Takardar daAka Gabatar A Kwalejin Shababil Islam Ta Koyon Harshen Larabci Da Addinin Musulunci. Unguwar Dosa, Kaduna. 18 ga Watan Satumba 2015.
ƘAWALLIYA ROMON JAƁA (ƘAUNARKI KE HANA JIN
WARINKI): TSOKACI A KAN ƘAWANCEN MATA, DA IRE-IRENSADA ALFANUNSA DA KUMA ILLOLINSA
DAGA:
DR.
MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD
DEPARTMENT OF LANGUAGES HAUSA UNIT
SULE
LAMIƊO UNIVERSITY KAFIN HAUSA, JIGAWA
STATE
1.0.0. Gabatarwa.
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai, Mai
kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so, a sadda Ya so, a
yadda Ya so, ko ana so ba a so dole bayi su so. Tsira da amincin Allah su
tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa da Sahabbansa. Wannan
maƙala na da ƙudurin fito da ma’ana, da
yanayi, da hanyoyi, ko dalilan ƙulla ƙawanceda fa’idoji da kuma illolinsa, da ire-iren ƙawaye, dahalayensu. Bayan wannan kuma an ɗan tsakuro wasu daga
cikin ɗabi’un ƙawaye (mata) , tare da nuna irin nauyinsu da matsayinsu a mizanin
al’adar Bahaushe. Wannan maƙala zata ɗan taɓo, wasu abubuwa game
da ƙawancen mata, tare da yin tsokaci a kan wasu daga cikin ɗabi’un da ke faruwa a
harkar ƙawance. Da farko akwai kyawawan ɗabi’u waɗanda akan samu a
dalilin ƙawance da mutanen ƙwarai (kirki). Haka kuma
akwai munanan ɗabi’u da akan ɗauka a dalilin yin ƙawance da miyagun mutane,
da Bahaushe ke ƙyama takowace fuska. Ba su da amfani ga rayuwar mutum duniya da
lahira. Don haka duk macen da ke ƙawance da muguwar ƙawa,ita ma ta zama abin ƙyamake nan ga mijinta, da
danginta,da abokan zama,kai da ma sauran al’umma baki ɗaya. In ban da ‘ya’yanta,
ko su ma don ya zama dole, Bahaushe ya ce “shegiyar uwa sai bukka”.
Wannan shi ne dalilina, ko hujja da suka sa na kira maƙalar da sunan“Ƙawalliya
Romon Jaɓa. ’’Wanda Bahaushe kan ce “ƙaunarki ke hana jin warinki. ”Aƙarshe
wannan maƙala hannunka mai sanda ce, duk wadda ta ji nasiha ta huta, wadda
kuwa ta ƙi ji, to ita ce ƙawalliya. Don haka dabarata
rage ga maishigarijiya, ko dai ki zama ƙawa
ta ƙwarai,son kowa ƙin wanda ya rasa. Ko ki
zama ƙawalliya.
1. 1. Fashin Baƙi:
Ƙawalliya: Na
nufin ƙawa, a nan, an yi wa sunan wata kinaya ce, ko kuma kwalliya.
Romo: Na nufin ruwan da aka dafa
nama dashi tare da kayan miya da maida sauransu.
Jaɓa: Wata ƙaramar dabbar gida ce dangin su ɓera, sai dai ita jaɓa tana da wari, da muni, da
dogon baki, ga baƙin jini, sannan ga ɓarna.
1. 2. Ma’anar ƙawa;Ƙawa na nufin wata mace wadda take hulɗa ko abota, ko aminci a
tsakaninta da wata. Akan ce ƙawa idan ɗaya ce, ko ƙawaye in suna da yawa, watau jam’i ke nan.
Akwai ƙawaye iri uku, da farko
akwai ƙawa ta ƙuruciya wadda aka taso
tare, tun ana datsa. Haka kuma akwai ta manyantawatau bayan an girma, a nan sun
kasu biyu da ta wucin gadi, sannan akwai ƙawa ta
dindindi (aminiya).
2. 0 Hanyoyin Da Dalilan Ƙulla Ƙawance.
Bahaushe yace, komai baya rasa dalili, “ba zan ƙi dalili ba,dalilin aure tsarance. ” (Ɗangoma 1990). Dangane da hanyoyin da ake samun ƙawa ko ƙawance kan ƙullu, su ne. Akwai zamantare, kamar zama a unguwa,ko gari ɗaya (Maƙwabtaka). Akwai hulɗa, kamar makaranta a dalilin yin karatu,
akwai kasuwa, saboda saye da sayarwa, akwai asibiti, ko gidan
biki, ko suna. Akwai tafiya ko hanya, saboda tarayya a mota, ko jirgi ko ayarin
fatake. Abotar mazaje masu aiki ko kasuwanci tare a wuri ɗaya.
2. 1. Zaman-tare; Haƙiƙa zamantare kan yi dalilin ƙulla ƙawance. Kusanci na maƙwabtaka kamar gidaje
makusanta, ko zama unguwa ɗaya, ko makusanta, yakan sanya mata su ƙulla ƙawance a tsakaninsu. Bayan
wannan zaman gida ɗaya (gidan haya) , ko makusanci na sanya mata su zama ƙawaye.
