Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Yi Bakance Ba Zai Sake Aikata Wani Sabo Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum Mallam Khamis na yi rantsuwa wato bakance cewa ba zan sake aikata wani saɓo ba da nike aikatawa ba, sai kuma na sake aikata saɓon. Shin zan yi kaffara ne?

HUKUNCIN WANDA YA YI BAKANCE BA ZAI SAKE AIKATA WANI SAƁO BA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Shi dai bakance kala biyu ne. Akwai bakancen yin biyayya ga Allah, akwai kuma na saɓon Allah. Shi yasa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce "Wanda ya yi bakance zai bi Allah, to yabi shi. Amma wanda ya yi bakance zai saɓa wa Allah, kada ya saɓa masa". (Sahihul Bukhariy hadisi na 6,696).

Shi bakance asalinsa makaruhine bai kamata mutum ya yi bakance akan wani aikin alkhairi ko saɓo ba, Saboda faɗin Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam); Bakance baya zuwa da alkhairi, kuma yana fitowa daga marowacine (Nisa'i 3801) Albani ya ingantashi a cikin Sunan Nisa'i.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya hana yin bakance kamar yaddd Imamu Muslim ya ruwaito ta hanyar Sayyiduna Abdullahi bn Umar (radhiyalLahu anhuma) Ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) watarana ya haɗu yana hanamu yin bakance, Ya ce saboda shi bakance ba ya mayar da kaddara, sai dai ta dalilinsa dai akan fidda (dukiya) daga hannun marowaci".

Shaik Usaimeen (rahimahullah) Ya ce: Muna yi wa 'yan'uwanmu nasiha akan kada mutum ya yi bakance akan dena saɓo, dan kada hakan yazamo masa al'ada, ta yanda baya iya barin aikin saɓo sai in ya yi bakance, Allah maɗaukakin sarki ya ce

وَأَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِنْ أَمَرْتَهُمْ لَيَخْرُجُنَّ ۖ قُلْ لَا تُقْسِمُوا ۖ طَاعَةٌ مَعْرُوفَةٌ ۚ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ

(Munafukai) Suna rantsuwa da Allah iyakar rantsuwa idan (Annabi Sallallahu alaihi Wasallam) ya yi musu izinin fita jihadi, za su fita, Allah Ya ce: Kace dasu kada su rantse akan karya, biyayyarku sananniya ce da harshe ce kawai. (Suratun Nuur Aya ta 53).

Kamar hakane ba'a bukatar yin bakance akan daina saɓo ko aikin alkhairi, abunda akeso shi ne ka ƙulla niyyar mai karfi ta dena saɓon ko jajircewa wajan aikin alkhairi ba tare da yin bakance ba, wannan shi ne abunda yafi alkhairi.

Sannan kuma ya kamata ka sani dukkan Ýan Adam Allah ya kaddara mana za mu dinga saɓa masa, Matukar mutum ba Annabi bane kuma ba mala'aka bane, to dole ne sai ka saɓa wa Allah, Annabawa da mala'ikune kaɗai basa aikata Saɓon Allah domin su tsarkakakkune Allah ne ya zaɓe su ya fifita su kuma ya tsarkakesu a cikin bayinsa. Sabida haka ya kamata kasan cewa baka isa kace ba za ka kara saɓawa Allah ba. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: Dukkan Ýan Adam Masu Aikata Zunubi Ne Mafi Alkhairin Cikinsu Sune Masu Tuba. {Sunan Ibn Majah}.

Sabida haka yanzu ya isa ka fahimci cewa baka isa kace ba za ka taɓa saɓa wa Allah ba sai dai abinda ake so shi ne; kakai makura wajen nisantar saɓon Allah duk wata hanya da kasan tana kai ka zuwa ga aikata saɓon. Sannan ka dage wajen neman shiriyar Allah tunda shiriyar taka ba a hannunka take ba.

Wanda ya yi bakance akan ba zai kara aikata wani saɓo ba sai kuma ya aikata, wajibine ya tuba, ya yi istigfari saboda aikata wannan saɓon, dakuma rashin cika wannan bakancen, sannan ya yi kaffarar rantsuwa, shi ne ciyar da miskinai goma, ko tufatar dasu, ko 'yanta baiwa, waɗannan abubuwan guda uku cikinsu zai zaɓi ɗaya ya yi, mutum zaiyi wanda yakeso a cikinsu, idan bai samu damaba sai ya yi azumi guda uku (kwana uku). Dan haka dolene sai kayi kaffarar rantsuwa, sannan kuma saikayi istigfari da tuba akan aikata wannan saɓon.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments