Ticker

6/recent/ticker-posts

Dare Mai Ban Tsoro: Tsokaci A Kan Matsayin Dare Da Tasirinsa Ga Al’adar Bahaushe

DAGA

MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD Ph. D.
 Phone: 07030803404 Email muazusaadukudan299@gmail. com
SASHIN HARSUNA NIJERIYA
JAMI’AR SULE LAMIƊO, KAFIN HAUSA

Tsakure

Wannan nazari ya dubi dare da matsayinsa, da gudummowarsa, da tasirinsa a rayuwar Bahaushe. Darene lokacin gudanar da kusan dukkan harkoki na al’adun gargajiya wanda Bahaushe ya gada tun iyaye da kakanni. Manufar wannan bincike shi ne zaƙulo ko kawo bayanai tare da fito da rawar dadare yake takawa a yanayin zamantakewar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar dare tare da fagagen da dare ya kankane, dalilai, da tsawon lokacin da yakan ɗauka. Hanyoyin tattara bayanai sun haɗa d a adabin Bahaushe na baka da rubutacce, da hira jama’a. Na ɗora aikin a kan ra’in zahirancin A’adun Al’ummma. Sakamakon nazarin ya fito da irin yadda zamantakewar Bahaushe ta bai wa dare muhimmanci kusan kamar na abinci, kamar a wajen bikin aure, da haihuwa, da sana’a, da magani, da sauransu. Haka kuma za a kalli irin yadda Hausawa kan yi kasuwancin dare a tsakaninsu a wasu wuraren. Maƙalar zata kawo jirwayen dare a adabin Bahaushe na baka da rubutacce wato na zamani, daga ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

1.0. Gabatarwa.

Al’ummar Hausawa sun taɓa kasancewa a wata irin rayuwa ta maguzanci, wato rayuwar da babu wani addini saukakke daga wurin Allahu (S. W. T) da Ya aiko wani Manzo don ya kawo wa bayin Sa. Gaba ɗaya rayuwar maguzanci, ta dogara ne ga tsare-tsare ko dokokin gargajiya, watau dai Hausawa sun kasance suna bin addinin gargajiya watau maguzanci, don haka ake kiran mabiyansa maguzawa. Wannan rayuwa ta gudana a zamani mai tsawo kafin zuwan Addinin Musulunci. Muhammad()

 Hausawa sun karɓi Addinin Musulunci tun a ƙarni na goma ko na sha ɗaya 10thor 11thCentury, kamar yadda masana tarihi suka bayyana. Akwai masu cewa addinin Musulunci ya shigo ne daga daular Borno, wasu kuma suka ce daga daular Mali. Wangarawa suka kawo, wasu suka ce masu fatauci, fatake masu cinikin ƙetare Hamada, da dai sauran bayanai damasana tarihi suka yi daban-daban. ()

Al’ada na nufin wata hanya ce, wadda wasu al’umma suka ɗaukar wa kansu da suke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum. Wadda suka yarda da ita kuma suka yi imani da ita. ()Al’ada ta ƙunshi duk wata harka ta rayuwa, tun daga addini, da shugabanci, da abinci, da makwanci wato muhalli, da bukukuwa, da tufafi, da magunguna da sauransu().

1. 1Manufar wannan bincike: shi ne, tattaro ko kawo bayanai a kan matsayin dare, da gudummowarsa, da tasirinsa a rayuwar Bahaushe. Takada ta kawo ma’anar dare, da fagagen da dare ya mamaye, tare da gano irin shaƙuwar da Bahaushe ya yi da dare ta yadda har bai iya gudanar da wasu abubuwa na rayuwarsa sai da dare.

Bugu da ƙari wannan nazari ya ƙara fito da muhimmancin dare a tunanin Bahaushe. Bayan wannan kuma, nazarin ya ƙara nuna muhmmancin dare a fagen magani da na tattalin arziki a rayuwar Bahaushe. Hanyoyin da na tattara bayanai sun haɗa d a adabin Bahaushe na baka da rubutacce, da hira jama’a. Na ɗora aikin a kan ra’in zahirancin A’adun Al’ummma. Sakamakon nazarin ya fito da irin yadda zamantakewar Bahaushe ta bai wa dare muhimmanci kusan kamar na abinci, kamar a wajen bikin aure, da haihuwa, da sana’a, da magani, da sauransu. An kuma ƙara fito da tsoro, da irin girmamawar da ake yiwa dare a Bahaushiyar al’ada. A ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

1. 1. Ma’anar Dare:

 Dangane da ma’anar dare kusan baki ya zo ɗaya sai ɗan abin daba a rasa ba, saboda Masana da dama sun bayar da ma’anar dare a matsayin; CNHN(2006: 98). wani lokaci ne mai duhu da yake biyowa bayan faɗuwar rana. Shi kuma Abubakar (2015: shf: 98),ya kawo cewa dare lokacin duhu ne a tsawon rana daga faɗuwar rana zuwa goshin asuba. Bargery (2015) ya bayyana dare a matsayin abin da ya fara daga faɗuwar rana da shigar duhu har zuwahudowar alfijir na safiya.

Bisa la’akari da bayanan masana magabata, ana iya cewa dare wani lokaci ne wanda yakan zo bayan rana ta faɗi. Kuma, a lokacin ne duhu kan fara. A lokacin dare ne, wata kan yi haske kuma taurari kan haska sama.

 Haƙiƙa lokacin dare wani lokaci ne babba kuma mai muhimmanci ga rayuwar Bahaushe. Dalilin da yasa haka kuma shi ne, kusan duk wani abu da Bahaushe zai gudanar, sai an samu tasirin dare a ciki. Wannan kuwa ya haɗa ne tun daga bautarsa tun kafin zuwan musulunci wato tun a lokacin maguzanci. Bahaushe yakan gudanar da wasu hidimomi da suka shafi abubuwan bauta kamar camfe-camfen Bahaushe. Bayan haka an samu jirwayensa a maganganun azanci, kamar karin maganganu da waƙoƙin baka da na rubutattu().

Bugu da ƙari, ana iya ganin tasirin dare a rayuwar Bahaushe tun daga bukukuwansa, da sana’o’insa, da maganganunsa. Haka kuma Bahaushe yakan yi amfani da dare wajen aiwatar da wasu ayyuka marasa kyau, kamar na ɓarna, don haka ne ma yakan ce “Dare rigar mugu”(). Da yawa an fi samun aukuwar laifuffuka da dare, misali, ɓarayi sun fi yin sata da dare kamar inda Alhaji Mamman Shata Katsina kan ce:

 Jagora: Iyalan Mamman,

waɗandaba su son a yi haske,

sun fi son a zabga duhu,

da ruwa yaf-yaf.

 Amshi: Haka nan ne,

 Ƙanin Idi wan Yelwa.

2. 0 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

Hanyoyin tattara bayanai sun haɗa da adabin Bahaushe na baka da rubutacce, da hira jama’a. A dalilin haka ya sa a kan ce fatakan dare. A bisa dalilin baiwa dare muhimmanci da Bahaushe ya yi, shi ya sa har dabbobi, da tsuntsaye da ƙwari, sai da ya yi nazarinsu kuma ya ware waɗanda suka fi yin harkokinsu da dare shi ne sai ya kirasu da mabi-dare. Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙar Umaru Ɗanɗanduna Na Gwandu yace:

Kura mabi dare,

 Umarun gidan Ɗanduna

Umaru Ɗanɗanduna Na Gwandu.

Shi kuwa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a waƙarsa ta Ɗanmaliki Umaru Sadauki yana cewa:

Kura mai yawon tsakad dare

 Tayo yaucin babu nama

hankalinta duk yaɓaci,

ta koma gida tanabaƙin rai.

Ɗanmaliki Umaru Sadauki

Kana da wuyar karo na Malam.

3. 0 Ra’in Bincike

Na ɗora wannan aikinbincike a kan ra’in zahirancin A’adun Al’ummma.

4. 0. Matsayin Dare da Tasirnsa ga Al’ummar Hausawa

Dare a mahangar al’ada, ana iya cewa wani lokaci ne mai mahimmanci matuƙa. Wannan yasa gaba ɗaya al’adar Bahaushe ta girmamashi ta hanyar gudanar da wasu harkoki da dare, sannan kuma ta ƙyamaci yin wasu da dare. A mafi yawan lokuta, hatta yin mu’amala dake bukatar sirri, an fi yi da dare. Duk da haka kuma, al’adar Bahaushe ta camfa dare, shi yasa wasu ayyuka ba a son yi da dare, ko kuma wurare baa son zuwa da dare saboda gudun kar zuwan ya haifar da mummunan sakamako. Bisa dalilin cewa dare rigar mugu ce, Bahausheya yi imanin cewa akan iya gamuwa da mugayen mutane, ko iskoki, ko dabbobi, da ƙwari da sauransu a lokacin dare. Haka kuma an camfa yawon dare don gudun kar a gamu dafatalwa().

Bisa al’adar Bahaushe, akan fifita dare ta fuskar bauta, wannan kuma ya haɗa da addinin gargajiya har da na musulunci. Ana iya ganin hujjar haka a cikin Littafin Habibu A. Sarki (2000) zuwan musulunci Afrika da shigowarsa Ƙasar Hausa. da ya bayyana cewa: a lokacin mulkin Barbushe a farfajiyar dutsen Dala ta Kano. Kamar haka:

“Daga cikin ire-iren bautar waɗannan maguzawa da akwai bikin cikar shekara. Dukkansu sukan taru a kan dutsen dala, su kewaye bukkar tsunburbura su tuɓe tsirara su kwana bauta. Su yanyanka baƙaƙen karnuka da bunsura. Daga nan sai Barbushe ya yi wa tsurburbura kirari ya ce: “jamuna a kasa mun gama (karagaya laya tsunburbura). Sauran maguzawa su amsa masa da cewa:

 “ga tsunburbura Kanawa ga Magajin Dala”. [1]

Kamar a addinin musulunci ana keɓe lokutan dare musamman ga tsayuwar dare(ƙiyamul laili), da wurudi da sauran ibadu. Akwai wata Karin Magana mai cewa ba faɗa da malami ke tsoro ba tsakad dare ke tsoro, wato ana tsoron kar malam ya tashi da dare ya zauna kan buzu ya ya yi masa addu’a.

Bahaushe ya ɗauki dare a matsayin wani lokaci ne na yaƙartalauci ko na neman arziki, da neman suna ko ɗaukaka. Domin tun a zamanin maguzanci akan yi wankan mararraba don a yi kuɗi, haka kuma da Bahaushe ya karɓi addinin musulunci sai aka samu addu’o’i na neman arziki, kamar karanta suratul waƙi’a tana korar talauci. Ban da wannan kuma akwai wurudin rauhanai wanda malaman tsubbu ke aiwatar wa har akan ce: wane ya dace. Kuma akan ce Yaro ɓata hankalin dare kayi suna(ɗaukaka).

Ban da wannan, samari da ‘yammata kan yi zancen samartaka a tsakaninsu shi ma da dare, mafi yawa an fi zuwa gidan su budurwa, amma akan haɗu a dandali shi ma da dare.

4. 2. DareA Matsayin Sutura:

 Bahaushe ya ɗauki dare a matsayin wata sutura ce da take lulluɓe sirrin mutum. A mafi yawan lokuta wasu abubuwa na sirri an fi yinsu da dare. Bahaushe ya fi samun natsuwa da dare,saboda duhun da kuma ƙarancin idanu jama’a domin har a kan ce a bari sai sawu ya ɗauke can talatainin dare sannan a yi abu kaza. Bisa dalilin kunya Bahaushe ya keɓe dare wajen kwanciya da iyali, wannan kan ba shi damar sakewa saboda yara sun yi barci, kuma maƙwabta sun yi barci. Bisa wannan dalili ne yasa al’adar Bahaushe ta yi hani idan an ji mata da miji na faɗa da dare to ba a zuwa rabo().

 Bahaushe kan yi amfani da lokacin dare don yin wasu tarurruka na tattaunawa a tsakanin manyan mutane. Alal misalineman aure, a wajen neman akan kai sallama ko neman izini, da kai sadaki duk da dare. Haka ma sulhu a tsakanin ma’aurata kamar biko idan mace ta yi yaji. Bugu da ƙari hatta yin sulhu a tsakanin mutane abokai ko maƙwabta mafi yawa an fi yinsa da dare.

Baya ga wannan kuma, a yanzu a wannan zamani ‘yan siyasa sun fi amfani da lokacin dare wajen tarurrukansu. Haka kuma, hatta jami’an tsaro sun fi yin amfani da dare wajen kama masu laifi. A kan yi bincike da sauran tsare-tsare na gano masu laifi da rana, amma an fi kai samame da dare don kamasu.

4. 3. Dare A Matsayin abin Tsoro

Ma’anar Tsoro

 Babu shakka Bahaushe na tsoron dare ko yin wasu harkokinsa da dare. Wannan kuwa ba ya rasa alaƙa da yanayin duhu da kuma kasancewar dare rigar mugu. Tun daga mutane da iskoki (Aljannu) da dabbobi, da tsuntsaye da ƙwari duk sun fi cutarwa da dare, saboda fakewa da duhu.

 Bayan haka, Bahaushe ya yi wasu dabaru na rage ko sauƙaƙa duhu da dare ke ƙunshe da shi ta hanyar ƙirƙirar fitilar alaƙa, zuwa aci balbal, har kuma Bature da ci-gaban zamani ya kawo masa fitilar ƙwai, da cocila, da lantarki don samar da haske. Tabbas haske da dare yana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da sauran harkoki da suka rage daga harkokin rana.

Ba wai amfani da fitila kamar wani labarin makaho mai fitila………Littafin Ƙaramin sani. Ba mutum ba hatta dabbobi kan bai wa haske wani irin kulawa wannan yasa maharba kan yi amfani da fitilar goshi.

 Bugu da ƙari, Bahaushe na tsoron dare shi yasa ya ƙyamaci fitar dare don yin fitsari ko kasha. Bisa wannan dalili ne yasa Bahaushe ya ƙirƙiri kaskon fitsari, saboda taƙaita fitar dare. Wannan dalili ne ya haifar da wata karinmagana mai cewa. “In ka ji rakani kasha ba zawo ba ne”. Ko “Ƙanƙanta kamar kashin tsoro”. “Babu gara ga kashi, da na dare da na rana duk wari garesu”. ()

4. 4. Tasirin Dare a Wasu Sana’o’in Bahaushe

Ma’anar Sana’a

 Akwai wasu sana’o’in Bahaushe da dama waɗanda an fi yinsu da dare. Akwai sana’ar kaɗin zare da matan Hausawa ke yi, a zamanin da, mafi yawa an fi yin wannan sana’a da dare. Haka kuma, akwai sana’ar saƙa da mata kan yi a ɗakinsu sun fi yi da dare. Sana’ar yin daddawa an fi yin dahuwar kalwa da dare ta kwana a kan wuta. Tsofaffin mata Hausawa sun fi yin harkokinsu da dare, kamar ɓarar gyaɗa wanda har sukan gayyaci ƙananan yara su tayasu ɓarar gyaɗar a inda su kuma suna yi masu tatsuniya. Haka kuma da dare ne suke sanya yara su taya su gyaran auduga, kamar cire angurya daga auduga().

 Bugu da ƙari, Bahaushe kan yi amfani da dare wajen rage wasu ayyukan da suka shafi sana’o’insa. Kamar sana’ar ɗinki akwai waɗanda kan yi da dare ko kuma su rage aikin da zasu yi gobe. Haka kuma Bahaushe kan yi sana’ar gadi da dare, sannan masunta ko kwarawa kan tafi kogi su kwana a can don kamun kifi. Bayan wannan kuma sai maharba ko mafarauta masu zuwa daji da bindigar baushe ko kwari da baka da dare. Akwai kuma masu sana’ar ɗibar zuma, su ma waɗannan sun fi zuwa da dare. Kamar yadda wani marubucin waƙoƙin Hausa Alhaji Auwalu Isah Bungudu a waƙarsa ta Mulkin Satsi Yaudara ne, yace:

“Raggo ba zai sha zuma ba,

Baya cin naman maharba,

Don ya kashe ba zai iya ba,

Inda ba sammai a kai ba.

 Mulkin Satsi Yaudara ne,

 Ba cika alƙawari suke ba.

4. 5 Tasirin Dare A Wasannin Yaran Bahaushe

 Bisa nazari da aka yi, wanda ya nuna a sarari yadda dare yayi tasiri a rayuwar Bahaushe. Wannan bai bar yaran Hausawa ba, don kuwa ko a wasanni da yara kan gudanar mafi yawa da dare bayan sunci abincin dare, wato jibi. Sukan fito wasannin motsa jiki da dare a dandali musamman lokacin farin wata. Bayan wannan kuma yaran kan shirya wasan tashe da dare a watan azumi.

 Bugu da ƙari, Bahaushe ya shirya tare da tsara tatsuniya don yaransa, sannan kuma ba a yenta sai da dare. In kuma har ya zama dole sai an yi tatsuniya da rana to dole sai an ɗaure gizo don kar wanda ya yi tatsuniya da rana ya yi makuwa.

 Wasan Yara Maza Wasan Yara Mata (Gaɗa)

4. 6. Tasirin Dare A Magungunan Bahaushe

A mafi yawan lokuta, Bahaushe kan yi amfani da dare wajen aiwatar da maganinsa. A wani lokaci wajen ɗebowa, ko haɗawa, ko dafawa, ko amfani da maganin. Idan muka dubi masu magungunan Bahaushe, tun daga ‘yanbori, da magori, da ‘yarmaiganye, da sarkin mayu, da malaman tsibbu, da bokaye, kai tsaye ana iya cewa kowanne daga cikinsu ya bai wa dare muhimmanci, saboda babu wandaba ya bayar da magani kuma yace wani sai da dare za a yi amfani da shi ta hanyar sha, ko ci, ko ayi turare da garwashin wuta ko ayi wanka da ruwan maganin.

Wannan kuma ya shafi magani na neman waraka da na riga-kafi, da na cutarwa har da na neman suna ko ɗaukaka.

4. 7. Tasirin Dare A Tsafe-Tsafen Bahaushe

 A mafi yawan lokuta tsafe-tsafen da Bahaushe ya rinƙa yi kafin zuwan addinin musulunci da kuma bayan zuwan musulunci, an fi gudanar da shi da dare ne. Bautar tsumburbura a dala, da madara a madarkaci, da magiro a kwatarkwashi da mafi yawan hatsabibanci da ake yi an fi yi da dare. Ko daga baya da ake sauya wa gyambo ƙafa Bokaye da malaman tsubbu da mayu duk an fi yi da dare. Rawar maita, da harbin kasko, da wankan mararraba, duk da dare aka fi aiwatar da su. Duk wani samun da za a yi don a bunne shi ko juji ko suri ko marabar hanya ko kabari ko maƙabarta da dare ake yi.

Dare Rigar Mugu

 Bahaushe na amfani da Karin Magana ne a bisa dalilin cewa: A mafi yawan mugu ciki an fi aikatashi da dare ne. Kamar sata, fyaɗe, kwartanci, shige, maita, sammu, da sauransu.

 Sata: Kusan nau’o’in sata da ake da su da ta shiga ɗaki, da ta tare hanya da fizge, an fi yi aikatasu da dare.

Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙar ɗiyar Bayye yana cewa:

 Jagora: Iyalin Mamman,

waɗandaba su son ayi haske,

sun fi son a zabga duhu da ruwa ya-yaf.

 Amshi: Haka nan ne Mamman ,

Ƙanin Idi wan Yalwa.

