Ticker

6/recent/ticker-posts

Yanayin Korona A Idon Al’umma: Tsokaci Daga Bakin Marubuta Wakokin Hausa

Cite this article as: Bashir A. S., Bunza U. A. & Abba M. M., (2026). Yanayin Korona A Idon Al’umma: Tsokaci Daga Bakin Marubuta Waƙoƙin Hausa. Zamfara International Journal of Humanities, 4(2), 36-45. www.doi.org/10.36349/zamijoh.2026.v04i02.004.

YANAYIN KORONA A IDON AL’UMMA: TSOKACI DAGA BAKIN MARUBUTA WAƘOƘIN HAUSA

By

Akilu SuleimanBashir1

Umar Aliyu Bunza2

Murjanatu Mohammed AbbaPh.D3

1Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Tarayya ta Lafia, Jihar Nasarawa

2Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

3Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, Tsangayar Kimiyyar Zamantakewa

Tsakure: Taken wannan maƙalar shi ne “Yanayin Korona a Idon Al’umma: Tsokaci Daga Bakin Marubuta Waƙoƙin Hausa”. An shirya wannan maƙalar ne domin duba yadda wasu marubuta waƙoƙin Hausa suka fito da yadda al’umma suke kallon annobar Korona a cikin waƙoƙinsu. Annobar Korona sabuwar cuta ce da Hausawa ba su san ta ba kafin watan Disamba 2019, inda ta bayyana a birnin Wuhan na ƙasar Sin, ta yaɗu a sassan duniya duka. Kasancewar waƙa wani nau’in adabi ne mai tafiya daidai da zamani ya sa aka samu wanzuwar wasu rubutattun waƙoƙin Hausa na Korona. Hanyoyin da aka bi wajen gudanar da binciken sun haɗa da tattaro rubutattun waƙoƙin Hausa da aka yi a kan annobar Korona, aka tsettsefe su da karance-karance a ɗakunan karatu na jami’o’i da tattaunawa da masana a harkar adabi da wasu marubuta waƙoƙin da kuma likitoci. Ra’in Tarihanci (Historicism Theory) ne ya jagoranci binciken domin samun ingantaccen sakamako. A ƙarshe maƙalar ta fito da gudummuwar da marubuta waƙoƙin Hausa suka bayar wajen bayyana yadda al’umma suke kallon annobar Korona kama daga Sarakuna da malamai da talakawa da kuma hukuma..

Fitilun Kalmomi:Annoba, Korona, Al’umma, Marubuta da Waƙoƙin Hausa.

1.1 Gabatarwa

Annobar Korona, wadda aka yi wa laƙabi da (COVID-19) ta faro daga gabashin duniya a ƙasar Sin, sannan sannu a hankali ta yaɗu zuwa sassan duniya. Ganin yanayin yaɗuwar annobar ya sa hukumomin lafiya da malaman addini da sarakuna da kuma marubuta adabin Hausa suka shiga faɗakar da al’umma hanyoyin kare kansu daga kamuwa da cutar Korona. Kasancewar waƙa ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin faɗakarwa ya sa aka sami wasu marubuta waƙoƙin suka yi rubuce-rubuce domin faɗakar da al’umma kan Korona. An sami marubuta waƙoƙin Hausa da yawa da suka yi bayani game da Korona da kuma tunanin al’umma a kan samuwarta da yaɗuwarta. Manufar wannan maƙala shi ne nazarin yadda al’umma suke kallon annobar Korona daga bakin marubuta waƙoƙin Hausa. An yi bayanin maƙalar ne ta hanyar kawo wasu baitocin waƙoƙin Hausa, sannan aka yi sharhi daidai gwargwado.

2.1 Ra’in Bincike

Anɗora wannan aiki a kan Ra’in Tarihanci (Historocism Theory), wanda masanin falsafa Karl Wilhelm Fredrick Schlegel (1829-1972) ya samar. An fara amfani da ra’in tun ƙarni na goma sha takwas (18 Century) inda ake bayyana hanyoyi da tsarin rayuwar al’umma. Haka kuma, ana bayyana yadda wasu al’amurra suka faru a cikin wani zamani da irin cigaba da aka samu cikin al’adu na can dauri da kuma bayanin wurin zaman wata al’umma.

Nazari ta mahangar ra’in tarihanci shi ne dubi zuwa ga al’amura na tarihi a cikin adabi ta hanyar danganta wannan adabi zuwa ga tarihi na haƙiƙa daga masana tarihi, kuma wannan tarihin ya kasance tabbatacce ta sigar rubutu.

Mabiya wannan Mazahaba sun haɗa da Louiz Montroze da Micheal da Montalgre da G.B Vico da George Hegel. Wasu daga cikin nazarce-nazarce na adabin Hausa da aka gudanar ta wannan mahangar ra’in tarihanci sun haɗa da: Usman (2016) da Bunza (2018) da Lawan (2018) da Yusuf (2018) da Ali (2020) da kuma Yusuf (2025).

3.1 Waiwaye Game da Wasu Ayyukan Adabi kan Cutar Korona

An gabatar da ayyuka da dama a kan annobar Korona. Waɗannan ayyuka sun haɗa da littattafai da kundayen bincike da kuma maƙalu. Daga cikin ayyuka da hannu ya kaigare suakwai; Ali da wasu (2020) sun yi nazarin yaɗuwar cutar Korona har ta zamo annoba a shekara ta 2020. Aikin Adegbami da Adesanmi (2020) sun kawo gudummawar gwamnati wajen hana annobarKoronayaɗuwa da taimako da gwamnatin ta yi wa al’umma. SukumaBala da Iman (2020)a nasu aikinsun kawo waƙoƙin daban-daban guda tamanin da shida (86) daga mawaƙan Hausa da na Ingilishi da suka waƙe cutar Korona. Akwai Adamu da Yahya (2020) sun yi nazarin faɗakarwa da salon wasu waƙoƙi biyu na mawaƙan Hausada suka yi a kanannobarKorona. A maƙalar Muhammad da Mustapha (2021) sun yin nazarin hanyoyin daƙile yaɗuwar annobar Korona da sauran cututtuka masu yaɗuwa a mahangar addinin Musulunci.Yunusa da Balle (2021)sun kawo ma’anar cutarKoronabairas da kuma ma’anar cuta daga nan suka yi nazarin waɗansu cututtuka waɗanda suka daɗe suna addabar al’ummar Hausawa da sauran al’ummomi na duniya. AcikinIbrahim (2021) an yi bayanin karɓanci (Transitivity Analysis) a waƙar Idi Loton Korona taKhalid Imam. A cikin aikin Okoye da Nwatu (2022) sun yi nazarin yadda annobar Korona ta sa duniya cikin ruɗani da tashin hankali. Har ila yau, maƙalar ta dubi illolin annobar da hanyoyin daƙile ta, daga nan sai suka bayyana rawar da gwamnati ta taka wajen daƙile annobar Korona, sai Imam da Musa (2023) a cikin nasu aikin an kawo ƙagaggun labarai a kan Korona guda talatin da huɗu (34) daga mabambanta marubuta talatin da ɗaya (31) daga ciki da wajen Nijeriya. Akwai aikin Yakasai da wasu (2023) sun yi tsokaci kan tasirin rubutu ga rayuwar al’umma, domin cimma manufarsu sun yi amfani da labarai guda uku da suka shafiyaƙi da annobar Korona.

Duk da irinrawar dawaɗannanmasana damanazartasuka taka, bai sa an samiwani aiki da aka gudanar da ya yi nazarin Yanayin Korona a Idon Al’umma: TsokaciDaga Bakin Marubuta waƙoƙinHausa ba.

4.1 Ma’anar Al’umma

Al’ummataronmutanene da suke zaune bisa wani tsari na rayuwa guda domin cigabansu.

Masana da manazarta sun bayyana ma’anar al’umma ta fuskoki daban-daban. Dagaciki an samu ayyukan masana da suka haɗa da Ƙamusun CNHN (2006:15) An bayyana ma’anar al’umma dacewa:

“Jama’ar ƙasa ɗaya, ko masu addini ɗaya, ko waɗanda wani abu guda ɗaya ya haɗa su”.

A ra’ayin Yakasai (2020:51) ya kawo an bayyana al’umma da cewa:

“Ɗaukacin mutanen da suke zaune a wuri ɗaya kuma suke da al’adu da ɗabi’u iri ɗaya”.

Masanailimin zamantakewarjama’a (Sociologist) sun bayyana ma’anar al’umma da cewa:

Al’umma wata ƙabila mai asali da yare ɗaya da kamanni (wato ƙirar jikinsu) kusan iri ɗaya, da al’adun gargajiya iri ɗaya da ra’ayin zaman duniya (falsafa) ɗaya sauran irinsu da dama, sannan lallai ne a cikin wannan al’umma kowa yana da’awar shi ɗan wannan ƙabilar ne.

Ya ƙara da cewa al’umma a matsayin “Taron mutane, ko jama’a da abubuwa guda suka wajabtawa zama tare cikin aminci, wannan ko yakan faru ne ta nasabar jini, da auratayya da zamantakewa”. Kenan duk ɗaukacin mutane a tsibiri ko bagire ko nahiya ɗaya wanda kuma jinisu da ɗabi’unsu da asalinsu da harshensu ya zamo iri ɗaya sannan kuma suke ƙoƙarin, samun dorewar zumunta bisa aminci da lumana da kuma ‘yan uwantaka ko abokantaka a tsakaninsu, su ake kira al’umma.

Bisa ga wannan ma’ana a nan an kasa al’umma zuwa gida huɗu kamar haka: Sarakuna da malamai da talakawa da hukuma (Gwamnati). Don haka wannan maƙalar za ta yi nazarin yadda al’umma suka kalli annobar Korona kama daga kan sarakuna da malamai da talakawa da kuma hukumomi.

4.1.1Sarakuna

Sarki shugaba ne na al’umma wanda ya kasance mafi girman martaba da matsayi a tsarin sarautar gargajiya.

An sami masana da manazarta da suka bayyana ma’anar sarakuna ta fuskoki da dama. Daga cikin ayyukan masana da aka samu akwai: Ƙamusun CNHN, (2006:392) an bayyana sarki da cewa:

“Mutumin da aka naɗa ta hanyar gargajiya don ya shugabanci mutane ta hanyar mulki ko sana’a ko wani abu”

Shi kuma Yakasai(2020:119) ya bayyana sarakuna da cewa:

“Sarakuna su ne shuwagabannin jama’a. A idon Bahaushe su ne uwa su ne uba ga al’umma. Bugu da ƙari kuma, su ne wuƙa su ne nama, a cikin harkokin jama’arsu. A kan abin da ya shafi jagoranci”.

Sarakunan gargajiya sun taka rawar gani wajen yaƙi da annobar Korona,inda sukawayar da kan al’umma a kan illar annobar sun kuma bayyana musu matakan da za abi wajen kariya daga kamuwa daga cutar Korona a masarautunsu.(Ɓaɓura da Abdallah, 2020:13)

Marubuta waƙoƙin Hausa sun taskace gudummawar da Sarakuna suka bayar domin daƙile yaɗuwar annobar Korona a waƙoƙinsu. Misali a waƙarCutar Korona”,. Ga abin da ya ce a wannan baiti kamar haka:

bt. 6Likkitoci sun bayani,

Malamai ma sun yi nuni,

Shugabanni sun umarni,

Bin matakai ba da gardama ba.

(Halliru Abdullahi: WaƙarCutarKorona)

A layi na uku, marubucin ya bayyana irin gudummawa da sarakuna (shugabanni)suka bayar domin daƙile yaɗuwar cutar Korona. Sarakuna rukuni ne babba na shugabancin al’umma wanda yake da ƙarfin ba da umurni na aikatawa ko hanawa. Sarakuna manya da ƙanana sun ba al’ummar da suke shugabanta umurni na kiyaye dokoki da aka fitar domin kare kai ga kamuwa da cutar Korona. Mawaƙin ya nuna sun ba da umurni na bin matakai da aka samar ba tare da yin jayayya a kansu ba. A zamanin tashen annobar Korona ba a sami wani sarki da ya yi gardama kan matakan da hukumomi lafiya suka fitar ba har aka yi, aka ƙare. A maimakon haka sai suka yi ta ƙarfafa wa talakawansu guiwa kan tsare dokoki da bin matakan da aka fitar domin kariya ga lafiyarsu.

A cikin wani baitin waƙar wani marubucin ya nuna irin gudummawar da Sarkin Musulmi ya bayar wajen faɗakar daal’umma musamman maMusulmi a kan annobar Korona. Ga yadda bayanin ya fito a wannan baiti:

bt. 1Ga shi dai Sarkin Musulmi,

Yai kiran dukkan Musulmi,

Da su ɗau magana ta ilmi,

Ba zancen masu gardama ba.

(Abdullahi Abubakar Lamido: Waƙar Koronabairas)

Sarkin Musulmi uba yake, kumashi ne jagora a wajenMusulman Nijeriya. Don haka,komai ya fito daga bakinsa suna karɓa hannu bibbiyu, su kuma yi amfani da shi. A wannan baiti an nuna kira Sarkin ya yi da babban murya ga dukkan Musulmi da su gaskata maganar masana, su yi aiki da ita dangane da yaɗuwar cutar ta Korona.Ya kuma gargaɗi mutane (Musulmi) baki ɗaya da su ɗauki maganar likitoci da masu ruwa-da-tsaki a kan harkar, su kuma guje wa maganganun masu ƙaryata wanzuwar cutar a Nijerya da ma duniya baki ɗaya.

Magana ta masana, ita ce mai muhimmanci da take samar da mafita da zaman lafiya a tsakanin jama’a. Wannan ya sa Sarkin Musulmi, matsayinsa na shugaba ya kira al’ummar Musulmi da su yi ɗa’a ga maganar masana domin a tsira daga sharrin cutar Korona.

Ita kuma maganar masu gardama ita ce zancen maras tushemai cike da ruɗani da yake fita daga bakunan marasa ilimi na lafiyar al’umma, ƙarshe da-na-sani ya biyo baya. Wannan ya sa Sarkin Musulmi ya yi kira da al’umma su daina ɗauka da yarda da irin wannan magana domin kauce wa abin da zai je ya dawo na faɗawa cikin ƙunci da annobar take haifarwa.

Bayanan tarihi sun tabbatar da cewa sarakuna sun taka rawar gani wajen daƙile yaɗuwar annobar Korona kamar yadda marubuta waƙoƙin Hausa suka bayyana.An sami wasu ayyukan tarihi da suka nuna irin rawar da sarakunan suka taka. Daga cikin ayyukan akwai:(Ɓaɓura da Abdallah, 2020:14) da aka kawo bayanin dacewa:

A lokaci da ake raɗe-raɗIn gujewa karɓar allurar riga-kafin cutar Korona, wasu daga cikinsarakuna a Arewacin Nijeriya, sun haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen ganin an wayar da kan al’umma a kan muhimmacin allurar. A jihar Kwara tsoma hannun sarakunan ya taimaka wajen tururuwar talakawa zuwa ga gwajin cutar. (Fassarar mai bincike).

An samu wasu ayyukan tarihi da suka bayyana gudummawar sarakuna wajen daƙile yaɗuwar annobar Korona. daga cikin ayyuka da aka samu akwai:

4.1.2 Malamai

Malamai a cikin al’ummar Hausawa sun kasance masu ƙimakusan duk abin da suka faɗa wa al’umma ba tantama akan karɓa hannu bibbiyu, kuma a yi amfani da shi domin abin da ake kallon su da shi na kirki, da tsoron Allah.

Malamai wasu kaso ne masu muhimmanci a cikin al’ummar Hausawa. Kaso ne da yake tsakanin shugabanni (sarakuna) da talakawa. Aikin malamai shi ne jan hankali da tsawatawa al’umma ya sa ake ɗaukar rukunin nasu babba, mai muhimmanci a cikin al’umma.

A ƙoƙarin fito da ma’anar malami an dubi ayyukan masana da manazarta domin sayen gaskiya biyan gaskiya wai malam ya sayi malam in ji masu iya magana.A fahimtarBunza, (2004:5) ya bayyana kalmarda cewa:

Malami asalinta daga Larabci take ba Bahaushiya ba ce (Bunza (1999). Gabanin bayyanar Musulunci aƙasar Hausa wannan kalma babu ita, bayan da Musulunci ya samu karɓuwa karatu ya samu gindin zama aƙasar Hausa, Malantaka ta bayyana, (Musa 1999). A aľadar Bahaushe Malami na da wasu sifofi bayan na karatu da koyarwa waɗanda ake iya rarrabe shi da waɗanda ba Malamai ba, (Bunza, 1999). Daga cikin sifofinsa akwai tsarin suturarsa ta fuskar naɗi da kawaicinsa, da kaɗaitarsa, da kamun kansa, da daimakamantansu. Duk da haka, kowane mutum na iya ya ari waɗannan siffofi da gangan ko ga dabi'a har ayi masa zaton Malanta ko da bai san ko bihin ba, (Imam, 1933).

An ƙara samun wani ma’anar malami da wani masani ya bayar inda ya ce:

“Bahaushe yana kallon malami ne a matsayin idanu ga al’amuransa. Don haka ne ma a kan ce, malamai magada annabawa,” abin nufi a nan shi ne, yadda annabawa suka kasance idanun al’umominsu. Haka, malamai suke a wurin mutanensu; kuma suke yin aikin shiryar da mutanensu. A haka ne malam Bahaushe ya ɗauki malami, kuma domin haka ne ma yake wancan kirarin da aka ambata”. (Yakasai, 2020:121).

Wasu ayyuka da suka bayyana ma’anar malami sun haɗa da: Musa, (1995:406) da Ƙamusun CNHN, (2006:238) da Birnin Tudu, (2013:341) da Aminu, (2013:3) da sauransu.

A cikin rubutattun waƙoƙin Hausa, an sami wasu marubuta da suka kawobayanaidangane da irin gudummawar da malamai suka bayar wajen daƙile yaɗuwar annobar Korona.Misalia cikin waƙar Abdullahi Abubakar Lamido. Ga abin da ya ce a waɗannan baitoci:

bt. 2Malamai sun yo bayani,

Bisa Hadisi da Ƙur’ani,

Da jawaban masu fannin,

Likitoci ba da yaudara ba.

Awaɗannan baitoci marubucin ya nuna yadda malamai suka tsayar da ƙafa wajen yi wa al’umma nasiha daga Hadisai da Ƙur’ani domin mutane su gaskata abin da likitoci suka faɗa dangane da cutar Korona kuma hakan ya yi daidai da cewar Annabin rahama (SAW) da kuma cewar Ƙur’ani, idan annoba ta shigo cikin gari ku ƙauracewa taro da cakuɗuwar jama’a a wurare taruwa kamar masallaci da kasuwa da sauransu.

Bayani kan annobar Korona bisa madogara guda uku: Ƙur’ani da Hadisi da bayanan masana kiwon lafiya. Waɗannan abubuwa uku su ne kaɗai hanyoyin sanin komai a tsarin Musulunci.

Ƙur’ani shi ne littafin Allah (SWT) wanda ya haɗa ilimin komai yake a cikinsa. Hadisi shi ne zancen Annabi (SAW) wanda sharhi yake yi kan ayoyin Ƙur’ani. Jawabin masu fanni shi ne masana a wani fanni na ilimi, a nan sai ya ce likitoci saboda sha’anin kiwon lafiya ne. Idan aka yi la’akari da wannan baiti,za a fahimci marubucin ya nuna abin da malamai suka yi na faɗakar da al’umma kan cutar Korona sun yi ne da wata madogara ta ilimi da addini ya amince da ita ba son ransu ba.

Wani bayani na gudummawar Malaman ya sake fitowa a baitin waƙar “Korona a Kano”, inda marubucin ya ce:

bt. 13Fatawa an yi ta na ji,

Juma’a za mui a ɗaki,

Duk Masallatai a ƙulle,

Zamani ya zo da riga,

Babu zaɓi sai sakawa.

(Khalid Imam: Waƙar Korona a Kano)

Wannan baitiyana magananea kan neman bayani kan wata matsala, musamman da ta shafi addini. Abin nufi a nan,marubucin ya yi bayani a kan irin rawar da Malamai suka taka wajen nuna wa al’umma muhimmancin yinSallar Juma’a aɗaki, maimakon yin ta a Masallaci kamar yadda aka saba. Wannan bayanin ba zai rasa nasaba da dokar da masanakiwon lafiyasuka sanar na hana taro ko cunkoson mutane a wuriɗayaba domin hana cutar Korona yaɗuwa. A layi na uku sai yaƙara da cewa dukMasallatai akulle, zamanineya zo da wata irin matsalawadda ta kai gahana salla cikin jam’i.Wannanbabban mataki ne na daƙileyaɗuwarcutarKorona.

An sake samun wani bayani na gudummawar Malamai a wani baitin waƙarMahmud Ahmad Musa. Ga abin da marubucinyace a wannan baiti:

bt. 12A Juma’ar jiyan nan a mumbarin karatu,

Mafiyawan limamanmu ga su nan fitattu,

Suna ta yin du’ai ga dukkanin halittu,

Da keɓe shugabannin bare na Bauchi nawa,

Da keɓe shugabannin bare na Bauchi nawa.

(Mahmud Ahmad: Waƙar Corona Ba Shiri Ba)

Acikinwannan baitin waƙa, marubucin ya kawo wani muhimmin wuri da malamai suke samun dandazon jama’a, su yi musu wa’azi. Wannan wuri shi ne mumbarin Jumu’a. Ranar Jumu’a, rana ce babba, kuma mai muhimmanci ga kowane Musulmi. Rana ce ɗaya a cikin kwanakin mako da mafi yawan Musulmi suke halarta a wani Masallaci domin yin sallar Juma’a da kuma sauraron huɗuba (wa’azin limami kafin salla).

A ranar Juma’a, limamai da dama sukan shirya huɗubarsu kan wani abu da ya taso mai muhimmanci ko illa. Tasowar Korona ya zama muhimmin abu da limamai suka mayar da hankali wajen karantar da al’umma lamarinsa. Limamai da dama sun yi bincike, sun tatttara bayanai kan Korona, sannan sun bayyana wa taron al’umma fahimtarsu kan annobar a numbarin Juma’a. Wannan batu ne marubucin ya kawo a layi na farko a wannan baiti.

Tarihiyatabbatar da cewa Malamai sun ba da gudummawa wajen daƙile yaɗuwar annobar Korona kamar yadda marubuta waƙoƙin Hausa suka nuna a baitocin waƙoƙinsu.An sami wasu ayyukan tarihi da suka nuna irin rawar daMalamai suka takakamar (Khalil, 2020:5) Inda aka ce:

“An daɗe ana gamuwa da ibtila’i da jarrabawa a faɗin duniya, kwalara da Annoba da yaɗuwar cututtuka ya daɗe yana addabar duniya, kuma ana iya masa fassara iri-iri, kowa gwargwadon abin da yake ɗauke da shi na aƙida ko hankali ko al’ada ko surkulle. Amma mu a mahanga ta addini muna ɗaukar waɗannan a matsayin jarrabawa da jan kunne da Allah yake yi wa mutane domin su saduda, su sallamawa Allah, su yadda wannan duniya akwai me ita, kuma yana da iko a kanta kuma zai iya tashi ta duk sadda ya ga dama.... Mu yi abubuwa biyar: na ɗaya yadda ƙaddara mai daɗi da mara daɗi duk daga Allah ne, mu ɗauki matakan kare kai yadda jami’an kiwon lafiya suke faɗa, mu duƙufa da tuba da istigfari da komawa ga Allah, domin ya yaye mana wannan Annoba, da yawaita zikiri da addu’a, duk musulmi da ya mutu ya yi shahada.

Kada mu shiga inda Annoba take, kada mu fita daga inda ake yi har sai an tabbatsr da bamu ɗauka ba”

4.1.3Talakawa

Talaka (tilo) talakawa (Jam’i) rukunin mutanemai muhimmanci a zamantakewar Hausawa. Shi ne rukuni da ya fi sauran yawan mutane. An sami ma’anoni da wasu masana suka bayar kan talaka kamar haka: Ƙamusun CNHN(2006:423) an bayyanakalmartalaka ta fuskoki biyu:

 i.  mutumin da bai riƙe da wani muƙami na sarauta

 ii.  mutum maras wadata.

Shi kumaBunza (2009:34) ya kawo ma’anar talaka kamar haka:

Talaka na nufin duk wani mutum da ke zaune aƙasakuma ba ya riƙe da kowace sarauta”. Abin lura a nan shi ne idan aka samu mutumɗauke da wata sarauta to ya tashi daga zama talaka ya koma Basarake. Domin yana ɗauke da wani muƙami da kan sa a kira shi Sarki.

A wannan bincike an ɗauki wannan ma’ana da ta nuna duk wanda ba ya riƙe da wani muƙami na sarauta shi ne talaka. Talakawa a ƙasar Hausa sun kalli cutar Korona ta fuskoki daban-daban. Wasu sun yarda akwai ta, wasu kuma suna gani ƙarya ce kawai, ƙirƙirar ta aka yi domin shugabanni su wawushe asusun gwamnati. Irin wannan bambancin fahimta an sami wasu marubuta waƙoƙin Hausa da suka kawo shi cikin wasu waƙoƙinsu. Misali, Khalid Imam ya kawo bayanin yadda talakawa suka kalli annobar Korona a matsayin kwangila ce babu ita a doron ƙasa. Ga abin da ya ce a wannan baiti:

bt. 10 Wannan niyya ta sharri,

Kwangila ce babu fashi,

Wadda za su sayar da riba.

(Khalid Imam: Waƙar Siyasa Ce Korona)

Wannan baiti marubucin yana bayanin yadda talakawa suka kalli annobar Korona a matsayin babu ita. Kwangila ce kawai na wasu mutane da suka yi amfani da ita suna azurta kansu da dukiyar ƙasa a matsayin nema wa talakawa mafita ko kuma maganinta.

Wani bayani na rashin yarda da cutar Korona a wajen talakawa ya fito a waɗannan baitocin waƙa. Ga abin da marubucin ya ce:

bt. 17Idan ka yi tari a ce wai Korona,

Kana Zazzaɓi ba batun ma a auna,

Abin ma da gangan akemaƙƙalawa.

(Mahmud Ahmad Musa: Waƙar Korona Ƙasata)

A zamanin Korona, talakawa da yawa sun nuna wasu abubuwa da dama na rashin yarda da cutar Korona ma’ana ba gaskiya a cikinsa. Tari da zazzaɓi yana cikin abin da aka nuna alamomi ne na cutar Korona. Dukkan waɗannan rashin lafiya ne da Hausawa suka saba da su tun lokaci mai tsawo kafin Korona. Akwai tarin mura da tarin sanyi da sauransu. Shi ma zazzaɓi akwai na cizon sauro da na mura da sauransu da yawa. A zamanin Korona sai ya zama idan ɗaya daga cikin waɗannan ya bayyana ga mutum, ya yi tsanani, kai tsaye sai masu alhakin lura da Korona, su ce Korona ce, ba tare da an tantance sosai ba. Wannan ne ya sa mawaƙin ya kawo batun rashin aunawa wanda ya sa ya ce da gangan ake liƙa wa jama’a Korona.

bt. 77 Batun nawa sam ba ba’a ba habaici,

Kashedi na ɗan yo mu farka a bacci,

Mu gane Korona da ƙarya haɗawa.

(Mahmud Ahmad Musa: Waƙar Korona Ƙasata)

Ɗaya daga cikin naƙasu da aka samu a zamanin Korona shi ne na rashin sakakancewa da talakawa ba su yi ba ga al’amarin Korona. Talakawa da yawa sun ɗaukaal’amarin Korona an cakuɗaƙarya a cikinsa. Talakawa da yawa sun ɗauka idan ma akwai Korona, to ba ta kai yadda hukuma ta ririta ba. Mutane da yawa sun lura zafin Korona ya ƙare kan mai ƙaramin ƙarfi ne kawai. Da yawa waɗanda aka killace talakawa ne, ƙalilan ne masu riƙe da madafun iko. haka kuma shugabanni sun tursasa wa talakawa bin dokokin Korona, alhali su suna gudanar da al’amuransu cikin tsanaki. Babban abu ma yadda Korona ta zama wata hanyar azurta kansu daga kuɗaɗen da aka fitar domin rage raɗaɗin Korona. Wannan ne ya sa marubucinya nuna da haɗin ƙarya cikin sha’anin Korona.

Idan aka yi la’akari da baitukan marubutan waƙoƙin Hausa kan yadda talakawa suke kallon annobar Korona ya yi daidai da abin da tarihi ya tabbatar.An sami wasu ayyukan tarihi da suka nuna yadda talakawa suke kallon annobar. Misali(Khalil, 2020:3) yana cewa:

“Wasu suna da ra’ayin wai ƙasar China ta ƙirƙiro cutarKoronane don ta saye hannun-jarina manyan kamfanonin duniya da suke ƙasar ta, don taƙarawa kantaƙarfinfaɗa a jiaduniya!Wai sun kau da kai ne wasu mutane a ƙasar suka mutu domin a ƙarshe su ci nasararɗaga tattalin arrzikinsu da ya fara daƙushewa. “

Sai kumaLamiɗo (2023:19) yana cewa kamar haka:

“Yanzu ga shi ka dawo sanyin gari ya kada ka, ka kulle kanka, wai kai ga ka mai cutar sarƙewar numfashi? To, ba a nan gidan ba! Kwangilar Nasara ko? Su da cin kuɗi, kai da ƙaryar ciwo? Tsaya ka ji! Tun kafin uban Mangofak ake mura.”

4.1.4 Hukuma

Hukuma (gwamnati) ita ce rukunin jama’a da ke tsarin lamurran jama’a bisa wani tsari da aka amince da shi. Akwai ma’anonin wasu masana da aka samu kan wannan rukuni. Ga misaliƘamusunCNHN(2006:181)ankawo ma’anar Gwamnati dacewa:

“Hukumar ƙasa ko ta jiha”.

A ra’ayin Mustapha, (2024:204) ya bayyana hukuma (Gwamnati)dacewa:

“Hukuma ko Gwamnati ita ce ke yin tsare-tsare da gudanar da ayyukan ƙasa ga jama’arta ta fuskar tsaron ƙasa da samar da buƙatun al’umma da kuma bunƙasa al’ummar baki ɗaya. Tsarin tafiyar da mulkin gwamnati ya kasu kashi biyu. Ta mulkin soja da ke tsarawa kuma ta yi amfani da ‘dokar Soja’ (decree) wadda babbar majalisar ƙoli ta soja ta ƙasa ke tsarawa. Gwamnatin farar hula (‘yan siyasa) da ke samar da tsarin mulkin soja (Constitution) wanda babban kwamitin gyara tsarin mulki ke yi ma gyaran fuska, ko kwamitin kula da dokoki na majalisar ƙasa”.

An sami wasu marubuta waƙoƙin Hausa da suka taskace rawar da hukumomi suka taka wajen yaƙi da hana yaɗuwar annobar Korona a cikin Nijeriya. Misali Aliyu Idris Birnin Kudu, ga abin da ya ce a wannan baiti:

bt. 24Gwamnati ta sa a killace mu,

Domin kare lafiyar jikinmu,

Amma gwamnati ki tallafe mu,

A taimaki al’ummar ƙasarmu

Domin yunwa kar ta kar mu.

(Aliyu Idris Birnin Kudu: Waƙar Korona Tana Da Illa)

Ɗaya daga cikin matakan daƙile yaɗuwar Korona da hukuma ta fitar shi ne killace mutane. Hukuma ta ɗauki matakin killace mutane da suka kamu da cutar Korona a wasu cibiyoyi da aka tanada a wurare da yawa. Duk wanda aka sami labarin ya kamu ko aka sami bayanin alamomin cutar Korona gare shi sai a kai shi can cibiya inda za a ci gaba da kula da shi. Sauran jama’a kuma aka killace sua cikin gidajensu ta hanyar tilasta musu zama gidatare da hana su sukunin zuwa wani wuri, ko yin taro ko halartar kowane nau’in aiki da zai haifar da cunkoson jama’a ciki har da salloli da sauransu. Irin wannan killacewar ta gurgunta al’amurran jama’a, tattalin arzikinsu ya karye. Wannan ya sa aka shiga kira ga gwamnati ta taimaka, ta ba al’umma wani tallafi domin rage raɗaɗin Korona kamar yadda marubucin ya kawo a layi na uku a baiti.

An sake ganin gudummawar hukuma wajen daƙile yaɗuwar annobar Korona awani baitin waƙar Ahmad Shanawa.Ga abin da marubucin ya ce a wannan baiti:

bt.5Ga gwamnatin ƙasa ko ta ina suna ƙoƙari,

Su daƙile yaɗuwar cutar cikin hanzari,

Mu ba hukuma haɗin kai karda muiyi ƙoƙari,

Mu jefa kayinmu a cikin halin damuwa,

Ga Corona ta hana mu ji daɗin rayuwa.

(Ahmad Shanawa: Waƙar KoronaƘuncin Rayuwa)

Wannan baitin waƙar ya nuna irin ƙoƙari da gwamnati ta yi wajen hana yaɗuwar annobar Korona a cikin hanzari. An samar daCibiyar Yaƙi da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) wacce aka ɗora wa alhakin gano mutane da suke ɗauke da cutar ko waɗanda aka samu labarin dawowarsu daga ƙasashen da ake da labarin ɓullar annobar domin a killace su a kuma ba su magani. Sauran matakai da aka ɗauka sun haɗa da hana zirga-zirga da rufe wuraren taruwar jama’a da sauransu. Wannan shi ne abin da marubucin ya yi ishara da su a cikin baitin.

Shi ma Halliru Abdullahia cikin waƙarsayabayyana gudummuwar hukuma wajen daƙile annobar Korona a wata waƙa da ya rubuta. Ga abin da ya ce a wannan baiti:

bt. 13Ai hukuma ta yi doka,

Kar waninmu da ɗai ya taka,

Kun ga wanda ya karya doka,

To hukuma ba ta kau da kai ba.

(Halliru Abdullahi: Waƙar Korona)

Bayanin wannan baiti ya kawo cewa,gwamnati ta yi doka inda aka hana zirga-zirga, aka rufe wuraren ibada da makarantu da filayen wasa, ta hana taruka da sauransu domin daƙile yaɗuwar annobar Korona. Wasu daga cikin dokokin sun yi nauyi ga talakawa, abin da ya sa wasu suka taka dokokin na hukuma. Ɗaya daga cikin haƙƙin hukuma kuma shi ne hukunta duk wanda ya karya dokarta. Wannan ne marubucin ya ja hankalin al’umma zuwa gare shi daga layi na biyu na baitin waƙar.

Bayanan tarihi sun tabbatar da cewa Gwamnati ba da gudummawa wajen daƙile yaɗuwar annobar Korona kamar yadda marubuta waƙoƙin Hausa suka bayyana.An sami wasu ayyukan tarihi da suka nuna wannan gudummawar kamarhaka(Omaka-Amari da Aleke da Obande-Ogubuinya da Ngwakwe da wasu. (2020:89)Inda suka ce:

Wani mataki da Gwamnati da masu ruwa da tsaki suka ɗauka shi ne wayar da kan talakawa a kan annobar Korona da kuma hanyoyin daƙile yaɗuwarta. Ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwa da suka haɗa da: rediyo da talabijin da jaridu da hanyoyin sada zumunta. Har ila yau, an ja hankalin mutane da a bi dokar ba da tazara da wanke hannu a kaia kai da sinadarin kashe ƙwayar cuta da sanya takunkumin rufe fuska da kuma tsaftace muhalli. Ganin annobar na cigaba yaɗuwa sai Gwamnatin ta sake ɗaukar matakan zaman gida a jihohi uku da annobar ta fi yin tasiri da rufe iyakokin ƙasar. (Fassarar mai bincike).

5.1 Sakamakon Bincike

Aƙarshen kowane bincike a kan fito da irin abin da ya gano. A wannan binciken maƙalar ta gano cewa:

 i.  Sarakuna sun haɗa kai da hukumomi wajen yaƙi da yaɗuwar annobar Korona a tsakanin al’umma.

 ii.  Maƙalar ta gano yadda malamai suka yi tsayin daka wajen yi wa al’umma bayani a kan illar annobar Korona tare da bin dokoki da mahukunta suka kawo. Malaman sun kafa hujja daga bayanan Alƙur’ani da hadisai da bayanan masana kiwon lafiya.

 iii.  Har ila yau, maƙalar ta gano yadda talakawa suke kallon annobar Korona, wasu sun ƙaryata ta suna gani ƙirƙirarta aka yi.

 iv.  Haka kuma maƙalar gano wasu talakawan na ganin annobar kwangila ce kawai na wasu mutane domin su azurta kansu da dukiyar ƙasa.

 v.  Daga ƙarshe maƙalar ta gano irin gudummawa da hukumomi suka bayar wajen yaƙar da cutar Korona. Daga ciki sun ɗauki matakan hana zirga-zirga a tsakanin jihohi da ƙasashe da killace al’umma da rufe kasuwanni da wuraren ibada da makarantu da filayen jiragen sama da sauransu.

6.1 Kammalawa

Amaƙalar an kawo gabatarwa sai bitar wasu ayyuka da aka yi daga nan sai aka kawo ma’anar al’umma kamar yadda masana suka kawo.Daga nan sai aka tsunduma yin nazarin yadda al’umma suke kallon annobar Korona,kama daga sarakuna da malamai da talakawa zuwa ga hukumomi tare da kafa hujjoji daga wasu baitocin rubutattun waƙoƙin Hausa da aka yi a kan cutar Korona,sai kuma sakamakon bincike ya zo daga ƙarshe

Manazarta

1. Adamu, A. A. da Yahya, A. B. (2020).Kukan Kurciya Cikin Waƙoƙin Korona Biyu.Zariya: Ahmadu Bello University Press Limited.

2. Ali, B. Y. (2020). Cuɗanyar Adabi da Al’ada: Nazarin Tarihi a Cikin Wasu Waƙoƙin Baka na Hausa. A cikinƊUNDAYE Journal of Hausa Studies. Vol. 2 no. 3, December 2020. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Shafi na 291-300.

3. Ali, M. G.,Ahmad, M. O.,da Husain, S. N. (2020). Spread of Corona Virus (COVID-19) from an Outbreak to Pandemic in the Year 2020. InAsian Journal of Research in Infectious Diseases.3(4):37-51, 2020; Article no. AJRID.56358. ISSN:2582:3221.

4. Aminu, N. (2013). Malami a Mahangar Marubuta Adabin Zamani: Nazari daga Littattafan Gasar Rubutu ta 1933”. A cikinA Great Scholar and Linguist.A Festscript in Honour ofProfessor Ibrahim Ahmad Mukoshy. Department of Nigeran Languages. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

5. Bala, I.,da Imam, K. (2020).Corona Blues A Bilingual Anthology of Poetry. Kano: Whetstone Publishers.

6. Birnin Tudu, A. Y. (2013). Falsafan Malanta Cikin LittafinRuwan Bagaja”. A cikin Bunza A. M. da Noofal M. A. (Editoci).Ruwan BagajaIn Perspective: Eight Decades of Hausa Master Piece In Prose (1933-2013). Zaria: AhmaduBello UniversityPrinting Press.

7. Bunza, A. M. (2004).Gwagwarmayar Malam Maikaturu da MalamanƘasar Hausa (Darasi Ga Malaman Yau, Ƙalubale Ga Na Gobe)Takardar Da Aka Gabatar ATaronƘarawa Juna Sani ABukukuwan Shekara 200 Da Kafa Daular Musulunci TaSakkwato, Mai Take.Gudummawar Malamai, Wanda AkaGabatar A Makarantar Hardar Alkur’ani Da Ilmukan Musulunci taAttahiru Bafarawa, Sakkwato, Daga 23 - 25, Yuni2004.

8. Bunza, A. M. (2009).Narambaɗa. Lagos: Ibrash Publications.

9. Bunza, D. B. (2018). Tarihi A Rubutaccen Adabi: Nazari A Kan RayuwarKyaftin Umaru Ɗa Suru Daga Waƙoƙinsa. Kundin Digiri na Uku, Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

10. Ɓaɓura, Z.daAbdallah, H, A. (2020).Fight Against COVID-19 and the Role of Traditional Rulers in Northern Nigeria. InCARI Journals of Advanced Sociology.Vol. 2 Issue 1 pp-9-18.www.com.journalcari.org.

11. Ibrahim, S. G. (2021). Transitivity Analysis of Idi Loton Korona by Khalid Imam. A Seasoned Hausa Phonologist: In A Gedenkschrift for the Late Professor M. A. Z. Sani. Official Publication of the Department of Nigerian Languages, Faculty of Arts and Islamic Studies,Kano: Bayero University,

12. Imam, K. da Musa, U. A. (2023).Rigakafin Korona Kundin Gajerun Labaran Hausa Kan Annobar Korona. Kano: Whetstone Publishers.

13. Musa, S. (1995). Malami a Ƙasar Hausa.A Paper Presented at the 5thInternationalHausaConference. Centre for the Study of Nigerian Languages. Kano: Bayero University.

14. Khalil, Y. A. (2020). Annobar ‘Corona-Virus ko Covid19’; Bambancin Ra’ayida Mahangar Malamai: Kano: Muslims Student Society of Nigeria.

15. Lamiɗo,A. (2023). Bari Ba Shegiya Ba ce........ a cikinRigakafin Korona Kundin Gajerun Labarai. Kano: Whetstone Publishers

16. Lawal, N. (2018). Adabi da Tarihanci: Nazarin Wasu Wasanni na Rudolf Prietze. Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

17. Muhammad, A. Y.,da Mustapha, A. B. (2021). An Overview of the Preventive Measures on Covid-19 Pandemic and Other Infectious Disease from Islamic Perspective. InDUNAMA Journal of Islamic Studies(DUJIS) Vol. 1. No.1 A Biannual Journal of the Department of Islamic Studies. Lafia: Federal University.

18. Okoye, U. O. da Nwatu, U. L. (2022). Covid-19 Pandemic in Nigeria: A Story Worth Telling from the Eyes of Social Workers. The Coronavirus Crisis and Challenges to Social Development.https://doi.org/10.1007/978-3-030-84678-7-24

19. Usman, M. Y. (2016). Waƙa: Tubalin Gina Tarihin Ƙasar Hausa. Kundin Digiri na Biyu. Zaria: Jami’ar Ahmadu Bello.

20. WHO, (2021). Nigeria Rallies over 7000 Traditional Leaders Against Covid-19.

21. Yakasai, S. A.,Bunza, U. A.,da Atuwo A. A. (2023). Yaƙin Alƙalami Ya Zarce Yaƙi da Kwari: Ƙawancen Tunani a Salon Rubutu akan Yaƙi da KORONA. Maƙalar da aka Gabatar a ranar 7/11/2023 a Taron Ƙara wa Juna Ilimi da Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,Sakkwato:Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

22. Yakasai, S. A, (2020).Jagoran Ilimin Walwarar Harshe. Printed in Nigeria by Amal Printing Press.

23. Yunusa, A.da Balle, A. M. (2021). Dangantakar Cutar Mashaƙo (Coronavirus) da Wasu Cututtukan da aka sani a Ƙasar Hausa. A cikinFARFARU Journal of Multi-Disciplinary Studies.Vol. 10 Series 1. Sokoto: Shehu Shagari College of Education.

24. Yusuf, J. (2018). Tarihin Jam’iyyar PDP A Bakin Marubuta Waƙa. Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

25. Yusuf, J. (2025). Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu a Cikin Rubutattun Zuben Hausa Daga 1950-2023. Kundin Digiri na Uku. Sakkwato Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

 

Post a Comment

0 Comments