Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Tashi Da Janaba Lokacin Sallar Asuba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Aassalamu alaikum mln tambayata ita che. Idan mutum ya tashi lokacin sallar Asuba, sai ya tashi a makare kuma da najasa, wato ya fitar da mani. Shin mln zai yi wanka neh, sai ya je masallacci neh, ko akwai abun da aka saukaka mai gameda hakan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuh.

Idan mutum ya tashi lokacin sallar Asuba, sai ya tarar da cewa ya fitar da maniyyi, to ya zama mai janaba, kuma wajibi ne ya yi wankan janaba kafin ya yi sallah. Allah Ya ce

 وَإِن كُنتُمْ جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا

“Idan kun kasance masu janaba, to ku tsarkake kanku.” (Suratul Ma’idah: 6).

Saboda haka, ba zai yi sallar Asuba da janaba ba domin kawai yana tsoron makara ko rasa jam’i; sai ya yi wankan janaba cikin gaggawa sannan ya tafi masallaci ya yi sallar. Idan ya riski raka’a, sai ya bi liman, abinda ya riska ya yi, abin daya kuɓuce masa kuma ya cika bayan sallamar liman. Amma idan babu ruwa, ko kuma amfani da ruwan zai cutar da shi sosai, to Shari’a ta tanadi taimama idan sharuddan taimaman sun cika. Haka kuma, idan barci ya rinjaye shi har lokacin Asuba ya wuce, da zarar ya farka sai ya yi wankan janaba sannan ya sallaci Asuba; Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “Duk wanda ya manta da wata sallah ko barci ya rinjaye shi, to ya sallace ta idan ya tuna.” (Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim).

A Ƙarshe ina son na yi anfani da Wannan dama na yi jan hankali da Nasiha ga yan'uwana na Wannan gida mai Albarka Ya kamata mu kula sosai da Sallar Asuba, domin ita ce daga cikin sallolin da mutane da yawa suke sakaci dasu saboda barci. Mu yi ƙoƙarin kwanciya da wuri, musa agogo ko wani abin tunatarwa, sannan mu yi addu’a ga Allah Ya taimake mu mu tashi. Kada mu bari son barci da hawa social media ya rinjayi abinda yafi komai muhimmanci wato sallah. Idan mutum ya tashi yana cikin janaba, kada yaji kunya ko ya yi ƙoƙarin neman wata hanya ta guje wa wanka saboda tsoron mutane; tsarkin da Allah Ya wajabta shi ne abin da ya kamata ya fifita. Mu tuna cewa rayuwa gajeriya ce, kuma sallah ita ce babban alƙawari tsakanin bawa da Ubangijinsa. Allah Yasa mu zama masu kiyaye salloli a kan lokutansu, Ya gafarta mana kura-kuranmu,

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments