Takardar da aka Gabatar a Jami’ar Jihar Bauchi, Itas Gadau, 2019
ZALƁE MAZAN KASADA: TSOKACI A
KAN ƊABI’AR KWARTANCI JIYA DA YAU
NA
Dr. MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD
SASHEN HARSUNA
JAMI’AR SULE LAMIƊO, JIHAR JIGAWA
TSAKURE
Wannan muƙalar zata yi magana ne a
kan harkar kwartanci. Da farko za’a dubi ma’anar kwartanci da kuma wane ne
kwarto, kuma wace ce farka? Bayan wannan za’a dubi bambancin kwartanci da shige
da fyaɗe. haka kuma za’a duba
matsayinsa a al’adar Bahaushe jiya da yau. Da dalilan da suka sauya masa
matsayi, da kuma yawaitan aukuwarsa a wurare sababbi waɗanda suke saɓanin wuraren da. Bayan haka
kuma, za a dubi jiwayen kwartanci a adabin Bahaushe na baka da kuma rubutacce.
Gabatarwa
Wannan takardar na da ƙudurin yin nazarin ɗabi’ar kwartanci a Ƙasar Hausa jiya da yau.
Za’a dubi wannan mummunar ɗabi’ar ta fuska biyu
tarihin wanzuwarta tun zamani mai tsawo. Duk da
yake Bahaushe ba ya ƙaunar kwartanci, amma da
yake ɗabi’ar
wasu mutane ce, wannan ta sa har yanzu ba a daina aikata wa ba. Al’ada ta yi
tir da masu yi maza da mata, addinin musulunci ya yi hani har da hukuncin kisa
ga wanda aka kama tare da shaidu, amma dai masu yi ba su bari ba. Tun zamanin
da ana ganin cewar kai bai waye ba ake aikata kwartanci, haka kuma har yanzu
ana aikata shi. Wani abin haushi da kuma mamaki, a yau wannan harka ta
kwartanci maimakon ta ragu, sai ƙaruwa ta yi.
Bugu da ƙari maimakon da zamani ya
ci gaba kuma ake cewa kai ya waye sai ma abin ya ƙaru. Babu shakka harkar kwartanci a yau faɗaɗa ta yi maimakon raguwa,
domin wasu sababbin hanyoyi da zamani ya zo da su mutanen zamani kuma
suka ɗauka suke
tafka ɓarna
a ɓoye. Duk
mai sauraren kafafen watsa labarai na rediyo da talabijin da jaridu yana jin
faruwar hakan.
MA’ANAR KWARTO:
Ƙamusun Hausa B. UK (2006). Mutumin da yake neman matar aure .
Advanced Learners Dictionary (2009)Wani mutum mai aure ya yi aure ya zina da
wadda ba matarsa ba)
MA’ANAR KWARTANCI.
Kwartanci na nufin mutum ya nemi matar aure da nufin ya yi
zina da ita. sai dai ana yi da yardarta ko amincewar ta. kwartanci ya saɓa wa shige da fyaɗe, saboda su ba tare da
yarda ake yin su ba. namiji mai yin wannan mummunan aiki a kan kira shi da
kwarto, ita kuma matar a kan kira ta da farka.
Wata mummunar ɗabi’a ce ta neman mace mai aure watau mai miji da lalata, mai yin
wannan ɗabi’a ana
kiran shi da kwarto wanda daga nan ne Kalmar kwartanci ta samo asali. Kwarto
kan samu dama in har ya ga fuska, watau in har ya ga matar aure ya yi mata
magana, to in ya iske lalatacciya ce ‘yar uwarsa har ya yi nasara, to ya samu
fuska ke nan, amma in ya yi ƙoƙarin shi ba ta ma saurare shi ba, balle ma har ya yi nasara, to a
nan bai samu fuska ba.
Mace kan iya faɗawa haɗarin kwartanci tun daga yin aurenta na farko, watau dai ta na
amarya har ya zuwa tsufanta. Matuƙar dai ta na da miji watau
matar aure.