2. 2. Hulɗa;Tabbas hulɗa a tsakanin juna, ta
harkokin yau da kullum da suka shafi rayuwa, sukan sa a ƙulla ƙawance. Misali, hulɗar karatu a makaranta,
wannan kuwa zai iya kasancewa makarantar boko, ko kuma ta Islamiyya, ko ta
allo. A lokuta da yawa, ‘yan makaranta ɗaya, musamman waɗanda suke aji guda tare, sukan zama ƙawayehar zuwa girmansu.
2. 3. Hulɗar kasuwanci;saye da sayarwa a kasuwa,
ko a gida, kan sanya wasu matan su zama ƙawaye.
Wani lokaci kuma, ko babu ciniki a tsakaninsu ana iya samun ƙulla ƙawance, ko a dalilin haɗuwa a rumfar wani a kasuwa
don sayen wani abu. A wani lokaci kuma a saboda ɗaukar bashin kaya,
sai ƙawance ya ƙullu.
2. 4. Hulɗa a asibiti; haɗuwa da mata kan yi a
asibiti, sabodazama tare na dogonlokaci, kuma a yi doguwar hira da juna,
yakan ƙulla ƙawance. Akan samu wasu
matan a dalilin haɗuwa a asibiti sukan ƙulle har su rinƙa ziyartar juna a gidajensu.
2. 5. Hulɗar gidan biki ko taron suna;dalilin
bikin aure, ko taron suna wanda kan haɗa mata daban daban. Akan samu wasu matan dakan ƙulla ƙawance, ta dalilin gayyatar
uwar biki ko ƙawar ƙawa. A irin waɗannan wurare, ƙawance kan ƙullu. Ana samun irin wannan
ne idan ƙawar ta kai wa mai bikin gudummuwarkuɗi, ko tufafi. Irin
wannan ƙawance kan yi danƙo ya zama kamar zumunci na
jini.
2. 6. Hulɗar tafiya;wadda hanya kan haɗa, saboda tarayya a mota,
ko a jirgi na ƙasa, ko na sama, ko na ruwa, ko haɗuwa a tashar mota. Awani lokaci kuma a cikin ayarin fatake. Dukkan
waɗannan hulɗoɗi kan ƙulla ƙawance a tsakanin mata.
2. 7. Abotar mazaje; ita
ma wata hanya ce wadda matansu kan ƙulla ƙawance. Idan aboki da aboki suka shaƙu da
juna, sai a iske wannan abotar ta yi naso har zuwa ga matansu a wani lokaci ma
harda ‘ya’yansu. A wasu lokuta kuma kasancewa tare a ma’aikata ɗaya shi ma yakan
sanya ƙawance ya ƙullu a tsakanin matan
ma’aikatan wurin.
2. 8. Hulɗar Adashi: Adashi,
ko wajiji wata hanya ceta yin tattalin kuɗi, ko tsimi da tanaji. A inda za a samu wata mace wadda akan kira
uwar adashi,ko wani namiji wanda akan kira uban adashi. Mutane zasu rinƙa kawo masa kuɗinsu yana tara masu, har zuwa wani ƙayyadadden lokaci. Idan aka tara, sai a bai wa wani kwasa, shi
kuma zai biya a hankali ta hanyar kawo kuɗin zubi. Uwar adashi ko uban adashi yana da ladan da yake cirewa
daga kuɗin wanda
ake kira karan adashi. Bisa al’ada, mata ne aka fi sani da yin adashi. Wannan
shi ma wata hanya ce mai ƙulla ƙawance, a tsakanin mata.
2. 9. Hulɗar Yara: Abotar
yara a tsakaninsu a wani lokaci kan zama dalilin ƙawance na wasu iyaye mata. Domin Bahaushe yace, “maso uwa ya
so ɗanta”,
haka kuma mata kan ce: “aida karanka kake ganin na wani”. A dalilin wannan, sai
kaga iyaye mata sun ƙulle da ƙawance abin ya zama kamar na zumunci.
3. 0. Ire-Iren Ƙawaye Da Halayensu.
Kamar yadda Bahaushe yace, “an daina kiwon dabba yanzu, mutum ake
kiwo. ” Bisa wannan dalili ne yasa tilas ne ga kowace ƙawa ta san irin ƙawancen da suke yi, sannan
kuma wace irin ƙawa ce kike tare da ita?A wannan nazari da nayi akan harkar ƙawance, na fahimci akwai ƙawaye
irin huɗu. Kowace
daga cikinsu, na bata sunan daya dace da ita:
1. Ƙuda ba ki bin kwandon
gawayi. 2. Kaska ba ki rayuwa sai da wani.
3. Shirinya raɓi ki kashe. 4. Sauyar dankali a bi ki a lalace.
3. 1. Ƙuda ba ki bin kwandon
gawayi: Wannan ƙawar, makwaɗaiciya ce, ba don Allah take yin ƙawance ba, a’a, sai don wani abin duniya ko wata buƙata. Matuƙarta fahimci ba zata samu
wani abin moriya ba, to ƙawance ba zai daɗe ba. Idan kuwa akwai maiƙo, to kowane irin wulaƙanci za a yi mata, za ta
daure. A wurin ta babu maganar addini, ko mutunci, sai dai kuɗi ko holewa, da zarar babu,
to gayya za ta watse ba kunya ba tsoron Allah.
3. 2. Kaska ba ki rayuwa sai da wani: Wannan ƙawar, ita ma muguwa ce,
saboda ita bata ƙulla abin arziƙi, kuma ba za ta bari wani ya ƙulla ba.
Da farko za ta dinga cutar ƙawar, ta hanyoyi
mabambanta. Ita ƙawar, bata iya ganewa,
sannan kuma ko an faɗa ma ta, ba zata yarda ba. Bisa dalilin cewa, wasu ƙawayen har bokaye da masu tsibbu suke shiga waisu samu ɗaurin baki, don kawai su
cuci ƙawarsu. Idan suka tasa ta gaba, sai sun ga bayanta, misali in suna
da jali na kasuwanci, saisu karyata, ko kuma kayan ɗaki, ko kadara su halakar
dasu. Ko kuma su ingiza ƙawar tarinƙa cutar miji ta hanyar cin bashi wanda dole sai ya biya, ko tarinƙa satar kayan abinci tana sayarwa, ko kuma kuɗin mijin. Haka kuma akwai
mai rage kuɗin
cefane, ko ta yi mazada a kuɗin makarantar yara, ko na magani (asibiti) , ko ƙaryar ciwo.
3. 3. Shirinya raɓi ki kashe: Ita kuma
wannan ƙawar takan yi ƙawance ne, da buri biyu a
ranta. Da farko bata ƙi mijin ƙawarta ya saki ƙawar ba, ita kuma ya
aureta. Ko kuma mijin ƙawar ya auri wata ƙanwarta, ko ‘yarta ba. Idan kuma haka bai samu ba, sai ta yi ƙoƙarin ta raba ƙawarda mijinta kwata-kwata,
ko da ba zai aureta, ko wata ‘yar uwarta ba. Wani abin takaici shi ne, ba zata
fito fili ba, sai dai ta dinga zuga ƙawar. Wai ita nan tana
nemar ma ta ‘yanci daga wulaƙanci. Wannan yasa nake
ganin dukkan mace mai hankali ta kiyayi ƙawaye da
yawa. Sannan ta kiyayi ƙawa bazawara, musamman
wadda ta daɗe tana
zawarci.
3. 4. Sauyar dankali a bi ki a lalace: Ita kuma wata ƙawace muguwa, wadda idan ba
a yi sa’a ba, takan halakar da ƙawar gaba ɗaya. Irin wannan ƙawar, takan ja aminiyarta zuwa ga miyagun ɗabi’u. Da farko takan koya
ma ta zuwa gidan boka, ko watsewa a waje (bin maza). Ko ta koya ma ta cin bashi
harta zama turun bashi. A irin wannan, shi ma sukan yi sanadiyyar mutuwar aure.
Wanda idan ba ki yi sa’a ba, sai ki rasa miji, ki rasa mutunci, sannan ki saɓa wa Allah. Kamar yadda
Adamu Ɗa Maraya Jos a waƙarsa ta Gulmawiya mai
sha’anin tsiya, ya ce:
Ashe boka
daban,
‘Yar
korar boka ma daban,
Gulmawiya
mai sha’anin tsiya,
Mai son
raba sunnar Rabbbana.
Kwaram
sai gata cikin gida,
Mai gidan
nan na nan kin jiya,
Shin a a
ko ya fita?
Uwar gida
ta cane mata,
Ai ko
malam ya fita.
Ga
labari ɗa kaɗan
Na jiwo
ne can ko ga unguwa,
Wai Malam
zai ma ki kishiya?
Sai
uwargida ta buga ƙirji nan da nan,
Yanzu
Malam zai min kishiya?
‘Yar
korar boka tace,
Wannan
zancen haka yake,
Wannan ba
shakka kuwa.
Uwar gida
tace to yaya zani yi?
‘Yar kora
ta faɗa mata,
Akwai
wani baƙon boka a nan,
Can
layin su magajiya.
Ki
tambayi mai gida
zaki
je kuma barkar haihuwa,
Mu haɗe layin su magajiya.
To dama
tun kan su zo,
‘Yan
korar boka daɗa,
Ta je
wurin boka kuma,
Ta
faɗa masa
komai ya sani.
Assalamu
Alaikum Malami,
Ai
daman na san zaku zo,
Ƙasar nan ta nuna mani,
Ƙasa ba ta ƙarya kuwa,
Abin Ƙasa ta faɗa mani,
Malam zai
miki kishiya.
Uwagida
tace Malam yaya zani yi?
Malam
sai ya faɗa ma ta,
Ki
ba ni farin zoɓo biyar,
Turmin
alawayyo guda biyar,
Ki ba ni
karaunu guda biyar,
Ki
ba ni kuɗinki sule ɗari,
Lallai
zan maki magani.
