An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
ZOGALE A
MUHALLIN TATTALIN ARZIKI
Shimfiɗa
A babin
da ya gabata, an dubi zogale a matsayin abinci da ƙwalama. Amfanin zogale bai tsaya ga magana da abinci ko ƙwalama kawai ba. Ya haɗa har da sana’a. Zogale
yana taka muhimmiyar rawa a duniya baki ɗaya ta fuskar tattalin arziki. Wannan ba ya rasa nasaba da darajar
da yake da shi da kuma ɗimbin amfaninsa a matsayin mahaɗin magunguna. A ɓangare ɗaya kuwa, akwai masu ƙananan sana’o’i da suke
sayar da zogale. Akan sayar da ɗanyen ganyen ko dafaffe ko busasshe ko kuma dakakken garin zogale.
Wannan babi na huɗu ya dubi yadda zogale yake taka rawa a matsayin
hanyar sana’a.
Dalilan Daukakuwar Darajar
Zogale
Zogale
yana da daraja a ƙasar Hausa, har ma da
matakin duniya. Ɗimbin alfanu da itaciyar
zogale take tattare da shi, shi ne ya ba ta daraja a duniya inda ake
kasuwancinta a matakai daban-daban. Kamar yadda aka sani ne, zogale ko
zogala ba baƙuwar aba ce ba, , musamman a karkarar da take
farfajiyar ƙasar Hausa, domin tana cikin jerin abincin yau da gobe. Sannu a
hankali, mutanen da suke zaune a alƙaryu da birane suka gano amfaninta, wadda tuni waɗanda suke karkara
suka daɗe suna
amfani da ita wajen aiwatar da magani domin magance nau’o’in cututtukan da suke addabar su. Sakamakon ɗimbin sinadaran da suke jibge a cikinta wanda Allah ya halicce ta da su. Ire-iren waɗannan sinadaran ne ya sa take ƙarfafa garkuwar jikin bani Adam
da take yaƙar cututtukan da suke cikin jikin wanda
duk suke amfani da ita. Kuma haƙora da gaɓoɓi da ƙasusuwan jiki su ƙara ƙarfi da inganci. Wannan
bincike ya gano cewa, tana ƙarfafa gani tare da ƙara lafiyar ido. Tana gina jikin ɗan’adam fiye da yadda
madara take gina shi. Tana taimakawa wajen gyara fatar jiki.
A taƙaice za a fahimci cewa, itaciyar zogale tana ƙunshe da fa’idoji masu
tarin yawa. Daga cikin su akwai:
a. Magance
hawan jini
b. Ƙara ruwan nonon mace mai
shayarwa
c. Daidaita
sukarin da ke cikin jini
d. Taimakawa
wajen narkar da abincin da aka ci
e. Yaƙa tare da kashe ƙwayoyin cutar bakateriya
f. Wanke
ciki
g. Ƙara wa hanta da ƙoda lafiya
h. Gyara ƙwaƙwalwa
i. Rage ƙiba ko taiɓa
j. Ƙara wa bani Adam kuzari
Irin
wannan alfanu da suke ƙunshe a cikin zogale ne ya sa ake kallon bishiyar zogale a ƙasar Hausa tamkar: “Nagge daɗi goma”. Wato komai nata abin amfani ne. Ta kasance abin moriya ta fannonin rayuwa daban-daban.
A ɓangare ɗaya kuwa, kasancewar
bishiyar zogale mai yawan amfani kamar yadda bayani ya gabata. Akan yi amfani da wannan itaciya a kewaye harabar gona da ke fadama
domin kariya daga dabbobi, ko muhalli domin a yi wa gida kwalliya. Wannan
wani ƙari ne na daga ribar da ake samu daga itaciyar.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.