Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihi Da Manufar Shirin Majigin ‘Kasarmu Ce’

Citation: Aliyu Isa Sulaiman (2017). Tarihi Da Manufar Shirin Majigin ‘Ƙasarmu Ce’. Yobe Journal of Language, Literature and Culture (YOJOLLAC), Vol. 5. Department of African Languages and Linguistics, Yobe State University, Damaturu, Nigeria. ISSN 2449-0660

TARIHI DA MANUFAR SHIRIN MAJIGIN ‘ƘASARMU CE

Na

Aliyu Isa Sulaiman (PhD)

Abstract

Psychologist have argued over a period of time that, people comprehend faster and much easier with what they saw rather than with what they read or heard. This fact make planners, Psychologist and Government official to set certain principles with which minds of a citizen are geared towards or if possible to act on the desired direction set upon by such people. Colonial films in Africa are clear examples. This agenda setting is achieved through media outlets; some of these media tends to focus on certain issues thereby neglecting other issues. In doing so set the agenda and shape what people will consider in making social and political decisions. The media do not tell people what to think but rather what to think about, Berger, (1995). Agender Setting Theory was used in this paper to examined critically a Hausa celluloid film ‘Kasarmu Ce’ to affirm that this film have been used as a vehicle for national consciousness, establishment of morality and value orientations.

GABATARWA

Sanannen abu ne tun kafin bayyanar wasannin kwaikwayo na talabijin Bahaushe yake da wasannin kwaikwayonsa na gargajiya waɗanda ya gada daga kaka da kakanni. Wasan Kwaikwayon talabijin kuwa, wata kafa ce wadda ta ƙara haɓɓaka wasan kwaikwayon Hausa. Waɗannan kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnati ne saboda haka ba abu ne mai wuya ba idan an iske tsare-tsaren da gwamnati take son al’umma su gani. Ko da aka samu gidajen talabijin masu zaman kansu, duk da haka ana iya cewa tsare-tsaren na kare ra’ayin mahukunta ne kurum. (Ewu, 1986 Sh. 27).

Ba ga wannan abin ya tsaya ba, wasu ma gani suke ko kafin a sami ‘yancin kai an samar da wasannin Majigi waɗanda suke ƙarfafa manufofi na ‘yan mulkin mallaka, Chamo, (2005) da Abbas, (2008) da Inuwa, (2009). Wasannin Majigi da aka samar tun lokacin mulkin mallaka wasannin ne da suke ɗauke da tsare-tsare don ƙarfafa wasu manufofin ‘yan mulkin mallaka. Majigi irin su Baban Larai da Ɗan Arewa a London da Musa ya zo Birni duk shirye-shirye ne da aka yi da wata manufa ta musamman. Hatta kamfanoni irin na Taba Sigari da Bankuna suna haɗa hannu wajen shirya wasannin kwaikwayo domin ya dace da muradunsu. Shin wannan na nufin mutane ba su da zaɓi kan shirye-shiryen da ake nunawa a gidajen talabijin musamman ta ɓangaren wasannin kwaikwayo? Wani hanzari ba gudu ba, waɗannan kafafen yaɗa labarai na iƙrarin cewa duk shirye-shiryensu don jama’a suke yi, domin su faɗakar da ilmantarwa da kuma nishaɗantarwa. Wannan manufa ita ke jagorancin duk wasu shirye-shirye na gidajen yaɗa labarai ko da kuwa akwai wata ɓoyayyar manufa da gwamnati take ƙoƙarin isar wa ga al’umma. Wannan shi ya kawo mu ga ra’in ‘Tsararriyar Manufa’ wato (Agenda-setting Theory) wanda ke nuna mahukunta na tsare-tsare a kafafen yaɗa labarai domin su cimma wata manufa ta musamman. Don haka ana ganin akwai abubuwa da yawa waɗanda jama’a za su amfana musamman idan hukuma za ta tsara aiwatar da manufofinta ta hanyar wasan kwaikwayon talabijin ko Majigi. An ga haka a wani tsohon wasan kwaikwayon majigi/talabijin da aka shirya mai suna Ƙasarmu Ce’.

Wannan maƙala na ƙoƙarin duba manufofin gwannatin Nijeriya musamman waɗanda gwamnatin tarayya ta bayyana wajen ƙwace gidajen talabijin na shiyoyi domin mai da su ƙarƙashinta a 1977, da kuma manufofin gwannati kan wasannin kwaikwayo na talabijin, kana a kwatanta da wasan ‘Ƙasarmu Ce’ domin fito da su ƙuru-ƙuru.

2.0 WAIWAYE KAN WASAN KWAIKWAYON MAJIGI

Shi wasan kwaikwayo ba ƙaramin mahimmaci gare shi ba ga al’ummar Hausawa. Ana aiwatar da wasan kwaikwayo ne don a ilmantar ko a faɗakar ko a nishaɗantar da al’umma. Wannan faɗakarwa da ilmantarwa ana yin su ne ta hanyoyi da dama da suka shafi al’amurran Hausawa. Waɗannan hanyoyi sun haɗa da ta al’amurran zamantakewa tsakaninsu da juna ko da wasu baƙin al’adu. Wannan ne ma ya sa manazarta da dama suka yi rubuce-rubuce don fiddo da fa’idojin wasan kwaikwayo ga al’umma. Rubuce-rubucen da suka shafi wasannin majigi ko na talabijin sun haɗa da:

Ewu (1986, sh. 90) wadda ta nuna ana amfani da wasan ‘Tambari’ don wayar da kai farfagandar hukuma. A yayin da Ewu ke wannan hangen, a Abdullahi, (2002, sh. 32-64) kuwa, ya faɗi maƙasudin kafa gidan Talabijin na S.T.Ɓ. 67 a 1980 shi ne siyasa. Shi ma Bunza (2008) ya nuna ana tsara wasannin Majigi ko na gidan talabijin domin kwatanta halayyar rayuwar al’umma cikin wasa domin bayyana waɗansu matsalolin da ke tattare da rayuwa. Waɗannan kaɗan daga cikin nazarce-nazarcen da aka yi ne kan wasannin kwaikwayon majigi/talabijin. Don haka abin da ya kamata a duba shi ne manufofin gwamnati kan wasannin kwaikwayo, sa’annan a auna a ga ko wasu wasannin sun cimma manufofin shirya su?

3.0 MANUFOFIN GWAMNATIN TARAYYA GA SHIRYE-SHIRYEN TALABIJIN.

A shekara ta 1975 lokacin da aka ƙara yawan Jihohin ƙasar nan zuwa goma sha tara gwamnatin tarayya ta karaya da cewa yawan gidajen Talabijin na iya ƙaruwa, kuma cin gashin kan da suke da su da kuma alamomi na rarrabuwar kawuna kan kishi na yankuna na iya ƙaruwa, sai gwamnatin tarayya ta yanke shawarar karɓa da mallakar duk wasu gidajen Talabijin a wannan lokaci.

Dokar soja mai lamba 24 ta 1977 wadda ta fara aiki tun ɗaya ga watan Afirilu 1976 ta mallaka duk wani gidan talabijin a ƙarƙashin majalisar mulkin soja ta ƙasa. Wannan doka ita ta kafa gidan Talabijin mallakar gwamnatin Tarayya mai suna (Nigerian Teleɓision Authority ‘N.T.A.’). An ba ta alhakin yaɗa shirye-shirye ba tare da nuna bambancin son kai ko yankuna ba.