4. 0. 0. Niyyar Ƙawance:
Bahaushe kan ce niyya numfashin aiki, dukkan abin da mutum zai yi
niyyarsa itace kan gaba. Bisa wannan dalili ne ya sa idan aka samu
ingantaccen ƙawance kuma sahihi yana dogaro ne da niyyar yinsa. Haka kuma idan
aka samu gurɓataccen ƙawance, shi ma yana tare da asalin niyyar ƙulla shi. A wani hadisi Umar Bin Khattab (R. A) yace: “dukkan aiki
sai da niyya. ”………[1]
Haka kuma akwai wani bayani da ya nuna cewa: duk wanda ya samu
abubuwa uku, haƙiƙa ya samu ƙololuwar imani. 1.
Soyayyarsa da Allah da ManzonSa. 2. Yin soyayya don Allah. 3. Yin ƙiyayya ga kafirci koda za a sa shi a wuta.
4. 1. Abubuwan Da Kan Sanya Ƙawance Ya Yi Ƙarko: Akwai wasu abubuwa na sarari da na ɓoye waɗanda kan sanya ƙawance yayi ƙarko, watau ya daɗe. Waɗannan abubuwa kuwa, sun haɗa da haƙuri da juna, da kyautatawa juna, da amincewa juna, da girmama
juna, mutunta juna, kawaici da sauransu. Matuƙar aka
rasa ɗaya daga
waɗannan
abubuwa, tabbas ƙawance bai zuwa ko’ina, ba
zai daɗe ba.
Koda ya daɗe za a
iske ana zaman doya da manja ne.
4. 2. Abubuwan Da Kan Sanya Ƙawance Ya Watse: Bisa lura
da bayanai da suka gabata, ana iya cewa in aka samu kishiyoyin waɗancan halaye, to ƙawance bai kai wa ko’ina. Da zarar aka ce akwai kwaɗayi, ko wulaƙanci, ko ha’inci, ko munafunci a tsakanin ƙawaye ba inda za a, zai ɓalɓalce.
5. 0. 0. Matsayin Ƙawa A
Wajen Ƙawa.
Ƙawa na da wani matsayi mai muhimmanci a wurin ƙawarta. Wannan matsayi kuwa, yana da fuska biyu ko harshen damo.
Da farko akwai ƙawarda take da kyakkyawan matsayi a wurin ƙawarta, saboda kyawawan shawarwari waɗanda take bai wa ƙawar. Bayan haka, kuma ta sanya ta cikin harkar addini da kuma bin
hanya ta ƙwarai. Kyautatawa wa miji, da sauran abokan zama.
Bayan ga wannan ƙawa kuma, sai wata wanda
take da mummunan matsayi. Wannan ƙawar kuwa itace wadda bata
da nufin alheri a ranta game da ƙawarta. Da farko ba zata
bata shawara ta ƙwarai ba, sai dai muguwar
shawara. A irin waɗannan ƙawaye ne ake samun masu
shirya wa ƙawa gadar zare su raba tada mijinta, a wani lokaci su kewaya su
aure shi. A wani lokaci ma ko ba zasu aura ba, su dai raba ta dashi. Haka kuma
irin su ne suke jan ƙawa zuwa gidajen bokaye da
malaman tsibbu. A irin wannan halin wasu matan har aurensu kan mutu, ko su faɗa tarkon zina. Misali. wata
mata da ƙawarta ta kaita gidan malamin tsibbu harta faɗa tarkon zina, ga babu
biyan buƙata, sannan mijinta ya saketa (Jaridar Aminiya 2008).
“Da zan cire rigarta, saida na tsaya ina tunani, amma dana
tuna maganar da ƙawata ta faɗa min cewa aikin malamin
kamar yankan wuƙa ne, sai kawai na cire,
yana ɗora bakinsa a kan nonona, shike nan ban ƙara sanin inda nake ba, sai a ƙarshe naga babu tufafi a jikina, shi ne na fahimci halin da na
samu kaina a ciki, ba wanda ya kai ni sai ƙawata”……[2]
Dangane da matsayin ƙawa a wajen ƙawa, ana iya cewa wani matsayi ne na cuɗanni-in-cuɗeka. Ma’ana rayuwa ceta
taimakekeniya, watau wannan ya taimaki wannan ta kowace fuska. Idan kuwa ƙawa ta kasance saɓanin haka, to ta zama muguwar ƙawa.
5. 1. Ƙawa Ta Fi Miji: Haƙiƙa matsayin ƙawa a wurin wasu matan, ta
fi mijinsu daraja. Domin kuwa suna ɗaukar maganar ƙawa, watau shawararta fiye
da yadda suke ɗaukar maganar mijinsu. Akwai wasu matan idan suna tare da ƙawarsu, ko da mijinsu ya shigo gida, ma’ana ya dawo daga waje ba
za su tashi su tarbe shi ba, kai wasu ko sannu da zuwa ba zasu yi masa ba. A
wani lokaci ma, su tashi su kawo masa abinci yakan gagara, sai daisu ce yara ko
masu aiki su kai masa. Ba don komai ba, sai don sun tsinke da hirarsu, ko kuma
kar su saɓa
wa ƙawar nan tasu.
Bayan wannan kuma, akwai macen da a dalilin zuwa bikin ƙawa, sai aurenta ya mutu. Domin wasu dasu bar zuwa gidan
bikin ƙawa wai don mijin ya hana su, sai dai a yi komai. Kamar wata waƙa imfiraji da Aliyu Namangi yayi inda yake cewa:
Ni da ma
auranka ni dai,
yi
da barin shi daidai,
Ba zai
hana ni zuwa bikin sa’a ba.
Wani abin haushi shi ne,wasu matan sai su rinƙa faɗawa ƙawayensu sirrin gidansu
dana mijinsu wai don amincewa.
5. 2. Ƙawa Ta Fi Iyaye: Akwai wasu mata marasa hankali dasuke ɗaukar ƙawarsu tafi iyayensu matsayi. Dalilin da kan tabbatar da wannan
magana kuwa shi ne, waɗannan mata sukan girmama maganar ƙawarsu fiye da maganar iyayensu. Akan samu wasu matan waɗanda iyayensu kan faɗa masu magana ta umarni, ko
shawara, ko nasiha, amma da zarar sun faɗawa ƙawarsu, in tace a a, to
maganar ƙawarzasu ɗauka. A wani lokaci ko da basu ci nasara ba, basa ganin
laifin ƙawar, sai daisu ja bakinsu su yi shiru. Sau da yawa, ƙawa kan warware tarbiyyar da iyaye suka yi wa wasu daga cikin
‘ya’yansu. Haka kuma wasu matan ko da ƙawarsu
tana cutarsu, ba zasu furta ba, balle su faɗawa iyayen. Bayan wannan kuma, wasu matan ƙawa kan more su fiye da iyayensu. Kamar irin kyautar da zasu yi
wa ƙawarsu, ko rabin haka ba zasu iya bai wa iyayensu ba. Bayan wannan
kuma, akwai ƙawar da idan ta je ɗakin ƙawarta, sai ta ɗauki abin da ta ke so,
amma ƙawar ba zata hana ba.
5. 3. Ƙawa Ta Fi Dangi: Akwai wasu matan da sukan bai wa ƙawa wani babban matsayi wanda ya zarce na danginsu. Wannan kuma ya
haɗa ne tun
daga danginsu na jini har ya zuwa dangin miji. Ana iya fahimtar hidima,
ko ɗawainiyar
da suke yi wa ƙawarsu. Akwai matan da ko allura basa iya bai wa ‘yan uwansu, to
amma ƙawarsu ko me ta nema zasu bata. Kamar idan ana bikin aure, ko
suna, basu da sukuni sai sun je. Dangane da gudummowar da zasu bata, ko rabi ba
zasu ba wani ɗan uwa ba.
Idan aka kalli matsayin ƙawa ta fuskar kusanci, sai
a ce akwai iri huɗu, kamar: -
5. 4. Ƙawa aminiya ko badaɗiya,itace wadda basa ɓoyewa junansu komai, sirinsu mai daɗi da mara daɗi. Duk abin daya faru ga ɗaya, to ɗaya ta sani, samu da rashinta ta sani. A wani lokaci, akan biyo ta
wajen ɗayar don
kamun ƙafa dangane da ƙawar. Wannan kan sa
Bahaushe kan ce ai wance da wance ba mai jin tsakaninsu. ko a ce ba mai sanin
tsakaninsu sai Allah.
5. 5. Ƙawa ko oho, itace wadda idan an haɗu, za a yi harka. Kusanci bai kai can ba, sai in wata buƙata ta taso. An fi samun wannan a tsakanin masu hali,kowa na jin
kansa. Kamar yadda Bahaushe ke cewa banza zuwan kare ga aboki.
5. 6. Ƙawa cusa kai, itace wadda ba a damu da ita ba, amma tana nan liƙe, duk wulaƙancin da za a yi ma ta, ba
zata yi fushi ba. An fi samun wannan tsakanin mai hali da mara hali, amma kuma
in da kwaɗayi.
Bahaushe yace, in da kwaɗayi da wulakanci, kuma an ce: “ƙuda wajen
kwaɗayi akan
mutu. ”
5. 7. Ƙawa bi-ta-zai-zai: itace wadda bata yi wa ƙawarta musu ko gardama a
kan kowace shawara ta kawo ma ta. Komai munin shawarar zata bi, a wani lokaci
ma, ko da wasu ‘yan uwa ko makusanta sun nuna ma ta aibu, ita ba zata gani ba.
Duk inda ta sa ƙafa tana biye da ita. A wani lokaci kamar wadda aka yi wa asiri.
Banda wannan, ba ta sona faɗi laifin ƙawar, kuma ba ta ganin
aibunta ko kuskurenta, komai ta yi daidai ne. Babu abin da ke kawo haka sai kwaɗayi.
6. 0. 0. Ƙawance Makaho Ne.
