Ticker

6/recent/ticker-posts

Zogale a Matsayin Sinadarin Tace Ruwan Sha

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Zogale a Matsayin Sinadarin Tace Ruwan Sha

Bayan abinci, muhalli, da sutura, tsaftataccen ruwan sha yana ɗaya daga cikin muhimman abubuwan buƙatar rayuwa. Rashinsa kuwa yakan zama sanadin yaɗuwar cututtuka da asarar rayuka. Ta wannan fuskar, zogale yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaftataccen ruwan sha cikin sauƙi domin kare lafiyar iyali.

Yayin da aka daka ƙwayoyin irin zogale suka zama gari mai laushi-laushi, ana amfani da garin wajen tace gurɓataccen ruwan gulbi, ƙorama, ko tafki. Bincike ya tabbatar da cewa, wannan sassauƙar hanyar ba ta tsaya kawai a kan rage ƙazantar ruwa ba, har ma tana kawar da ƙwayoyin cuta masu lahani da suke ciki.

Garin ‘ya’yan zogalen yakan haɗe da daskararrun abubuwan da suke cikin ruwan, ya nitsar da su zuwa ƙasa (kwanta ƙasa). Ta wannan hanyar, ana iya cire ƙwayoyin cutar bakteriya kimanin kashi 90% zuwa 99% da suke cikin ruwan. Bayan sun kwanta a ƙasa, sai ruwan ya kasance sarai a sama, ta yadda za a iya shan sa ba tare da ya haifar da cutarwa ba. Wannan hanyar tana maye gurbin amfani da sinadarai irin su alum, wanda suke da tsada sosai, ga kuma haɗari ga rayuwa da muhalli.

Matakan Tsaftace Ruwan Sha da Garin Zogale

Bambancin hanyoyin samun ruwa shi ne yake ƙayyade adadin garin zogalen da za a yi amfani da shi da kuma yawan ruwan da za a tace.

Misali, idan za a tace ruwa kimanin lita 20:

1. Nemo zangarniyar zogale ka ɓare ta, sannan ka fere bayan ƙwayoyin irin domin samun ɓangaren ciki mai farin launi.

2. Daka fararen ƙwayoyin har su zama gari mai laushi.

3. Ɗebi cokali biyu na garin ka zuba a cikin kwalba, sannan ka ƙara tsaftataccen ruwa kaɗan a ciki.

4. Girgiza kwalbar sosai har tsawon kimanin mintuna biyar.

5. Zuba ruwan kwalbar a cikin lita 20 na ruwan da kake son tacewa.

6. Juya ruwan cikin hanzari na tsawon minti biyu, sannan ka ci gaba da juyawa a hankali har tsawon minti goma.

7. Bar ruwan ya huta na tsawon awa ɗaya ko har sai ka ga dukan dattin ya kwanta a ƙasa.

8. Yi amfani da ƙyalle mai tsafta wajen tace ruwan saman zuwa wani masaki na daban, kamar bokiti domin sha.

Hoton Ɗanyun Zangarniyar ‘Ya’yan Zogale

Hoton Ɗanyun Zangarniyar ‘Ya’yan Zogale

Naɗewa

A wannan babi, mun ga cewa itaciyar zogale tana da matsayi na musamman a fagen magani, wanda hakan ya samo asali ne daga al'adun gargajiya na Hausawa da sauran al'ummomin Afirka da Asiya, kuma kimiyyar zamani ta tabbatar da ingancinta ta hanyar bincike mai zurfi. Mun gano cewa zogale yana ɗauke da sinadarai masu muhimmanci waɗanda suke taimakawa wajen magance cututtuka daban-daban kamar su ciwon sukari, hawan jini, zazzabin cizon sauro, da kuma cututtukan fata. Bugu da ƙari, ikonta na kare garkuwar jiki (antioxidant) da kuma yaƙar ƙwayoyin cuta (antibacterial) ya sa ta zama ɗaya daga cikin tsirran da aka fi amfani da su a magungunan gargajiya a ƙasar Hausa., Akwai tabbacin cewa, Allah ya halicce ta da hikima ta musamman domin ta zama magani ga al'umma.

Duk da haka, ya kamata a lura cewa akwai buƙatar ƙarin bincike na kimiyya don tabbatar da ingantaccen amfani da zogale a matsayin magani. Yana da kyau a lura, musamman wajen ƙayyade adadin da ya dace a yi amfani da shi. Akwai buƙatar a kyautata hanyoyin da za a bi wajen sarrafawa don samun mafi kyawun sakamako. Wannan babi ya kafa harsashi mai ƙarfi game da mahimmancin zogale a fannin magani, kuma zai taimaka wajen fahimtar yadda al'adun gargajiya da kimiyyar zamani suka haɗu don inganta lafiyar ɗan'adam. A cikin babi na gaba, za mu ci gaba da nazarin amfanin zogale a fannin abinci da ƙwalama, don cika burin wannan littafi na bayyana cikakken darajar wannan itaciya mai albarka a ƙasar Hausa.

Post a Comment

0 Comments