An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Tsaraka
Asalin kalmar Bahaushiyar ce wadda take cikin tsarin sunayen kalmomin Hausa,
jinsin mace. Ana tunanin cewa kalmar
ta samo asali ne daga kalmomi biyu na Hausa wato tsara da kuma kayi
(kai). Kalmar tsara tana iya ɗaukar
ma’anar shirya ko gyara. Kayi kuwa yana nufin kai. Idan
aka haɗa waɗannan
kalmomin da suke cikin jerin kalmomin aikatau, za su bayar da lafazin shirya
kai, ko kuma gyara kai.
Da yake lafazin shirya
kai da tsara kai, duk ma’ana ɗaya ce,
yau da gobe ta yi halinta a sakamakon sassauyawar zamani da sauye-sauyen da shi
harshen yake fuskanta, sai kalmomin
suka rikiɗa suka koma tsaraka. Tun kafin
bayyanar Musulunci,
Bahaushe ba ya shiga kowane irin sha’ani sai ya shirya masa. Shirin da ake
aiwatar kuwa, yakan haɗa da neman kare kai ko sa’a
ko nasara ga dukkan lamuran da za a fuskanta. Abin da ya ƙarfafa guiwar ɗaukar
wannan ra’ayi shi ne, a karin harshen Katsinanci, kalmar tsaraka bayan
ma’anarta ta neman maganin sa’a a fagen sana’a tana kuma ɗauke
da ma’anar kwana a shirye, kamar yadda Abraham (1975 sh. 878) ya nuna.
Akwai tsiron tsaraka wanda
ya kasance masu sana’ar sayar da dafaffen ganye da fura da nono da wasu abubuwa
da dama sukan ɗiba su saka a cikin sana’arsu da ƙudurin samun kasuwa. Sukan yi hakan ne
domin neman sa’a na yin saurin sayar da abin da suke talla. Wannan haki na
tsaraka, mata sukan haɗa da shi wajen ɗaurin
lalle domin samun kanwar hannu (samun sa’a ko kasuwa) don haɓakar
sana’a, da cin nasara a fagen kasuwanci.
Haka kuma, tana ɗaukar ma’anar neman
sa’a wajen kamun kifi. Hasali an kawo karin magana, wadda Hausawa suke cewa: “Su
babu tsaraka wanka ne. Ta yiwu, wannan
ne ya haifar da wanzuwar keɓaɓɓar kalmar fannu a cikin lamarin sarkanci wadda
sarkawa suke kira gyandi wato addu’a ko maganin da ake aiwatarwa domin
neman sa’a.
Bargery (1933 sh. 1030) ya
kawo ma’anar kalmar
tsaraka a matsayin duk wani abu da ɗan kasuwa yake yin amfani da shi ta fuskar magani domin samun nasarar
haɓakar
kasuwancinsa. Ya kuma kawo wata ma’ana da take cewa: “Hango haɗari
a kuma kauce masa.”
Abin lura a nan shi ne, tsaraka tana iya kasancewa addu’a ko ‘yan ɗebe-ɗeben
ganyaye ko hakukuwa ko saƙe-saƙin itatuwa waɗanda
akan murza ko a jiƙa
domin shafa wa kayan sana’a ko aiki.
Hausawa suna amfani da ganyen
zogale wajen yin tsaraka da ƙudurin
samun sa’a a fagen saye da sayarwa. Mata masu sayar da kaya iri daban-daban sukan
jiƙa ganyen zogale a cikin ruwa, in ya jiƙa, sai a ɗauki
ruwan a yi wanka da su. Wasu kuwa, ganyen ne sukan saka a cikin kayan sana’ar
da nufin samun kasuwa, sai kuwa a samu biyan buƙata
(Kande, 2015).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.