Alhaji Musa ƊanƙwairoMaradun a waƙar Sarki Muri yana cewa:

 Jagora: In dare ya yi har kun shige barci,

indai kunji karnai suna haushi,

 In ba kura ta wuce nan ba,

to wata baƙin ɓarayi ne.

Amshi: Zaki ba ja ka gaba ba,

Sarki Muri Uban Galadima

MakaɗaKasu Zurmi a waƙar Ɓarawo masifa in dare ya yi yana cewa:

Jagora: Ɓarawo bala’i ne in dare ya yi,

Ajiya ɗaka ba ajiya ba,

 Ka iske mai abu na ja,

 Mara abu na ja,

Kai mai abu sau mai.

Dabbobi Mabiya Dare

 Bisa lura da kiyayewa da Bahaushe ya yi dangane da halaye da ɗabi’un wasu dabbobin daji. An ware wasu dabbobi na daji musamman maciya nama wato mafi fiƙa da dagi, kamar zaki, da damisa, da siyaki, da kura, da kyarkeci, da dila da sauransu. Dangane da dabbobin gida sun haɗa da kare, da mage. Game da wannan batu ana iya kawo wata waƙa da Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun waƙar Ɗanmaliki Umaru Sadaukiya ce:

 Jagora: Kura mai yawon tsakaddare,

ta yo yawonta babu nama.

 Amshi: Ɗan maliki Umaru Sadauki

 Kan wuyar karo na malam.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun a waƙar Sarkin Muri ya ce:

 Jagora: In dare yayi duk shige barci,

in dai kun ji karnai suna haushi,

in ba kura tab biya nan ba,

to wataƙila bakin ɓarayi ne”.

 Amshi: Zaki ba ja ka gaba ba,

 Sarki Muri Uban Galadima.

Alhaji Mamman Shata Katsina a wata waƙarsata Umaru Ɗanɗanduna na Gwandu matuƙin mota sai ya ce,

 Jagora: Kura ma bi dare ,

ummar gidan ɗanduna.

 Amshi: Umaru Ɗanɗanduna na Gwandu.

 Bayan dabbobi kuma Bahaushe ya keɓe wasu tsuntsaye kamar mujiya, da jemage, da mikiya, da yaburbura, da birbiri.

 Dangane da ƙwari su ma akwai waɗanda suka fi yin harkokinsu da dare kamar kunama, buzuzu tsanyar biri, rozozo, kyankyaso da sauransu.

 Bugu da ƙari, dabbobi irin su ɓera, da gafiya, da kwaɗo, da jaɓa, da maciji, da bushiya, da tsaka. Dukkan waɗannan jeri sun fi yin mu’amallarsu da dare. Ko da yake Bahaushe ya rarraba su bisa halayensu. Da farko akwai mugaye waɗanda da an gansu sai kisa. Kamar maciji da jaɓa da tsaka, bisa dalilin cewa suna cutarwa. Bayan su sai kuma gafiya da ɓera, bushiya su laifinsu shi ne ɓarna da sata. Duk da yake Bahaushe nakashe su a wani lokaci in an dace a kan yanka gafiya da bushiya don a ci namansu. Shi kuwa ɓera ba a cika cin namansa ba sai dai ɓeran daji. Baya ga dabbobi mabiya dare, Bahaushe ya keɓe wasu tsuntsaye masu harkarsu da dare. Tsuntsaye irin su, mikiya, da yaburbura, da birbiri da jemage, ko da yake ana lissafa jemage a jerin dabbobi masu tashi.

4. 0 Dare Mahutar Bawa

 Babu shakka Bahaushe ya ɗauki dare a matsayin wani keɓaɓɓen lokacin da yakan huta bayan gudanar da harkokin rana. Wannan kuwa ya bayyana ne tun daga lokacin da bahaushe kan cin abincin dare wato jibi. Al’adar ciyayya wacce magidanta kan yi a ƙofar gidansu, kowanne magidanci zai fito da abinci a taru a ci tare. Bayan ciyayya, sai kuma lokacin hira, da zarar an kammala cin abincin dare sai kuma a kafa dandalin hira ko majalisar hira. A irin wannan hira ce kowa kan faɗi irin gwagwarmayar da ya sha a wannan wuni. Bayan hira kuma sai tafiya unguwa da matan Hausawa kan yi a inda sukan ziyarci ‘yan uwa da dangi, saboda gaisawa, ko jaje, ko barker haihuwa, da sauransu.

 Bayan wannan kuma sai zuwa kwanciya barci, kwanciya barci kusan ana iya cewa shi ne aiki na ƙarshe da Bahaushe kan yi da dare.

5. 1. 2Jirwayen Dare A Camfin Hausawa

An camfa fitar dare.

An hana zuwa juji da dare.

An hana ratsa kasuwa da dare.

An camfa kukan mujiya da dare.

An camfa jifan baƙin kare da dare.

Baƙin Kare: Bahaushe ya camfa, kuma bai cika yarda da baƙin kare, sabo da alaƙarsa da iskoki. A wasu lokuta iska kan rikiɗa zuwa baƙin kare, ko kuma su shiga jikin baƙin kare na haƙiƙa. Don haka ne ba a duka ko jifansa. Wannan ya wuce hasashe ko zargi, saboda waɗansu hujjoji da suka tabbata a wurare, da lokutta da kuma mutane daban-daban. Misali.

Labarin wani mutum da baƙin kare

“Na dawo yawo da dare na shiga wani lungu sai na ga baƙin kare sai na ɗauki dutse na jefe shi, sai ya gudu ba a ɗauki wani lokaci ba, sai naga wani mutum ya bayyanar min. Nan take sai yace kai yaro kar ka ƙara jifan kare ka ji. ” [2]

6. 0 Jirwayen Dare A Mahangar Addinin Musulunci

 Idan muka kalli dare, ana iya cewa lokaci ne da yake da daraja a musulunci. Dalili kuwa shi ne, ana kwaɗaitar da musulmi da yawaita ibada da dare musamman sallar dare da ake cewa Ƙiyamul laili. Ban da wannan kuma an kwaɗaitar da cewa ana karɓar addu’a da dare.

 Haka kuma, muhimmancin dare ya ƙara bayyana ta inda aka ambaci dare a cikin Alƙur’ani a wurare da yawa a surori da dama. Akwai wasu surori inda Allah ya yi rantsuwa da dare.

 Bugu da ƙari, Allah yace, “mun sanya dare ya zama hutu a gareku”.

Akwai inda aka nuna a nemi tsari da dare lokacin da ya yi duhu. suratul Falaƙ

An nuna cewa: Cikin dare aka hallakar da mutanen Annabi Luɗu.

An nuna cewa: Cikin dare aka hallakar da Fir’auna da mutanensa.

An nuna cewa: Cikin dare ne aka yi Isra’I da Mi’iraji.

An nuna cewa: Cikin daren watan Ramalana ake samun lailatun ƙadari.

An nuna cewa: Annabi yakan tafi maƙabartar baƙiya cikin dare.

An nuna cewa: Ba a son a bar mutum a kasuwa ya zama na ƙarshen fita.

An nuna cewa: Ana girmama darare goma na ƙarshen watan azumin Ramalana.

5. 1. Dare A Adabin Baka

Akwai jirwayen dare a adabin Bahaushe, a rassan adabin baka da rubutacce. A karin magana, da almara, da tatsuniya, da barkwanci, da waƙar baka.

5. 1. 1 Dare a Karin Maganganu:

1. Tsakad dare maraicen kura.

2. Dare ga mai rabo asalatu.

3. Da’u fatakan dare, da rana kuke barci.

4. Dare mahutar bawa.

5. Dare rigar mugu.

6. In dare yai dare buzuzu ma nama ne.

7. Sai dare yai dare a sai da fatar kura, na ‘yan awaki ta kare.

8. Mai daren tuwo kya ci da buzuzu.

9. Mujiya wasa da ranaba naki ba ne.

10. Komai nisan dare gari zai waye.

11. Allah yai dare gari ya waye.

12. Dare mai danne duniya

13. Ba faɗa da Malam ba, tsakad dare ke tsoro.

14. Bari in tashi ciwo ya ji dare.

15. Katankatana mutuwar almuru.

16. Duk ɗaya makafi sun yi dare.

17. Ruwan dare tada hankalin baƙo.

18. Dare mai ban tsoro.

19. Ruwan dare mai game duniya.

20. Mai gari ba ya daren tuwo.

21. Yunwar dare mai hana barci.

22. Rigima kamar daren Sallah.

23. Wane dare ne jemage bai gani ba?

24. Duk wanda ya ce kasuwa gida ne, bari dare ya yi.

25. Ɗan tsakad dare jikar asuba.

26. Damuna dare in kaka ta yi gari ya waye.

27. Yaro ɓata hankalin dare ka yi suna.

28. Dare ɗaya Allah kan yi Bature.

29. Arziƙi kashi ne, da dare kan taka shi.

30. Dare maƙura yawo.

5. 1. 4. Dare A Tatsuniya

Tatsuniyar Ɗan auta da Dodo:

A tsakar dare ne dodo ya shigo gari sai ya ji warin mutum, tun daga nesa ya fara waƙa shi Ɗan auta yana bas hi amsa kamar haka:

Wa ya yi ni,

ni Dodon nana,

wa ya yi ni.

 Na yi yake,

 Ɗan auta iya

ya yi ya kai har fika.

Tatsuniyar Ta-kitse:

Da dare gizo ya zo bara gidan tsohuwa ya ga bijiminsa, ya dawo ya ga ‘yan mata.

Tatsuniyar Ta-kitse.

