Being a mandatory Ph. D seminar paper, presented at the Department of Nigerian Languages. Faculty of Arts and Islamic Studies Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto, 2014
TA
SA’ADU MUHAMMAD MU’AZU
Department of Nigerian Languages.
Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto
1.0. GABATARWA
Haƙiƙa kowace halitta ta duniya tana da waɗansu ɗabi’u da ta keɓantu da su. Mu’amalar da mutane suke yi da mutane
‘yan’uwansu shi ya sa kai tsaye za a iya fahimtar ɗabi’un kowa cikin sauƙi. Haka kuma abu ne mai sauƙi a iya yin bayani kai
tsaye dangane da mutanen da aka yi wata hulɗa da su. Wannan abu haka yake ko a wajen ma’abota
mu’amala da dabbobi, ko tsirrai, ko mutanen ɓoye da dai sauransu. Kai tsaye za su iya
ambaton ɗabi’un da suka keɓanta da su kwatankwacin irin na mutane.
Muhimmin abin da za a yi a wannan maƙala shi ne, zaƙulo ɗabi’ar wayo
da wasu dabbobi da tsuntsaye ke da su kamar yadda Bahaushe ya nazarce su
musamman a al’adance. Wannan yana da fa’ida matuƙa, domin ko ba komai akwai tabbacin wanzuwar hakan a cikin adabin Bahaushe. Hakazalika irin wannan hanzari tankar hannunka mai sanda ne ga mutane, wajen sanin irin mu’amalar da za su yi da waɗannan dabbobi. Hausawa na cewa, “idan aka san halin mutum sai a ci maganin zama da shi”. To, a wannan maƙala, ɗabi’ar
wayon dabbobi
ne za
mu ɗora a wani mizanin awo,
domin ɗan Adam ya samu nemo maganin zama da su ta
kowace fuska. Bisa wannan dalili ne ya sa
aka kira wannan maƙala da taken Wayon
Dabbobi A Ma’aunin Adabin Bahaushe. Bayan haka kuma nazarin zai
kawo waɗansu rukunan adabin bakan
Bahaushe, irin su; Karin Magana, da waƙar baka, da take da kirari, da almara da
sauransu, domin kafa hujja da kuma ƙara samun madogara.
1. 1.
Ma’anar Kalmar wayo:
Kalmar
wayo wata sananniyar kalma ce a wurin Bahaushe, wadda take ana iya cewa kowa ya
san ma’anarta. Haka kuma Bahaushe na yin amfani da ita ne, idan yana son
bayyana, ko siffanta wani mai kaifin tunani. Wanda yake a duk lokacin da ya
shiga wani halizai san yadda zai yi ya fita. Duk da haka, waɗansu masana sun fassara
ma’anar wayo ta fuskoki iri daban daban.
Neil
Skinner ga yadda ya fassara Kalmar:
“Hankali,
ko kangado, ko wayo, ko fahimta, ko basira”[1].
Bergery
G. P. shi kuma ga yadda ya fassara Kalmar:
“wayo,
ko dabara, ko dabarbaru”[2].
Ƙamusun Hausa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero
Kano
ga yadda suka fassara kalmar:
“kyakkyawan
shiri, ko wayo, ko hikima, tsari. ” [3]
Hornby.
A. S. shi kuma sai ya fassara Kalmar da cewa:
“
Gane, ko fahimta, ko hasashe, da tunani a kan wasu abubuwa,
ana
danganta wannan ga mutum ko dabba. [4]
R.
C. Mish da Promila su kuma ga yadda suka fassara Kalmar:
“
Fita, ko kuɓuta, ko
iya warware matsaloli da aka shiga,
ta
hanyar yin amfani da ilmin yau da kullum,
ko
kuma goguwa da harkar rayuwa”. [5]
McGraw Hill ga yadda
ya fassara Kalmar wayo:
“ Kyakkyawan tunani
wanda kan kuɓutar da
mai shi,
tare da ɗaukar mataki ta hanyar lura
da al’amuran rayuwa
da suka
gabata”. [6]
Ilyas Bn Ilyas ga
yadda ya fassara Kalmar wayo:
“ Dabara, ko hankali,
ko falsafa”[7]
Bunza A. M. shi kuma
sai ya fassara Kalmar da cewa:
“Wayo a wajen Bahaushe wani
nau’i ne na hankali
wanda yake kula da lissafi na hangen rarrabe
abubuwan
dake cutarwa da na ƙaruwa da kuma samun mafita
idan
aka shiga runtsi cikin kowace irin
matsala, a mai hankali
ya shiga, sai ya yi aiki da wayon da ke cikin
hankalinsa
in yana son ya kuɓuta gwargwadon zurfin wayonsa.
A al’adar Bahaushe,
da hankali da wayo ba a son su
yi yawa su wuce
mizani. [8]
Wayo a adabin Bahaushe.
Haƙiƙa an samu jirwayen kalmar wayo a rassan adabin Bahaushe
daban-daban. Kamar karin magana, da waƙar baka, da kirari, da
tatsuniya da sauransu.
Karin Magana:
Ko wayo ya san na ƙi.
Tsuntsun mai wayo a wuya
ake kama shi.
Wayo ba ya sai da taba sai
yajinta.
Duk wayon amarya sai
an sha manta.
Wayon mutum a kan kayansa.
Dabarar mutum abinsa na
hannunsa.
Waƙar Baka:
A wata waƙa da Salihu Jankiɗi ya yi ta Sa Abubakar Na uku cewa ya yi:
Jagora: Kai
tankatarma sai kai hankali,
Kun san Baƙauye ba tsinka garai ba,
Babu lisahi wauta
garai
Har ta sa a yi mai
girman zama.
Gindi:
Shugabannin Ɗakin Duniya,
Abubakar hana
gwangwamin maza.
Shi kuwa Ibrahim Narambaɗa cewa yayi :
Jagora: Hankali yafi
wayo yawa,
Mai biɗar bashi shi da mai biɗar ramce,
Su ad da wayon rashin
wayo
Randa kab basu sai
murna,
Ran biya ai ta ƙunduttu.
Gindi: Amadun Bubakar
Gwarzon Yari
Dodo na Alƙali
Shi kuwa
Sani Aliyu Ɗandawo a waƙarsa ta Baban Tawo Ɗan kwangila inda ya ce:
Jagra:
Dabarar rashin dabara ga wane,
Ya
sai da fodu ya sha fura.
Na
iske wane Ɗankwangila,
Motar
da ya ara ya sayar.
Gindi:
Manya a bi ku ag gaskiya,
Baban
Tawo Ɗankwangila.
Bisa lura
da bayanan da masana suka yi, game da wannan kalma ta wayo. Tare da yin
la’akari da jirwayen Kalmar a adabin Bahaushe. Kai tsaye muna iya cewa, Kalmar
wayo na nufin dabara, ko basira, ko sanin makamar al’amura, ko samar wa kai
mafita (kuɓuta) idan
an shiga wani baƙon yanayi.
1. 2. Ma’anar Kalmar Dabbobi.
Kalmar dabbobi jam’i ne na kalmar dabba. Ita
kuma kalmar dabba duk da yake Bahaushe aro ta ya
yi daga
harshen Larabci, a yanzu ta zama
Bahaushiyar kalma, domin kusan babu wata ingantacciyar kalma da ake amfani da
ita. Duk da haka, waɗansu masana sun fassara ma’anar dabba ta fuskoki mabambanta.
Abraham, R. C. yadda
ya fassara Kalmar da cewa:
“Halittu ne
masu ƙafafu huɗu na gida da na daji”[9]
A Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero Kano an bayyana ma’anar kalmar da cewa:
“Dabbobi su ne dukkan halitta
mai ƙafa huɗu”. [10]
Bargery ya fassara
kalmar da cewa:
“Dabbobi waɗansu halittu ne masu ƙafa huɗu,
Jikinsu kuma lulluɓe da gashi”. [11]
Bisa dogaro da bayanan da suka gabata, muna iya cewa: kalmar dabbobi, na nufin waɗansu nau’in halittu ne masu ƙafa huɗu, da masu ƙafa biyu, sannan da masu
jan ciki, haka kuma akwai masu fuffukuwa su tashi sama. Mafi rinjayensu jikinsu
lulluɓe yake da
gashi, akwai kuma marasa gashi a cikinsu, sai fatar jiki kawai.
Bugu
da ƙari kuma, waɗannan irin halittu sun karkasu
iri daban-daban; akwai masu ƙafa huɗu da masu biyu. Daga cikinsu kuma akwai dabbobin gida da na daji, da na tudu, da
na ruwa. Har-wa-yau kuma daga cikinsu akwai masu yawo a doron ƙasa kan ƙafafunsu, da kuma masu
rarrafe, da masu jan ciki (maja-ciki). Akwai masu haihuwa a cikinsu (watau masu fatun kunnuwa) da masu ƙwai (masu ramin kunne) da
sauransu.
2.0. WAYON DABBOBI A TUNANIN BAHAUSHE.
Bahaushe
ya nazarci ɗabi’un waɗansu dabbobi na gida da na daji, sannan kuma ya karkasa su
gwargwadon yadda suke gudanar da rayuwarsu. Bayan wannan kuma sai ya danganta
su da waɗansu ɗabi’un mutane,
musamman ɗabi’ar wayo. Wannan alaƙantawar da Bahaushe ya yi,
har ya yi naso a tunaninsa. Haka kuma maganar ba ta tsaya ga furtawa ta fatar
baki kawai ba, a’a abin ya wuce haka. Domin kuwa, ya yi jirwaye a dukkan rassan
adabin Bahaushe. Wani abin mamaki shi ne, da zarar aka ambaci wata dabba ta
gida ko ta dawa, ko tsuntsu, sannan aka faɗi ɗabi’u, ko halayen da aka danganta ta da su, sai ka ga babu wata
tababa, don kuwa a zahiri abin haka yake. Wannan maƙalar za ta nazarci wasu dabbobi da Bahaushe ke alaƙanta su da ɗabi’ar wayo. Musamman dabbobi irin su biri, da dila, da kurege, da
zomo, da ɓera. Wannan kasafi da Bahaushe ya yi baya rasa nasaba da
irin ɗabi’unsu,
ko ƙirar jikinsu, a wani lokaci har da muhalli, da abincin waɗannan dabbobi da tsuntsaye.
Dukkan waɗannan
bayanai za a ɗora su ne a kan rassan adabin Bahaushe na baka.
Biri: Siffa watau ƙirar jiki, kasancewar biri
na da ƙaramin jiki, tare da wasu ɗabi’u waɗanda ya keɓanta da su, su ne hujjar da yasa ake danganta wayo gareshi.
Bahaushe yana kallon biri da wayo, musamman saboda waɗansu abubuwa waɗanda biri yake aikatawa.
Akwai rassan adabi da suka tabbatar da hakan, kamar wata karin maganar Bahaushe
da ke cewa, “Biri ya yi kama da mutum”. Ma’ana biri na iya aikata wasu
abubuwa da ba duka dabba zata iya yinsu ba. Biri na iya miƙewa yayi tafiya kamar mutum, saboda akan samu biri ya tare mace
bil’adama har yayi mata fyaɗe. Allah ya yiwa biri wayo, saboda wayon da biri ke da shi, ya
wuce duk inda kake tunani. A dalilin wayo da biri ke shi yasa Bahaushe ke yin
wata Karin Magana mai cewa ba a yi wa biri burtu, ma’ana saboda wayon sa bai
yarda a yaudareshi kamar sauran dabbobi da tsuntsaye. Wannan yasa ko an yi
mutummutimi an sa a gona sai dai ya hana wasu dabbobin ɓarna amma ban da biri.
Wannan yasa Musa Ɗanƙwairo a wata waƙa mai suna: Bello shiri nai
yai kyau bai ya da gudun Arna ba, yake cewa:
Jagora:
Mutummutumi mutumin banza,
Ko
ka yi shi ka kai gona,
ba
za ya tsare komai ba,
Ɓarnar da a kai sai an yi,
Don
ba za ya tsare komai ba.
Gindi:
Bello shiri nai yai kyau,
Bai
ya da gudun Arna ba.
Alh Abdur rahman Galadiman
kotso Kano a waƙarsa ta sa Sunusi Sarkin yaƙi, Sarkin Kano. Inda yake
cewa:
Jagora: Arziki ba
wayo ne ba,
: Da biri ya tara
sulalla,
: Arziki ba wayo ne
ba,
: Da biri ya tara
awakai.
: Sa Sunusi Sarkin yaƙI,
: Zakin daga Na
abashe
Bahaushe na ganin ɗabi’ar kwaikwayo da biri ke da shi, yana daga cikin wayonsa. Domin kuwa babu
wata dabba da ta kai biri iya kwaikwayo, na dukkan abin da ya
gani ana yi. Wannan dalili ne ma ya sa Bahaushe ke yin wasa da biri ta hanyar
koya masa waɗansu abubuwa da zai rinƙa burge mutane, ana ba shi
kuɗi.
Wata karin Maganar kuma cewa ta yi : An san biri yana da
wuya, ake ɗaure shi a ƙugu.
Bahaushe
na nufin, saboda wayon da biri ke da shi ne, yasa ba a ɗaura masa igiya a wuya, sai dai a ƙugunsa shi ɗin ma, sai daga baya akan yi ƙulle igiyar, idan za a yi
wasa da shi. Dalilin haka shi ne, don kar ya kwance ya
gudu. Akwai wani Mutum mai suna
Malam Abdullahi Aliyu Galadiman kura (Sarkin Gardi na Malumfashi) da yace:
“ Na taɓa rainon wani biri wanda na
rinƙa wasa da shi.
Akwai wata rana da
birin nan yasa ‘Yansanda suka tsare
ni a Kaduna. A
nufinsu wai ba biri ba ne, mutum ne na
mayar da shi biri.
Bisa dalilin ayyukan da yake yi
waɗanda na koya mashi. Wannan
birin Magana ne ba ya yi,
ya iya tsallen canis,
tsayuwar ɗanfulani ba shanu, rawar bungalo,
ya iya shan fura, da
kokakola kai har taba sigari ya iya sha.
‘Yansandan nan ba su
sake ni ba, har sai wajen magariba
bayan sun yi min wasu
tambayoyi. A ƙarshe dai suka haƙura
suka sake ni, daga
nan na wuto gida Malumfashi kai tsaye”. [12]
Wata karin Maganar kuma cewa ta yi : Ko biri ya karye zai iya langa da kare. Ma’ana biri na da wayon da
zai yi ya kuɓuta daga
karen farauta. Sannan kuma akan ce: “ an yi kare jini, biri jini”. Ma’ana idan
aka tura karen da bai ƙware da farauta ba da nufin
ya kama biri, sukan ji wa junansu rauni, ko kuma a yi mutuwar kasko. Domin biri
kan kwanta rigingine, da zarar karen ya faɗa masa sai farke wa karen ciki.
Bisa sanin wannan wayon da biri ke yi wa karen farauta, shi ya sa maharba suke yin dabarar tura wa biri gogaggen kare wanda
ya samu horo sosai.
Dila; Dangane da ɗabi’ar wayo a jerin dabbobi, shi ma dila ba a
bar shi a baya ba, kamar yadda Bahaushe ke cewa, “Dila malamin dawa”. Tabbas! Allah Ya yi wa dila wayo, saboda kuwa wayon da dila ke da
shi, ya wuce duk inda ake tunani. Dabaru ko wayo da dila yake da su, suna da
yawa. Dubi irin yadda yake shan ruwa, da kwanciya, da yadda yake yin kuka da
sauransu.
Dila ne
kawai daga ciki dabbobi ba ya shan ruwa da baki, sai dai ya tsoma jela ya haye
tudu ya tsotsa. Duk wannan a dalilin rashin yarda ne, ya sanya ba ya shan ruwa
da baki.
1.
Shan ruwa: Dila ne kawai ba ya shan ruwa da baki, saboda tsabar wayo, sai
dai ya tsoma jela ya haye tudu ya tsotsa. Duk wannan a dalilin rashin yardar
ne, ya sanya ba ya shan ruwa da baki. Dila in ya zo kogi, baya shan ruwa da
baki kamar sauran dabbobi ‘yan uwansa. Maimakon haka sai dai ya tsoma jela
(wutsiya) a ruwa, sannan ya koma tudu ya tsotsa. Wani Makaɗin Gambara Dogo Na Abu
Kano, a waƙarsa yake cewa:
Jagora: Duk wanda
yace ba mu ba,
: Cikin maza ko mata,
: Na goye ko yayayye,
: Ubansa shi dila ne,
: Bai shan ruwa da
baki,
: Sai dai ya tsoma
jela,
: Ya haye tudu ya
tsotsa. ”
2.
Kwanciya: Ko irin yadda yake kwanciya
baccinsa, shi ba ya kwanciya a sarari, sai dai a sarƙaƙiya. Haka kuma, a tsakanin busasshen ganye yake yi, shi ma alamar
wayo ne ga dila. Imam (1937).
3.
Kuka: irin yadda yake yin kuka
abin lura ne. Dila baya yin kuka a wuri ya tsaya, sai dai da ya yi a kudu sai
ya koma yamma. Ko ya yi a gabas ya koma arewa. Haka kuma saboda tsabar wayon
dila ne ya sanya ba a kama shi da tarko. Haka kuma in ya yi kuka sai a ce shewar
dila, ko a ce guɗar dila guɗar banza. Wai don kar mafarauta su mamayeshi. Audu Mai Tandu Garu,
a waƙarsa, a wata waƙarsa mai suna mu a gida mun
gode Allah, yake cewa:
Jagora: A gaida dila
sarkin dabara,dila,
: A gaida dila wayo
gareka,dila,
: Idan ya fito duba
ka gane,dila,
: Idan ya fito sai ya
yi guɗa,
: Ba zaya tsaya ba,
sai ya ruga,
: Idan ya taho
kogi,ka duba,
: Sai ya tsaya gaɓa ya duba,
: Idan ya tsaya kuma,
sai ya waiga,
: Sannan ya ciro
bindi ya tsoma,
: Sannan ya haye
tsauni ya tsotse,
: Kadan ya ƙoshi daga nan ya ruga,
: Idan bai ƙoshi ba,sai ya koma.
: A gaida dila sarkin
dabara,dila,
Gindi: Mu a gida mun
gode Allah.
Haka nan kuma, a rubutaccen adabi akwai wani Labari Mai suna Dila
Sarkin Dabara.
“Labarin Dila Sarkin Dabara”
Wata rana wata hankakiya tana yawo sai ta hangi wani guntun nama a
kusa da wani gida. Ta sauka ta ɗauka,ta tafi kan wata bishiya ta sauka. Ashe dila na ganinta, kuma
ransa ya biya da guntun nama nan. Dila sai tunanin yadda zai raba ta da naman,
kawai sai ya nufi gindin bishiyar. Yana isa yace da hankakiya jiya naji kina
yin wata waƙa kuma naji daɗin muryarki. Ko da hankakiya taji an yabe ta, sai ta ji daɗI, ta wangame baki zata yi
waƙa, ta mance da naman dake bakinta. Tana fara waƙa nama ya faɗo, shi kuwa dila ya ɗauke nama ya gudu abinsa.
A wata waƙar kuma ta Ali ‘YanDoto
Alhaji Musa Ɗan ƙwairo, yake cewa;
Jagora: Da zomo, da
burgu, da kurege.
Kowanne hali yakai
banban,
Burgu shi ka rami
cikin ƙunƙu,
Zomo shi ka rami
gaton kalgo,
Na ga kurege ya yi
gajar gaba,
Sai yai jawabi nai
shi kau,
Narega mai gida ɗai wawa,
In nas shiga ban
fitowa nan,
Inda duk na shiga ban
fitowa nan,
Sai yay yi ɓulo nai can da ban,
In an ragaɗa in ficewata.
Kurege: Shi ma yana da irin nasa wayon, kamar yadda Bahaushe ya nazarce
shi. Wannan ya sa ya saɓa wa sauran dabbobi masu shiga rami. Shi raminsa bai yin
hanya ɗaya, sai
dai ya yi hanyoyi da yawa, waɗanda ake kira ɓuga ko ɓula. Waɗannan hanyoyi yana amfani da su don ya gudu ya tsirar da ransa,
idan aka biyo shi. Haka kuma ƙurar da yakan tayar wajen
gudu duk dabara ce ta kuɓuta. Kamar yadda Salihu Jan kiɗi yake cewa a wata waƙarsa:
Jagora:
Fitar kurege rami
Ba
tserewa yai ba
Wata ƙura na baya.
