƙari : Komi mutum za shi yi ya gama da ‘yan
Sakkwato,
Takidi + Ƙulli : Lalle
dak Kaduna haz Zariya had da manyan Kano,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari : Komi
mutum za shi yi ya gama da ‘yan Sakkwato,
Gindin Waƙa : Harka da ilmi mukai,
: Allah ya gyara mana,
: Mu gama da
ban-gaskiya.
(Muhammad,
2012, sh. 184)
Har wa yau
a cikin waƙar Sarkin Tashar motar garin Sabon Birni, Alhaji Idi ɗan Argiji ta ‘Ya kwan yana aikin mota’ Makaɗa Maidaji ya rera wannan waƙa ne
ta amfani da tsarin rerawar takidi a saɗarun tsakiya na ɗan waƙa kamar haka:
Ƙulli : Ga ni ina shirin tahiya Zazzau,
: Kuma ga ni ba ‘yan kuɗɗi,
Takidi : Ina nuhin
tahiya Zazzau,
: Kuma ga ni ba ‘yan
kuɗɗi,
: Ina dibin mota ni ko suna kallo na,
Takidi : ‘Yan
kamishon suna dibin mota,
: Ni ko suna kallo
na,
: Don sun gane ni da taron,
: Yara zay yawa bayana,
: Har an yi jinga na tada,
: Ba zan biyan kuɗɗi ba,
Gindin Waƙa + Ƙari : Ya kwan yana aikin mota,
: Ɗan Argiji ɗan Shawai,
: Sarkin tasha jikan Idi,
: Jikan fulanin Ɓaure.
(Muhammad,
2012, sh. 185)
A waƙar ‘Ɗangara
jikan ɗan Lahiya” wadda ya rera wa Sarkin Maraɗi Ɗangara, Alhaji Bala ɗan Sani, Makaɗa Maidaji ya kawo fasalin takidi ne wanda makaɗa da mawaƙa
suke aiwatarwa a farkon saɗara da nau’in fasalin takidi a rabin saɗara inda yake bayyana:
Ƙulli : Ɗangara kai as sinadari,
Ƙari : Ko da ɗai abin kallo, kallo nai
akai,
Takidi + Ƙulli
: Ɗangara kai am muzakkari,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Ko da ɗai abin kallo, kallonai
akai,
Gindin Waƙa : Ɗangara
jikan ɗan lahiya,
: Bala ɗan Sani gaisai mu kai.
Ƙulli : Na Alhajiya Gwamma,
Ƙari : Wanga zamani ku am
manyan duniya,
Takidi + Ƙulli
: Ƙanin Hajiya Gwamma,
Karɓeɓɓeniya + Ƙari
: Wanga zamani ku am manyan duniya,
Gindin Waƙa : Ɗangara
jikan ɗan lahiya,
: Bala ɗan Sani gaisai mu kai.
(Muhammad,
2012, sh. 185)
5.0 KAMMALAWA
Wannan
bincike yanazarciawo a matanin waƙoƙin
Makaɗa Maidaji ne ta amfani da
ra’in WBB wajen fito da hanyoyi ko dabarun da yake amfani da su yayin rera waƙoƙinsa.
Kamar yadda wannan bincike ya gano, yana amfani da sigar + Jagora +‘Y/Amshi+Ƙulli+Ƙari+Tarbe+/-Rakiya/Karɓaɓɓeniya+Takidi+Gindin Waƙa+Rauji.
Manufar a nan ita ce shi ne yake fara ƙulla waƙarsa
a matsayinsa na jagora, sannan ‘yan amshi su karɓa suna yi masa ƙari. A wani ɗan waƙar
kuma, ‘yan amshi za su iya yi masa tarbe, inda a wani ƙaulin
suna haɗawa da rakiya ko karɓeɓeniya a tsakaninsu da
jagora, daga bisani sai su rufe rerawar da gindin waƙa. A
haɗe kuma cikin waƙar
suna amfani ne da sauti na kiɗan gangar taushi. Sannan, takardar ta fito da awon ɗiya a waƙoƙin
Makaɗa Maidaji inda aka bayyana
yakan yi amfani da awon ɗa mai sauƙi ko awon ɗa mai tsauri wajen isar da saƙonni ko manufofi a cikin waƙoƙinsa.
Har wa yau, yakan yi amfani da tsarin hawa+hauhawa+ajewa+sauka+saukar-sauka yayin tsara zaren
tunaninsa. Daga bisani, wannan binciken ya fahimci lallai Makaɗa Maidaji a matsayinsa na
jagoran ƙungiyarsa,
shi ne yake da ikon juya rerawa daga wata waƙar zuwa ga wata. Sannan idan
aka ji Makaɗa Maidaji
yana ta rera ko maimaita gindin waƙa, to, waƙar
ke nan ta ƙare zai juya zuwa ga wata. Duk da a wasu lokuta kuma, ‘yan
amshinsa ne suke ɗaukar wannan nauyi na maimaita gindin waƙa
sau biyu zuwa uku, daga nan kuma Makaɗa Maidaji yakan ɗora waƙar da yake tunanin ita za su rerawa. Binciken ke nan yana ƙara
tabbatar da tagomashin karɓuwar waƙoƙin baka na Hausa musamman saboda zalaƙar
harshe tare da fasihancin da matanin waƙoƙin
ke tattare da su. Tabbas, duba da waɗannan hujjoji, ta amfani da ra’in WBB wannan bincike ya kafa
hujja tare da ƙalailaice awon baka a waƙoƙin
Makaɗa Maidaji. Hakan yai daidai
da faɗar Hausawa da suke faɗar da na gaba akan gane
zurfin ruwa, dalili kuwa shi ne, dangane da awon baka a waƙoƙin
baka na Hausa, ra’in WBB na kallonsa a matsayin alkintacciyar sifar rerawa a
bakin makaɗa.Domin
haka, binciken ya gano Makaɗa Maidaji kan yi amfani da tsarin rerawa inda wani lokaci
akan yi takidi a dukkan ɗa na waƙa. Har wa yau, wannan nau’in takidi ne wanda ‘yan amshi suke
yi wa jagora rakiya wanda ra’in WBB ke kira da ‘takidin karɓeɓɓeniya’. Wannan na ɗaya daga cikin abin sha’awar
da ke bayyana zalaƙa tare da balagar Makaɗa Maidaji dangane da iya wasa da harshe, sannan da saƙa
zancensa cikin hikima ta amfani azanci da suka danganci habaici ko kirari ko
yabo ko zuga. Sannan yakan yi amfani da sigar awon baka a rerawarsa wajen
kinayar sakaya zance kamar isar da godiya tare da bayyana tarihi ko kuma sifar
wasa da harshe kamar ƙarangiya da dai sauran nau’in salon magana.
MANAZARTA
Abba, M.
& Zulyyadaini, B. (2000). Nazari kan
waƙar baka ta Hausa. Zaria:
Gaskiya Corporation Limited Publishing.
Abdulƙadir,
Ɗ.
(1975). The role of an oral singer in Hausa/Fulani society: A case study of
Mamman Shata. Kundin digiri na uku. Bloomington, U.S.A: Indiana University.
Abdulƙadir,
Ɗ.
(1981). Oral composition: A historical appraisal. A cikin U.N. Abalogu, G.
Ashiwaju, & M.R. Amadi-Tshiwala (Eds.), Oral
Poetry in Nigeria(18-36). Lagos:
Emaconprint Limited Publishing.
Burgess,
J.W. (1964). English literature.
London: Longmans, Green & Company Limited.
Burton,
S.H. (1954). The criticisms of poetry.
London: Longman Publishers.
Dorson,
R.A. (1972). Folklore and folklife: An
introdution. Chicago:U.S.A.
Dunfawa,
A.A. (2003). Ma’aunin waƙa. Sokoto: Garkuwa Publishers.
Finnegan,
R. (2012). Oralliterature in Africa.
London: Oɗford University
Press.
Gray, B.
(1975). The phenomenon of literature. Netherlands: Mouton & Co. N.Ɓ. Publishers.
Gusau, S.M.
(2001). Waƙar gogarman tudu ta Ibrahim Narambaɗa a mazubin nazari. Algaita: Journal of Current Research in
Hausa Studies, 1(1), 73-101.
Gusau, S.M.
(2003a). Jagoran nazarin waƙar
baka ta Hausa. Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S.M.
(2003b). Waƙar Sa Sanusi Sarkin Yaƙi a mazubin nazari. FAIS Journal of Humanities, 2(4),
182-208.
Gusau, S.M.
(2008). Dabarun nazarin adabin Hausa.
Kano: Benchmark Publishers.
Gusau, S.M.
(2011). Adabin Hausa a sauƙaƙe. Kano: Century Research Publishers.
Gusau, S.M. (2014). Waƙar baka Bahaushiya: The Hausa oral song. Kano: Bayero University Kano Professorial
Lecture Series No. 14.
King, A.Ɓ.
(1967). Music at the court of Katsina. Kundin Digiri na uku. London: SOAS University.
King, A.Ɓ.
(1981). Form and functions in Hausa professional songs.A cikin U.N. Abalogu, G.
Ashiwaju, & M.R. Amadi-Tshiwala (Eds.), Oral
Poetry in Nigeria(118-138).
Lagos: Emaconprint Limited Publishing.
King, A.Ɓ.
(1986). Statement, restatement and eɗtension: Stanzaic structure in Hausa court songs. Department
of African Language and Culture. Zaria: Ahmadu Bello University.
Muhammad,
A.S. (2012). Nazarin ayyukan Makaɗa Sa’idu Maidaji Sabon Birni 1938-2000. Kundin digiri na
biyu. Sashen Harsuna da Al’adun Afirka. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.
Muhammad, Ɗ.
(1978). Waƙa Bahaushiya. Studies
in Hausa Language and LiteratureI: The First International Hausa Conference
(47-62). Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Muhammad, Ɗ.
(1981). Bakandamiya: Towards a characterization of the poetic masterpiece in
Hausa. A cikin U.N. Abalogu, G. Ashiwaju, & M.R. Amadi-Tshiwala (Eds.), Oral Poetry in Nigeria(57-70). Lagos: Emaconprint Limited Publishing.
Olatunji,
O.O. (2005). Features of Yoruba oral
poetry. Ibadan: University Press.
Richards,
I.A. (1976). Principles of literary
criticism. London: Routledge & Keegan Paul.
Satatima,
I.G. (2009). Waƙoƙin baka na ɗarsashin zuciya: Yanaye-yanayensu da sigoginsu. Kundin digiri
na uku. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano: Jami’ar Bayero.
Schuh, R.G. (2002). Karin waƙoƙin aure na Ɗanmaraya
Jos. A cikin Hausa Language, Literature
and Culture: The Fifth Hausa International Conference (154-164). Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero.
[1]Bisa
tsarin bincike, tarihin Makaɗa Maidaji yanuna
shahararsa wajen rera waƙoƙin baka na Hausa, kuma ya rayu daga shekarar 1938-2000. An
haife shi ne a ƙasar Gobir, a
garin Tara da ke a ƙauyen Rambaɗawa
na ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar
Sakkwato (Muhammad, 2012). Kafin rasuwarsa, Makaɗa
Maidaji manomi ne kuma malamin Makarantar Allo ne. Allah ya azurta shi da
iyalai; matan aure guda uku (3) da kuma ‘ya’ya takwas (8). Bisa fasalin waƙoƙinsa, Makaɗa
Maidaji yana ɓangaren makaɗan ƙungiya ne, sannan akasarin ‘yan ƙungiyarsa jininsa ne daga ‘ya’yansa na cikinsa, sai babban
wansa, sai kuwa ƙannen mahaifinsa.
Mahaifinsa bai yi nisa a harkar waƙa
ba, amma ɗaya yayan nasa, wato Alhaji Musa Nadada ya yi waƙa (Muhammad, 2012).

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.