Bugu da ƙari wasu matan kan jefa kan
su cikin wannan muguwar ɗabi’a, saboda kwaɗayi na son abin duniya, matsananciyar sha’awar ɗa namiji, rashin kamun kai
da sauransu.
Akwai wasu lokutta da kwartanci yafi aukuwa, misali idan
miji ya yi tafiya ko dare ko kuma da damina. Akan samu yin kwartanci mafi yawa
in miji ya yi tafiya, watau dai ba ya nan, daga nan ne in har matar lalatacciya
ce sai su shirya a inda zasu haɗu ko lokacin da zasu haɗu.
Kwarto yafi yin amfani da duhun dare don gudun tonon asiri, ko da
yake akwai masu yin kwartanci haka nan don sha’awa ta taso musu, ko kuma sun
samu fuska. To amma kuma, akwai waɗanda suke mayar da ita kamar sana’ar su ke nan, don har akwai masu
yin asiri(ƙifif, bit-zaizai, bi-ni kamar kare) don kawai kar a tona su ko
kuma su rinƙa yin nasara a kowanne lokaci. A wani lokaci kuma wasu kwartaye
kan yi amfani da lokacin damina watau don ƙatancin
jama’a saboda tafiya aikin gona, in babu kowa watau maza ba su a gidan, sai su
yi amfani da dammar yin nufin su.
A ƙarshe, kwarto kan yi amfani
da wasu hanyoyi don jawo ra’ayin mace don yin amfani da ita misali: -
1) Kyauta mara dalili.
2) Nuna sani na ƙarya.
3) Amfani da asiri.
4) Yaudara.
5) Samun fuska.
6) Gyaran murya.
HARKAR KWARTANCI A JIYA.
‘’ABIN JIYA YA DAWO’’
Tarihi ya nuna ko zamanin
da, kwartanci bai aukuwa a mafi yawan lokuta, sai dai don kwaɗayi da hawa dokin zuciyadaga kowane ɓangare. Misali ta ɓangaren mace, sau da yawa kwarto ya fi samun fuska a
wajen mace,s maui kwaɗayi ta inda har zai shawo
kanta har su daidaita a ajiye mahaɗa watau inda za su haɗu, ta hanyar fara yi mata kyauta. Wannan kwaɗayi na iya zama na abin duniya kamar kuɗi ko kuma na nama, wasu matan da tsire kawai
kwarta na iya yaudararsu har ya same su. Ko da yake akwai wasu kwartayen masu
yin amfani da sihiri kamar maganin kifuil, ko bi-ta-zai-zai.
Ta ɓangarebn maza su kuma kwaɗayi na hsa’awa ke jefa su zuwa kwartanci ta
inda suke bin son zuciya, saboda wasu mazan ko matar maƙwabtansu ba ta tsira ba, ko
da kuwa suna da mata nawa ne, sannan kuma komai ƙuruciyar matar ko kyawonsu
duk bai dame su ba.
TASIRIN ZAMANI A
HARAKAR KWARTANCI
Kamar yadda aka sani
zamani bai bar komai ba, ta fuskar kawo sauye-sauye ko wane iri kuma
komai ƙanƙantar sa. To haka shi ma harakar kwartanci ba ta tsira
ba, saboda kakwai wasu baƙin abubuwa da suka ƙara kawo yawaitar kwartanci
kamar kwaɗayi, son abin duniya,
hanyoyin tayar da sha’awa, yawaitar cuɗanyar mata da maza, bayyanar ci-gaban zamanui na
na’urori, wuraren shaƙatawa, hotaloli da sauransu
Zamani ya kawo wasu baƙin hanyoyi na motsa ko
tayar da sha’awa kamar nuna tsiraici ta inda wasu mata kan yi yawo kusan rabin
jikinsu tsirara da musulmai da waɗanda ba musulman ba, ‘yan
mata da zawarawa, da matan aure. Ta inda
waɗannan
mata sukan jawo hankalin wasu mazaje ta inda in aka iske mara kamun kai sai
kwartranci ya auku.
Bayan wannan kuma sai kallace kallace na na’urorin zamani
irirn su talabijin, da bidiyo, da sidi, ko hotuna na littattafai ko mujallau,
ko wayar hannu yanar gizo da sauransu. Dukkan waɗannan abubuwa sukan taimaka ɓarna ta auku.