Egbon, (1982:27) ya bayyana dalilan da gwamnatin tarayya ta bayar wajen karɓe waɗannan gidajen Talabijin kamar haka:

a. Ta aikata ko cika duk wani abu wanda ya shafi ƙasa baki ɗaya, ba kawai abubuwan siyasa ko wani ɓangare na ƙasa ba.

b. Don ta nuna ƙarara a kan gudanarwa da manufofi masu yawa da bambancin al’umma da ƙasa ta ke da shi, duk da wannan bambance –bambancen ƙasa na da haɗin kai.

c. Don ‘yan ƙasa su amfana da kyawawan al’adun da ke ko’ ina a cikin ƙasar ta hanyar nuna su a gargajiyance.

d. Don taimakawa wajen ilmantarwa da nishaɗantarwa da ƙarin ƙarfin guiwar al’ummar ƙasa.

e. Don samar da al’adu da wasu shirye – shiryen da za a iya tallatarwa ga ƙashashen waje.

Waɗannan su ne dalilan da gwamnatin tarayya ta bayar wajen jaddada karɓe waɗannan gidajen ya zama mallakin gwamnatin tarayya. Har zuwa shekara ta 1979 akwai gidajen talabijin na ƙasa guda ashirin da ɗaya a duk manyan biranen jahohin da ke ƙasar nan da kuma guda ɗaya da aka aza tubalin gini a Abuja.

Uzodima, (1981sh. 9) ya nuna cewa daga wannan lokaci ne N.T.A. ta raba ƙasar zuwa yankuna shida ta yin la’akari da al’adu da kusantar waɗannan wurare. Ta karkasa gidajen talabijin a ƙarƙashin yanki – yanki. Kowane yanki yana ɗauke da Jihohi uku in ban da yankin B wanda yake ɗauke da Jihohi huɗu. Yankunan su ne kamar haka:-

N.T.A Abekuta da Ikeja da Ibadan, Ibadan ce cibiya.

N.T.A Aba/Owerri da Akure da Portharcourt da Benin, Benin ce cibiya.

N.T.A. Calabar da Makurdi da Enugu, Enugu ce cibiya.

N.T.A. Jos da Kano da Kaduna, Kaduna ce cibiya.

NTA Bauchi da Yola da Maiduguri, Maiduguri ce cibiya.

N.T.A. Ilorin da Minna da Sokoto, Sokoto ce cibiya.

Waɗannan manufofi na karɓe waɗannan gidajen yaɗa labarai na ƙara tabbatar da wannan ra’i mai nuna cewa gwamnati na tsare-tsare domin ganin ta daidaita tunanin al’umma da haɗin kan ‘yan ƙasa.

4.0 MANUFOFIN GWAMNATI KAN WASAN KWAIKWAYO

Idan kuwa ana batun manufofin gwamnati kan wasannin kwaikwayo na talabijin, nan ma akwai bayanai ƙarara waɗanda suka kasance fitila mai haskaka ire-iren wasannin da za a samar. Hukumar gidan talabijin ta ƙasa ta bayyana ƙarara manufofin gwamnati kan ire-iren wasan kwaikwayon da take buƙata kamar haka :

Domin Ilmantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa.

Tallatar da kyawawan al’adu da ɗabi’un al’umma.

Don haɓaka da ƙarfafa fasahar wasannin kwaikwayo rubutacce da aiwatacce (dandamali da talabijin).

Don Fito da munanann ɗabi’u da hanyoyin magance su.

Don bayyana hoton rayuwar al’umma.

Don ƙarfafa kyawawan tunani da kishin ƙasa.

Don a faɗakar da al’umma kan su rungumi kyawawan tunani.

Ko da yake wasu na ganin wannan a matsayi tarnaƙi domin kuwa ba a sake wa gidajen talabijin akala wajen aiwatar da duk wasu wasannin kwaikwayon da suka ga dama ba, wannan tarnaƙi na daga cikin matsalolin da suka addabi gidajen talabijin wajen samar da wasan kwaikwayon Hausa. Haka kuma cika waɗannan manufofi da gwamnati ta ɗauka shi ne aka ƙudiri aniyar dubawa ta hanyar ɗora wasan ‘Ƙasarmu Ce’ bisa faifan nazari.

5.0 TSARIN LABARIN WASAN ‘ƘASARMU CE’

Wannan wasa na ‘Ƙasarmu Ce’ an samar da shi da gudummuwar gwamnatin mulkin Soja da wata ƙungiya ta ƙasar waje mai suna European Economic Community da kuma Mutane da gwamnatin jihar Bauchi. Wanda ya rubuta, ya kuma bayar da umurni shi ne Saddik Ɓalewa, sai wadda ta shirya Matthew Rose. Shiri ‘Ƙasarmu Ce’ na da kashi biyu, kashi na ɗaya na da tsawon minti arba’in da daƙiƙa goma sha huɗu. Kashin na da fitowa-fitowa guda talatin da biyar. Kashi na biyu na da fitowa-fitowa guda arba’in na tsawon minti arba’in da ɗaya da daƙiƙa ashirin da huɗu. ‘Yan wasa da suka fito a cikin wannan shiri sun haɗa da Umar Uba Gaya wanda ya fito a matsayin Alhaji Musa da Ƙasimu Yero wanda ya fito a matsayin mai sayar da atamfofi da Ɗan wazam wanda ya fito a matsayin malam Ibrahin Ɗan-aruwa da Shehu Jibrin (Goloɓo) wanda ya fito a matsayin Kabiru, da dai sauran fitattun ‘yan wasan kwaikwayon talabijin na Hausa.

An gina tsarin wasan kan fafutukar da wani Alhaji yake yi ganin ya mallake gonakin wasu talakawa saboda irin arziƙi da albarkatun ƙasa irin su zinari da azurfa da dai sauransu da ke maƙare ƙarƙashin waɗannan gonaki. Ga ma hirarsu da wani Baturen Ingila wanda yana daga cikin waɗanda suka gano wannan arziƙi a lokacin da aka baje wa Alhaji samfurin abin da aka samo :

Alhaji :   This one, where did you find it?

Baturen Ingila: Just here, (refering to a map spread on the table) The task confirmed our suspicion. Those poor peasant farmers are sitting on wealth beyond their dreams.

(Kashi na 1, fitowa ta 3.)

Fassara da Hausa :

(Alhaji :Wannan, (yana riƙe da guda a hannunsa) a ina ka sami wannan ?

Baturen Ingila: A nan wurin, (yana magana yana nuna wurin a taswirar da ke teburin Alhaji). Wannan abu ya tabbatar da tsammanin da muke yi. Waɗannan makiyaya da manoma na zaune bisa dukiya wadda ta wuce tunaninsu.

(Kashi na 1, fitowa ta 3.)

Waɗannan mutane sun haɗa baki da wani Alhaji Musa mai tireda domin karɓe waɗannan gonaki.

Ga ma yadda firarsu ta kasance da Alhaji Musa.

Alhaji: Alhaji Musa ka sadu da saƙona?

Alh. Musa : Ranka ya daɗe na sadu da saƙon shi ya sa na taho da wuri.

Alhaji: Yaya maganar gonakin ?

Alh. Musa : Maganar gonaki, tun da na je gonar malam Aliyu da ta Korau, duk wanda na yi masa magana ba ya ba ni haɗin kai, musamman malam Ibrahim Ɗan-aruwa.

Alhaji: Ashe dai zaɓen tumun dare na yi ke nan.

Alh. Musa : Ba zaɓen tumun dare ka yi ba ranka ya daɗe, gonakin ne suke da yawa.

Alhaji: To kana nufin ba zan iya saye ba ne ?

Alhaji Musa : Ba ba za ka iya saye ba ne, mutanen ne da yawa kuma kowa da tasa gonar.

Alhaji: Alhaji Musa duk ta hanyar da za ka bi ka bi ka tabbatar na mallaki gonakin nan.