Al’amarin ƙawance, ana iya cewa makaho
ne. Daman Bahaushe yace, “so hana ganin laifi. ” Don kuwa baya rarrabe kamannu,
ko matsayi na shekaru ko na yanayin rayuwa ko ɗabi’u. Babban dalilin da
yasa haka kuwa, shi ne, ƙawance kan samo asali ne
daga ƙauna da soyayya wadda take tsirowa daga zuciya. A mafi yawan
lokuta, ƙawance kan ƙullu ba tare da wani
tantance matsayin kamannu ba. Domin akan samu kyakkyawa na yin ƙawance da mummuna. A inda kuma za a iske kyawawa biyu basa shiri,
ko munana biyu, su ma basa shiri. Haka kuma idan aka dubi ɓangaren shekaru, nan ma
idon ƙawaye kan rufe su ƙulla ƙawance a tsakaninsu ba tare da nuna wata damuwa ba, dangane da
shekarunsu. Akwai inda akan samu wata ƙawar ta
girmi ɗaya, a
wani lokaci ma, sai ta kusan haifarta, amma bai hana ƙulla ƙawance ba.
Baya ga wannan kuma, ƙawance bai cika damuwa da
matsayin yanayin rayuwa ba. Matuƙar aka ce ƙauna c eta haɗa ƙawance, wadata ko talauci bai cika hanawa ba. Domin akan samu
wasu ƙawaye ɗaya mai wadata ce, ko kuma iyaye ko miji masu wadata ne, amma kuma
a iska matansu, ko ‘ya’yansu na yin ƙawance da ‘ya’ya ko matan
talakawa. A wani lokaci ma, irin wannan ƙawancen
ya fidanƙo, saboda za a iske mawadatan na taimakawa masu rauni.
Banda wannan kuma, ƙawance kan runtse ido wajen
zaɓen
abokiyar harka. Wata ƙawar bata tantance ɗabi’ar ƙawarta, sai kawai a ƙulla ƙawance. A wani lokaci ma, ko da ta gane wancan ƙawar nada wata muguwar ɗabi’a, sai ta rufe ido ta kauda kai a ci-gaba da ƙawance. Duk da yake cewar Bahaushe yace: “abokin ɓarawo, ɓarawo ne. ” ko kuma “zama
da maɗaukin
kanwa na kawo farin kai. ”
Bugu da ƙari, ana iya cewa, ƙawance makaho ne bisa dalilin cewa mace tana da saurin sabo. Kamar
wata Karin Magana mai cewa: “Ai mace tunkiya ce mai saurin sabo”. Wannan na
bayyane ne a wurare da dama, misali inda za a iske mace taga wata da haɗuwa sai ta fara bayyana
mata sirrinta. A wani lokaci sai kace sun shekara da sanin juna. Babu wani
bincike, sai su amincewa juna, ka iske ana hulɗa tamkar ‘yan uwa na jini.
6. 1. Daidaitaccen Ƙawance: Dukkan ƙawance da aka haɗa shi tsakani da Allah,
wanda babu wata niyya ko wani buri, wannan shi ne daidaitaccen ƙawance. Matuƙar aka ƙulla alaƙa ba don cimma wata buƙata ba, akwai tsare amanar juna. A daidaitaccen ƙawance shi ne ake faɗawa juna gaskiya ba yaudara, kuma babu tsoron juna. A irin
wannan ƙawance ne ake samun taimakekeniya a tsakanin juna. Idan abin farin
ciki ya samu za a taya juna murna, haka kuma in abin baƙin ciki ya samu, za a nuna tausayi tare da juyayi,kamar aure, ko
haihuwa, ko wani ci-gaba ta fuskar rayuwa. Ko mutuwa, ko rashin lafiya, ko wata
asara kamar gobara, ko haɗari, ko a yi wa mutum sata da sauransu. Bahaushe na ɗaukar wannan ƙawarda muhimmanci, sannan kuma ya raba ƙawance kamar haka, akwai aminiya da sahiba.
6. 2. Fanɗararren Ƙawance: Babu shakka, akwai wani ƙawance da za aiya kiransa
da fanɗararre.
Wannan ƙawance kuwa, shi ne ƙawance tsakanin jinsi
mabambanta. Watau ƙawance tsakanin mace da
namiji, wanda yake kuma bana neman aure ba ne. Akan samu irin wannan a tsakanin
‘yan makaranta (School Mate) , ko masu aiki wuri ɗaya (Co-workers) ko
(colleague) , a wani lokaci kuma akan ce musu (Family Friends). Dukkan waɗannan tsari ko jeri ba
al’adar Bahaushe ba ce, wasu baƙin al’adu ne na Turawa da
muka ara muka yafa. Bisa wannan ne Aƙilu Aliyu yake cewa a waƙar Alhaji Dolo ka saki layi, yace:
Kai girma bai amfana ba
Babba da kai da ƙawancen mata.
Alhaji Dolo ka saki layi
Tunda ka kira wance ƙawata.
Tuntuni daman mun san juna.
Tun yayin da suke ‘yan mata.