Alhaji
Musa Ɗan ƙwairo Maradun a waƙarsa ta ‘Yan Doton Tsafe Mai suna Gagarau Mai jiran daga Ali na
Magaji ci fansa cewa ya yi:
Jagora:
Na rega mai gida ɗai wawa,
Sai
yai ɓulo nai
can daban,
In
an ragaɗa in
ficewa ta.
Gindi:
Gagarau Mai jiran daga,
Ali
na Magaji ci fansa.
Zomo: Haka shi ma Bahaushe na jingina masa wayo ne, saboda yanayin
siffarsa, saboda yana da ƙaramin jiki. Don haka ba
wuya ya samu wurin ɓuya, da kuma wasu ɗabi’unsa, kamar a inda yakan tayar ƙura in
yana gudu. Da zarar aka biyo sai ya tayar ƙura,
sannan ya samu gindin kalgo, ko sabara ya ɓoye. Wannan ya sa Bahaushe ke yin wasu Karin maganganu kamar haka:
An wuce zomo a sabara, ko can ga su gada zomo ya ji kiɗan farauta. Haka kuma da
wasu almarori guda biyu, “Almarar zaki da zomo” da almarar Namuduka, kamar
haka:
Banza
girman mahaukaci, ƙaramin mai wayo yafi shi.
“wani mugun zaki ya damu dabbobin daji da kisa sun rasa yadda za
su yi sai aka tura zomo sai ya tafi yace da zaki akwai wani baƙon zaki ya zo yana cutar da su kuma yace babu wanda ya isa ya taka
shi, sai zaki ya fusata yace, mu tafi in ganshi, sai zomo ya taho da shi bakin
wata rijiya ina yace yana cikin nan, zaki na leƙawa sai ya ga hotonsa a cikin ruwa a zatonsa wani zakin ne sai
kawai ya faɗa rijiya don ya kashe wancan zaki shi ke nan ya mutu dabbobi suka
huta shi ne ake cewa banza girman mahaukaci ƙarami mai wayo ya fi shi. [13]
Almarar Namuduka (zomo da kura ‘ya’yanta.
Zomo ne ya tarar da kura ta ɓoye ‘ya’yanta a rami, shi
ma sai ya shiga yace sunansa namuduka. Don haka duk lokacin da kura ta kawo wa
‘ya’yanta abinci, sai zomo ya tambaya, na wane ne?, sai kura tacenaku ne,sai
zomo yace namuduka?,sai kura tace e. Shi kuma zomo sai ya cinye ya hana kowa.
Wata rana sai kura tace da ‘ya’yanta su fito ta gansu. Ko da suka fito, sai tag
a sun rame,tace ina abincin da nake kawo maku? Sai suka ce namuduka ne ke
cinyewa. Kura cikin fushi tace: waye namuduka? Suka ce yana ciki,sai tace kai
ma fito, maimakon ya fito sai ya miƙo kunnuwansa yace da kura
ga takalmana nan riƙe min. Kura cikin fushi ko
da ta kama kunnuwan zomo sai ta yi jifa da shi. Zomo kuwa ya tashi ya ruga da
gudu abinsa, shiru-shiru tace fito mana! Sai ‘ya’yan suka ce ai shi ne kika
jefar kuma ya gudu. [14].
Hatta
irin bacci da zomo yakan yi, sai da Bahaushe ya nazarceshi, sannan kuma yana
kallonsa a matsayin wayo. Kamar wata Karin Magana mai cewa: baccin zomo, ma’ana
baccin da ba a rufe ido gaba ɗaya. Akwai wani mawaƙi Ɗanmani Gumel mai gurmi a wata waƙarsa ta
Direbobi inda yake cewa:
Jagora:
Mai shirin gudu zomo,
A
tsugune yake kwana,
Don
shirin gudu zomo,
A
faɗawa
direbobi
Ga
mai kibiyar ya zo.
Ɓera: shi ma Bahaushe na jingina
masa wayo ne, saboda yanayin siffarsa, kuma yana da ƙaramin jiki, don haka yake samun wurin ɓuya a cikin ɗakunan Bahaushe, da kuma
wasu ɗabi’unsa.
Kamar a inda yakan ƙetere tarko daban-daban
wanda Bahaushe kan haɗa masa ya gudu. Da zarar ya biyo inda tarko yake, sai ya ƙetare, sai dai tsautsayi, ko ajali. Kasancewar rayuwar ɓera kusan a ɓoye cikin rami bai hana shi
wayo ba. Wannan ya sa Bahaushe ke yin wasu Karin maganganu kamar haka: “Idan an
ciza to a hura”, wai ɓera ne kaɗai ke cizon mutum bai ji ba, saboda in ya ciji mutum sai ya tsaya
ya hura wurin. Bayan wannan kuma, ɓera kan gwagwiyi gashin kan mutum ya tafi raminsa don ya yi wa
‘ya’yansa sheƙa. Wayon ɓera ke sawa mutum bai ji, sai da safe a rinƙa cewa wai ma’askin dare ya aske gashin. Haka kuma da wata almara,
“Almarar ɓeran birni da ɓeran daji”, kamar haka:
“Wata rana ɓeran birni ta tafi daji wurin ɓeran daji. Ko da ya je
sai ya ga abincin `ɓeran daji daga harawa,sai dankali, sai ciyawa.
Nan
take sai ɓeran birni ya kushe abinci, sai yace ɓeran daji
shi
ma ya zo birni don ya ga irin daɗin da yake ci. Ɓeran daji
wataran
ya tashi ya tafi birni. Da isarsa sai ɓeran birni ya
tarbeshi,
sai ga soyayyen nama ɓeran daji zai ci ke nan sai
ɓeran birni ya hana shi yace
kar ka taɓa tarko ne, suka wuce.
Daga
nan kuma, sai ga wani abincin har zai taɓa, ɓeran birni yace
wannan
da magani in ka ci zaka mutu. Bayan wannan kuma
suna
cikin tattaunawa kawai sai ɓeran birni yace yi maza ka
shiga
rami ga mage nan,suka shige rami a guje. Ganin irin
wannan
rayuwa mai cike da hatsari wadda ɓeran birni ke ciki,
sai ɓeran daji yace: A gaskiya
rakani in koma daji in ci-gaba da
rayuwata
a sake, bairin wannan ba. Da arziki da tashin hankali,
ai
gwamma tsiya da kwanciyar rai, inji ɓeran daji. ” [15]
3. 0.
WAYON TSUNTSAYE A TUNANIN BAHAUSHE.
Dangane
da tsuntsaye su ma akwai waɗanda Bahaushe ke alaƙanta su da wayo, kamar
hankaka, da makwarwa ( fakara) , da yautai, da kurciya, da tsadda da gado.
Hankaka: Bahaushe na danganta wayo ga hankaka, bisa wannan dalili ne ya
sanya hankaka ba shi da yarda, da zarar ya ga mutum sai ya yi shirin tashi ya
gudu. Akwai wata karin Magana mai cewa: Ɗan adam
in yana tsaye ne yake mutum idan ya duƙa ya zama
mugu, inji hankaka.
Labarin
Hankaka Mai hikima:
Wani hankaka ne yana jin kishirwa yana neman inda zai sha ruwa.
Sai ya hangi wani tulu. Ya yi ƙasa-ƙasa ya sauka a bakin tulun, ya leƙa ya ga akwai ruwa a ciki sai dai kash! Yawan ruwan rabin tulu ne,
bakinsa ba zai kai yadda zai sha ba. Yana nan bakin tulu, yana tunani. Ga ƙishirwa yana ji, ga ruwa yana gani,amma ba hali ya sha, yaya ke
nan. Kawai sai ya je yana tsino duwatsu yana jefawa cikin tulun, da haka ruwa
ya rinƙa yiwo sama har yakai yadda bakin hankaka zai kai, ya sha iyakar
yadda ya ishe shi ya tashi. [16]
Kurciya: Bahaushe ya danganta kurciya da wayo, bisa wannan
dalili ne ya sanya ba ta da yarda, da zarar ta ga mutum sai ta yi shirin tashi
ta gudu. Akwai wata karin Magana mai cewa: an nunawa kurciya baka. Ko kuma a ce
kukan kurciya ma jawabi ne, mai hankali ke ganewa.
Haka kuma a tatsunniyoyi da dama kurciya kan fito ne a mawaƙiya, saboda mai wayon kaɗai ke iya shirya waƙa. Kamar a tatsuniyar
Ta-kitse, da tatsuniyar kurciya da shaida, tatsuniyar Gizo da Dodanniya,
tatsuniyar Kurciya da shaida.
Tatsuniyar
Ta-kitse.
Bayan Sarki ya hana a sanya Ta-kitse aiki, sai wata rana ya tafi
yaƙi. Kishiyoyinta kawai sai suka c eta fito ta yi. Fitowar ta ke
wuya, saboda zafin rana, da zafin wutar girki, sai ta fara narkewa. Nan da nan
gida ya fara ruɗewa, kowa na kawo shawara ta yadda za a faɗawa Sarki. Ana cikin haka,
sai kurciya ta zo tace, zata iya faɗawa Sarki a bakin daga, aka yarda ta tafi, da isar ta sai tace:
Sarki Sarki a mai da yaƙi baya. Ta-kitse ta nark
eta nark eta zama gulbin tsakar gida. Sarki na jin wannan waƙa da kurciya ke yi, sai ya dakatar da yaƙi ya koma gida.
Tatsuniyar Gizo da Dodanniya.
Wata rana gizo ya tafi gidan dodanniya ya karɓo bashin bajimin sa, da alƙawarin zai biya shekara mai zuwa. Ya zo ya cinye, ya hana kowa. Ko
da shekara ta zagayo, sai dodanniya ta zo bin bashi gidan gizo. Bayan dodanniya
ta iso gidan sai ƙoƙI tace gizo ya mutu. Har ta kama hanya zata koma, sai kurciya
tace ƙarya ne. Daga nan sai suka koma gidan gizo, ta fara waƙa tana cewa:
Kurciya:
Mabiyan bashin gizo sun iso,
Mabiyan
bashin gizo sun iso,
Zai
yi biyan bashi a kushewa,
Gizo:
Un uhun wai ya kurciya,
Ki
biyo ta gidan mu ki sha ruwa,
Ruwanki
na nan a kururrumi,
Bari
in fita in taɓa ‘yar rawa,
Bari
in fita in taɓa ‘yar rawa.
Daga nan
sai gizo ya fito dodonniya ta kama shi ta tafi da shi gidanta.
Tsadda: Ita ma Bahaushe na jingina mata wayo, saboda ƙanƙantar jikinta. Domin kuwa ita ce mafi ƙanƙanta a cikin tsuntsaye. Bahaushe na ganin tsabar wayo ne, ya sanya
tsadda ba ta da yarda, duk irin hali da take ciki ba ta amince wa Ɗan adam. Hatta mata da sukan yi surfe ko sussuka, tsadda ba ta
amince masu. Akwai wata karin magana mai cewa: “in kun tashi ma dawo,” wai
tsadda ta ga masu surfe. Haka kuma Bahaushe ya fassara tafiyar tsadda da cewa
wayo ne, saboda tafiyarta tsalle take yi, kar tarko ya kama ta.
Makwarwa: Game da makwarwa ita ma Bahaushe yana jingina mata ɗabi’ar wayo, ana iya cewa
ta saɓawa
sauran tsuntsaye. Domin wayonta, ita ba a iya kama ta da hannu ko harbi, sai
dai da ashifta wani irin tarko da ake baza shi a ƙasa ko da yake ana alaƙanta ta layar zana da take
yi, shi yasa ake shan wahala wajen kamata. AKwai wasu hujjoji a rassan adbin
Bahaushe, kamar wata karin Magana mai cewa: “An yi shuka a idon makwarwa. ”
Ma’ana an yi wani abu a gaban mai wayo, kuma ya gano abin da aka shirya. Kamar
yadda Alhaji Ɗan Mani Gumel mai gurmi yake yi mata waƙa yake cewa:
Jagora
: Tone masu shuka ‘yar fakara,
:
Tsintsi abinki ’yar fakara
:
Ke tashi ki bar su ’yar fakara.
:
Ke bar su da tarko ’yar fakara
Gindi :
Girma aka fi ki ‘yar fakara,
:
Nuna masu laya yar fakara,
Yautai: Shi ma yana da wayo, don haka ake yi masa, kirari da cewa: yautai
mugun tsuntsu maso jininka ya kwana a daji, saboda ɗan karan wayo bai kamuwa da
hannu, sannan kuma ba zai gudu gaba ɗaya ba, sai dai ya yi ta yaudararka. Haka kuma akan ce: Yautai
maso miya da kai ya yi dare. Kamar yadda Malam Amadu Ɗanmatawalle Haɗeja a waƙarsa ta Tsuntsaye Zasu
Neman Sarki cewa ya yi:
Jagora:
Yautai ka baiwa mulki,
Sun
ce yautai munafuki ne,
Wannan
shi za ya ɓata mullkinsa,
Mai
halin kilaki shege ɗan yawon shakiyin tsuntsu.
Gado: shi ma yana da wayo fiye da wasu tsuntsaye, wannan ne ma ya sa
ake yi masa kirari da cewa: “ gado ba don kana da wayo ba, wai sai yace da
yanzu ina gaban wuta na yi ƙerere. ”
Ko kuma
wata fassara da ake yiwa kukansa inda wai yake cewa:
Mata uku
da daɗi suke,
Mata
uku da daɗi suke,
Guda
tana “yi kazar- kazar taku ta maza”,
Guda
tana “yi lamo kamar ka mutu”
Guda
na “sai a je juji a yar !!!”.
4. 0.
KAMMALAWA.
Bahaushe ya ce “mai hankali
ke gane baccin makaho”, don haka babu mamaki idan aka ga Bahaushe ya naƙalci ɗabi’un waɗansu dabbobi. Har ya gano cewa wasu dabbobin sun fi wasu wayo daga
cikinsu. Wannan ba ya rasa nasaba da irin cuɗanyar da ke wakana a tsakaninsu, saboda su dabbobin gida sun zama
kamar tsumma ne da ƙwarƙwata. Haka kuma ko su dabbobin dajin bai bar su kawai ba, sai da
ya taɓo su.
Wannan irin matsayi na nazari wanda Bahaushe ke alaƙanta waɗansu ɗabi’u, ko halaye ga dabbobi, ya tabbatar da kaifin tunaninsa. An
dubi wannan tunanin ne, ta hanyar yin amfani da waɗansu hujjoji da a ka samo
daga wasu rassan adabin baka. Bayan haka kuma, maƙalar
ta ƙara fito da muhimmancin adabi, da kuma dabbobin su kansu.
Babu
shakka, an fito da waɗansu abubuwa a wannan muƙala, don an gano irin shaƙuwar da ke tsakanin Bahaushe da dabbobi tun daga na gida, har zuwa
ga na daji. Haka kuma, an ƙara fito da bambancin da ke
tsakanin dabbobin su kansu, musamman ta fuskar ɗabi’unsu. Wannan zai sa
mutum ya san irin zama da zai yi da dabbobin. Bayan haka, irin kallon da
Bahaushe ke yi wa dabbobi shi kansa abin lura ne. Domin kuwa ya nuna cewa
Bahaushe bai yanke wannan hukunci ba, sai da ya ɗauki dogon lokaci yana
nazarinsu. A ƙarshe Bahaushe na cewa: yau da kullum ta fi wasan yaro.
MANAZARTA.
Abraham,
R. C. (1947) Dictionary of the Hausa Language London Hodder
&
Stoughton.
Bargery, G. F. (1993) A
Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary
Ahmadu Bello
University Zaria.
Bunza
A. M. (2006) “Gadon Feɗe Al’ada”,Tiwel Nigeria Limited
Lagos.
Bunza
A. M. (2009) “Narambaɗa”,Ibrash Islamic Publication
Centre Limited Lagos
Bunza
A. M. (2014) “Wauta A Tunanin Bahaushe”Takarda da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru
‘Yar’adua, Katsina
Dogarai
I. A. (1992) “Namun Daji a Ƙasar Hausa, ire-irensu da
magungunan da ake samu
daga
garesu”. B. A Hausa. Bayero University, Kano.
Ɗangambo, A. (2007) Ɗaurayar gadon feɗe waƙa” sashin koyar harshen,
B. A. Hausa.
Bayero University Kano.
Gusau
S. M. (1988) Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu Da Yanayinsu Musamman a Ƙasar sakkwato”. Ph. D. Hausa. Bayero University Kano.
Garba M.
(1998) Azancin Magana a Waƙoƙin Makaɗan Baka. M. A. Hausa.
Bayero
University Kano.
Ilyas Bn I.
(1986) Ƙamusun Larabci Arabic-English Dictionary.
Mahe I.
A. (2008) “Amfani da Dabbobi a fagen gina Adabin Hausa”. M.
A. Hausa.
Bayero
University Kano.
Muhammadu
Ingawa da Jean Boyd (1972) littafin Ka yi ta karatu na 4 Northern
Nigerian
Publication Company, Zaria.
Mish R. C. da Promila
(2010) International Encyclopaedia of Education, & Philosophy
of Education Vol. 4.
McGraw Hill (2011)
The Science Psychology An Appreciative View 2nd Edition.
Sa’id B. (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar
Bayero Kano A. B. U. Press Zaria.
Skinner
N. (1999) Ƙamus na Turanci da Hausa. Northern Nigerian Publication
Company,
Zaria.
Saleh (2002) “Hanyoyin
Sufuri na Gargajiya”. B. A Hausa. Bayero University, Kano
Yahya A.
B. (2001) Salo Asirin Waƙa, Sashen Harsunan
Nijeriya,
Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto.
Yahaya
I. Y. (1971) “Tatsunniyoyi da Wasanni”, Oxford
University Press, Ibadan.
[1] Skinner (1999) Ƙamus na Turanci da Hausa. Northern Nigeria
Publication Company, Zaria.p 91
[2] Bargery, G. P. (1934) a Hausa-English Dictionary.London
Oxford University Press.shafi 174
[3] Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006) , shafi na 82
[4] Hornby.A.S (2006) Oxford Advanced Learner’s Dictionary
University Press NewYork pg1688: Wisdom- the ability to make sensible decisions
and give good advice because of experience & knowledge that you have.
[5] International Encyclopaedia of Education, Philosophy of
EducationVol.4.2010: Consist of the ability to solve problems &to adpt to
learn from everyday experiences.
[6] McGraw Hill The Science Psychology An Appreciative View 2nd Edition
(2011) Wisdom,good sense the ability to make sensible decision and judgement
base on personal knowledge and experience.
[7] Ƙamusun Larabci Arabic-English Dictionary (1986) na Ilyas Bn Ilyas.
Shafi na 161. Hikmatun, Aƙal, Falsafa.
[8] Dubi Littafin Gadon feɗe Al’ada na Bunza A.M.2006 shafi na 290.
[9]Abraham, R. C. (1947) Dictionary of the Hausa Language, shafi 222.
[10] Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006) , shafi 143
[11]Bargery, G. P. (1934) a Hausa-English Dictionary.London Oxford
University Press.shafi 178
[12] Malam Abdullahi Galadiman kura (Sarkin Gardi na Malumfashi)
hira da shi a gidansa a Malumfashi. Juma’a 15/7/2011
[13] Dubi littafin Ka yi ta karatu na 4 (1972) Muhammadu Ingawa
da Jean Boyd shf—43-47
[14] Dubi littafin Ka yi ta karatu na 4 (1972) Muhammadu Ingawa
da Jean Boyd shafi na —43-47
[15] Dubi littafin Ka yi ta karatu na 4 (1972) Muhammadu Ingawa
da Jean Boyd shafi na —43-47
[16] Dubi littafin Ka yi ta karatu na 4 (1972) Muhammadu Ingawa
da Jean Boyd shafi—12-13
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.