Alhaji Musa: To ranka ya daɗe tun da ka yi izini, za a bi duk hanyar da za a bi don ka mallaki waɗannan gonaki ranka ya daɗe.

(Kashi na 1 fitowa ta 18.)

Da farko Alhaji Musa ya yi ƙaƙarin manoman da su sayar masa da gonakin, amma abu ya ci tura. A wannan lokaci ne shi da yaransa suka riƙa shigar Burtu na dodanni ko aljannu domin ba mutanen garin tsoro. Sun cinna wa rumbun malam Ibrahim Ɗan-aruwa wuta, kuma daga baya suka bi shi daji suka kashe shi saboda ya fi kowa tirjiya wajen ƙin sayar da gonarsa. Bayan ƙoƙarin ƙwace gonakin mutane, Alhaji Musa ya siffantu da ɗabi’ar handame takin zamani da aka tanadar domin amfanin al’umma. Da jikan malam Ibrahim mai suna Sani ya fahinci abubuwan da Alhaji Musa yake ƙullawa ta hannun wani mai yankar aljihu, sai shi da abokansa suka yi dabara ta taimakon kai-da-kai ta hanyar yin sintiri da kai ɗauki ga duk wani wanda ya nemi taimako. Su ma sun yi shigar dodannin ƙarya domin korar yaran Alhaji Musa a lokacin da suka je kwashe takin da Alhaji ya ɓoye. Ga ma abin da ya faru :

Tanko: Dodanni Alhaji, (Tanko na magana yana hakki sakamakon gudun da suka yi shi da Audu)

Audu : Dodanni Alhaji

Alh. Musa : Kai don Allah ku yi wa mutane shiru. Mene ne Audu ?

Audu : Mun je ne ɗaukar taki, ina buɗewa sai muka ga dodanni, shi ne Tanko ya rugo a guje yana cewa dodanni-dodanni, ni kuma na biyo shi.

Alh. Musa : Wace irin maganar banza ce wannan ? Su wane ne dodannin ? Ba mu ne dodannin ba? Mu ke yin shiga don mu tsoratar da manoma. Wannan ai maganar banza ce. Kun haɗa baki za ku yi mani sata ko? Duk abin da za ku yi a tafin hannuna kuke. Saboda haka ku je ku dawo mani da motata da taki na.

(Kashi na 2 fitowa ta 34.)

Alhaji Musa ya yi ƙoƙarin gamawa da Sani jikan malam Ibrahim Ɗan-aruwa saboda idan Sani ya bi su to kowa ma zai bi baya. Shi kuwa Sani da ma can ya bayar da shawara kamar haka :

Sani : Ina da magana, za mu samu wasu mutane kullum dare su riƙa yin sintiri. Da rana kuma kowannen mu ya kasance yana da ƙaho, da zarar ya ga wani abu na tashin hankali, sai ya busa mu kuma sai mu kai masa gudunmuwa. Tsintsiya ɗaya ai ba ta shara.

(Kashi na 2 fitowa ta 14.)

Alhaji Musa ya ci gaba da ƙoƙarin sai ya ga bayan Sani, sakamakon yunƙurin da ya yi ne na ƙarshe asirinsa ya tonu, gudun da ya yi a lokacin da aka biyo shi ya sa numfashinsa ya ɗauke har ya rasa ransa. Wannan shi ne tsarin labarin wasan.

6.0 TUBALAN GININ MANUFAR MAJIGIN ƘASARMU CE’

Idan mun aza wannan shiri a faifan nazari za a fahinci cewa akwai abubuwa da dama waɗanda gwamnati ke ƙoƙarin nusarwa na ɗabi’u da sauya tunanin al’umma.