Dangane da yawaitar cuɗanyar maza da mata, zamani ya buɗe ko kawo kafafe inda maza da mata sukan yi cuɗanya da juna ta fuskoki da
yawa kamar kasuwanni, da ofisoshi na gwamnati, da kamfanoni, ko masana’antu,
sannan ga kuma gidajen haya, da wuraren sana’a, wajen hulɗa ko koyon sana’ar. Zamani
ya kawo ƙawance ko aminci tsakanin matar aure da wani ƙato namiji wai shi abokin karatu ko abokiun aiki.
Ci gaban zamani da ake iƙirari a
yuanzu ya kawo wai wayewar da yanzu mafi yawan mazaje ba sa kishin matansu na
aure, wai ai an yi ilimi kai ya waye sai mutum ya ji ko ya gani matarsa na yin
hulɗa
da ƙawance ko aminci ko abin arziƙi da wani namiji da babu
dangin iya babu na baba, sai dai kawai wai suna ma’aikata ɗaya, ko sun yi karatun tare
ko suna ciniki tare. Sannan wasu daga cikin matan nan basu da kamun kai, wai
don suna ilimi.
Wasu matan kuwa ganin suke kuwa ai suna da ‘yanci don haka
babu mai takura masu, don nuna isa sai ka ga suna yin abin da suka ga dama.
Ban da wannan kuma tsarin zaman gidan haya shi kanshi zamani
bai bar shi ba don ya kawo baƙin abubuwa na ƙyama da dama. Haka su ma barori (‘yan aiki, da masu reno) masu yin
aiki a gidajen masu hali da sauransu nan ba ba a tsira ba.
Wani babban ci-gaban da aka samu kuma shi ne samuwar
na’urori ta inda wasu lalatattun mutane ke amfani da wayar hannu suke shirya
yadda zasu aiwatar da ɓarna cikin sirri, wani lokaci ma ko da mijin na kusa ana shirya
tsiya a tafi bain san abin da aka ƙulla ba.
Bayan wannan kuma akwai masu amfani da motar hawa wajen
yaudarar mata ta hanyar yi musu ƙarya ko fakewa da cewa zasu
taimaka musu su rage musu hanya watau (lift), ko kuma direbobin motocin haya
manya da ƙanana ba inda ba a samun irinsu.
Haka kuma akwai masu amfani da komfuta da yanar gizo-gizo
don shirya ɓarna.
Akwai masu fakewa da wuraren shaƙatawa su shirya kwartanci.
Akwai amsu amfani da hotaloli don aikata kwartanci ta inda
sukan shirya mahaɗa a can a kan haɗu.
Akwai masu amfani da gidajen saukar baƙi (guest house).
Akwai masu shirya tsiyar da za ‘a yi a waje a gama a dawo
gida miji bai sani ba.
Baƙin al’adu da muka ara daga
wasu al’ummmomi sun bayar da ƙofa na faruwar kwartanci
kamar rashin kishi da aka yi maganarsa a baya, muna iya cewa tuiranci ya kawo
mana shi domin kuwa bature bashi da kishin matarsa gaba ɗaya, misali abokin miji zai
shiga gidan aboki ko baya nan yayi abin da ya ga dama ko kuma su fita da matar
aboki. Ko kuma\ ita matar ta fita da abokin aikinta ko abokin karatu shi miji
bai damu ba.
Bayan wannan, hatta zuwa kasuwa yin cefane da mata ke yi
zamani ya kawo shi, sai ka iske mata ke zuwa cefane yanzu a kasuwanni, to anan
abin tsoro shi ne saurin sabo tsakanin matan da ‘yan kasuwa.
Kwartanci karuwanci shige da fyaɗe, kushille da maɗigo. Dukkan waɗannan ayyuka sun samo asali
ne daga maguzanci amma har yanzu akwai masu yinsu a cikin al’umma, wani abin
lalacewa ma har ƙara ƙawata shi suke yi, watau an zamannatar da shi.
Dangane da kamanni ko kusanci da juna ana iya cewa kwaratanci ya
yi kama da ko kusanci da karuwanci, ko da yake akwai ɗan bambanci, kamar
kwartanci mutum ne zai nemi matar aure mai miji amma tare da yardarta sannan
kuma da yarjejeniya da kuma wani hasafi ko kyauta, shi ma karuwanci mace ce
babba za ta kama ɗakin haya tana jiran wani namiji ya zo shi ma akwai yarjejeniya na
lokaci da ciniki sannan kuma duk ana matar da take da kwarto cewa kwartuwa ko
farka, to ita ma karuwa ana kiranta karuwa ko dadaro ko farkar wane.
A ƙarshe muna iya cvewa akwai
wasu abubuwa da ke kawo kwartanci da suke laifin miji ko laifin mata, maƙwabta har da ƙawaye. A wani lokaci akan
samu aukuwarsane a dalilin sakacin miji wajen lura ko sauke nauyin da ya rataya
a wuyansu kamar buƙatun yau da kullum da buƙatuwa ta sha’awa
(kwanciya).
DALILAN DA KAN JAWO FYAƊE
Akwai wasu dalilai da kan
jawo aikata fyaɗe kamar kaɗaicewa da mace da namiji, bayyanar tsiraici ko yawaita maganganun
banza tasowar mummunar sha’awa daga juna a dalilin yawaita dogon kallo, ko
doguwar hira, kusantar juna da sauransu.
A ɗabi’ance ko ba a ma yi maganar shari’a ba, kaɗaicewar mace da namiji yana
da haɗari don
ba zai yiwu a keɓe mace da namiji a ce shaiɗan bai zo ba don zai dinga jefa ma ɗaya daga ciki mugun tunani
har sai ya haɗa wani mummunan aiki a tskaninsu, musamman da dare kuma ace ace
da ƙuruciya.
Bayan waɗannan kuma akwai yawaita maganganun banza kamar batsa da dai
kalmomi da zasu iya motsa sha’awa idan ba a yi sa a ba sai ɓarna ta auku.
Wani babban sanadin fyaɗe shi ne tasawar ko bijirowar mummunar sha’awa daga ɗaya daga cikinsu mace ko
namiji wanda aka kasa danne zuciya watau sha’awar ta rinjayi ɗaya ya fita hayyacinsa ta
inda zai nuna buƙatarsa to a nan ne ma ake rarrabe fyaɗe da wanda ba shi ba in har
da yarda da amincewa ne aka sadu to ba fyaɗe ba ne, amma in har an yi amfani da ƙarfi ta hanyar nuna makami. Barazanar cutarwa ko halakarwa aka
sadu bisa tilasci, to ya zama fyaɗe.
SHIN WAI MATA KAWAI AKE YI WA FYAƊE KO SU MA SUNA YI WA MAZA?
Wannan wata tambayace babba kuma mai wuyar amsawa. A bisa ɗabi’a ta yau da
kullum an fi samun labarin wani namiji ya yi wa wata fyaɗe.
Wannan tambaya ba za a iya amsata ba sai an koma ga ma’anar
fyaɗe.
Fyaɗe na nufin mutum namiji ya faɗa wa mace ya neme ta da yin lalata ta hanyar amfani da ƙarfi ba tare da son ranta ba, ta hanyar amfani da makami, muƙami, matsayi don ya tsoratar da ita.
In kuwa wannan bayani ko ma’anar fyaɗe haka yake,to lallai su ma
maza skan auka a cikin irin wannan abu sai dai ba a cika bashi muhimmanci ba
ne.
Mutanen da kan auka cikin irin wannan haɗari sun haɗa da matasa da kan yi aiki
a ƙarƙashin manyan mutane, a gidaje ko a ofisoshi a inda wasu shugabanni
mata kan neme su su tilasta su, ko kuma matan shugabanni su neme su su tilasta
su.
KAƊAN DAGA CIKIN ABUBUWAN DA KAN JAWO HAKA.
Aukuwar wannan, kamar rashin tarbiya, rayuwar turawa, rashin
biya wa juna buƙata wajen kwanciya, yawaitar kaɗaicewa da sauran wasu dalilai da ban iya kawo su ba.
