Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Magunguna Daga Zogale: Tsakuwar Ciki (Appendis), Tsutsar Ciki, Bugun Aljani

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Tsakuwar Ciki (Appendis)

A sami saiwar zogale a gama da ‘ya’yan kankana a dake su har su zama gari. Garin za a rinƙa zubawa a nono ana sha. Insha Allah za a sami lafiya (Hayin Gulbi, 2015).

Tsutsar Ciki

Idan yaro yana fama da tsutsar ciki, sai a sami ɗanyen ganyen zogale, a wanke a ba mai fama da lalurar ya ci, sau biyu a rana (Hayin Gulbi, 2015).

Maganin Bugun Aljani

Idan aljani ya bugi mutum har ya faɗi, sai a sami garin zogale a shaƙa masa a hanci. Zai yi saurin sakin sa. Wani zubin ma aljanin yakan yi magana (Hayin Gulbi, 2015). 

Post a Comment

0 Comments