CUSA KISHIN ƘASA A ZUKATAN AL’UMMA

Wannan shiri yana hannun-ka-mai-sanda ga al’umma ta nuna Alhaji da abokinsa Baturen Ingila a matsayin ‘yan mulkin mallaka waɗanda sai bayan sun miƙa mulki ga ‘yan Nijeriya kana suka fahimci ɗimbin arziƙin da Allah ya albarkaci wannan ƙasa da shi. An nuna duk da sun bayar da mulki, ba su bar mu ba ta hanyar haɗa baki da wasu masu arziƙi a cikin ƙasa domin tabbatar da burinsu ya cika. Alhaji da abokinsa Bature su ne a matsayin Turawan mulkin mallaka waɗanda ke da niyyar mallakar gonakin mutane saboda su tatse albarkatun ƙasa. Duk da Alhaji Musa ya rasu a ƙarshen wasan, maganar malami wadda ya ce ‘An kashe mugun maciji amma ba a sare kansa ba’ ta zama gaskiya. Ba domin komai ba sai don kasancewar Alhaji wanda yake zaune a cikin gari da shi da abokinsa Bature na nan da ransu. Wannan shiri na gwada wa mutane irin kishin zuci da na ƙasa ta hanyar dogaro da kai da taimakon juna da kaucewa munanan halaye da ɗabi’u waɗanda ake son mutane su siffantu da su domin a sami ci gaba da bunƙasar tattalin arziƙi.

Idan muka duba ga manufofin gwamnati ta wannan fuska sai a ce ko da kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba to gwamnati ta aiwatar da wannan manufa tata.

6.2 YAƙAR MUNANAN HALAYE DA ƊABI’U

Munanan halaye da ɗabi’u da aka nuna a cikin wannan shiri tun daga shaye-shayen giya da illolinta wanda aka nuna irin sakamakon da suka faɗa wa Bulus da irin tanɓelen da yake yi idan ya sha giya. Haka nan kuma an nuna wani mugun hali na sace-sace waɗanda aka nuna a wurare da yawa a cikin wasan. Ga kuma illar cin hanci da danne haƙƙoƙin mutane wajen rabon taki. Alhaji Musa shi ne wanda za a iya ajiye shi a matsayin abokin hamayya (Antagonist) ko kuma muga (ɓillian) a cikin wasan. Mun ga irin ƙoƙarin da ya yi wajen bayar da cin hanci kamar haka:

Jami’in gwamnati: Wannan takarda ta ce a ba ka buhun taki sittin, amma abin da muke da su a store ba su kai sittin ba.

Alh. Musa : Ranka ya daɗe ai sai a duba (yana magana yana zaro wata ambulan mai cike da kuɗi a ciki.) Ranka ya daɗe ai sai a duba.

Jami’in gwamnati: Kana neman ka ba ni cin hanci ne? Ai ni tun da nake aiki ban taɓa karɓar cin hanci ba.

Alh. Musa : Ranka ya daɗe ba hanci ba ne, albarkar ofis ne kurum (yana magana yana ƙara zaro wasu takardun kuɗi yana haɗa su da na kan tebur)

Jami’in gwamnati: Amma fa waɗanda za a gani maganar takin nan suna da yawa.

Alh. Musa : Kai ( Alhaji Musa ya sauya murya mai cike da faɗa) idan ba za ka yarda mu yi hulɗa da kai ba sai in tafi wurin na sama da kai su turo ni ka ban takin.

(Kashi na 2 fitowa ta 21.)

Wannan su ne kaɗan daga cikin munanan halayen Alhaji Musa a cikin wannan shiri, an kuma nuna mana illar irin waɗannan halaye domin kuwa mun ga sakamakon ayyukan da ya aikata a ƙarshen wasan. A nan ana ƙoƙarin cusa wa mutane tunanin aikata ayyukan ƙwarai saboda a sami sakamako mai kyau, haka nan sakamako mummuna ga wanda ya aikata ayyukan assha. An gwada mutane ƙalilan suka sallaci gawar Alhaji Musa lokacin da ya mutu, haka nan kuma ƙalilan suka raka shi zuwa ga makwancinsa.

