Cite this article as: Al-Musawi, I. U., Girei, I. I., & Umar, H. (2026). Gurbin Naƙasa a Cikin Karin Maganar Hausawa.Sokoto Journal of Linguistics and Communication Studies (SOJOLICS), 2(2), 492-504. https://doi.org/10.36349/sojolics.2026.v02i02.046
GURBIN NAƘASA A CIKIN KARIN
MAGANAR HAUSAWA
Na
Isa Umar AlMusawi
Sashen Nazarin Harshen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Yola
Jihar Adamawa
+2347037131666
&
Ibrahim, Ismaila Girei, PhD
Sashen Nazarin Harshen Hausa
Kwalejin Ilimi ta Jihar Adamawa,
Hong
Jihar Adamawa
_+2348022495128
&
Hussaini Umar
Special Education
Jamiʼar Bayero, Kano
+2347065951951
Abstract
Proverb is one sense statements in Hausa; it takes someone longtime to achieve something. Life is a mixture of sweetness as well as bitterness; scholars are saying life of an individual would not be complete until he/she comes to an end. This paper titled place of disability in Hausa proverb, aims to bring out proverbs that are in relations with disability in Hausa literature and to rescue these proverbs from extinction. The objectives of this paper are to show to the world how Hausas use proverbs that have relationship with disability in their daily activities. This paper applied interview and the used some related books on disability in gathering data. However, the paper gives more light on Hausa proverbs and proverbs that are mainly on disability in order to express sense statements in an aspect of language and literature of Hausa. Finally, the paper found that, Hausa has verse sense statements, where it touches all aspect of human endeavor. This paper also found out that, some disabilities are inborn people inherited them from their forefathers, while some are as a result of accidence.
Keywords: Disability, Hausa, literature, place, proverb
Tsakure
Karin Magana yana daga cikin
zantukan hikimar Hausawa. Sannan kuma ai ba a yabon ɗan kuturu sai ya mutu da
yatsunsa. Kasancewar rayuwar duniya juyi-juyi ce, yau ana lafiya gobe kuma wata
larurar takan iya aukuwa. Masu hikimar Magana sukan ce halittar mutum ba ta
cika sai ranar da ya bar duniya (mutu). Saboda haka ne, wannan takarda mai
taken: Gurbin Naƙasa a Cikin Karin Maganar Hausawa, ta yi nazarin maʼanar
naƙasa da dalilan da sukan sanya naƙasa da misalanta. Haka nan, ta yi ƙarin
haske game da karin maganar Hausawa, kuma ta tsamo wasu karin Magana masu alaƙa
da naƙasa, domin nuna irin hikimar da ke tattare a cikin harshe da adabin
Hausa. Sannan ta bayyana halin komai da ruwanka da harshen Hausa yake da shi,
na babu ɓangaren da bai taɓo ba na daga rayuwar mutane. Manufar wannan takarda
ita ce zaƙulo karin maganar da suke cikin adabin Hausa masu dangantaka da
naƙasa, tare da taskace su maganin salwanta, dominʼyan baya su amfana.
Maƙasudin Bincike kuwa, shi ne wajjahar wa duniya irin hikimar da Hausawa suke
da ita wurin amfani da karin Magana masu dangantaka da naƙasa a cikin zantukan
suna yau da kullum. Sannan an yi amfani da binciken littattafai masu dangantaka
da wannan aiki a cikin ɗakunan karatu. Haka nan, an tattauna da masu larurar
naƙasa daban-daban, domin samun ƙarin haske game da wasu karin maganan. Sannan
takardar da jero karin maganar Hausawa waɗanda suke da dangantaka da naƙasa.
Daga ƙarshe sakamakon binciken ya nuna irin faɗi da hikimar da harshen Hausa
yake da suna cewa babu ɓangaren da ya ware a rayuwar mutane ba tare da ya samar
masa da matsuguni ba. Haka kuma ya nuna wata naƙasar ana gadonta ne tun wurin
iyaye da kakanni ba a nan duniya ake gamuwa da ita ba.
Fitilun Kalmomi: Adabi, Hausa, gurbi, karin magana, naƙasa.
1.0 Gabatarwa
Allah yakan halicci mutane
daban-daban, yayin da wasu suke kama da wasu, wasu kuwa sun saɓa da wasu. Haka
nan wasu a halittar zahiri a kammale suke wasun kuwa akasin haka. Waɗanda suke
da akasin kamala ta zahiri su ake kira da naƙasassu a harshen Hausa. Saboda
suna da ragi ko ƙari daga cikin halittar da aka saba ganin mutane da ita.
Harshen Hausa, harshe ne wanda yake da yalwa, musamman ta fannin hikimomin
zance. Domin akan samu azancin Magana masu yawa a cikinsa, waɗanda suka ƙunshi
karin magana da zambo da habaici da kirari da salon magana da gatse da baʼa da
waskiya da sauransu, duk waɗannan suna daga cikin adabin Bahaushe.
Wannan takarda mai taken: Gurbin
Naƙasa a Cikin Karin Maganar Hausawa, ta yi nazarin karin maganar Hausawa ne
sannan ta tsamo wasu karin Magana masu alaƙa da naƙasa, domin nuna irin hikimar
da harshen Hausa yake da shi. Sannan ta bayyana halin komai da ruwanka da
harshen yake da shi, na babu ɓangaren da bai taɓo ba daga rayuwar mutane
(halitta).
1.1 Manufar Bincike
Manufar wannan takarda ita ce
zaƙulo karin maganar da suke cikin adabin Hausa masu dangantaka da naƙasa, tare
da taskace su domin bayyana wa duniya.
1.2 Bayanin Maƙasudin Bincike
Kasancewar masu binciken suna da
'yar masaniya game da harshen Hausa da adabinsa, sai kuma suke cin karo da wasu
karin Magana masu alaƙa da naƙasa a cikin adabin (karin maganar) Hausa, sai
suke ganin ashe akwai buƙatar bayyana wa duniya irin hikimar da Hausawa suke da
ita, wurin amfani da karin Magana masu dangantaka da naƙasa a cikin zantukan
suna yau da kullum.
1.3 Muhimmancin Bincike
Wannan takarda tana da muhimmanci a
fannoni kamar haka: Tataskace tare da adana karin maganan Hausawa masu
dangantaka da naƙasa, kuma ta zama abin nazari ga ʼyan baya. Sannan a fannin
ilmi za ta zama mafarin zaƙulo wasu fannonin ilmi waɗanda wannan takardar ba ta
taɓo su ba. Haka nan ga su kuwa ɗalibai, za ta haska musu hanya game da waɗanda
suke son gudanar da wani bincike mai salon wannan, ko kuma ɗorawa daga wurin da
aka tsaya.
2.0 Sharhin Ayyukan Magabata
Magabata da manazarta sun yi
wallafe-wallafe da kuma bincike-bincike masu yawa game da abin da ya shafi
naƙasa da kuma adabi a keɓe, kamar yadda wannan takardar ta kawo wasu daga
cikin su kamar haka:
2.1 Naƙasa
Naƙasa ita ce ƙari ko kuwa ragi
daga halittar da aka saba ganin mutum da ita. Sai dai CNHN (2006), ta ƙara
haske da cewa naƙasa na nufin tawaya ko gaza ko raunana. Sannan duk wata larura
da ake samu ta dalilin aiki wanda mutum yakan haɗu da shi a wurin wata hidimar
yau da kullum akan ce da ita naƙasa (Mujaheed, 2019). Shi kuwa Bunguɗu (2015),
ya ƙara da cewa duk wata tawaya da akan samu a wata gaɓa ta jikin mutum ana
kiran ta da naƙasa, wannan kuwa ya haɗa da har da taɓin hankali. Saboda haka,
takan shafi yaro ko babba, mace ko namiji kamar yadda Ɗantata da Ali da kuma
Sulaiman (2018), suka tabbatar da cewa naƙasa takan shafi yaro ko matashi ko
tsoho.
Sannan akwai dalilan da sukan sanya
naƙasa, waɗannan dalilan kuwa sukan saɓa kamar yanda Guzuman da Tam (2007),
suka jero:
i. Gado: Wata naƙasar ana gadonta ne daga iyaye da kakanni zuwa ga
ʼyaʼya da jikokinsu.Misalan waɗannan naƙasa sun haɗa da makanta da kurunta da
zabiya da sauransu.
ii. Haɗari
Lokacin Haihuwa: Wata kuwa naƙasar takan
auku ne lokacin da mace ta zo haihuwa. Takan haɗu da wata larurar da za ta
sanyahar ta shafi abin (jaririn) da za a haifa. Ire-iren waɗannan naƙasar
kuwa sun haɗa da farfaɗiya da waninsa.
iii. Haɗari Bayan Haihuwa: Wata naƙasar kuwa takan auku ne bayan mutum ya girma ko
kuma bayan ya manyanta. Waɗannan naƙasa da sukan auku sun haɗa da haɗarin mota
ko tsautsayin gobara ko kuma wanin waɗannan.
2.1.1 Makanta
Rashin gani da idanu biyu shi ake
cewa makanta. Abin nufi makanta ta shafi rashin gani saboda kamuwa da ciwon ido
ko haɗari a lokacin yarinta ko bayan an girma (Mujaheed, 2019 & Sarkin
Gulbi, 2007). Sai dai Bunza (2006), ya bayyana cewa larurar makanta ba wata
naƙasa ce da take taɓa hankali ba. Makan ta naƙasa ce ga wanda ake cewa makaho
(namiji) ko makahuwa/makauniya (mace), makafi kuwa jamʼinsu, makanta tana nufin
rashin gani ko kuwa gani da taimakon naʼura (Gezawa, Ali da Ɗantiye, 2018).
Bisa wannan maʼana duk wanda baya gani, ko kuwa yana gani amma da taimakon wani
naʼura ko da kuwa madubi ne sunansa makaho.
Sannan Abba, (2007) da Ɗanlami da
Dawakin Kudu, (2017), sun faɗaɗa lamarin da cewa rashin gani kwata-kwata ko
kuwa rashin ganin abin da ke kusa, sai na nesa ko kuma gani tare da taimakon
madubi. Ba abu ne mawuyaci ba wurin gane makaho, saboda bayyanannun alamomi da
suke tare da shi. Ga ɗalibi, a fannin karatu kuwa bai zai iya ba sai da
taimakon naʼura, domin suna gani duru-duru ko kuwa ba su gani sam (Obalchumne,
2009 da Onuigbo, 2012 da kuma Ozoji, 2006). Tirkashi! Ashe gani duru-duru ma
makanta ce bisa wannan taʼarifi.
2.1.2 Kurumta
Mai naƙasar kurumta ana ce da shi
kurma, Kurumta tana nufin rashin jin sauti na gaba ɗaya ko kuwa ji daga lokaci
zuwa wani, ko kuma rashin jin sauti kamar yanda sauran mutane suka saba ji.
Wasu akan haifesu ne kurame, wasu kuwa sukan rasa jin sauti ne tun kafin su
fara magana (Wangara, 2014). Haka nan rashin iya Magana sai tare da taimakon
naʼura ma kurunta ce (Reddy da Rammer da kuma Kusumu, 2000). Wani lokacin akan
haɗe bebe ma cikin ajin kurame, domin shi bebe yana fiskantar wahalar furta
kalmomin cikin sauƙi ko kuma yakan tsallake wasu sautukan yayin Magana kamar
yanda Musa da Gwarzo (2018), suka ƙara bayyanawa.
2.1.3. Kuturta
Kuturu shi ne wanda cutar kuturta
ta kama shi har ya rasa ʼyan yatsunsa, mace kuma kuturwa, kutare kuwa, jamʼinsu
(CNHN, 2006). Kuturta wata cuta ce mai yaɗuwa tsakanin alʼumma, wanda
ƙwayar bakteriya take kawowa. Sannan galiban cutar takan shafi
fata ne da kuma gaɓoɓin jikin mutane. Wanda in ba an yi saurin tararta ba, daga
ƙarshe takan cutar da mutum ta hanyar mayar da shi naƙasasshe, ya zamanto ya
rasa ʼyan yatsun hannuwa da ƙafafu tare da yanƙwanar da fuska (WHO, 2024). Ga
alʼadar Bahaushe, kuturu mutum ne mai saurin tsarguwa da kuma fushi tare da
baƙar magana. Wannan ba zai rasa nasaba da irin cutar da yake fama da ita ba
(Mujaheed, 2019).
2.1.4. Hauka
Mahaukaci shi ne mai naƙasar hauka,
ita kuwa hauka tana nufin gazawar ƙwaƙwalwa wurin aikata abin da aka san mai
hankali yana aikatawa (Ɗantata, 2014). Sannan yakan faru ne ta dalilin jinya ko
haɗari ko firgici ko cuta ko kuwa wanin waɗannan (Okeke, 2001). Yayin da mafi
yawa daga cikina lʼumma suke ganin hauka tana da alaƙa da iskoki (jinnu), su
waɗannan masana suna da raʼayin cewa hauka tana da danganta da gazawar
ƙwaƙwalwa ne.
2.1.5 Gurgunta
Gurgunta ita ce zamowa gurgu, gurgu
kuwa shi ne wanda ba ya iya tafiya kamar yanda aka saba ganin sauran mutane
suna taka ƙafafunsu. Mujaheed (2019), yana cewa gurgunta wata naƙasace wanda
takan hana wa mutum tafiya daidai, wannan daidai yake da gurguntaka ko gurgunci
ko ɗingishi. Hakan kuwa yana faruwa ne sanadiyar cuta ko rasa wani ɓangaren a
ƙafa ɗaya ko kuwa duka biyu, a dalilin haɗari ko shanyewa ko kuwa a haifeshi da
hakan (Collins Dictionary 2019).
2.2 Karin Magana
Kowace al’umma tana da hanyoyin da
take bi wurin nuna hikimar zancenta, karin magana tana daga cikin zantukan
hikimar Hausawa. Junaidu da ‘Yar’aduwa (2007), suna ganin karin magana da
cewa‘yar jimla ce gajeriya wanda mai Magana zai faɗa ta hikima, kuma ta ƙunshi
ma’ana mai yawa idan an tashi yin sharhinta.
Su kuwa Muhammad (2005) da Kurfi
(2019). Suna ganin cewa wataʼyar gajeriyar jumla ce ta hikima, wadda ta ƙunshi
maʼana mai yawa, in za a tsaya a yi bayaninta. Kuma yakan ƙara wa salon magana
daɗi da armashi, sannan yana nuna gwanintar iya Maganar mai magana. Sannan
yakan sanya mai sauraron maganar rashin ƙosawa daga jin zancen da ake gaya masa.
Sannan wasu kuwa sun tafi a kancewa
wata ʼyar taƙaitacciyar Magana ce ta hikima da basira wacce ta ƙunshi maʼana
mai tarin yawa idan har za a yi bayaninta dalla-dalla. A taƙaice karin magana
kamar kukan kurciya ne, hakan kuma yakan sanya maganar ta yi daɗi kamar an
sanya gishiri a miya. Sau da dama karin magana yakan nuna gaskiyar abin da ake
faɗa ne. Wato yana bayyanar da ɗabiʼu iri-iri kamar gaskiya da kirki da ƙwazo
da lalaci da baiwa ko rashinsa da lamuran da suka shafi rayuwar Bahaushe ta yau
da kullum (Gwammaja, 2010 da Ɗanhausa, 2012).
