Ticker

6/recent/ticker-posts

Zogale a Wasu Nau’ukan Abincin Zamani (Kuskus, Soyayyen Kwai Da Zogale)

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Zogale a Wasu Nau’ukan Abincin Zamani

A wannan zamani da ake ciki, sauye-sauye da cigaban zamani sun kawo sababbin hanyoyin sarrafa zogale da kuma sauya tsarin girke-girke na al'ada. Sakamakon wayar da kai a kan muhimmancin ganyen zogale ga lafiyar ɗan’adam, a yanzu an fara amfani da shi wajen ƙawatawa da kuma haɓaka sinadaran abincin zamani daban-daban. Waɗannan sababbin hanyoyi sun haɗa da sanya zogale a cikin abinci irin su kuskus da kuma suya ko toya ƙwai, da sauran makamantansu.

Kuskus da Zogale

Wannan nau’i ne na abincin zamani da ake dafa kuskus tare da sanya ganyen zogale a ciki domin ƙara masa kyawun launi, ɗanɗano, da kuma sinadaran gina jiki.

A kan dafa kuskus ɗin tare da kayan lambu da maggi, sannan a sa ganyen zogale da aka wanke da kyau a ƙarshen girkin domin ya turara tare da kuskus ɗin ba tare da ya ƙone ko ya rage ingancinsa ba.

Kayan haɗin da ake amfani da su yayin wannan dafuwa sun haɗa da:

a. Albasa da Tattasai

b. Kayan ƙamshi da na ɗanɗano (magi, gishiri da sauransu)

c. Kuskus

d. Mai ko bota (butter)

e. Ruwa

f. Zogale (ɗanye ko busasshe)

Hoton Dambun Kuskus da Zogale

Hoton Dambun Kuskus da Zogale

Soyayya ko Toyon Ƙwai da Zogale

Suya ko toya ƙwai da zogale wata hanya ce ta zamani da ake haɗa ƙwai da albasa tare da ganyen zogale. Akan yi hakan ne domin samun sarrafuwa mai daɗi haɗe da sinadaran gina jiki da ƙara ƙarfin garkuwa jiki tare da samar da magungunan wasu cututtuka. Ana kaɗa ƙwai sannan a jefa albasa da tattasai da kuma ɗanyen ganyen zogale a ciki. Daga nan sai a toya shi a cikin mai ko bota a kan wuta matsakaiciya.

Kayan haɗin da ake amfani da su yayin wannan dafuwa sun haɗa da:

a. Albasa da tattasai

b. Gishiri ko maggi

c. Ƙwai

d. Mai ko bota

e. Zogale (ganyen zogale)

Hoton Soyayya ko Toyon Ƙwai da Zogale

Hoton Soyayya ko Toyon Ƙwai da Zogale

Naɗewa

Lallai zogale yana taka muhimmiyar rawa a ɓangaren abinci da maƙulashe a ƙasar Hausa. Kamar yadda aka gani a cikin wannan babi na uku, ana amfani da zogale wajen samar da kwaɗo (ɗatu) ko miya ko dambu. Bayan daɗi da yake da shi a abinci, yana kuma tattare da alfanu na magani ga jiki. Zuwan zamani da samuwar sauye-sauye ga abincin Hausawa ya sa an samar da sababbin hanyoyin sarrafa zogale. A yau akan saka shi a cikin nau’ukan abinci da ƙwalama daban-daban. Daga cikinsu har da dambun kuskus da soyayyen ƙwai da sauransu. A babi na huɗu, za a a kalli yadda itacen zogale yake taka rawa a ɓangaren tattalin arziki da sana’o’i.

Post a Comment

0 Comments