𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aassalamu alaikum. An wuni lafiya. Tambaya nake da shi, Ina da wani bukatar ne sai Allah ya cika min shi. Toh shin zan iya yin Azumi ko sadaƙa na godiya ga Allah da ya cika min wannan bukatan ko kuma haramun ne haka? Na gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh..
Yin azumi ko sadaka
don nuna godiya ga Allah bayan ya biya miki bukata ya halatta kuma yana da lada
sosai a musulunci. Wannan ba haramun ba ne; akasin haka, yabo ne da murna da
ni'imar Ubangiji ta hanyar ayyukan alheri, muddin ba ki ƙulla shi da sharaɗi tun farko ba (irin
bakance).
BAMBANCI TSAKANIN
"BAKANCE" DA "GODIYA TA HAKA KAWAI"
GODIYA TA GASKIYA
(SHUKR): Ita ce ki tashi da kanki kiyi sadaka ko azumi don kawai kina farin
ciki da abin da Allah ya yi miki, ba tare da kin fadi cewa "Idan Allah ya
yi min kaza zan yi kaza" ba. Wannan shi ne mafi alheri. kuma Allah yana
cewa: "Idan kuka gode, lallai zan ƙara muku.
Wannan yana da kyau
sosai, Ciyar da matalauta, taimaka wa na kasa da kai, ko bayar da kuɗi ga mabukata yana ɗaya daga cikin mafi
kyawun hanyoyin gode wa Allah. Za ka iya yin ta a kowane lokaci gwargwadon
ikonka, ba tare da ka takura wa kanka ba.
Hadisi ya tabba ta
daga Sahabin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Abu Bakrata Allah ya ƙara masa yarda cewa:
"Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance idan wani abun
alheri ya zo masa, ko kuma aka yi masa bushara da shi, yakan gurfana yana mai
sujjada, yana mai godiya ga Allah". Imam Attirmizhiy ya ruwaito kuma ya
kyautata shi a hadisi mai lamba ta (1578), Abu Dáwud a lamba ta (2774), Ibn
Majah kuma lamba ta (1394).
BAKANCE (NAZAR): Idan
kuma da can kinyi alkawari (misali kin ce: "Idan Allah ya biya min
bukatata zan yi azumi kwana uku ko zan ba da sadaka"), to tunda Allah ya
biya miki, ya zama wajibi (dole) a kanki ki cika wannan alkawarin. Duk wani
alkawarin da mutum zai daukar wa kansa na yin wata ibada ta musamman bisa
sharadin cikar wata bukata tasa, idan har wannan bukatar tasa ta biya, to fa
wajibi ne akansa sai ya aikata abinda ya yi wa Allah alkawarin akansa.
Wasu daga cikin
malaman hadisi sun ta fi akan cewa idan mutum ya yi bakance ya kasa cikawa zai
iya yin kaffarar rantsuwa, saboda hadisin da aka rawaito daga Muslim a lamba
ta: 1645 a sahihinsa, wanda Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) yake cewa :
"Kaffarar bakance irin kaffarar rantsuwa ce". Duba Alminhaaj na
Nawawy 4/269
Halak ne kuma
kyawawan ayyuka ne yin azumi ko sadaka don nuna godiya ga Allah bayan Ya biya
miki bukata. A cikin shari'ar Musulunci, nuna godiya ga Ubangiji (Shukr) ta
hanyar ayyukan alheri abu ne da ake so kwa rai da gaske. Za ki iya gudanar da
azuminki ko sadakarki cikin farin ciki da fatan Allah ya karba.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.