Bisa rayuwa ta haƙiƙa, in har za a faɗawa juna gaskiya, wannan tsarin bai yi daidai ba. Domin Bahaushe
yace: “tafiyar kura da bunsuru bata tsawo, don in tai tsawo bunsuru nama ne”.
Haka kuma an ce, “idan dare yayi dare, buzuzu ma nama ne”. To don
haka, haɗari
ne ƙawancen namiji da mace. Wani abin haushi ma, tare da rashin kishi,
sai ka iske matar aure, wai suna da family friend, ko school mate. A inda zai
zo har gidan mijinta su yi duk abinda zasu yi ba damuwa. A wani lokaci ma,
mijin na gidan, amma ba komai, do rashin kishi.
Bayan wannan kuma, a yanzu zamani ya kawo na’urorin komfuta, da
wayoyi, da yanar gizo. Duka waɗannan wasu hanyoyi ne miyagu da ake ƙulla fanɗararren ƙawance. A inda za a iske
mace matar aure suna yin hira ko muhawara a shafin “facebook,” ko catin, ko
whatsapp. Idan aka nazarci waɗannan hanyoyi, sai a iske ba ƙaramar ɓarna suke haifarwa ba.
Bugu da ƙari, bayan wancan kashi na
farko, sai wani fanɗararren ƙawancen. Wannan kuwa, shi
tsakanin jinsi ɗaya ne, mace da mace. Dalilin da yasa ya zama fanɗararre kuwa, shi ne, ana
yin ƙawancen ne don baɗala. A inda za a iske mace na ƙawance da
mace don ta gusar mata da sha’awa. Akan samu wasu matan da kan ƙulla ƙawance don su rinƙa yin maɗigo a tsakaninsu. Babban abin da ya kawo wannan, shi ne zamani ko
baƙin al’adu (ci-gaba ko wayewa).
6. 3. Ƙawance Na Wucin Gadi: Akwai inda akan ƙulla ƙawance na ɗan gajeren lokaci, kamar ƙawance na
tafiya ko na biki. Wasu idan tafiya ta haɗasu musamman doguwar tafiya, sukan zama ƙawaye. Koda yake in aka rabu da juna kuma shike nan, babu
mai ƙara ganin wani. Haka kuma biki, idan biki ya haɗa wasu matan su kan
yi ƙawance, amma in aka rabu shi ke nan. Bayan wannan kuma, ko a ƙawance da ‘yan matan amarya kan haɗu a lokacin biki, mafi yawa in aka watse, ba a ƙara haɗuwa. Wata babbar ƙawar kan riƙa ziyartar amaryar, amma wasu ba ruwansu. Haka kuma abin yake a
wajen ƙanwar rana ko ‘yar zaman ɗaki, sau da yawa ƙaramar yarinya akan sanya,
ita ma ba duka amare ne kan riƙe wannan alaƙar ba. Ko da yake akan samu masu riƙe amana
har girma yarinyar a rinƙa zumunci.
7. 0. 0. Fa’idojin Ƙawance.
Wannan sanannen abu ne a rayuwa, kusan duk wani abu da mutum zai
yi a samu wata fa’ida, ko illa. Ƙawance shi ma yana da irin
nasa fa’idojin da masu yi kan samu. Tabbas ne a samu ɗaya na fa’idantuwa ko da ba
duka ba. Domin ƙawance kan haifar da taimakekeniya, koda kuwa da shawara ta fatar
baki ce. Balle kuma akan samu taimakon juna ta fuskar kuɗi, ko kayan abinci, ko
tufafi. Yana daga cikin fa’idarsa ƙulla zumunci, saboda a
dalilin wata ƙawar, sai dangin wannan su ƙulle dana
waccan. A wani lokaci ƙawaye kan ƙulla aure a tsakanin ‘ya’yansu. Haka kuma, a dalilin ƙawance a kan samu riƙo.
8. 0. 0. Illolin Ƙawance.
Kamar yadda muka ji fa’idojin ƙawance,
to haka kuma za mu dubi illolinsa. Babu shakka, akwai wasu illoli da ƙawance kan haifar, ga ƙawayen duka biyu, ko kuma
ga guda ɗaya. A wani lokaci akan samu ƙawaye ɗaya na cutar da ɗaya, ko kuma suna cutar da
juna. Akwai ƙawarda kan cuci ƙawarta, ko ta gane, ko bata
gane ba, amma kuma su kasa rabuwa. Haka kuma wata ƙawar zata iya zubar da mutuncin ɗaya, ko ɓata mata suna, amma suna
nan tare. Akwai ƙawarda zata halakar
da ƙawarta ta hanyar koya mata miyagun halaye, kamar zuwa wurin bokaye
(Malaman tsibbu) ko bori, ko ƙungiyar asiri ko bin maza.
Yawan ƙawaye kan jawowa mace zargi, ko kuma wasu matsaloli da zai iya
sanya rayuwarta ta lalace.
Bugu da ƙari, wasu matan auransu kan
mutu a dalilin ƙawance da ske da wasu. Haka kuma zumuncin su da ‘yan uwansu kan
lalace a dalilin ƙawayen da sukan ‘ya’ya da
iyaye. A inda sukan haddasa saɓani a tsakaninsu.
9. 0. 0. Shawarwari.
Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa ya zama dole ga
dukkan mai hankali ta kula tare da lura da duk wacce zata yi ƙawance da ita. Tunda farko, dole ne ki kula da ɗabi’unta, shin ko tana da
son addini ko a a. Haka kuma in za ki yi ƙawance
ki ƙulla shi don Allah, ba don wani abin duniya ba. Kar ki yi shi don
tana da kuɗi ko
asali, ko nasaba, kamar a ce matar mai muƙami iri kaza. Dukkan
soyayyar da aka gina ta don Allah, haƙiƙa Allah Zai sanya albarka a cikinta. Bayan haka kuma, shaiɗan ba zai sanya albarka a
cikinta. Bayan haka kuma, shaiɗan ba zai samu dammar halakar da kuba. Ita kuwa soyayyar (ƙawance) da aka gina don son zuciya ko son abin duniya bata
yin ƙarshe mai kyau. Haka kuma babu wuyar shaiɗan ya dulmiyar da masoyan.
Dangane da wasu dabaru, waɗanda zaki yi amfani dasu wajen tantance wadda zaki yi ƙwance da ita. Akwai wasu abubuwa da zaki fara auna duk wata mace
da kuka haɗu zaku
fara ƙawance, kamar haka: -
1. Son addini, da tarbiyya, da tsoron Allah. 2. Kwaɗayinta na son abin duniya.
3. Hankalinta. 4. Haƙurinta. 5. Kunyarta.
Matuƙar mace ta neme kida yin ƙawance,
to ki aunata a kan waɗannan al’amura guda biyar. Kar ki ruɗu da karatunta, ko wayewarta, ko shekarunta, ko kuɗinta, ko muƙaminta da nasabarta. Haka kuma komai daɗewarku kuna tare da ita, da
zarar ta kasa cika waɗannan ƙa’idoji, ki rabu da ita.
Dalilin da yasa ya zama dole ki yi taka-tsantsan wajen zaɓar ƙawa, shi ne, duk wanda ya ganku tare zai ɗauke ku halinku ɗaya. Domin Bahaushe ya ce
sai hali ya zo daidai akan yi abota, ko abokin ɓarawo, ɓarawo ne.
9. 1. Jirwayen Ƙawance A Adabin Bahaushe.
Karin Magana: 1. Ƙawa zuwa ƙawa,2. Gayya soɗi, zuwan bikin ƙawar ƙawa,
3. ƙawalliya romon jaɓa, 4. kasangama giwar mata
kin fi ƙawa, sai yaya.
Antin mata ba ki sami aminiya, sai ‘ya, sai ƙanwa. 5. Abin ƙawa na ƙawa ne.
10. 0. Kammalawa.
A ƙarshe wannan muƙala ta ɗan taɓo, ma’ana da kuma yanayin ƙawance, da hanyoyi ko
dalilan ƙullashi da ire-iren ƙawaye da halayensu da
fa’idoji da kuma illolinsa. Bayan
wannan kuma an ɗan tsakuro wasu daga cikin ɗabi’un ƙawaye (mata) , tare da nuna
irin nauyinsu da irin muninsu da matsayinsu a mizanin al’adar Bahaushe.
Bahaushe na kyamar ɗabi’un takowace fuska. Idan aka dubesu ta mahanga al’ada,da
addinin musulunci,da kuma a hankalce sun saɓawakyakkyawan tafarki. Mun riga munji irin illolin da waɗannan ɗabi’u suka yi,ko zasu yi
mana, ta fuskoki marasa iyaka, kuma ta kusurwoyi daban daban. Domin haka,ina
fatan wannan muƙala, ta zama kamarmatashiya ce ga masu hankali daga cikiniyayen mu
mata. Allah Ya tsare mu Ya bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum.
MANAZARTA
Ladan Y. (1980) Zaman Duniya iyawa ne. Northern Nigeria
Publication
Company Zaria.
Maryam S. L. (1993) Kishi kumallon mata Bushara Publication House,
Gusau.
Madauci I. (1963) Al'adun Hausawa Northern Nigeria Publication
Company, Zaria.
Zainab M. K. (2008) Hira da ita a gidanta No. 1 Ƙofar Fada Kudan.
Amina M. S (2009) Kallabi. Jaridar Leadership Hausa.
21/5/2009.
Umma U. S. (2008) Don Iyali. Jaridar Nasara,20/10/2008.
Bello M. (2009) Kiwon lafiya. Jaridar gaskiya tafi Kwabo.
26/3/2009.
Safiya J. (2006) Himma dai mata. Jaridar gaskiya ta fi Kwabo.
20/4/2006.
Choge B. (1990) Waƙar Sakarai ba ta da wayau.
Ballagaza Bankaura.
[1] Dubi Littfin Arba’una Hadis Fassarar Abubakar Gummi 1988
NNPC Zaria
[2] Amina B.Iyayen giji Jaridar Aminiya 20/10/2008 shafi na 23.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.