𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam, mene ne hukuncin cin kuɗin haram alhali mutum ya san cewa wanda ya ba shi kuɗin ya same su ne ta hanyar haram? Ina yi wa malam fatan alheri.
HUKUNCIN CIN KUƊIN HARAM
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa
rahmatullahi wa barakatuh.
Idan mutum ya san
tabbatacce cewa kuɗin da aka bashi an
samo su ne ta hanyar haram, to hukuncin karɓarsu ya danganta da dalilin da aka bashi.
Idan an bashi kuɗin ne a matsayin lada,
kyauta ko taimako daga dukiyar haram da aka sani, malamai da yawa sun ce ya
kamata ya guje musu saboda hakan yana taimakawa wajen cin haram.
Amma idan kuɗin an bashi ne a
matsayin biyan haƙƙinsa, kamar albashi, bashin da ake binsa ko
kuɗin kayan da ya sayar,
to ya halatta ya karɓi haƙƙinsa, domin zunubin
haramcin yana kan wanda ya samo kuɗin ta haramtacciyar hanya. Haka kuma idan ba
a san tabbas kuɗin haram ba ne, sai
dai zato kawai, to ba a haramta karɓarsu saboda zato.
Saboda haka, abinda
yafj dacewa ga Mutun shi ne ya nisanci abinda yake da shakku, yaci abinda yake
halal kuma mai tsarki, domin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce:
"Ka bar abin da yake sa ka shiga shakka zuwa abinda baya saka shiga
shakka. Allah yasa mudace
Manzon Allah
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Duk wani jikin da aka ciyar da
abincin haram ko ya ginu daga haram, ba zai shiga aljanna ba. wuta ce tafi
cancanta (ko mafi dacewa) da shi."
An rawaito makamancin
wannan fadi daga sahabai kamar Ka'ab bin Ujrah, Abu Bakr As-Siddik, da Jabir
bin Abdullahi (Allah ya yarda da su), kuma Imam Tirmidhi da sauran malaman hadisi
sun rawaito shi, inda Albani ya inganta shi. Kalmar "Suhut" (السحت) a cikin
hadisin tana nufin dukiya ko abinci na haram (kamar riba, sata, cin hanci, ko
zalunci).
An ruwaito Hadisi
daga Sahabi Ka'ab bin Ujrah (RA). Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya
ce wa Ka'ab: "Ya Ka'ab bin Ujrah! Sallah garkuwa ce, kuma sadaka tana
shafa zunubi, azumi kuma garkuwa ce. Jikin da bai tashi da halal ba, wuta ce ta
fi dacewa da shi."
A wani hadisin kuma
da ya zo daga Jabir bin Abdillah (RA), Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya
ce: "Ba zai shiga Aljanna ba wani jiki da aka ciyar da haram; wuta ce ta
fi dacewa da shi." (Imam Ahmad da Abu Ya'la da Al-Albani sun inganta shi a
Sahihul Jami').
Ma'anar Hadisin Ciyar
da Haram: Yana nufin cin abinci ko amfani da kuɗin da aka samu ta hanyar da ba ta dace
ba a muslunci. Misalai sun haɗa da cin kudin riba, kuɗin sata, da cin hanci, da kudin da aka
samu ta hanyar damfara. Wannan gargadi ne mai tsauri ga musulmi kan muhimmancin
neman na halak da kuma nisantar haram ko da kaɗan ne.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.