TAMBAYA❓
Assalamu Alaikum warahmatullahi wa barakatuhu mallam barka da ƙoƙari Allah ya saka maka da aljanna firdausi ameen, malam tambayata shi ne meye ake nufi da tawassuli? Kuma dame dame ya kamata mutum yy tawassali da shi wanda aka samu hujjar a Qur'an ko hadis, na gode
AMSA:‼️
Wa'alaikumun salamu
warahamatullah,
Tawassuli yana nufin
mutum ya nemi kusanci zuwa ga Allah سبحانه وتعالى ta hanyar da
Shari’a ta tabba tar. Allah Ya ce
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا
اللَّهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ
“Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ji tsoron Allah, kuma
ku nemi hanyar kusanci zuwa gare Shi.” (Suratul
Ma’idah: 35).
Tawassulin daya
inganta bisa Al-Ƙur’ani da Sunnah ya haɗa da mutum ya yi addu’a ga Allah ta hanyar
sunayen Allah da siffofinsa, kamar ya ce: “Ya Allah, ina roƙonka da Rahamarka…
ko ya Allah ina roƙonka don Rahamarka data yalwaci komai ka biya min
bukatata kaza?
Ko kuma mutun ya ce:
اللَّهُمَّ
إِنِّي أَسْأَلُكَ بِأَنَّ لَكَ الْحَمْدَ، لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، وَحْدَكَ
لَا شَرِيكَ لَكَ، الْمَنَّانُ، بَدِيعُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ، ذُو
الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ
Ya Allah! Ina roƙonka da cewa lallai
godiya ta tabba ta gare Ka. Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Kai, Kai kaɗai, ba Ka da abokin
tarayya. Mai bayarwa Mahaliccin sammai da ƙasa, Mai girma da
daraja."
Annabi (SAW) yaji
wani mutum yana yin wannan addu'ar, sai ya ce: "Ya roƙi Allah da Babban
Sunansa (Ismul A'azam), wanda idan aka roƙe Shi da shi yakan
bayar, kuma idan aka kira Shi da shi yakan amsa."
Sannan mutun zai iya
yin tawassuli da ayyukan alheri da shi da kansa ya aikata, kamar yadda mutanen
ukun da suka makale a cikin kogo inda Kowannensu ya roƙi Allah ta hanyar
ambaton wani aiki na alheri daya aikata da ikhlasi—ɗaya ya ambaci
kyautata wa iyayensa, ɗaya ya bar zina
saboda tsoron Allah, ɗaya kuma ya kiyaye
amana. Sai Allah Ya buɗe musu hanyar fita.
Wannan yana cikin hadisin (Sahihul al-Bukhari, 2272; Sahihul Muslim, 2743).
Haka kuma ya halatta
mutum ya yi tawassuli da addu’ar mutum salihi mai rai, wato ya roƙe shi ya yi masa addu’a,
kamar yadda Sahabbai suke neman Annabi ﷺ ya yi musu addu’a a lokacin da yake raye.
Bayan wafatinsa kuma, ba a roƙon Annabi ﷺ ko wani mutum daya rasu ya biya buƙata; addu’a
ibada ce, kuma Allah ne kaɗai ake roƙa. Saboda haka, abinda yafi aminci shi
ne mutum ya roƙi Allah kai tsaye, yana amfani da sunayenSa da siffofinSa
da ayyukan alherinsa, ko ya roƙi Allah Ya amsa addu’ar
wani bawanSa salihi. Amma kada a rikita tawassuli da roƙon wani ba Allah ba;
Allah سبحانه
وتعالى Ya
ce:
﴿وَقَالَ
رَبُّكُمُ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ﴾
“Ubangijinku Ya ce:
Ku roƙe Ni, Zan amsa muku.” (Ghafir: 60). Don
haka, a duk lokacin da muke buƙatar taimako, arziki, lafiya, gafara
ko wata bukata, mu mayar da zuciyarmu ga Allah, domin Shi kaɗai ne Mai iko da
komai. Allah Ya shiryar damu zuwa abinda yake daidai, Ya kuma karɓi ibadunmu da
addu’o’inmu.
Wallahu ta'ala aalam
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.