CUSA DOGARO DA KAI

Wannan manufa ce wadda hukuma ke ƙoƙarin cusa wa al’ummar ƙasa ta hanyar dogaro da kai da riƙe sana’a. Mun ga haka a wurare da yawa a cikin wannan wasa saboda an nuna hanyoyin ƙarfafa tattalin arziƙi da sana’o‘i iri-iri a cikin wasan. Waƙar da Shehu Jibrin (Goloɓo) wanda ya fito a matsayin Kabiru ya yi ta gwada yadda aka ɗauki noma da tattalin amfaninsa da adana abinci wanda daga nan ne alheri kan biyo baya.

Kabiru: Mun yi noman dawa, sai mu gode Allah yanzu ba mu da yunwa. Ku matasa ku jiya, ba a sauran bauta, mu da ɗai mun gane.

Amshi : Mun yi noman Dawa.

Kabiru : Zaman gida sai raggo wanda bai da kishin kai, bai cike rumbunshi. Yanzu ga dawa nan

Amshi : Fala-fala mun noma, fala-fala mun noma,.

(Kashi na 1 fitowa ta 11.)

6.4 ƘARFAFA SHUGABANCI NA GASKIYA

Shugabannin da aka nuna a shirin sun kasance masu kyawawan halaye abin koyi ga kowa. Hakimi da limami da sauran shugabannin ƙauyen sun nuna halaye na dattaku da tausaya wa al’umma da sauraran matsalolin jama’a da ba su shawarwari waɗanda za su taimaka wajen ci gaban al’umma. Mun ga haka a lokacin da Hakima ya shawarci mutane kan gyaran Masallaci da wani mai kuɗi daga ƙauyen ya ƙudiri aniyar yi. Ga ma abin da yake ce wa mutane :

Hakimi: To alhamdu lillahi, wato abin da ya sa na ce Liman ya yi magana da ku domin na ga maganar ta shafi masallaci ce. Amma ina son ku fahimta kowanne daga cikinmu nan yana son a ce ya gyara gidansa bare masallaci ɗakin Allah. Don haka ina ganin ai babu wani abu illa Alhaji Musa ya ci gaba da aikin nan.

(Kashi na 1 fitowa ta 14.)

Haka kuma a lokacin da samari suka je ga Hakimi da zancen aljannu ko dodanni su suka cinna wuta a rumbun malam Ibrahim da neman shawara ko mafita daga magabata, sai Hakimi ya shawarce su ta wannan hanya.

Hakimi: Ku matasa, maimakon ku zo kuna mani zancen aljannu da dodanni, ai kamata ya yi ku ce za ku gyara rumbun ɗan uwan nan namu malam Ibrahim da ya ƙone.

Kabiru : Jama’a saboda Allah ran asabar kowa da kowa ya fito tun da safe.

(Kashi na 1 fitowa ta 21.)

7.0 KAMMALAWA

Hausawa kan ce “Kowane irin abu da mazauninsa, wai an ɗaure mai dungu ya sumɓule”. Wannan haka yake don an ga manufofin gwamnatin tarayya game da karɓe gidajen talabijin a zamanin mulkin Soja. Haka kuma masu mulkin ne a wannan lokaci suka bayyana ƙarara irin manufar da suke fata su yi jagoranci ga samar da wasannin kwaikwayo na talabijin. A taƙaice wannan takarda ta duba waɗannan manufofin da suka haɗa da samar da wasannin kwaikwayo masu tallatar da kyawawan al’adu da ɗabi’un al’umma. Mun ga haka a wannan shiri na Ƙasarmu Ce inda aka nuna al’adu kyawawa na taimakon kai-da-kai ta hanyar aikin gayya da tausaya wa gajiyayyu da kare dukiya da lafiya haɗe da mutuncin al’umma. Haka kuma an nuna illar munanan ɗabi’u na zaman banza da sace-sace da dai sauransu. Takardar ta bayyana ƙarara tubalan ginin manufar wannan shiri waɗanda suka haɗa da : Cusa kishin ƙasa ga al’umma da yaƙar munanan halaye da ɗabi’u irin waɗanda Bature haɗe da Alhaji Babba da muƙarrabansa suka nuna. Duk da yake Alhaji Musa ya mutu a ƙarshen shirin, amma akwai sauran Rina a Kaba. Rashin hukumta Bature da Alhaji Babba a ƙarshen shirin shi wasu ke ganin hujjar da za a yi amfani da ita wajen sauya wa shirin suna ya koma ‘An kashe Maciji amma ba a sare kansa ba’.