Bisa dogaro da bayanan masana, shi
karin magana hanya ce ta dunƙule zance mai yawa wuri guda tare da bayyanar da
hikima da zalaƙar harshe sannan bai ƙebanta ga harshen Hausa kawai ba, har da
sauran harsunan duniya.
2.2.1 Raberaben Karin Magana
Saboda yawan da karin magana na
Hausawa suke da shi ne ya sanya masana da manazarta adabin Hausa suka rarrabe
su zuwa rukuni-rukuni. Sannan waɗannan rabe-raben karin maganan Hausawan suna
da dama, ga wasu daga cikinsu kamar yanda masana irinsu Ɗangambo, (1984)
da Hadiza S. Koko, (1989) da Nahuce, (2008) suka kawo:
i. Karin Magana Mai Labari: Shi wannan karin magana yana da alaƙa da labari, ba safai
mai sauraro yakan gane shi ba, matuƙar bai san labarin da yake da danganta da
shi ba. Misalan waɗannan karin magana sun haɗa da: Zuwan fara Garko da Faɗan
Goggo a ƙofa da Jifar gafiyar Ɓaidu da sauransu.
ii. Karin Magana Kafin Zuwan
Musulunci: Shi wannan nauʼi na karin
magana, Hausawa suna amfani da shi ne tun kafin su karɓi addinin Musulunci,
saboda haka sau da dama akan tsinci wani abu mai kama da saɓo a cikinsa,
misalansa sun haɗa da: Bori ɗaya ake yi wa tsafi da A raba arne da makaminsa da
Ranar tsafi bunsuru ke kuɗi da makamantansu.
iii. Karin
Magana Bayan Zuwan Musulunci: Irin
waɗannan karin Magana, Bahaushe yana amfani da su ne bayan addinin Musulunci ya
zo masa, domin haka akan tsinci tasirin addinin Musulunci a cikin zantukansa na
hikima musamman karin magana. Misalan waɗannan karin magana sun ƙunshi: Allah
ɗaya gari bamban da Allahn da yayi sarkin Kano shi ya yi ɓera da Allah
suturibuƙui inji kishiyar ƙonanniya da Allah sarki inji barawon takanɗa da
sauransu.
iv. Karin
Magana mai Falle Biyu: Shi wannan nauʼi na
karin Magana yana tafiya ne da ɓangare biyu, domin da an faɗi ɗaya nan take ake
biyo shi da ɗayan, wani lokaci yakan zo da kalmar ʻsaiʼ. Misalin waɗannan karin
magana sun haɗa da: Sai bango ya tsage: Кadangare ke samun filin ɓoyo da Daɗan
gari: Akan ci gari da Tafiya sannu-sannu: Kwana nesa da Kallo ya koma sama:
Shaho yaɗauki giwa da sauransu.
v. Karin
Magana Mai Habaici: Shi kuwa wannan karin
magana yana da dangantaka da tsokana, saboda akan yi da wani ne a fakaice.
Misalan waɗannan karin Magana su ne kamar haka: Allah sarki halittar Allah:
Jaba ta ga bakin mijinta da Daga ganin sarkinf awasai miya ta yi zaki? da Bawa baya
wasa da ɗa, da sauransu.
vi. Karin
Magana Mai Nasiha: Wannan karin Magana
yana jan hankali ne ko kuwa ƙarfafa mutun domin ya yi aiki ko halin ƙwarai a
rayuwarsa tare da yi masa gargaɗi a kan wani halinsa mummuna. Misalansu sun
haɗa da: Nuna halin ƙwarai haƙuri wa dan mai shi da Sannu ba ta hana zuwa da Kowanne
gauta ja ne, da sauransu.
vii. Karin
Magana Mai Dangantaka da Sanaʼoʼi: Saboda
muhimmancin da sanaʼoʼi suke da shi ga rayuwar Bahaushe, ya sanya bai manta da
su ba a cikin azancin maganarsa. Irin waɗannan karin magana sun haɗa da: Nasan
a rina: An saci zanin mahaukaciya da Кaiƙayi koma kan masheƙiya da Ciko ya biyo
gyartai, da wanin waɗannan.
2.2.2 Jigon Karin Magana
Karin magana yana da jigogi masu
yawa, waɗanda suke ɗauke da saƙonni daban-daban, sun ƙushi: jigon faɗakarwa da
gargaɗi da tarbiyya da siyasa da tarihi da ilmantarwa da nishaɗantarwa da
waʼazi ko nasiha (Hadiza S. Koko, 2011).
