An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Kalmar miya tana cikin kalmomin Hausa
jinsin sunayen mata. Tana ɗauke da ma’anar romo-romo
da ake kaɗa wa kuka ko kuɓewa, ko karkashi ko kuma a zuba masa ganye
kamar yakuwa ko alayyaho ko lalo, a haɗa da tuwo ko na shinkafa a ci (BUK, 2006 sh. 347).
Yayin da za a yi miyar zogale ɗanye ko busasshe, sai a nemi abubuwa kamar haka:
a. Nama, idan da halin saya
b. Kayan miya
c. Gishiri
d. Daddawa
e. Mai, kaɗan
f. Zogale ɗanye ko busasshe
Daga nan sai a tafasa nama, ko a soya shi. A markaɗa kayan miya, a haɗa tare da naman a tafasa, a sa gishiri. Lokacin da ya
dafu sosai, a tsai da ruwan miya, a sa daddawa da kayan ƙamshi. Idan aka ga ya kusa
nuna, sai a zuba ganyen zogale a rufe tukunya, a bar ta ta dahu. Ana iya ci da
tuwon shinkafa ko na dawa ko ɓula ko taiba ko sakwara ko
hoce.
Hoton Miyar Zogale
Ƙarin Nau’ukan
Kwaɗo Da Ake Yi Da Zogale
Kwaɗon zogale da aka yi bayani
a sama ya shafi zogale ne kai tsaye a matsayin babban abin da ake kwaɗantawa. Bayan shi wannan nau’in kwaɗo, akwai kuma wasu nau’ukan kwaɗo da ake da su a ƙasar Hausa waɗanda ake sanya zogale a cikinsu a matsayin
kayan haɗi. Sani da Umar (2022) sun
kawo wasu daga cikinsu. Misalansu sun haɗa da:
Kwaɗon Shinkafa Da
Zogale
Irin wannan kwaɗo, ana dafa shinkafa ne dafuwar wasa-wasa kafin a yi shi.
Bayan ta dafu, sai a kawo kayan haɗi a kwaɗanta. Kayan haɗin da ake amfani da su sun haɗa da:
a. Albasa
b. Gishiri
c. Gyaɗa
d. Ƙuli-ƙuli
e. Mai (idan an ga dama)
f. Ruwa
g. Shinkafa
h. Tarugu
i. Tattasai
j. Zogale
Kwaɗon Garin Kwaki
Da Zogale
Garin kwaki ma ana kwaɗanta shi tare da dafaffen ganyen zogale. Da fari, ana jiƙa garin kwakin ne, a tace
ruwan jikinsa, sannan a shanya shi ya ɗan sha iska. Bayan an dafa zogalen shi ma ya sha iska,
sai a gauraya garin kwakin da zogalen tare da sauran kayan haɗi domin samun kwaɗo mai daɗi.
Kayan haɗin da ake amfani da su
sun ƙunshi:
a. Garin kwaki
b. Gishiri
c. Ƙuli-ƙuli
d. Mai (idan an ga dama)
e. Ruwa (domin dafawa da jiƙawa)
f. Tumatur da Tattasai
g. Zogale
Kwaɗon Tuwo Da
Zogale
Irin wannan kwaɗo ana yin sa ne ta hanyar sarrafa sauran tuwon da ya
kwana ko wanda aka rage. Za a yayyanka ko a murjije shi sannan a gauraya shi da
dafaffen ganyen zogale. Bayan zogalen ya dafu kuma tuwon ya tsane, sai a haɗa su da sauran kayan haɗi a kwaɗanta domin samun abinci
mai ɗanɗano da gina jiki.
Kayan haɗin da ake amfani da su
sun ƙunshi:
a. Albasa
b. Barkono (tonka)
c. Kayan yaji
d. Ƙuli-ƙuli
e. Mai (idan an ga dama)
f. Tuwo (gayan tuwo)
g. Zogale
Wannan nau’i ne na kunu da ake haɗawa ta hanyar amfani da ganyen zogale tare da gero.
Bambancinsa da sauran nau’o’in kunu shi ne, yayin tafasa ruwan kunun, ana sanya
zogalen a tafasa su tare, ko kuma a sanya shi cikin geron yayin da za a kai niƙan gumba domin a niƙo su tare. Wannan kunu
yakan kasance yana ɗauke da ƙamshi da kuma ɗanɗanon zogale. Masana suna ba da shawarar amfani da shi
domin ɗimbin amfanin da zogale
yake da shi ga lafiyar ɗan’adam.
Kayan haɗin da ake amfani da su
sun haɗa da:
a. Gero
b. Kayan yaji
c. Ruwa
d. Zogale
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.