Shirin ya nuna makwafin munanan ɗabi’un da kyawawa irin dogaro da kai da tsare gaskiya da amana da shugabanci na adalci. Idan aka kwatanta manufofin gwamnati da wannan shirin, a iya ambaton samun daidaito da ra’in ‘Tsararriyar Manufa’ a shirya shiryen gidajen talbijin musamman wannan wasan kwaikwayon. Saboda haka ana iya cewa, haƙiƙa wannan wasa ya bayyana ƙarara ra’in nan na ‘Tsararriyar-manufa’. Idan kuma har za a kwatanta waɗannan manufofi da wasannin da aka samar, sai mu ce tubarkalla.

Manazarta

Abbas, U. A. (2008). ‘Sassarƙuwar Adabi cikin Adabi: Nazarin Adon Harshe a Waƙoƙin Fina-finan Hausa’. Kundin Digiri na Ƙoli. Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami`ar Bayero.

Abdullahi, B.H. (2002). Gudummuwar Gidan Talabijin na Jihar Kano (S.T.Ɓ.67) Wajen haɓaka Wasan Kwaikwayon Hausa. Kano : Kundin digirin Farko Jami’ar Bayero.

Berger, A. A. (1995). Cultural Criticism: A Primer of Key Concepts. Foundation of Popular Culture, Vol. 4, London: Sage Publication Inc.

Bourcault, L. M. (1996). ‘Teleɓision Drama In Hausa Land: The Search For A New Aesthetics And A New Ethic’, In Critical Arts. Vol 10. No 1.

Bunza, M.S ((2008). ‘Duniyar Wasan Kwaikwayo: Nazari Daga Rayuwar Shehu Jibrin (Goloɓo); Kundin Digiri na Biyu. Sokoto: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Usmanu Ɗanfodiyo University.

Chamo, I. Y. (2005). ‘Saƙo a Finafinan Hausa: Nazari a kan Jigo da Ire-irensa'. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami`ar Bayero.

Ewu, R. J. (1986). “The Politics of Teleɓision Drama in Nigeria, A Case Study of N.T.A Kaduna”. Unpublished M.A. Thesis Department of English A.B.U Zaria.

Egbon, M. (1982). “Origin and Deɓelopment of Teleɓision Broadcasting in Nigeria”. Teleɓision Journal (December).

Farounbi, Y. (1979). “Television Politics and Society in Nigeria Options for the Future”, Television Ƙuarterly (October - December).

Inuwa, U A. (2000). ‘Tarbiyya Cikin Fina-finan Wasannin Kwaikwayo na Hausa’. Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami`ar Bayero.

N.T.A Decree No 24, (1977). (Section 6 Sub Section 1).

Segun, O. (1981). “The Adɓent of Teleɓision Drama in Nigeria” in Yemi Ogunbiyi (ed) Drama and Theatre in Nigeria: A critical Source Book. Nigerian Magazine Logos.

Uzodima, I. B. (ed) (1981). N.T.A Hand Book. Corporate Affairs Diɓision N.T.A Headƙuarters Lagos.

Yobe Journal - Volume 5

Post a Comment

0 Comments