2.2.3 Muhimmancin Karin Magana
Karin magana yana da muhimmanci ga
kowanne harshe da kuma kowacce alʼumma, domin yana taimakawa a fahimci irin
balagar da harshen yayi a ɓangaren cigaba. Ga kaɗan ne daga cikin amfanin karin
magana:
i. Dunƙule Magana mai Yawa Wuri
Guda: Ta amfani da karin magana ana iya dunƙule Magana mai tsawo wurin
guda. Misalin tawa ta same ni Liman da tallar jigida da Aradu ke horon kurma da
Allura cikin ruwa da Wuce gona da iri da sauransu.
ii. Kaifafa Tunani: Yana
daga cikin muhimmancin karin Magana yana kaifafa tunani, saboda wani lokacin in
an kawo wani karin Magana sai an yi tunani mai zurfi kafin a fahimci maʼanarsa.
Misali Allah shi ya san karatun kurma da Rijiyar mahassada wawa ke shanta da
Sha talla ƙahon doki da sauransu.
iii. Wanzar da Zaman Lafiya
Tsakanin Alʼumma: Ko kuwa kwantar da tarzoma ana amfani da karin Magana
domin a kwantar da tarzoma tsakanin mutane mabambanta. Misali: Kar a mayar da
ƙurji gyambo da Zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki da A bar kaza cikin gashinta
da sauransu.
iv. Sirranta Magana: Daga
cikin amfanin karin magana, akwai sirranta magana ga wanda ake son ya fahimci
zancen shi daya ko kuma isar da saƙo a fakaice zuwa ga wanda ake buƙatar ya
fahimci zancen. Misalin: Kowa ya rena tsayuwar wata ya hau ya gyara da Kurɓi ya
ɓata sha da Sunkuya wa wada ba gajiyawa ba ne da sauransu.
v. Nuna Кwarewar Harshe:
Kowanne harshe yana da nasa hanyar da yake bi wurin taskace adabinsa. Ga
harshen Hausa, karin Magana yana daga cikin hanyoyin taskace harshen da kuma
adabinsa. Ga wasu daga cikinsu: Mun gaji da kyau hali muke so da Agola ya fi
ɗan masu gida da Ba da son mafarauta ba, damisa ta yi ɗiya da sauransu.
vi. Taskace Kalmomi: Yin
amfani da karin Magana yana hana tsofin kalmomin ɓacewa, saboda yawaita yin
amfani da su yau da gobe zai sanya yara su tashi da yin amfani da kalmomin
hikima kamar: Tambaɗa adashen abu da Ya ƙure adakarsa da Wa ka faɗi banten
sarki ya tsinke da sauransu.
viii. Yana Jan
Hankalin mai Sauraro: amfani da karin
magana a cikin zance yakan sanya masu sauraro ba za su gajiya daga jin zantukan
da ake yi ba, ko da an ɗauki lokaci mai tsawo ana yinsa. Misali Ba a neman kifi
a faƙo da Bakinka ƙanin ƙafarka da Daga riya sai bara da sauransu.
ix. Koyar da
Dogaro da Kai. Ta hanyar amfani da karin
Magana akan koyar da zantukan da za su sanya wa mutum dogaro da kai tare da yin
azama a kan abin da ya sanya a gaba kamar: Guntun gatarin kaya fi sari ka ba ni
da Mai arziki ko a ƙwara ya sai da ruwa da Allah ya ce tashi in taimakeka da
sauransu.
x. Tarbiyyantarwa. A cikin karin Magana akwai zantuka masu yawa waɗanda suke
jan hankali ko kuwa umarni ko horo da hani misali: Haƙuri maganin zaman duniya
da Bin na gaba bin Allah da Babban wa uba ne da sauransu.
xi. Tabbatar
da Adabin Alʼumma: Karin Magana yana daga
cikin hanyoyin tabbatar da adabi da alʼadu da ɗabiʼun kowacce alʼumma waɗanda
sukan gada tun iyaye da kakanni. Sannan yin amfani da karin magana yau da
kullum yana taskace adabi daga halaka. Kamar: Ramin kura sai ʼyaʼyanta da Kamar
kumbo kamar ʼyaʼyanta da Tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela da farinta
da sauransu.
3.0 HanyoyinBincike
An yi amfani da binciken
littattafai masu dangantaka da wannan aiki a cikin ɗakunan karatu. Sannan an
kuma tattauna da masu larurar naƙasa daban-daban, domin samun ƙarin haske game
da wasu karin maganan.
4.0 Gurbin Naƙasa a Cikin Karin
Maganar Hausawa
Abin da suke biye jerin karin
maganar Hausawa ne waɗanda suke ɗauke da naƙasa. Waɗanda suka ƙunshi hauka (mahaukaci)
da kurumta (kurma) da gurgunta (gurgu)
da wauta (wawa) da kuturta (kuturu) da makanta (makaho)
da sauransu. Kamar haka:
1. Wawa ba mahaukaci ba
ne in ya ci kasuwa gida zai koma.
2. Mu je zuwa mahaukaci ya hau kura.
3. In makaho ya ce mu yiwa san jifa ya taka
dutse.
4. Ta nan muka faro: kuturuya ga mai ƙyasbi.
5. Gida ya fi nan auren mahaukaci.
6. A bakin wawa ake jin magana.
7. Ɗinyar makaho ta nuna a aljihunsa.
8. Na ji wannan an ce da kurma cinye
duk.
9. Makaho bai
san ana kallonsaba, sai an dafa shi.
10. Ana hauka domin a burge mai hankali.
11. Na san a rina wai an saci zanin mahaukaciya.
12. A rashin kira karen bebe ya bata.
13. Kuturu da kuɗinsa alkaki sai naƙasan
langa.
14. Haka tara in ji kishiyar mai mageduwa.
15. Duk ɗaya makaho ya
yi dare.
16. Kun tuna mani an ce da mahaukaci ba
ya duka.
17. Abu mai sauƙi
an sanya mai ido ɗaya leƙa
shantu.
18. Babu shiga ba fita an bai wa mahaukaci gadin
ƙofa.
19. A rashin sani Karen bebe ya kori
bazawara.
20. Ta tata kuturwa zuwa baraya.
21. Riƙon mahaukaci sai
sarki.
22. Hauka da naɗenaɗenta.
23. Abin da kamar wuya gurguwa da
aurenesa.
24. Kaɗan kenan wai an yiwa gurgu ƙafar laka.
25. Kowa ya ci ladan kuturu dole ya yi
masa aski.
26. Gane mani hanya wai makaho ya so
tsegumi.
27. Kwasan karan mahaukaciya.
28. Cin ƙwan makauniya.
29. Allah suture buƙui
in ji kishiyar mai ƙusumbi.
30. Da wasa ake ga yawa wawa magana.
31. Araduke horon kurma.
32. Ba a yabon ɗan kuturu sai
ya mutu da yatsu.
33. Sabo turken wawa.
34. Bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba
ne.
35. Gurgu bai
sauya tafiya.
36. Abu maisauƙi, ƙwace goruba a hannun kuturu.
37. Mafarin hauka zubar da yawu.
38. Кaramin kuturu ke zufa, manyan sai
gwalo.
39. Abu mai sauƙi
kasha makaho da dare.
40. Buhun gishiri ko gidan mahaukata ya
fi gaban kwaɗo.
41. In ba a kwaɗo da kuturu,
a ba shi daddawarsa.
42. Yau da kallo, an bai wa kuturu sakar
lauje.
43. Idan ido ya mutu kwalli ba ya ta da
shi.
44. Gwari banten mahaukaciya.
45. Ba zai yiwu ba wankan kuturu da
sabulu.
46. A ja mu a kai mu, an bai wa uwar makaho kashi.
47. Muƙami, kuturu a
London.
48. Gadauniya, makauniya da da yekuwar
wuta.
49. Ga wake ya yi damo yana neman ya makance.
50. Da magana a bakin kurma, sai ranar da ya
samu baki.
51. Gara kowa da ni inji matar bebe.
52. Allah gyara, makaho ya ce a yaushe?
53. Bari neman ji ga bebe, don Allah bai
nufe shi ba.
54. Allah yake gyara tuwon makauniya ba
domin tana ganinsa ba.
55. Mai ido ɗaya ba ya godiyar Allah, sai ya
ga makaho.
56. Ko oho, makaho ya yi dare.
57. Ina ruwan makaho da kunya?
58. Biyar da daƙi, kuturta biyar
ɗan aboki.
59. Sun yi ban hannun makafi.
60. Na rufe idanu ban ga kyawun makanta ba.
61. Naƙasa ba kasawa ce ba.
62. Кwancin ƙwalinto, kuturu ƙwancin gyambo.
63. Rashin sani ke sanya makaho ya taka
sarki.
64. Runtse ido ba makanta ba ce.
65. Sabo da yi makaho da waiwaiye.
66. Sau ɗaya gyaɗar makaho ka ƙuna.
67. Allah shi yake gyara tuwon makauniya ya
yi daɗi.
68. Naci, damben kuturu.
69. Allah da ikonsa kuturu ya hau giwa.
70. Nan yini nan kwana, an bai wa kuturu tallan
jaki.
71. Allah da ya yi makaho shi ya yi
masa ɗan jagora.
72. Na raina damben makaho, ko yashirya.
73. Mutanen kirki, damo ya ga makaho.
74. Babu ji babu gani aure kuma da makaho.
75. Wanda ya yi hauka, ɗimuwa ba zai gagare shi ba.
76. Abin ana dai? An bai wa makaho hanjin
jimina.
77. Abin banza hanci babu ƙafa.
78. Maƙetaci
mijin gurguwa, a ranar tafiya ya sayar da jaki.
79. Mutuwar jiki naƙasa ce.
80. Magaza gani ido ya rufe.
81. Makaho ba ya
shaida.
82. Mai ido ba ya godewa Allah sai ya ga makaho.
83. A garin makafi, mai ido ɗaya sarki ne.
84. Makahon doki
sha kasuwa, dillali ya gaji dokin ma ya gaji.
85. Makaho yana
gani, amma ba na ganin gari ba.
86. Gurguwar tsanya
da wuri take fara tiƙa.
87. Komai da muhallinsa, wai an sanyawa kuturu ankwa
ta sabule.
88. Ruguduma an kama kurma da kwartanci.
89. Abin faɗa na mai baki ne, bebe sai
ka dangana.
90. Abin wani abu ne, faɗar makaho da
daddare.
91. Goron magana ga mai baki, kurma sai
dangana.
92. Kadan ba ƙarya
ba, kuturu zai yi dambe da mai yatsu?
93. Idan ba rigimar makaho ba, ya yi
kokawa da mai ido?
94. Kallon ka nake, wai makauniya ta yi
faɗa da mijinta.
95. Na raina damben makaho ko ya shirya.
96. Mai ido ɗaya kiyayi gauɗe.
97. Kuturu ake yi
wa gayya, ba mai yatsu ba.
98. Kuturu ya so
dambe babu yatsu.
99. Kuturun kutare mai
bara da jaka.
100. Кafar kuturu muhimmancinta takalmi.
5.0
Sakamakon Bincike
Daga ƙarshe sakamakon binciken ya
nuna irin faɗi da hikima wanda harshen Hausa yake da suna babu ɓangaren da ya
ware a rayuwar mutane ba tare da ya samar masa da matsuguni ba. Sannan kuma ya
hasko cewa wata naƙasar ana gadonta ne tun a wurin iyaye da kakanni ba a nan
duniya ake gamuwa da ita ba. Yayin da wata naƙasar kuwa akan haɗu da ita ne a
nan duniya ta dalilai mabambanta waɗanda suka haɗa da cuta da haɗari da
sauransu.
6.0
Kammalawa
Takardar ta yi nazarin maʼanar
naƙasa da dalilan da sukan sanya naƙasa da misalan wasu daga cikin naƙasa kamar
hauka da makanta da kuturta... Haka nan, ta yi ƙarin haske game da karin
maganar Hausawa, sannan ta tsamo wasu daga cikin karin maganan Hausawa masu
alaƙa da naƙasa, domin nuna irin hikimar da ke tattare cikin harshe da adabin
Hausa. Kuma ta bayyana halin komai da ruwanka da harshen Hausa yake da shi, na
babu ɓangaren da bai taɓo ba na daga rayuwar mutane. Sannan an jero karin
maganar Hausawa waɗanda suke da dangantaka da naƙasa. Daga ƙarshe Sakamakon
binciken kuwa ya nuna irin faɗi da hikimar da harshen Hausa yake da suna babu
ɓangaren da ya ware a rayuwar mutane ba tare da ya samar masa da matsuguni ba.
Kuma ya hasko wata naƙasar ana gadonta ne tun daga wurin iyaye da kakanni ba a
nan duniya ake gamuwa da ita ba.
Manazarta
Abba, A. etal. (2007). Special
needs education. I & P Computer Services.
Aliyu, M. S. & Muhammad, M.
(2019). Braille reading and writing: Tool for achieving academic achievement of
students with visual impairment. National Journal of Special Needs
Education. Vol. V., No.VI. Dec. 2019. (5164). ISSN: 24657387.
Alhassan, F. A. (2014). Special
needs services for students with visual impairment in an inclusive
environment. National Journal of Special Needs Education. Vol. I. No.
I. Dec. 2014. (2531). ISSN: 24657387.
Bunguɗu, H. U. (2015).
Nazarinwaƙoƙin bara a ƙarninaashirin da ɗaya a Zamfara. Kundindigirina uku.
Jamiʼar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Bunza, A. M. (2006). Gadon
feɗeal'ada. Tiwal Nigeria Limited.
CibiyarNazarinHarsunan Nijeriya.
(2006). Кamusun Hausa naJami’arBayero. AhmaduBello University Press
Limited.
Collins Dictionary (2019). https://www.collinsdictionary.com. Retreaved on 31, August, 2025.
Ɗangambo, A. (1984). Rabe-rabenadabin
Hausa da muhimmancinsa ga rayuwarHausawa. Kano: Triump Publishers.
Ɗanhausa, A. M. (2012). Hausa
maidubunhikima. Kano: Centuary research and publication Company.
Ɗanlami, A. &Dawakin Kudu, A.
M. (2017). Accessibility to academic library resourses by students with visual
impairment. National Journal of Special Needs Education. Vol. IV, Dec.
2017. (6573). ISSN: 24657387.
Ɗantata, G. F. (2014). Mental
retardation: Concept, causes, classifications, residential and educational
placement opportunities for inclusive education. National Journal of
Special Needs Education. Vol. I. No. I. Dec. 2014. (129139). ISSN: 24657387.
Ɗantata, Y. M. &Diso, J. I.
(ND). Visual impairment: classifications, characteristics, prevention and
intervention. Maiwa, D. A. Dantata, G. F (Ed). Reading in special
education. (2439). Ahmadu Bello University Press Ltd.
Ɗantata, Y. M., Ali, D. S. & Sulaiman,
S. A. (2018). Physical and health impairment: concept, classification,
categories, causes and educational strategies of students with physical and
health impairment. National Journal of Special Needs Education. Vol. V,
Dec. 2018. (1025). ISSN: 24657387.
Gezawa, A. A., Ali, S. &Datiye,
H. N. (2018). Innovation in entrepreneurship education for people with visual
impairment in Nigeria. National Journal of Special Needs Education.
Vol. V, Dec. 2018. (7385). ISSN: 24657387.
Gwammaja, K. D. (2010). Karin
magana a ƙasar Hausa. Kano: KDG. Publishers.
Guzman, A. B. & Tan, E. B.
(2007). Understanding essence of scholarship from the live experiences of a
select group of outstanding Filipino researchers. Educational research Journal,
guidelines for children and families social services. Child and Family Agency.
Gwarzo, A. B. (ND). Children with
low physical and health abibilities. Maiwa, D. A. &Ɗantata, G. F.
(Ed). Reading in special education. (4060). Zariya: ABU Press Ltd.
Ibrahim, K. (ND). Hearing
impairments: causes, categories, characteristics and effects. Maiwa, D. A.
Dantata, G. F (Ed). Reading in special education. (123). ABU Press
Ltd.
Isah, M. S. (2017). Epilepsy:
Concept causes, signs,and classification of students with epilepsy in
Nigeria. National Journal of Special Needs Education. Vol. V. Dec. 2017.
(7487). ISSN: 24657387.
Junaidu, I. & 'Yarʼaduwa, T. M.
(2007). Harshe da adabin Hausa a kammale don manyanmakarantunsakandare.
Lagos: Spectrum Books Ltd.
Kirk, S. A. (1975). Educating
exceptional children. 3rd Edition. Houghton Mifflin.
Koko, H. S. (1989). Karin magana a
hannunmata a garinSakkwato. Kundindigirinafarko. Jamiʼar Sokoto.
Koko, H. S. (2011). Hausa
cikin Hausa. SashenNazarin Harsunan Nijeriya COE Sokoto.
Kurfi, M. M. (2019). Magana
iyawace. Katsina: Kanki classical media venturers.
Ladipo, S. O. (2006). The
physically handicapped in regular schools. Obaini, T. C. (Ed). Teaching
pupils with special needs in regular UBE classroom. Ikeja:
Bookbuilders.
Lowenstein, D. H. (2003). Epilepsy.
N. Engl. J. Med 349(13):125766. Doi: 10.1056/NEJMra022308.PMID14507951.
Musa, A. &Gwarzo, A. S. M.
(2018). Children with language impairment: psychological implication for
parents. National Journal of Special Needs Education. Vol. V, Dec. 2018.
(170179). ISSN: 24657387.
Muhammad, M. M. (2005). Adabin
Hausa. Zariya: Ahmadu Bello University press Ltd.
Mujaheed, A. (2019).
Burbushinnaƙasaaadabin Hausa: Tsokacidagakarinmagana. Kadaura Journal
of Hausa Multi Disciplinary Studies. Vol. 1, No. 5. September, 2019. (240-249).
ISSN: 2536-7609
Nahuce, I. M. (2008). Karin maganar
Hausa a rubuce. Kundindigirinabiyu. SashenNazarin Harsunan Nijeriya Jamiʼar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto.
Obalchume, N. (2009). Resources
available to the visually impaired library uses in Nigeria: The wayout. Journal
of Association Libraries for Visually Impaired 2(3), 6574.
Okeke, B. A. (2001). Essential
of special education. Jos: AfroOrbr Publication Ltd.
Onuigbo, L. (2012). Reading
comprehension intervention for students with visual impairment: International
Journal of English and Literature. Vol. 2.
Ozoji, E. D. (2006). Repositioning
special needs education for effective services delivery in Nigeria. Minna:
Deka public publications.
Reddy, G. L., Ramar, R.
&Kusumu, A. (2000). Education of children with special needs.
Delhi: New Discovery Publications House.
Sarkin Gulbi, A. (2007). Nazari a
kanalʼadar bara a ƙasarSakkwato. Kundindigirinabiyu. Jamiʼar Usmanu Ɗanfodiyo.
Sokoto.
Wangara, H. G. (2014). Strategies
for classroom management of children with hearing impairment. National
Journal of Special Needs Education. Vol. I. No. I. Dec. 2014. 7884. ISSN:
24657387.
World Health Organization. (2024).
Global leprosy (Hansen disease) update, 2023: Elimination of leprosy disease is
possible. Weekly epidemiological record, 13 September 2024, vol. 99.
(501-521). https://enmedicine.medscape.com. Retreved on 30, August, 2025.
Rataye
SunayenWaɗanda Aka yi Hira da su
|
Lamba |
Suna |
Shekaru |
Matsayi |
Rana |
WurinHira |
|
|
Malam Mohammed Arɗo Abubakar |
53 |
Sarkin makafin Adamawa |
30/08/2025 |
A gidansa da
keunguwarfaransa, Gombi, Adamawa |
|
|
Malam Dahiru Iyawa |
49 |
ShugabanmasularurarnaƙasanaGombi,
Adamawa |
02/09/2025 |
Кofar Mal. Arabiya, Gombi,
Adamawa |
|
|
Malam Yerima Muhammad |
56 |
GaladimanmakafinGombi,
Adamawa |
04/09/2025 |
KasuwarButu Gombi, Adamawa |
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.