Bayan Sarki ya hana a sanya Ta-kitse aiki, sai wata rana ya tafi yaƙi. Kishiyoyinta kawai sai suka ceta fito ta yi. Fitowar ta ke da wuya, saboda zafin rana, da zafin wutar girki, sai ta fara narkewa. Nan da nan gida ya fara ruɗewa, kowa na kawo shawara ta yadda za a faɗawa Sarki. Ana cikin haka, sai kurciya ta zo tace, zata iya faɗawa Sarki a bakin daga, aka yarda ta tafi, da isar ta sai tace: Sarki Sarki a mai da yaƙi baya. Ta-kitse ta narketa narketa zamagulbin tsakar gida. Sarki na jin wannan waƙa da kurciya ke yi, sai ya dakatar da yaƙi ya koma gida. [3]

Tatsuniyar Gizo da Dodanniya.

Wata rana gizo ya tafi gidan dodanniya ya karɓo bashin bajimin sa, da alƙawarin zai biya shekara mai zuwa. Ya zo ya cinye, ya hana kowa. Ko da shekara ta zagayo, sai dodanniya ta zo bin bashi gidan gizo. Bayan dodanniya ta iso gidan sai ƙoƙi tace gizo ya mutu. Har ta kama hanya zata koma, sai kurciya tace ƙarya ne. Daga nan sai suka koma gidan gizo, ta fara waƙa tana cewa: [4]

 Kurciya: Mabiyan bashin gizo sun iso,

 Mabiyan bashin gizo sun iso,

 Zai yi biyan bashi a kushewa,

 Gizo: Un uhun wai ya kurciya,

 Ki biyo ta gidan mu ki sha ruwa,

 Ruwanki na nan a kururrumi,

 Bari in fita in taɓa ‘yar rawa,

Bari in fita in taɓa ‘yar rawa.

Daga nan sai gizo ya fito dodonniya ta kama shi ta tafi da shi gidanta.

Ø Tatsuniyar Ruwan Bagaja.

Ø Tatsuniyar Ɗanƙashin guiwa da namun daji.

Ø Tatsuniyar Gizo da hankaki.

Ø Tatsuniyar Gizo da Dodanniya.

Ø Tatsuniyar Gizo da ‘yan ruwa.

Ø Tatsuniyar Gizo da kura.

5. 1. 3 Dare A Waƙoƙin Baka

Waƙar Bikon Aure:

Dare, dare baba,

dare da rana abin kallo.

A wata waƙa wadda Uwaliya Mai Amada ta yi inda take cewa:

 Jagora: Dare Allah magani.

Annabin Allah na magani,

Dare Allah magani.

Zan taɓa maku waƙar kishiya,

 Amshi: Dare Allah magani.

Mamman Duka mai goge a wata waƙa yace:

 Jagora: Sai dare ya yi dare

Sai dare ya yi dare

a sai da fatar kura,

Sannan ta bunsuru,

Ta ƙare kwata-kwata.

Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙar Umaru Ɗanɗanduna Na Gwandu yake cewa:

 Jagora: Kura mabi dare,

Umarun gidan Ɗanduna.

 Amshi: Umaru Ɗanɗanduna Na Gwandu.

5. 2Dare A Rubutaccen Adabi

A rubutacce adabi ma an samu jiwayen dare da dama, akwai littattafai kamar zube, da wasan kwaikwayo, da rubutacciyar waƙa.

daga Littattafan Zube.

Littafin Ruwan Bagaja:

1. Malam ya tunkuɗa Alhaji Imam cikin ɗaki da ya zo kwartanci.

2. Ɓarayi sun damu Alhaji Imam ya koma gidan sarkin gardi.

3. Alhaji Imam ya kai cin hanci wurin Alƙali.

4. Saƙimu da dare ya kasha Liman / Uwar Alhaji Imam.

Littafin Jiki magayi:

1. Abubakar ya zo hira wurin Zainabu da dare.

2. Abubakar ya shiga gidan Malam Shehu ya yanki gashin kan Kyauta don haɗa sammu, ya tafi ya bunne a kabari da dare.

3. A garin Zanna da Shirinka ana kwana ana yin garaya.

4. Abubakar ya tafi neman ƙaron kalgo da dare.

Littafin Magana Jari ce:

1. Jarabawar Sarkin ɓarayi Noman ta uku da dare aka yi mafi yawa.

2. Jarabawar Yusha’u Narimi da dare aka yi.

3. Masu satar Likkafani a kabari da dare.

4. Masu satar rogo da dare.

5. Mansur da dare ya ɗauki fansa ga Ɗanshedan.

6. Bawa mai ƙusumbi da dare ya yi gamo.

7. Telu fari da sarkin fawa da dare ya kama.

Littafin Nagari Na kowa:

1. Ɗanduna ya gana da Mai dubu da dare ya bar mashi amanar Salihi.