JIRWAYEN KWARTANCI A ADABIN BAKA
§ Kwarto da
wanzami-kasan na sani.
§ Kwarto
kurma- baka da gaskiya
§ Kwarto da
yaro- na baba na tiyiyi-na nna na tiyiyi
§ Kwarto da
kazar kwanci, wallahi maciji
§ Kwarto da
ya dafa gemu-nazo faɗama gayya
§ Kwarton
Daura-ayi duka amma banda kama suna
§ Kwarton kuma-wasane tun muna yara
§ Buzu da kwartanci-saɗaf-ɗinku-saɗaf
§ Kwarto a
gidan fulani-dingangauyshi ko ɗin
§ Kwarto
daga sama- daga saa aka aikoni
§ Liman da
kwartanci-inda liman yake na ake
§ Mai kuɗI kwarton maroƙi
§ Kwarton
uwa mai wuyar kamawa-a faɗa ka tona asirin uwa kayi shiru kaci amanar baba
§ Kwarto
uban kasada
§ Kwarto
kafi ɓarawo ban
haushi
§ Banza ta
kori wofi-kwarto ya kori kwarto
§ Kura ba
farkar kare bace
§ ArangaɗI maɗiso kwarto ya kayar da mai
mata
§ Kasan na sani-kasan na bari
§ Baka da gaskiya-kurma yaje kwartanci mai gida
ya dawo
§ Baka ce min ka dawo ?maƙwabci ya shiga kwartanci
§ Saɗaf-saɗaf masu gida buzu ya jE
kwarttanci.
JIRWAYEN KWARTANCI A RUBUTACCEN ADABI
1. An samu jirwayen kwartanci a Littafin Ruwan bagaja
“Ina yawo a kasuwa rannan ina tambayar labarin ruwan Bagaja sai
na ga wata yarinya, sai na ce mata zan aureta. Ashe tana da miji ba ta son sa
ne kawai na kirata muka shirya in zo yau da dare. Daren nan kuwa an yi ruwa
mijinta ya dawo ta hura masa wuta yana jin ɗumi yana ƙahon dandi. Ko da na zo sai na laɓe ina leƙensa. Ashe Malam Zulƙe yana gari shi ma ya
shirya da ita shi ma ya zo. Ka san shi sarkin lalata, sai kawai ya lallaɓo ya tura ni sai kwaram
mijin ya gan ni, ni kuwa na ce wallahi turo ni aka yi” [1]
2. An samu jirwayen kwartanci a Littafin Magana jari ce.
JIRWAYEN KWARTANCJI A WAƙOƙIN BAKA
1. An samu jirwayen kwartanci a waƙar Salmai
Albasu “maye kai ka ɗaki kirki ka hau gado”[2]
2. An samu jirwayen kwartanci a waƙar
Idi ɗan galma
“
3. An samu jirwayen kwartanci a waƙar
Kwarkwaro Ɗan sale
4. An samu jirwayen kwartanci a waƙar Sale
gambara bilbis
5. An samu jirwayen kwartanci a waƙar Garba
sufa “ina da mata ba zani bi matar yaronmu ba”
MATA MASU FUSKANTAR KWARTANCI
1. Matan fatake
2. Matan masu gadi
3. Matan marasa kamun kai
4. Matan Masu kwaɗayi da matsiyaciyar sha’awa
lokutan da aka fi samun
aukuwarsa
1. Lokacin zafi
2. Tafiyar mai gida
3. Damina.
Wuraran da aka fi samun aukuwarsa
Zaman gidan haya
Haƙiƙa zamani ya kawo wani sabon
yanayin zamantakewa wanda a zamnin da Bahaushe bai san da shi ba. A wannan
zamanin an samu ƙaruwar jama’a da kuma aikace-aikacen gwamnati da na
kamfanoni. Samuwar wannan ya sanya tilas sai wasu mujtane sun yi baƙonci a garinda ba nasu ba.
A wani lokaci kuma yawan jama’a ya sanya zaman gandu ba zai yiyu ba. Haka kuma
son cin gashin kai a yanzu kowa so yake ya zama ba’a gidan gado yake zaune ba.
Banda wannan kuma talauci da matsin rayuwa ya sanya ba kowa ne zai iya mallakar
gidan kansa ba.
Waɗannan dalilai su suka sanya aka ƙirƙiri gidan haya. Samuwar
gidan haya ya haifar da abubuwa masu yawa baƙi ga al’ummar Hausawa.
Zaman gidan haya wani zama ne na kazo-na nazo kowa na da ‘yanci kansa babu mai
yiwa wani iko ko tsawa saboda kowa haya yake biya. Haka kuma zaman gidan haya
iri-iri ne, akwai na yaka malam ko yaku bayi wato na talakawa marasa ƙarfi. A irin wannan zama sai a iske gida mai ɗakuna guda goma, ko fiye da
haka. Mutane masu haya a gidan wato ‘yan haya sai sukai mutane 7 ko 5 ko sama
da haka duk a gida ɗaya kuma kowa da matarsa.
A irin wannan zama akan yi rashin sa’a, wasu daga cikin ‘yan
haya a samu marasa tarbiyya, a inda za ‘a samu wani na miji yana neman matar
wani daga cikinsu, ma’ana dai kwartanci na gudana a gidan, a wani lokaci laifin
matar ne a wani lokaci kuma laifin mijinta ne.
‘yan aiki da iyayen gidansu
Zamani ya kawo wata sabuwar rayuwa ga Bahaushe. Bisa faruwar wani
sauyi da aka samu, saboda ci-gaba na zamani. Yanzu akwai gidajen ‘yan boko, ko
manyan ma’aikata da shugabanni da masu kuɗI a birane da ake sama musu masu yimujsu aikia gidajensu suna
biyansu a duk mako ko wata. Waɗannan masu aikin ko ‘yan aikin sukan haɗa maza da mata. Akwai yara
da manya wani lokacin ma arda tsofaffi. Dukkkan waɗannan mutanen babu wanda
baya faɗawa cikin
haɗarin
kwartanci. Kodayake abun kansha ban-ban daga wani zuwa wani. Domin akan samu
direbobi da masu wanki da guga da masu girki da masu raino.
Dangane da abubuwan da kan faru kuwa yakan saɓa daga gida zuwa gida.
Misali wasu ‘yan aikin musamman yara mata sukan fuskanci fyaɗe daga ‘ya’yan masu gidan
kokuma shi mai gidan kansa. A wani lokacin kuma ‘yan aiki maza kamar masu yin
wanki ko direbobi kan fuskanci matsalar nema tsakaninsu da uwar gidan m ai
gidansu. Akwai wasu matan maigida da suke tilastawa ‘yan aikin da su biya musu
buƙata ta sha’awa inkuma sunƙI a bakin aikinsu. O bisa
tsautsayi ko gudun karsu rasa aikinsu sai su cikata. A wani lokaci kuma ‘ya’yan masu gidan mata su
ne sukan tilasta ‘yan aikin gidan maza don su yi lalata da su.
Kwartanci a cikin kasuwa
A yau lalacewar al’umma
takai har a rumfuna ko kanti ko shaguna ake aikata keartanci. Duk kasuwa da ta
amsa kasuwa zai yi wuya a wannan zamanin a ce ba’a samu wasu ‘yan kasuwa ɓata gari ba da kan aikata kwartanci da matan
aure wasu da rana wasu kuwa suyi amfani da duhun dare.
Babban dalilin da kan
kawo wannan shima dai bai wuce kwaɗayi da rashin kamun kai duk
daga kowane ɓangare da maza ‘ytan
kasuwar har da mata ‘yan soyayya. Akan samu wasu mata marasa kunya, waɗanda in suka zo soyayya sai su dinga tsokanar
‘yan kasuwa maza da zancen banza ko batsa a kaikaice, wanda idan akayi rashin
sa’a suka iske lalatacce sai su shirya tsiya. A wani loakci garin neman sauƙi ko arha ko son banza
ma’ana a basu kyauta. A wani lokaci kuma ‘yan kasuwa maza ne kan fara tsokanar
mata masu sayayya da zancen banza ko batsa, idan sun tarra da lalatattun mata
sai su shirya abun tsiya.
Baya ga waɗannan rukunin kuma, sai mata masu sayar da
abinci a kasuwanni, musamman waɗanda sukan kai abinci
rumfa-rumfa ga ‘yan kasuwa maza. Wasu ‘yan kasuwa basu da tara ko marat aure ko
bazawara ko budurwa suka samu sudai su biya buƙata.
Kwartanci a tashoshin mota
Bahaushe ya ce ‘’tasha ta shashashai’’. Tasha wani wuri ne da yayi
kama da kasuwa, saidai akwai banbanci. Tashar mota wani wuri ne da zamani ya
kawo wanda yake da alaƙa da sufuri. A wani fuskar
kuma ana iya cewa tasha wata mahaɗa ce wanda al’umma kan haɗu don shiga mota. Ana iya cewa mutane iri huɗu ne a tasha, da farko
direbobi ne masu mota, sannan na biyu sai ‘yan kamasho (‘yan uniyon), na uku
kuwa su ne matafiya, na ƙarshe kuwa su ne ‘yan
kasuwa masu abin sayarwa don matafiya da sauran jama’a daga cikin masu kayan
sayarwa a kasuwa akwai maza da mata da yara a cikinsu akwai mutanen kirki da
mutanen banza. Bahaushe ya ce “wake ɗaya ke ɓata gari”.
Bugu da ƙari daga cikin rukunin waɗannan mutanen ake
samun ɓata gari
su rinƙa aikata ɓarna, wanda daga ciki har akan samu masu aikata kwartanci. Waɗansuma daga nan sukan faɗa harkar karuwanci.
Ba-za-to kwartanci a
shagon/zauren matsubbata
Bahaushe na cewa ana zaton
wuta a maƙera sai ta tashi a masaƙa’’. wannan abun mamaki ne
a ce wai ana samun wasu matsubbata (malaman tsibbu) suna aikata kwartanci a
wuraren da suke yin trsibbu. A inda sukan yi lalata da wasu matan auren, wasu
matan da son ransu wasu kuwa da ƙarfin sihiri.
Babu shakka wannan
abun sanennen abu ne a wanna zamanin da muke ciki. Dalili kuwa shi ne an sha
samun labarin faruwar hakan a garuruwa da dama a ƙasar Hausa, musamman ta
kafafen watsa labarai kamar su rediyo da talabijin da jaridu. Akwai waɗanda matan da kansu sukan faɗa malaman tsibbu sunyi lalata da su. Misali a
D. I. T. V. Kaduna, wani matsubbaci a unguwar sabon kawo ya kama shago a inda
ya yaudari wata mata wacce ta zo wajensa neman maganin da za ta koma gidan
mijinta, sai wannan malamin ya ce mata akwai laƙanin da zai ba ta, amma sai
a cinya za’a rubuta, sai ta amince cikin haka sai ɓarna ta auku, ya yi mata ciki daga nan sai ya gudu.
Jaridar aminiya inda wata
mata ƙawarta ta kai ta gidan wani matsubbaci don kar mijinta ya
yi mata kishiya a ƙarshe ya ce mata sai an haɗa da ruwan nononta ko da ta kasa tatso ruwan nonon, sai
ya ce mata shi zai iya. Ko da ta amince sai ya yi amfani da sihiri ya biya buƙatarsa, sannan ta fahimci
halakar da ta faɗa.
Jakar magori rediyo kaduna
a inda aka kama wani matsubbaci a sabon garin zaroya a inda ya yi lalata da ya
da ƙanwa da ‘yarta, saida ta kai an kulle shi a caji ofis na
‘yan sanda.
Ƙwaryar ƙira rediyo kano, inda wani
mutum ya yi kirari cewa ya tuba da yin tsibbu har ya ƙona kayayyakin tsibbu. Ya
bayyana yadda matsubbata kan aikata ɓarna da matan aure.
SABON SALON KWARTANCI A
OFISOSHI
“zamani mai juyi” a wannan
zamani kuwa wani juyin aka samu. Wannan juyin
kuwa shi ne hulɗa tsakanin maza da mata a matsayin abokan aiki, wato waɗanda ke aiki a ofishi ɗaya. Wannan kuwa ya haɗa ne tun daga ma’aikatan
gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu. Akwai inda za’a iske namiji da mace
a ofishi guda ɗaya ko kuma ɗaya na falo ɗaya na shirayi (uwar ɗaka). Haka kuma akan samu masu matsayi ɗaya, wasu kuma masu
mabambantan matakai wato na sama da ƙasa ko shugaba da mai
binsa.
Dangane da yadda akan samu aukuwar kwartanci a irin waɗannan wuraren kuwa yakan
bambanta. Akwai inda abokan aiki da matsayi guda kan nemi junansu, wannan kan
faru ne a dalilin rashin kamun kai da kuma kwaɗayi. A wani lokacin kuwa macen ce kan fara neman namiji idan ta ga
fuska, ko kuma shi namijin ya fara neman macen in ya ga fuska.
Bugu da ƙari bayan wannan yanayin
sai kuma irin yadda wasu shugabannin kan yi amfani da ofishinsu ko matsayi su
nemi na ƙasa da su wato mai aiki a ƙarƙashinsu, mace ko namiji. Wannan kan faru a inda shugaba na miji
kan nemi mace mai aiki a ƙarƙashinsa ko macen tra nemi namiji mai aiki a ƙarƙashinta
Tabbas
wannan abun sanannen abu ne kuma ya sha faruwa a wannan zamanin namu.
KAMMALAWA
A ƙarshe dai Wannan takardar ta yi bayanai a kan ɗabi’ar kwartanci da kuma shi kansa kwarton
a Ƙasar Hausa jiya da yau. Wannan mummunar ɗabi’ar an dubeta ne ta fuska biyu tarihin
wanzuwarta tun zamani mai tsawo da akan ce Bahaushe bai waye ba. Bayanai sun
gabata tare da nuna irin yadda Bahaushe ya ƙyamar kwartanci, amma da
yake ɗabi’ar wasu mutane ce,
wannan ta sa har yanzu ba a daina aikata wa ba. Al’ada ta yi tir da masu yi
maza da mata, addinin musulunci ya yi hani har da hukuncin kisa ga wanda aka
kama tare da shaidu, amma dai masu yi ba su bari ba. Tun zamanin da ana ganin cewar kai bai waye ba ake aikata
kwartanci, haka kuma har yanzu ana aikata shi. Wani abin haushi da kuma mamaki,
a yau wannan harka ta kwartanci maimakon ta ragu, sai ƙaruwa ta yi. Nazarin kuma fito hali da aka tsinci rayuwa a yau,
maimakon da zamani ya ci gaba kuma ake cewa kai ya waye, ɓarnar ta ragu, sai ma abin
ya ƙaru da sababbin salo. Babu shakka harkar kwartanci a yau faɗaɗa ta yi maimakon raguwa,
domin wasu sababbin hanyoyi da zamani ya zo da su mutanen zamani kuma
suka ɗauka suke
tafka ɓarna
a ɓoye.
MANAZARTA
Alhassan H. D. (1982) Zaman Hausawa. Islamic Publication Bureau,
Lagos.
Bunza A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere,Lagos.
Banbale M. B. (1994) Kukan Kurciya. Ibramud Nigeria Limited,Zaria.
Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga
rayuwar Hausawa. Triunph Publication Kano.
Ɗan Gambo A. (1983) Kitsen Rogo. Triumph Publication Kano.
Ɗanjuma U. (1983) Kulɓa na ɓarna. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.
Daura S. A. (1971) Tauraruwar Hamada. Northern Nigerian
Publication Company, Zaria.
Imam A. (1937) Magana Jar ice 1,2,3. Northern Nigerian Publication
Company, Zaria.
Ingawa A. (1970) Iliya Ɗan Mai ƙarfi. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.
Imam A. (1939) Ruwan Bagaja. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.
[1] Dubi Littafin Ruwan Bagaja Abubakar Imam
1937
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.