𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, barka da warahaka. Allah ya ƙara maka lafiya, ameen. Tambayata ita ce: Malam, shin ya halatta in bi sallar jama'a a masallacin da ke maƙale da ɗakina a matsayina na mace? Ina jin kiran salla ko ba abun magana (iƙama). Sannan ina bin su sallolin farilla guda biyar (5). Idan Ramadan ya zo, shi ma ina bin su sallar tara rawih (qiymul layl) da tahajjud. Malam, ya matsayin sallata yake? Malam, na ci gaba da bin su ne ko kuma in riƙa yin tawa daban? Na gode malam, Allah ya ƙara lafiya da basira, ameen.
HUKUNCIN MACE TA BI
SALLAR JAM'I DAGA ƊAKINTA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Ya hallata mace ta bi
sallah tare da liman a masallaci tana a cikin ɗakinta da ke manne da masallacin. amma
mafifici da mafi aiki ga mace shi ne ta yi sallah a cikin ɗakinta kawai ba tare
da ta bi mai sallah a masallaci ba.
Akwai saɓanin Malamai game da
wannan. Mafiya rinjayen maluma suna ganin cewa bai halatta ba, saboda yin hakan
ya saɓa wa sunnar Ma'aiki
(Sallallahu Alaihi Wasallam) wacce ta wajabta wa mazaje halartar jam'in sallah
a masallaci.
Wasu malaman suna
ganin karhancin yin haka. Wasu kuma sun ce za a iya yi idan akwai larurar jinya
wacce ta hana namiji halartar jam'in sallar a Masallaci.
Amma ita mace abinda
ya rataya da hakkinta shi ne ta yi sallarta ita kaɗai adakin mijinta shi
ne yafi daidai kuma yafi lada gareta fiye da yin sallah akowanne masallaci. Komai
kusancinta da masallaci kuwa. Wannan shi ne umurnin da Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ba wa mata.
Bin sallar jam'i daga
ɗaki ko gida yayin da
liman ke sallah a masallaci (ko ta hanyar lasifika) wannan masalar ta kasu
kashi biyu:
1. ldan ya zama ɗakinki yana like da
masallacin, to tabbas wannan ya Halatta Saboda NANA AISHA tabi sallar kisfewar
Rana daga ɗakinta. Azamanin
ANNABI (Sallallahu alaihi Wasallam) Kamar yadda BUKHARI ya ruwaito hakan A
hadisi mai lamba ta 184. Sannan ABDURRAZAK ya ruwaito cewa ta kanbi ragowar
salloli daga ɗakinta Kamar yadda ya
zo a littafinsa na MUSANNAFA a hadisi mai lamba ta 4883. Saboda ɗakinta ajikin
masallacin ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam) yake.
2. ldan ya zama ɗakin baya haɗe da masallacin, to
zance mafi lnganci shi ne Bai halattaba. Saboda azamanin ANNABI (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Sahabbai suna haɗuwa ne a wuri ɗaya ne idan za su yi sallar jam'i. ba sa
rarrabuwa, Wannan sai yake nuni cewa hakan shi ne siffar sallar jam'i, Sannan
jera sawu a sallah, wani na bin wani, dole ne a sallar jam'i.
Saboda haka Idan kina
jin kiran sallah ko karatun liman kuma kina da niya yiar bin sa, jam'in ki ya
tabbata. Amma Dole ki yi niya yiar bin liman a lokacin sallah. Kodayake akwai
saɓani a tsakanin
malamai kan cikar sallar idan bango ya raba gaba ɗaya, amma idan dakinki na like da
masallacin kuma babu wani babban katanga da ya hana ki jin motsi ko sanin halin
da ake ciki, to sallarki ta yi, kuma za ki samu ladan jam'i.
WALLAHU A ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.