An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Zogale a Mahaɗin Magungunan Kariya Da Buƙatun Zuci
Magungunan kariya da na
bukatun zuci su ne waɗanda
akan yi amfani da su don taimakon ɗan’adam wajen kare lafiyar
jikinsa tare da biyan wasu buƙatunsa
da suka jiɓinci jin daɗin
rayuwarsa. A wannan haujin ma zogale yana taka muhimmiyar rawa, musamman idan aka yi la’akari da amfanin da
ake yi da shi ta ɓangarori kamar:
Hawan
Jini Da Ƙarin Kuzari
Sanya zogale cikin abinci
ana ci, yana maganin matsalar hawan jini. Yana kuma ƙara wa mutun kuzari a jikinsa (Agrawal da
Mehta, 2008 sh. 20; Junju, 1990 sh. 32). Haka kuma, Godinez (2015) ya nuna shan
ruwan zogale a kowace rana yana
hana kasalar jiki. Samuel (2013) ya nuna amfani da zogale yake yi ta fuskar ƙara kuzarin jiki.
Kare
Kai Daga Cuta
Magunguna ne da suke taimaka wa mutun wajen kare lafiyar jikinsa daga cuta
da take haifar masa da wata illa a jikinsa. Akan yi amfani da zogale domin ƙoƙarin dakatar da wata cuta daga shiga cikin jikin
mutun, ko kuma hana ta yaɗuwa.
Don haka za a iya cewa zogale yana maganin da ya danganci riga-kafi tare da hana yaɗuwar
cuta (Samuel, 2013).
Hawan
Jini (Tashin Jini)
A sami albasa, a kasa ta
kashi huɗu, a
yanka kashi ɗaya
bisa huɗu na
albasar a gama da dafaffen ganyen zogale a ci. A aiwatar da wannan haɗi sau uku ko huɗu a
wata. Yin haka yana maganin hawan jini, kamar yadda Axe (2016) da Jinju (1990
sh. 32) suka bayyana. Axe ya nuna amfani da zogale yana rage wanzuwar tsufa. Wato
ko mutun ya tsufa ba za a ga alamar
tsufa a jikinsa ba. Wannan bai rasa nasaba da irin sinadirai da itaciyar ta ƙunsa da suka ruɓanya
waɗanda
suke cikin madara da karas da ayaba da lemon zaƙi, da
kuma wasu ɗimbin sinadaran da suke gina jiki.
Ƙara Yawan Ruwan Mama (Nono)
A sami furen zogale a dafa
shi tare da zuma. Mace mai shayarwa ta rinƙa ci
sau uku a yini. Yin haka yana ƙara
yawan ruwan mama (Hayin Gulbi, 2015).
Ƙarin Nishaɗi
A sami zangarniyar zogale
tare da ‘ya’yan da suke ciki, a haɗa da
kanumfari da citta da masoro da kimba a dake su, har sai sun koma gari. A riƙa sakawa a cikin abinci ana ci. Yin irin
wannan haɗin yana ƙara
wa mata ni’ima da nishaɗi (Ruƙayya, 2015).
Ƙara Ni’imar Kwanciyar Aure
Mata ma’aurata suna iya
samun garin ganyen zogale su riƙa haɗa
shi da madara ko nono suna sha domin ƙarin
ni’imar kwanciyar aure da maigida. Amfani da wannan haɗin yana
ƙara sa mace ta ni’imtu, kwanciyar aure
da maigidanta ya yi armashi sosai har kuma a kwaɗaitu
da sake maimaitawa (Kande, 2015) da (Axe, 2016).
Sa
Maigida Sambatu
A haɗa saiwar zogale da saiwar kankana da kanunfari a dafa su. Idan sun
dafu, sai a tace ruwan.
Daga nan sai a nemi mazarƙwaila da zuma a zuba (saka) a cikin tataccen
ruwan, sai a sake ɗora su a kan wuta har sai sun dafu. Idan suka dafu, sai
a juye a rinƙa sha safe da yamma. Za
a ga mamaki. Wannan haɗin ya keɓanta
ga mata kawai (Kande, 2015).
Rage
Ƙiba
A nemo ganyen zogale, a
tsabtace shi, a tafasa a rinƙa
shan ruwan kullum. Insha Allah za a yi mamaki (Godinez, 2015). Haka kuma, ana
iya haɗiyar ‘ya’yan zogale guda biyu (2)
kowace rana. Shi ma yana rage ƙiba da yardar Ubangiji.
Ƙarin Ni’ima Da Kuzari Ga Maza
A nemo furen zogale tare da
‘ya’yanta, sai a shanya su cikin inuwa har su bushe. Daga nan za a haɗa da
dabino a dake su har su zama gari. Garin za a rinƙa
zubawa a nono ko madarar Peak ana sha. Wannan haɗin
yana ƙara wa namiji yawan ruwan maniyyi da
kuzari. Ana yi wa haɗin laƙabi da karya gado saboda
ingancinsa (Hayin Gulbi, 2015).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.