2. Salihi ya rinƙa a toka ba da sauri Mai dubu ba.

3. Sarauniyar Bori ta ba uwar gida turare da borkono.

4. Addu’ar Mai dubu don dukiyarsa ta ɓace da dare.

5. Cikin dare aka tura Salihi a rijiya.

6. Cikin dare aka ba Salihi Sarauta.

Littafin Shehu Umar:

1. Da dare ne su makan suka kai harin kama bayi.

2. Da dare ne kura ta cinye ɓarawon umar.

Littafin Dare Dubu Biyu da Ɗaya:

1. Lokacin dare aka ba da labari.

Littafin Kitsen Rogo:

1. Lokacin da aka sace madubin mota da dare ne.

2. Da dare ne aka je wurin Malamin tsibbu.

Littafin Da’u fatakan dare:

Da’u da Sambo baƙin duhu.

Littafin Iliya Ɗan mai ƙarfi:

Haɗuwar Iliya da Gogaji.

Littafin Tauraruwar Hamada:

Malam Ɗanye da dare yake haɗa kayan tsibbu.

5. 2Dare A Rubutattun Wasan Kwaikwayo

Littafin Kulɓa na Ɓarna:

1. Lokacin da Alhaji Ruwan Ido yake zuwa da dare ya ɗauki Zaliha.

2. Ɗan London da dare yake zuwa zance da Zaliha.

Littafin Zaman Duniya Iyawa ne:

1. Tagudu da dare ta faɗa da mijinta wai bai dawo da wuri.

2. Tagudu tai faɗa da wata karuwa da dare.

Littafin Tabarmar kunya:

1. Da dare ne Idi ya je ya sato geron turunkuna ya faɗa ɗakin surukansa.

2. Cikin dare ya gudu don kaucewa abin kunya.

Littafin Uwar Gulma:

1. Hayatu sai dare ya yi yake dawowa a buge kuma ya bugi Halima.

Hujja daga Alhaji Sule Buttu, Mai Maganin Mayu Jihar Naija:

1. Ana gwada tona asirin mayu ne da dare.

2. Ana cire masu maita da dare.

Daga Jakar Magori Rediyo Nigeria Kaduna:

1. Wata mata mayya ta damu surukarta, matar ɗanta. Don ya bugeta da dare.

2. Wata yarinya ta faɗa rijiya a garin Kudan 2003

3. Kwalekwale ya kife a kogin Ɓagwai da mata da amarya da dare.

8. 0 Kammalawa:

A ƙarshe wannan nazari ya hararo matsayin dare, da gudummowarsa, da tasirinsa a rayuwar Bahaushe ta mahanga al’ada. Maƙalar ta kawo ma’anar dare, da bayyana fagagen da dare ya mamaye, tare da gano irin shaƙuwar da Bahaushe ya yi da dare ta yadda har bai iya gudanar da wasu al’amura na rayuwarsa sai da dare.

Babu shakka wannan nazari ya ƙara fito da wasu abubuwa game da muhimmancin dare ta inda ya shafi tunanin Bahaushe, kamar taimakawa mawaƙa a fagen waƙa, mafi yawan mawaƙa sun fi gudanar da waƙoƙinsu da dare, sannan dangane da malamai a fagen ilmi. Domin dare yana ƙara kaifafa tunani tare da aiwatar da ibada cikin sauƙi. Bayan wannan kuma, nazarin ya ƙara nuna muhmmancin dare a fagen magani da na tattalin arziki a rayuwar Bahaushe ta fuskar gudanar da wasu sana’o’insa. An kuma ƙara fito da irin girmamawar da ake yiwa dare a Bahaushiyar al’ada musamman wajen bauta da bukukuwansa.

Manazarta

Abubakar A. T. (2015) Ƙamusun Hausa . Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Bargery (1937) Ƙamus Turanci zuwa Hausa Northern Nigerian Publication Company,Zaria

BUK(2006) Ƙamusun Hausa .

Bunza AM (2006) Gadon feɗe Al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere, Lagos.

Imam A (1955) Magana Jari ce. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Imam A (1937) Ruwan Bagaja. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

John T. U (1937) Jiki Magayi. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ɓalewa A (1955) Shehu Umar. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Kano M da wasu (1933) Dare dubu da ɗaya. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ɗangambo (1980) Kitsen Rogo. Kamfani Triumph Kano

Zango T. (1959) Da’u Fataken Dare. Northern Nigerian Publication Company,Zaria

Ingawa A (1970) Iliya Ɗan Maiƙarfi. Northern Nigerian Publication Company,Zaria

Daura S A (1970) Tauraruwar Hamada. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Katsina D. U (1980) Kulɓa na Ɓarna. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ladan Y. (1980) Zaman Duniya Iyawa ne. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ɗangogo (1970) Tabarmar Kunya. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Katsina M. S (1960) Uwar Gulma. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Yahaya Y. I (1980) Tatsuniyoyi. Longman Press Ibadan




[1] Habibu A. Sarki (2000) zuwan musulunci Afrika da shigowarsa Ƙasar Hausa babu kamfani a kano.

[2]Sa’idu Abubakar hira da shi a bakin Kasuwar Sati Kaduna 18/6/2012.

[3] Dubi Littafin Tatsuniyoyi. Yahaya Y.I (1980) Longman Press Ibadan

[4] Filin Yara Manyan Gobe Radiyo Najeriya Kaduna 20/5/1999. 

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments