Ticker

6/recent/ticker-posts

Hangen Kitse Ake Yi Wa Rogo: Nazari A Kan Rayuwar Matasanmu A Yau

DAGA

DR. MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD KUDAN

GABATARWA

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki, tsira da Aminci su tabbata ga fiyayyen halittu Annabi Muhammadu (S. A. W). Wannan muƙala, na da ƙudurin yin tsokaci a kan rayuwar matasa da matsayinta a wannan zamani tare da danganta ta da rayuwar Bahaushe jiya da kuma yau. Haka kuma tare da fito da irin sauye-sauye da rayuwar Bahaushe ta samu dangane da ɗabi’ar tafiye-tafiye da matasanmu ke yi zuwa kudan Ƙasar nan. Bayan haka, za mu dubi dalilan da suka kawo waɗannan sauye-sauye. Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen nuna fa’idoji da kuma illolin taye-tayen da kuma sakamakon da sukan haifar ga mai yin su da kuma al’umma. A wannan nazari, zan dubi tafiye-tafiyen ta ƙusurwowi daban-daban. A mahangar Al’adar Bahaushe, da Mahangar Addinin Musulunci, sannan ta Mahangar Zamani. Bisa wannan dalili ne yasa na yi wa wannan maƙalar take da Hangen Kitse Ake Yi Wa Rogo”. Na kawo taken a matsayin ne, don ya ba mu damar lalubo mafita. Tare da fatan mai karatu ko saurare zai gano ko zaƙulo amsar a ƙarshen maƙalar, don samun tabbatacciyar mafita ko a fid da jaki a duma.

FASHIN BAƘI

Ma’anar Hange: Na nufin wani aiki ne wanda mutum kan yi ta hanyar gano ko kallo wani abu daga nesa da gulalan idanu ko kuma da idanun zuci.

Kitse: Na nufin nau’in mai ne daskararre mai launi fari wanda ake samunshi a jikin nama ko kuma a cikin warjiya, ko wanda yake a jiki ƙoda ko na jikin tumbi.

Rogo: Na nufin wani nau’in abinci ne mai kama da doya wanda ake dafawa domin a ci.

Rayuwa: Na nufin duk wata harka da mutum zai yi don ya rayu kuma ya samu natsuwa, kalmar ta samo asali ne daga kalmar rai,(rai—raye, rayu, rayayye, rayayyu= rayuwa).

MATASA: Na nufin Kalmar jam’I c eta Kalmar matashi, Matashi shi ne yaro mai shekara 9-13, saurayi kuma daga 14-17. Ko da yake yanzu an yi masu kuɗin goro samari sai a kirasu da matasa.

MATAKAN GIRMA.

Ƙuruciya na nufin wata rayuwa dake farawa daga haihuwa zuwa samartaka zuwa dattijantaka da tsufa.

jariri/

Jaririya

 sabuwar Haihuwa

Laɓuɓu

Laɓuɓuwa

 wata1-6

Barden goyo

Barden goyo

 wata6-24

yayayye/

yayayyiya,

 wata24-36

sagari/

Sagara

 shekara3-6

Madaci

Ƙwaila,

 shekara6-9

 Matashi

Bera

 shekara9-13

 saurayi/

Budurwa.

 Shekara13-17

 Magidanci

Gunduwa/uwar mata

 shekara17-45

Dattijo

Dattijiya

 shekara45-59

Tsoho

Tsohuwa

 shekara 60-70

Tsoho Tukuf

Tsohuwa Tukuf

 shekara70-80

Tsoho Tukuf Tukuf

TsohuwaTukuf-Tukuf

 shekara80-100

Tsoho Takwarkwasasshe

Tsohuwa Takwarkwasasshiya

 shekara 100-120

 

 Wannan rayuwa ita ake kira yarinta, ko da yake wasu kan kirata da cewa da farkon yarinta har zuwa tsakiya, amma zuwa ƙarshe watau samartaka sukan kirata da balaga.

Ta wata fuska ana kiran ƙuruciya da farkon rayuwa, saboda wata karin magana mai cewa “yaro masomin babba”, ko wata karin magana mai cewa “ƙuruciya matakin farko”, “Yaro ba mutum ba sai ya girma”, In ka ga tsohon banza daga yaron banza ya taso” da sauransu.

TAFIYE-TAFIYEN BAHAUSHE

Ma’anar Tafiya; Yi yawo, yi tafiya(a ƙasa) Yawo, sha iska, wangaɗa, yauta, yi tafiya, tura ko miƙa ƙafa zuwa gaba da nufin barin wani muhalli zuwa wani a ƙasa

Bisa ga dogaro da bayanan da masana suka yi ana iya cewa, tafiya na nufin wani aiki ko motsi da mutum kan ɗaga ƙafa ɗaya, ya ajiye ɗaya a ƙasa, tare da miƙa ɗayar zuwa gaba, a sakamakon haka zai rinƙa matsawa daga wurin da yake, kuma da nufin barin muhallin da yake don zuwa wani muhallin na daban kusa ko nesa. Tafiya saɓanin sauri ne, ko gudu, ko sassarfa, don zuwa wani muhallin na daban kusa ko nesa.

Faɗaɗa ma’anar tafiya: Bahaushe kan ce wane ya yi tafiya da nufin ya bar garinsa zuwa wani gari. Inda akan ce wa ne ya yi tafiya.

Kinaya a kan tafiya: Bahaushe kan sakaya, ko ɓoye sunan tafiya ta hanyar ambaton wasu kalmomi a maimakonta kamar haka: yawo ko balaguro ko tattaki ko miƙe ƙafa ko shawagi ko zagaye ko kewaya da sauransu.

Bahaushe kan ce “duma mai kai iri nesa” ko“Na zaune bai ga gari ba. ” Za a yi bayani kan yanayi, da lokaci da dalilai da kan sanya Bahaushe barin garinsa .

 Babu shakka kamar yadda ya bayanai suka gabata daga wasu masana daban-daban dangane da irin yawace-yawace da Bahaushe kan yi a rayuwarsa zuwa wasu wurare da ba na shi ba a sararin duniyar nan suna da yawa. Ana iya cewa kowa ya bayar da hujjoji, ko dalilai ne gwargwadon fahimtarsa. Idan muka dubi kowace fita da Bahaushe kan yi, inda ya kan bar gidansa, ko garinsa, muna iya cewa kowane da lokacin yake ɗauka in ya fita ɗin. Bayan haka kuma, akwai irin sunan da Bahaushe ya ba shi don rarrabewa. Haka nan kuma, a ƙarshe kowanne na ɗamfare da dalilan da kan sanya a yi shi. Bisa wannan dalili ne, ma da zarar ka ambaci irin sunan tafiya, ko fita da Bahaushe ya yi. Tabbas za’a gane cewar lallai ga dalilin da ya fitar da shi daga gida.

 Dangane da sunaye waɗanda al’adar Bahaushe ta bai wa fitar, ko barin gida da Bahaushe kan yi suna da yawa, sune kamar haka:

Ci-rani,

Ga-aiki

 Kaɗar raba,

In-yi-gwado,

Dandi

Jaura,

Fatauci

Ujula,

Kore

 Raraka

 Garam,

 Kilisa

 Rangadi

 Zagaye ko zage.

Haka kuma akwai nau’in tafiye-tafiye na biyu sune yawon duniya ko dandi ko zara. Daga su kuma sai wanda ya shafi bauta watau addini kamar, ziyara, aikin hajji. Bayan waɗannan kuma sai tafiya neman karatu, sannan kuma sai ƙaura, da kucciya da sauransu.

 Idan muka ɗauki nau’in tafiye-tafiyen Bahaushe na farko sai mu ce: Dalili ɗaya ne kan sanya a yi su, shi ne, kuwa neman kuɗi ko abinci kamar haka:

1-Ci-rani: Bahaushe kan bar gidansa da garinsa ya tafi wani gari a lokacin rani, watau babu noma don kawai ya samu kuɗi ko abincin da zai ci. Bahaushe kance noman rani maganin ci- rani. A tsarin wannan tafiya ba a daɗewa da an samu alheri sai a dawo gida.

2- Ga-aiki: Game da wannan, Bahaushe kan fita ne da bazara can karshen rani an kusa samu ruwan sama, a inda sukan rinka yin aikace-akace kamar kwabin kasa, sharar gona, danni, haka rijiya da sauransu. Shi ma da ruwan sama ya samu, watan damuna ta sauka.

3-In-yi gwado: Bahaushe kan fita ne a lokacin da aka fara girbi, ko an kusa gamawa dab da za a fara sanyin hunturu. Abin da Bahaushe ke nufi a nan shi ne mutum zai samo kuɗin da zai sayi gwado. Wani mayafi ne wanda ake rufa, ko lulluɓa a lokacin sanyin hunturu. Akwai ‘yan baranda, shi ma ba a daɗewa ake dawowa in an fita.

4-Kaɗar-raɓa: Shi kuma da kaka ake tafiya gab da ɗaukewar ruwan sama watau an fara zubar da raɓa. To shi ma ba a daɗewa ake dawo wa. Bahaushe kan ce “kowa ya sha raɓa a raɓeshi”. Akwai masu dawowa da zarar an fara girbin hatsi.

 Duk dai a wannan tsarin tafiye-tafiye sai dai su kuma na dogon lokaci ne akwai:

5-Jaura: Watau tafiye-tafiye waɗanda ɗankoli kan yi su, a inda yakan bar gidansa ya tafi wata kasuwa. Bayan ya ci kasuwa, sai ya kwana a garin sannan ya wuce wata kasuwar. Ita ma daga nan wata zai wuce, yana iya yin watanni huɗu zuwa shida. Daga baya kuma sai ya juyo, a nan ma ba kai tsaye yake nufo gida ba, sai dai da cin wannan kasuwa zuwa waccan zai iso gida.

6-Fatauci: Da jaura da fatauci suna da kamannu sai dai shi fatauci mai yin sa ana kiransa da Falke, jam’i Fatake, ƙungiyar fatake ko kuma ayari, shugabansu shi ne madugu, wuri da sukan sauka su huta ana kiransa da zango. Dangane da fatauci shi ma akan daɗe ba a dawo gida ba. Haka kuma akan yi fataucin abubuwa da yawa, wanda yake saɓanin ɗankoli. Daga cikin fatake akwai wasu rabe-rabe da aka yi masu suna don rarrabewa, kamar, ‘yan bojuwa, da ‘yan ja’oje, da masu kora shanu, zuwa kudu, da kuma ‘yan ujila masu jakai zuwa kudu, sai ‘yankore ko are-are masu kawo raguna daga arewa (Nijer da maƙwabta).

 Bayan wannan kuma, akwai wasu ƙungiyar masu tafiye-tafiye daga cikin wannan tsari na masu barin garin su zuwa wasu garuruwan don neman kuɗi. Ko da yake Bahaushe na masu kallonsu a matsayin masu ganganci, ko kasada. Waɗannan mutane kuwa, su ne masu fita gida zuwa garam da raraka.

Garam da raraka: A mafi yawan lokuta an fi samun banbaɗawa watau maroƙa na fili da na ɓoye. A inda sukan tafi wurin wani mutum mai hali su gaisheshi, idan zasu tafi sai ya yi masu kyauta. A irin wannan fita ba a bukatar daɗewa, ‘yan kwanaki kaɗan ake yi a dawo, domin ba a wuce kwana huɗu ko bakwai.

Dandi: Bayan wannan kuma, sai ɓangare na biyu, shi ne dandi ko yawon duniya ko zara, ko ragaita, ko sheƙe aya, ko gantali, ko bariki. Matuƙar Bahaushe ya faɗi wannan, to yana nufin barin gida da Bahaushe kan yi a bisa dalilin ɓacin rai. Misali idan mutum ya aikata wani abin kunya, ko aka yi masa ko mata auren dole ko kuma aka kasa namiji a neman aure, watau ya nema ya rasa ko kuma aka yi takarar sarauta ya faɗi.

 Ziyara: Dangane da barin gida mai alaƙa da addini kuwa, watau bauta. Wannan ya haɗa da na maguzanci kafin zuwan musulinci. Haka kuma, da na musulunci kamar zuwa aikin hajji a Ƙasar Makka, da ziyarar hubbare, da zuwa neman ilimi. Ban da waɗancan ziyarce-ziyarce da aka ambata a sama, akwai na sada zumunci, da gaida mara lafiya, ko ta’aziyya da na yin jaje saboda faruwar wani abu mara daɗi.

Ƙaura: Baya ga wannan kuma, akwai wanda yake shi ba girma ba arziki, babu shiri, ba tunani ina aka dosa. Irin wannan shi ne kamar ƙaura a dalilin aukuwar annoba, ko yunwa, ko tsuntsaye jambaki, ko farin ɗango, ko ƙarancin ruwan sama, ko ambaliyar ruwa, ko wutar daji.

Kurciya: shi kuma fita ne, ko barin gida mai alaƙa da sihiri, da ake yi wa abokin hamayya. Domin ya bar gida babu shiri, sannan kuma ya tafi har abada ba dawowa.

Bakance: wani barin gida mai alaƙa da bakance, kamar mutum ya sha alwashi, ko alƙawarin cewa, sai ya yi abu kaza, idan wani abu ya faru.

 Rangadi: Haka kuma sarakuna kan fita don yin rangadi ko zagaye kilisa: Shata katsina yace:

Ya fita yai rangadi,

Ina gida bai aika min ba,

Akai hawan salla ba na nan,

Akai biki ba ka aika mini ba,

Narambaɗa a waƙar Sarkin Zazzau

 yau in aka hau kilisa,

 gaba faduwa akai

MARAINA KAƊAN ƁARAWO NE

 Bahaushe ya ce, “maraina kaɗan ɓarawo ne”, ma’ana idan Allah ya yi maka baiwa sai ka rain aka koma hangen na wani, to lallai b aka nuna godiyarka ga Allah ba.

 Bisa zance na gaskiya da matasanmu za su yi haƙuri da abin da Allah ya yi mana na arziƙi da wadata, da wallahi ba inda zasu. Muna da manyan birane a Arewa, babu irin sana’ar da ba zaka yi ka samu alheri ba. Abin haushi da takaici sai matasanmu su tashi su nufi kudu, ko kudu maso gabas, ko kudu maso kudu, ko kudu maso yamma. Babu girma ba daraja ba ƙima, sai wulaƙanci da zubar da girma. Idan suka tafi manyan sana’o’in da sukan yi guda biyar ne, su ne kamar haka: Dako, gadi, tura baro, yankan farce sai acaɓa.

BUNSURU YA TAFI BARBARA

 Bunsuru ya tafi Barbara ya dawo da ciki. Abin nufi a nan shi ne, kowa ya sani bunsuru yana tafiya neman akuya don ya barbareta, kuma shi ne zai mata ciki. To a maimakon haka sai bunsuru ya dawo da ciki, to ashe abu ya lalace. Tabbasa irin wannan rayuwar ce mafi yawan matasanmu ke yi yayin da suka je kudu neman abin duniya.

CIRANIN SANIYA

 Ciranin Saniya na nufin ita Saniya duk inda ta tafi komai nisan wurin, sannan kuma duk da daɗewar da zata yi ba za ta dawo da komai ba. Ita ribarta shi ne, ta ci abinci ta ƙoshi, wato ta cika cikinta shi ne nasararta.

 In ban da kar in cika baki, da sai in ce mafi yawan samarin Arewa da suke zuwa kudu ciranin Saniya suke yi.

DA MUGUWAR RAWA

 Bahaushe na cewa, “da muguwar rawa gara ƙin tashi”. Ma’ana da mutum ya aikata wani aiki wand aba zai haifar masa da alheri ba, to gara kar ya fara aikin. Bisa dogaro da wannan Karin Magana ce zan jan hankalin ‘yan uwana da cewa su sanya idon fahimta su auna idan sun yi tafiya zuwa kudu wacce riba za su samo? Dalili kuwa shi ne mutane nawa ne suka tafi kudu suka dawo da wani abin arziƙi.

GANI GA WANE

 Bahaushe na cewa, “ gani ga wane ya ishi wani tsoron Allah”. Abin nufi a nan shi ne, idan mutum na raye zai ga wani abu ya faru a kan wani ɗan uwansa. Tabbasa matuƙar mutum zai yi aiki da hankalinsa dole ne ya wa’azantu ya zama darasi a gareshi.

 Akwai wasu al’amura da dama da suka faru ga ‘yan uwanmu masu zuwa kudu marasa daɗin ji, da ba za su lissafu ba. Duk da yake ɗan Adam saurin mantuwa gareshi, amma kowa ya ga ƙari ya san ba ƙurji ba ne, ba kuma kaluluwa ba ne, sannan ba maruru ba ne, Bai dace mutum mai lafiyayyen hankali ya rufe ido sannan yak au da kai ga abin da ya faru ko yake faruwa ba.

 Duk da haka g akaɗan a matsayin misali:

Rikicin Shagamu 2000

Rikicin Afinife

Rikicin Ibo zalla

‘Yan biyafara

Matasan da aka kama ‘yan Jigawa aka ce ‘yan Boko Haram ne

Rigimar Yunusa Yelo

‘Yan Acaɓa 123 da aka kama a Lagos

Rikicin ma tuwaf

Rikicin Ille-ife, da sauransu.

Dangane da waɗanna rikice-rikice ko tashin-tashina da suka auku a kudu, babu ko shakka ‘yan Arewa matasa maza da mata da suka cutu ko suka halaka Allah kaɗai ya san adadinsu. Ko mai saurare ya yarda ko bai yard aba wannan ba ƙaramar Magana bace ga sashin arewa.

Bayan haka idan kuma matshi ya dawo kudu to Allah ya taimakeshi bai dawo da wani ciwo ba an yi sa’a. Domin wasu sukan ɗauko wasu cututtuka waɗanda sai dai a dawo su in sun yi sa’a su warke, in kuma aka kuskure sai kushewa. Wasu kuma, ba a kansu ciwon ke tsayawa ba a’a abin har yak an harbi wasu. Kamar ‘ya’ya ko ƙanne, ko matansu ko makwabta.

ME KA KE SHA’AWA GA ARNA?

 Bahaushe na cewa, “Arne ka fi kyau tsirara-tsirara”. Shi kuwa Muhammad Ɗan Anace mawaƙin Hausa cewa ya yi:

Arna da kaka kuke shan giya

Alhaji Musa Ɗanƙwairo na cewa:

In na baro Bena sai in wuce zuru,

in ga inda Arna kan ɓankaura,

suna ta rawarsu sun sha giyar dawa.

Ga wasu na arna su yi ta fasadi

sun fi bukatar hakan ga kayansu

Ga kare gar ago an ɗaure an ce mu zaɓa

Mu dai mun zaɓI rago

Sauran mahaukata sun zaɓi kare

Juma mai baƙin baki

Kare juma kafiri ne

Bai taɓa aikin da anna Allah ba.

Bayan wannan Alhaji Aliyu Namangi Zariya a wata waƙarsa yana cewa:

Me kake sha’awa ga anna?

Shan giya ko ɓata suna?

Mai Bakandamiya shi kuwa sai ya ce:

Sun ɗau adiko zasu Ƙasar Jaba

Su ne ɓarayi su ne ‘yan fashi

Su ne maneman matan duniya.

Duk waɗannan bayanai an yi su da daɗewa, amma kuma idan ka ji su ka rantse da Allah ‘yan aka yi kuma da mu ake yin maganar.

ME KE GA JAƁA BALLE ROMONTA

 Babu shakka, akwai wasu abubuwa waɗanda kan bange wasu matasa idan wani matashi ya dawo daga kudu. Kaɗan daga ciki sun haɗa da yanayi sauya tufafi kamar singileti wandon jins da hula hana-salla (Fesin kaf) ko askin banza da ake cewa gida da mafaɗi. Abin takaici da ban haushi ka ga matashi musulmi ɗan Arewa ya yi shigar ‘yan kokuwa ko ‘yan iska, amma wai shi ya burge. Wanda da zai mutu da wannan shigar (tufafi) sai a yi kyamar yi masa sallar janaa don za a yi zaton ba musulmi ba ne Jakob ne.

 Bayan wannan, in an dawo a kan koyo shaye-shaye da rashin kunya da sauran miyagun ɗabi’u waɗanda suka ci karo da al’adu da addininmu.

BIN NA GABA BIN ALLAH

 Girmama iyaye wajibi ne, wannan shi ne ya sanya ya zama dole ga duk ɗan da yake son ya ci nasara a rayuwarsa kuma ya ga abin da yake so a duniya da lahira to ya bi maganar iyaye. Ga hujja daga Alƙur’ani mai girma inda Allah (S. W. T. ) ya ce: Kar ku bautawa wani sai ni iyaye kuma ku kyautata masu…….

Akwai inda ya ce, “kar ku ce masu tir.

 Haka kuma akwai hadisai masu yawa da suka umarci ‘ya’ya su kyautatawa iyaye, a bi umarnin da suka baya matuƙar bai saɓawa Allah ba. Kamar wani hadisi da wani matashi ya zo wurin Annabi (SAW) yana neman izini zai bi rundunar jihadi, sai Annabi ya tambayi matashin nan iyayenka na raye? Saurayin ya ce suna raye, sai Annabi ya ce ka je ka kyautata masu jihadinka na wurinsu.

 Wani mutum ya zo wurin Annabi (SAW) ya ce wa zan kyautatawa a duniya? Sai Annabi (SAW) ya ce mahaifiyarka, mahaifiyarka, mahaifiyarka har sau uku, Sai a na huɗu ya ce mahaifinka.

 A wani hadisi kuma, wata rana Annabi zai hau munbari sai sahabbai suka ji Annabi yana cewa amin, amin, amin har sau uku. Daga baya sahabbai suka tambayi Annabi cewa: ya manzon Allah mun ji k ace amin har sau uku. Annabi ya ce: Mala’ika Jibrilu ya zo yace duk wanda ya girma da mahaifansa har suka rasu amma bai yi aikin da za a gafarta mas aba Allah ya turmusa hancinsa a wuta ya ce in ce amin, na ce amin.

 Duk wanda watan azumin ramalana ya kama ya ƙare mutum bai yi aikin da zai shiga aljanna ba Allah ya turmusa hancinsa a wuta yace ince amin, nace amin. Duk wanda aka ambaci sunan Annabi yana wurin amma bai ce sallallahu alaihi wasallam ba, Allah ya turmusa hancinsa a wuta kace amin, nace amin.

 Ya wuce wai bai zan waiwai ba. Bahaushe na cewa “gani ya kori ji. Ni ɗin nan mai Magana ina da shekara 50 ya ‘yan rakiya. Tun daga waɗanda suka girmeni zuwa tsararrakina har zuwa na ƙasa da ni wato waɗanda na girma. Ba zan iya ƙirga mutane 7-10 ba a garin kudan waɗanda suka tafi kudu suka ci ribar tafiyar ba. Idan kuwa k ace in lissafa maka mutum 20 da suka tafi kudu suka lalace a can, ko aka dawo da su a lalace zan iya.

INDA AKA SAN DARAJAR GORO

Babu shakka Bahaushe na cewa, “inda aka san darajar goro nan ake sanya masa ganye”. A matsayinka na musulmi mai Imani wanda Allah (SWT) ya girmama kuma ya yabeshi a Ƙur’ani mai girma yace, “Kuntun hairan ummatan ukhrijat linnasi………. Ku ne mafi alherin al’umma da aka fitar daga mutane kuna umarni da kyakkyawan aiki, kuna yin hani da mummunan aiki.

 Malam mai ahalari na cewa kar ka aikata wani aiki sai ka san me shari’a ta ce? Ma’ana mene ne umarni Allah a kansa.

Da farko Malam, ana so ka yi Imani cewa babu mai arzurta wani sai Allah, kuma a duk inda kake arziƙinka na wurin Allah. Da wane dalili zaka kai kanka wurin halaka, ko wuri mai haɗari, ba ka ƙetare arziƙinka, ba ka kasa isa rabonka.

Na biyu kar ka yi wa iyayenka tawaye, don Allah mutane nawa ne suke tafiya kudu da yardarm iyayensu? Guda nawa ne sukke tunawa da iyaye har su kula da su.

Na uku Mazaje nawa ne suka tsare haƙƙin matansu? Malam ka tafi ka bar matarka b aka tsare mata haƙƙinta ba. Kana zaton Allah ba zai tambayeka ba?

Na huɗu iyaye nawa suka bar yaransu ƙanana ba kulawa suka nufi kudu? To tarbiyyarsu tana wuyanka, ka sani Allah zai tambayeka sannan kuma idan ka tsufa yaran suka girma ba za su tausaya maka ba.

ABIN HAUSHI NAMA NA JAN KARE

Bisa ɗabi’a ta yau da kullum, an san cewa kare ne ke jan nama kowanne iri ne kuwa. To amma in aka ce ga nama na jan kare, ka san al’amari ya lalace.

Babban abin takaici a yau shi ne, matasanmu masu tafiya cirani kudu har da masu ilmi. Akwai inda zaka iske mutum mahaddacin Ƙur’ani ya kama hanya ya kudu idan ba a yi sa’a ba sai yayi ɓarin miya a yashi ya dawo babu karatu, kuma bai samo kuɗin ba, kuma ba tarbiyya. Ban da wannan kuma, wani ya kamala karatun sakandire har ya yi WAEC ko NECO, amma sai yah aura ya yi kudu Ƙarshe ya dawo a lalace. Babban mai wauta cikinsu shi ne ya yi NCE, ko Diploma, ko Digiri ko kuma yana yin karatu wai da an yi hutu sai ya runtuma zuwa kudu. To wannan kuma sai ya yi rasasa-rasasa. Ko biyu-biyu kamun gafiyar ɓaidu, ya dawo babu karatu babu kuɗin.

Bugu da ƙari, abu ne mawuyaci, mutum ya tafi kudu bai yi asarar ɗayan uku ba. Da farko zai asarar tarbiyya, ko lafiya ta jiki ko hankali ko kuma addini in ba duka ba to za a yi masa sartse a imaninsa.

YA KAI ƊAN’UWA! KA KIYAYE ABUBUWA SHIDA (6) KA SHIGA ALJANNAH.

 Haƙiƙa duk Musulmin da ya lizimci abubuwa shida (6), lallai Manzon Allah zai lamunce masa shiga Aljannah. Wannan abubuwa kuwa su ne kamar haka: - 1. Faɗin gaskiya. 2. Cika alƙawari. 3. Kiyaye amana. 4. Kiyaye farji.

5. Kiyaye ido daga kallon haramun. 6. Kiyaye dukiyoyin mutane.

Baihaƙi ya ruwaito shi daga Ubadata Ɗan samit.

TO JAMA’A INA MAFITA? Matuƙar aka rutsa mage a cikin ɗaki, to dole ta nemi mafita inda zata gudu, don ta tsira da ranta ta samu ta kuɓuta. Bisa wannan dalili, ina mai yin kira ga dukkan Bahaushe da Bahaushiya, da cewa mu farka daga baccin da muke yi, mu san kanmu, mu kula da kanmu, da mu tsare kanmu.

Dukkan mai hankali a jikinsa ya kamata ya dawo cikin hayyancinsa ya tsaya ya yi wa rayuwarsa kallon natsuwa. Watau kallo irin na sayen goron tsohuwa. Wajibi ne mu sanya kishin harshen mu, al’adunum da addininmu, saboda su ne rayuwar mutum gaba ɗaya. Matuƙar aka ce mutum ya rasa su to zai yi ballagazar rayuwa mara manufa da amfani. Domin ya yi ɗigirgire ko kan-tafi da rayuwarsa,an kuwa ce kan-tafi masomin asara .

Ga wata tambaya ga masu ra’ayin nasara, shin wai sun san cewa, sauran Ƙasashe da suka ci gaba, ba irin wannan hanyar suka biyo ba?. To idan masu irin wannan tunanin ba su sani ba,to ga wani bayani: Ƙasashe da yawa da suka riƙi harshensu a matsayin harshen ma’amulla,watau Harshen Ƙasa. Suka tsare al’adarsu suka tsare addininsu, sun ci gaba nesa ba kusa ba. Misali: Sin (china) Indiya, Japan, Iran,Kyuba, Birazil da sauran su.

Matashiya ga masu irin wannan ra’ayi . Tabbas wannan magana gaskiya ce, kuma a zahiri duk mai hankali zai yarda da ita. Al’ada dai kamar riga ta ke, don haka al’adarka ita ce rigarka wadda ta ke daidai da kai. Idan kuwa har ka ɗauki rigar wani, in har ba a yi sa a ba, za ta yi maka yawa ko a tsawo ko a kauri ko faɗI. A ƙarshen al’amari ko ka sanya ba za ta yi maka kyau ba. Shi ya sa aka ce naka shi ne naka kayan aro abin shirme ne,in mai abin ya karɓi abinsa to dole zaka komo naka.

Ina kira ga masu hankali a jikinsu da su san cewa kaza ba ta zama agwagwa, haka ita ma agwagwa ba ta zama kaza. Don haka mu tsaya a inda Allah ya ajiye mu, kar mu wuce gona da iri. Domin in ba haka ba zamu yi saki na dafe, zamu zama ba Turawa ba, kuma ba baƙaƙe ba. Da farko mun watsar da al’adunmu, harshen mu waɗansu ma har da addininsu.

Ina yi wa Bahaushe albishir, idan bai sani ba ya sani cewa, Allah ya yi wa harshensa da ala’dunsa ɗaukaka a duniya. Domin a yanzu harshen Hausa ya karɓu ƙwarai, tufafin Bahaushe na da kwarjini a ko ina a duniya, sannan addinisa na musulunci ya gagagara a duniya. Duk da irin tsangwama da Turawan yamma da Yahudawa suke yi masa, shi ne a sama cikin ikon Allah. To dama Bahaushe ya ce “an so kare da gwaiwa Allah ya bai wa rago” don haka mu taru mu yi kishin kan mu, saboda wasu Hausawa sun ɓata biyu ɗaya ba ta gyaru ba. Su dai ba harshen Turancin, kuma sun saki Hausar a ƙarshe sun saki reshe sun kama ganye. Haka ita ma al’adar sun bar ala’adar Bahaushe sun ɗauki ta Bature, sai dai kuma ba a Turai suke ba. Gashi kuma Turawan ba za su karɓe su ba, sai su ƙare a rasasa-rasasa. Alhali kuwa masu hikima sun kasa ribar rayuwa mataki uku zuwa huɗu kamar haka:

san samu (mutum ya samu alherin duniya da na lahira)

samu rasa (mutum ya samu alheirn duniya ya rasa na lahira)

rasa ka samu (mutum ya rasa alheri duniya ya samu na lahira)

rasasa-rasasa (mutum ya rasa alherin duniya da na lahira)

Allah ya tsare mu amin.

KAMMALAWA;

A ƙarshe wannan takarda, ta tsakuro wasu halaye ne na wasu mutanen mu waɗanda Turwa suka yaudaresu suka kuma sake su a igiyar ruwa. Irin waɗannan mutane ana samunsu a maza da mata. Don haka akwai baƙin Batutre, akwai baƙar Baturiya, ko baƙin mutum da kan Banasare da kuma baƙar mace da kan Banasariya. Kamar yadda bayani ya gabata cewa, an ɗan taɓo ne. Domin abubuwan suna da yawa. Ina fatan al’umma su fahimci inda wannan muƙala ta sanya gaba. Manufar ita ce mutum ya san shi wane ne, kuma mene ne matsayinsa?Don ya yi kishin kansa, saboda an ce’’ da uba aksse ado, in don riga ko a kasuwa sai a saya’’.

Mun riga munji irin illolin da Turawan nan suka yi mana, ta fuskoki marasa iyaka kuma ta kusurwoyi daban daban. Domin wasu har halitarsu suke sauyawa, daga baƙi zuwa fari ta hanyar shafe-shafe (bleaching) ko dasa gahin kai, nuna tsiraici da sauransu. Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum

MANAZARTA.

Alhassan H. D (1982) Zaman Hausawa. Islamic Publication Bureau, Lagos.

Bunza A. M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere, Lagos.

Banbale M. B. (1994) Kukan Kurciya. Ibramud Nigeria Limited, Zaria.

 Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa. Triunph Publication Kano.

Ɗangambo A. (1983) Kitsen Rogo. Triunph Publication Kano. .

Ɗahiru B (2007) Tafsirin Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.

Imam A. (1937) Magana Jar ice na 1, da 2, da 3. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Madauci I. (1963) Al’adun Hausawa. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Sadiya G. Y. (2005) Talauci Hauka ne? Super Prints Press, Kano.

Williams B. (1979) Human Design. Harvard University Printed USA.

Yaro Y. I. (1971) Tatsunniyoyi da Wasanni. Oxford University Press, Ibadan.

Zindani A. A. (2000) Human Development. Muslim World League Printing Press. Saudi Arabia.

Sarki H. A (2000) Zuwan Musulunci a Afirka da shigowarsu Ƙasar Hausa. G. A. Computer Centre. Ikere – Ekiti, Ekiti State.

 Ɗanfodiyo S. U. (2002) Faɗakar da ‘Yan’uwa a kan halayyar Ƙasar Sudan. 

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments