Ticker

6/recent/ticker-posts

Jibadau Kayan Nauyi (Wanda Ya Ce Babu Yi Masa Aka Yi): Tsokaci A Kan Rayuwar Aure Da Kuma Matsayinta

WANDA AKA GABATAR A TARON WALIMAR AUREN MUHAMMAD TANIMU HARUNA DA ZAINAB MUHAMMAD TAHIR A BADARAWA GARIN KADUNA A RANAR ASABAR 15 GA MARIS 2014, DA ƘARFE 04: 00 NA YAMMA.

JIBADAU KAYAN NAUYI (WANDA YA CE BABU YI MASA AKA YI): TSOKACI A KAN RAYUWAR AURE DA KUMA MATSAYINTA

DAGA

MU’AZU SA’ADU KUDAN. DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES

JIGAWA STATE UNIVERSITY KAFIN HAUSA. (07030803404)

SHIMFIƊA:

JIBADAU: Wata ƙatuwar babbar riga ce, daga cikin nau’o’in girke ta saƙi, ko ta tsamiya, ko fari. [1]

KAYA: Dila, ko agigi, ko laftu wanda za a iya ɗauka a kai ko a kan dabba. [2]

NAUYI: Duk abin da za a ɗaga, ko a ɗauka, ko jijjina a gaji, ko ya gajiyar. [3]

GABATARWA.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga wanda Ya so, a sadda Ya so, a yadda Ya so, ko ana so, ko ba a so, dole bayi su so. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa da Sahabbansa.

Wannan muƙala z ata ɗan taɓo, wani abu da ya shafi rayuwar aure da matsayinta. Wannan rayuwa ta aure saboda muhimmancin da take da shi, ga dukkan wani abu mai rai. Tun daga mutum har dabbobi, da tsuntsaye, ƙwari, da tsirrai. Bisa wannan dalili ya sanya Bahaushe ya bai wa aure babban matsayi. A inda yake ganin duk namijin da ya riƙa (balaga) , ma’ana ya isa aure amma bai yi ba, a matsayin mai rauni kuma ba cikakken mutum ba. Bahaushe ya karkasa mutane marasa aure zuwa gida uku ko huɗu. Kamar haka, saurayi, ko tuzuru, ko gwadangwarƙi, ko gwauro, idan kuma mace ce sai a ce mata budurwa, ko karfa, ko bazawara, ko gwauruwa. Kowane daga cikinsu akwai irin matsayinsa a al’adar Bahaushe, tare da dalilai da suka sa aka bashi sunan. Haka kuma, saboda sanin irin ɗawainiyar dake tare da aure, musaamman ga sabon shiga,sai Bahaushe ya yi masa kirari da dama. Wannan yasa na kira muƙalar da suna “Jibadau kayan Nauyi’’ (Wanda yace babu yi masa aka yi). Ma’ana gashi aure yana cikin matakan rayuwa da ya zama kusan dole, to amma kuma ana tunanin abubuwan da suke tare da shi. Wannan muƙala zata tsakuro wasu dalilan da suka Bahaushe ya faɗi wannan kirari mu kallesu, don mu ga irin tasirin da suka yi. Bugu da ƙari, an kawo falalar da yin aure ke da shi, tare da kwaɗaitarwar da shari’ar addinin musulunci ta yi. Bayan haka kuma, an jero wasu haƙƙoƙi da suke kan ma’auratan.

MA’ANAR AURE:

Aure wani zama ne halastacce tsakanin mace da namiji a matsayin mata da miji wanda al’ada da Addini suka yarda da shi. Babban dalilin da yasa ake yin aure shi ne domin yaɗa iri tare da fatan al’umma ta wanzu. Aure baya inganta sai da rukunai kamar haka: sadaki, waliyi, shaidu.

Bisa wannan dalili, duk wanda ya ƙetare iyaka ya kutsa wata mace ba tare cika waɗancan rukunai ba. Haƙiƙa ya saɓawa shari’a da kuma al’ada, saboda ladabtarwa shari’a tace ba aure. Al’ada ta bashi sunaye, sannan kuma ta kira aikin da ya yi da sunaye kamar haka:

Za’a kira shi Kwarto, ya yi kwartanci, ko shige, ko fyaɗe. Ita matar kuma a kira ta farka, ko dadaro. Matar da kuma ta sallamar da kanta ga kowa, ana kiranta karuwa. Shi kuwa ɗan ko ‘ya da aka haifa ba ta hanyar aure ba, akan kira su da shege, ko shegiya, ɗan rariya, ko ɗan gaba da fatiya, ko ɗan dakan-kuka da sauransu.

FALALAR YIN AURE

 Tabbas akwai falala a kan aure mara iyaka wadda ba za tya bayyanu ba sai dai a ɗan tsakuro kamar yadda shari’a ta yi umarni da a yi aure tare da nuna muhimmancinsa, to haka ita ma al’ada ta bayyana falalar aure ga al’umma. Falalar aure da ɗan Adam ke samu sun haɗa da: -

1. Cikar mutunci. 2. Natsuwa. 3. Kamun kai. 4. Runtse idanu. 5. Yaɗa zuriyya (haihuwa)

 UMARNIN YIN AURE: Bayan wannan falala kuma, sai maganar umarni da shari’a ta yi a kan yin aure a Al-ƙur’ani aka ce:

وإن خفتم ألا تفسطوا فى اليتامى فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثلاث ورباع، فإنخفتم ألا تعدلوا فواحدة أو ما ملكت أيمانكم، ذالك أدنى ألاتعولو.

 “Ku auri abin da ranku yake so daga bibbiyu, uku-uku, ko hur-huɗu, in kunji ba za ku yi adalci ba, to ku tsaya a guda ɗaya”. Abin nufi shi ne ku auri mata 2 ko 3 ko 4 in ba za ku iya adalci ba mata ɗaya (1).

Wani hadisi yace ku yi aure ku hayayyafa ranar ƙiyama in yi alfahari da ku. Ko wani hadisin da yace: “Ku yi aure samari shi yafi runtse idanu.

GIRMAMA MACE SABODA MATSAYINTA

 Duk inda ka ga mace ka girmama ta saboda wasu dalilai kamar haka: matsayin da Allah Ya bata na Uwa ga dukkan mahaluki kuma makarantar farko ga dukan mahaluki.

1. Matar wani. 2. Uwar wani. 3. Kakar wani.

Da farko dai ya zama wajibi a girmama mace bisa wasu dalilai, na farko shi ne duk in da ka ga mace kamila to dole ne ta kasance cikin ɗayan uku ko dai matar wani ko uwar wani ko kakar wani, ko da yake wannan na ƙarshe ya danganci shekarunta.

عن أنس رضى الله عنه قال: قال النبى صلى الله عليه وسلم قال: إذا تزوخ العبد فقد استكمل نصف الدين, فليتق الله فى النصف الباقى.

 An karɓo daga Anas (R. A) yace Annabi (S. A. W) ya ce idan mutum ya yi aure to ya sami rabin Addininsa sauran rabin sai ya ji tsoron Allah ya cika sauran. (Jami’ul hadis: Imamus-suyuɗi).

GIRMAMA MACE A MATSAYIN MATAR AURE

Akwai dalilai masu yawa da suka sa mutum dole zai girmama mace ko ba don komai ba, ko saboda wani matsayi da take da shi al’umma na farko a matsayin matar aure, wani babban mataki ne na rayuwa ga dukkan namiji. Babu wani wanda rayuwar sa za ta kammala in ba shi da aure. To ashe kuwa in har haka ne to mace ta zama abokiyar rayuwa, kuma abokiyar rufin asiri ga mai ita. Wata hujja itace Allah (S. W. T) yace a cikin Al-ƙur’ani cikin Suratul Baƙara aya ta 237 ya ce miji da mata tufa ne ga juna, sannan yace a Suratul Baƙara aya ta 228, 29-30 cewa mata da miji a yi karamci ga juna.

Bayan wannan kuma, irin gudunmuwar da mace take bayarwa a fagen aure wanda ba za su lissafu ba, kaɗan daga ciki sun haɗa da:

1. Kula da miji shi kansa.

2. Kula da gida da iyali.

3. Karewa da ƙarawa mutum mutunci a cikin al’umma.

4. Tsare kai daga faɗawa cikin wasu munanan ayyuka.

5. Runtse idanunsa daga wasu matan daban.

6. Taimakawa wajen samun zuriyya (yaɗa iri).

7. Matar ƙwarai na sanya miji ya yi alfahari.

8. Ƙulla zumunci da sauransu.

Wani sirri kuma abin mamaki game da dangantakar aure, ga ma’auratan nan biyu. Watau mata da miji, shi ne kula da juna musamman aka ce auren farko tsakanin saurayi da budurwa. Matuƙar an yi shi bisa so da ƙauna kuma an amincewa juna. To za ka iske babu mai son ya rabu da juna, domin samun kulawa. Akwai wata magana da masana ɗabi’ar Ɗan Adam suka yi na cewa duk wanda ya rasa matar farko ko mace ta rasa mijin farko to da wuya ya/ta sake samun dai-dai sai kawai haƙuri. kai ko da wajen ba shi shawara mai kyau.

A mafi yawan lokutta akan samu a inda mata ke kula da miji kuma har ta rinƙa lallashi da tattalinsa da kayansa kamar ɗanta ko na ƙaramin yaro ko da baya nan kuwa.

Ban da wannan kuma, mata kan kula da gida tare da iyali kai a wani lokaci har da dangi. Tun daga yi mu su abinci raino, tsabtar jiki da ta tufafi (wanka da wanki) tarbiyya.

Mace ga mijinta takan zama ƙyaure da kuma ado ko garkuwa ta mtunci a cikin al’umma. Game da wannan babu jayayya bisa ga wasu dalilai kamar haka: ko ba shari’a a ɗabi’a ma kawai ya isa hujja a mutane musamman Hausawa matuƙar aka ce ga namiji ya kai wani matsayi na minzalin isa aure aka ce bai yi ba, har suna akan bashi da cewar “tuzuru”, ko “gwadankwarƙi”,/”goriyo”, shi kuwa wanda matar ta fita watau ya taɓa yin aure amma suka rabu to shi akan kira shi da “gwauro”. Haka ita ma macen akan ce “karfa” ko kuma ta rabu mijin a ce “bazawara” ko a tsokaneta da “gwauruwa”.

Wata daraja da Allah (S. W. T) ya baiwa matar aure ga miji ba ƙarama ba ce, saboda falalar da miji kan samu a dalilin yin aure, kamar a inda wani hadisis ya nuna ko da kallon fuskar matarsa kawai ya yi, za a rubuta ma sa lada. Ga hadisin kamar haka:

“An karɓo daga Abu Hurairah (R. A) cewa: Ya ji Manzon Allah (S. A. W) idan namiji ya dubi fuskar matarsa, Allah (S. W. T) zan rubuta masa ladan kyawawan ayyuka guda ɗari a cikin littafinsa na lada, idan ya kama hannunta, kuma ya sadu da ita, Allah Zai rubuta masa lada a kan kowanne silin gashin da ke jikinsa, idan ya yi wankan janaba Allah Zai halicci Mala’ika a kan kowanne ɗigon ruwan da ya ɗiga a ƙasa a lokacin da yake yin wankan. Kowane Mala’ika zai rinƙa yi wa Allah tasbihi, kuma yana roƙa masa uban giji tun daga wannan lokacin da ya yi wankan har zuwa ranar lahira. Kuma ladan dukkan tasbihin da Mala’ikun za su yi za a rubuta masa ne a cikin littafinsa na lada. Idan matar ta yi sa a ta ɗauki ciki a wannan saduwar, dukkan mala’ikun da ke cikin Al’arshi da kifayen dake cikin ruwa za su rinƙa roƙa masa lahira gurin ubangiji. Ita matar kuwa za a rinƙa rubuta mata lada guda dubu a kankare mata zunubai dubu, kuma a bata ladar da mutane suka fita yaƙi (jihadi).

ZAƁARWA 'YA'YA UWA TA GARI: Wajibi ne ga dukkan mahaluki mai hankali da yayi niyyar yin aure, to ya yi ƙoƙarin zaɓarwa 'ya'yansa uwa ta gari, ma'ana mai tarbiyya da son addini. Kar ya bi son zuciya ya auro mace don kyau, watau kyakkyawa, ko 'yar wane, watau mai nasaba (mai kuɗi, sarauta, muƙami). Wannan magana ta yi dai-dai da wani bayani da Manzon Allah (S. A. W) ya yi cewa ku auri mace ma'abuciyar addini. Domin yace in ka aura don kyau to lallai kyau kan ƙare in ta tsufa, ko nasaba don mulki na iya ƙarewa, amma shi addini ba ya ƙarewa.

Bayan haka, zaɓarwa 'ya'ya uwa ta gari kamar hutar da kai ne, domin in ka haifi yara da mace ta ƙwarai. To kamar ita ce makarantar su don zasu koyi komai na ƙwarai daga wurinta. Saboda masu hikima sun ce uwa itace makarantar farko ga yaro. Haka kuma in mutum ya kurkure ya auri Ballagazar mace mara tarbiya. To ya kashe kansa da kansa, kuma yaransa sun shiga uku. Babban dalili shi ne, ita ba ta da tarbiya, ba ilimi balle addini, to a nan ina makarantar farko take? Sai dai su koyi zagi da miyagun halaye.

KOWA NA DA HAƘƘIN DA YA RAYATA A WUYANSA.

Akwai haƙƙi na ƙasa ko ƙarami ko mai rauni ko talaka, akan na sama, shugaba, iyaye da duk wani jagora. Wajibi ne a tsare-tsare da lura da waɗannan haƙƙoƙi ta kowacce fuska. Wani hadisi wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, wanda yayi bayani a kan cewa duk wani jagora akan al'amari to lallai ne ya tsare amana da aka bashi. Domin kuwa za a tambaye shi ranar lahira. Ga yadda hadisin yake kamar haka: -

وعن ابن عمر رضى الله عنهما قال: سمعت رسول الله صلى الله علسه وسلم يقول: كلكم راع, وكلكم مسئول عن رعيته, ألإمام راع, ومسئول عن رعيته, والجل راع فى أهله ومسئول عن رعيته, والمرأة راعية فى بيت زوجها, ومسئولة عن رعيتها, والخلدم راع عن مال سيده ومسئول عن رعيته, فكلكم راع, ومسئول عن رعيته. متفق عليه. رواه البخارى و مسلم.

 An karɓo daga Ibn Umar (R. A) yace: Naji Manzon Allah (S. A. W) yace: "Dukkan ku makiyaya ne, kuma dukkan ku abin tambaya ne a kan abin da aka bashi kiwo. Shugaba abin tambaya ne a kan na ƙarƙashin sa. Kowane mutum mai kiwo ne a kan iyalan sa, kuma abin tambaya ne, ita kuma mace mai kulawa ce a kan dukiyar (gida) mijinta, kuma abin tambaya ce a kan su. Mai yin hidima (bara) , mai kulawa ne ga dukiyar uban gidansa, kuma abin tambaya ne a kan su. Dukkan ku makiyaya ne kuma abin kulawa ne. An yi ittifaki a kan wannan hadisin. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Shari'ar musulunci ta tsoratar da cewa duk wanda ya take haƙƙin wani ɗan'uwansa na kusa ko nesa, musulmi ne ko wanda ba musulmi ba? Kai hatta dabbobi su ma an yi hanin a cutar da su haka kurum.

 Haka kuma shari'ar musulunci ta kwaɗaitar tare kuma da yin albishir ga duk wani mahaluki da ya tsare tare da sauke haƙƙin wani da yake kansa, baya ga tarin lada da falala da ƙauna da zai samu a nan duniya, sannan kuma ga tanajin gidan aljannah. Misali a cikin Al-ƙur'ani a cikin Suratul Zilzilat inda Allah (S. W. T) yace: فمن يعمل مثقال ذرة خيرا يره.

"To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarrah, na alheri, to zai gan shi". ومن يعمل مثقال ذرة شرا يره.

"Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarrah na sharri, zai gan shi".

HAƘƘIN MATA A KAN MIJINTA: Matar aure da na haƙƙoƙi masu yawa da suka zama tilas mijinta da yake aurenta ya tsare su. Tun da farko dai shari'a ta sharɗanta babu aure sai da abubuwa uku, sune waliyyi, sadaki, sai kuma shaidu. Daga cikin waɗannan abubuwa guda uku to ɗaya shine mafi ƙarfi a cikinsu a matsayin haƙƙi na ita matar, shi ne sadaki, domin kuwa wajibi a baiwa mace sadakin ta a hannun ta, ko kuma a saya mata wani abu muhimmi wanda za ta rinƙa amfani da shi.

Bayan waɗannan kuma, sai maganar wasu haƙƙoƙin kuma, bayan an ɗaura are, wajibi ne miji ya tsare su, sune ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, ɗakin kwana, sannan da biya mata buƙata wajen kwanciya. Matuƙar aka rasa ɗaya daga cikinsu, to ana iya raba aure.

Bisa ga maganar magani kuwa, baya cikin sharaɗin aure, cewar mutum ya yi wa matarsa magani ba ta da lafiya, sai dai in ya yi mata maganin to ya kyautata, amma ba dole ba ne. Sai dai kuma malamai sun yi Ijtihadin cewar in miji ya yi wa matarsa magani to ya kyautata, haka ita ma ba dole ne ta yi masa girkin abinci ba, amma in ta yi to ta kyautata.

An karɓo daga Amru Ɗan Ahwas, Aljushami (R. A) , yaji Annabi (S. A. W) a hajjinsa na bankwana bayan ya yi yabo da godiya ga Allah, kuma ya yi wa'azi, kuma ya yi gargaɗi, sannan yace: "Ku saurara! Ku karɓI wasiyyar alheri dangane da al'amarin mata, lallai su (mata) kamar kamammu ne, a wurinku baku mallaki komai ba a kan su in ban da (igiyar aure) , sai dai in sun zo da alfasha bayyananniya. Idan sun aikata (alfasha) , ku ƙaurace musu a wurin kwanciya, ku buge su duka ba mai tsanani ba. Idan suka yi muku biyayya kada ku nemi wata hanyar kama su da laifi. "

"Ku saurara! Lallai kuna da haƙƙi a kan matan ku, kuma matanku suna da haƙƙi a kan ku. Haƙin ku a kan su shi ne kada su zaunar da wanda baku so a kan shimfiɗar ku, kuma kada suyi wanda baku soizinin shiga gidajen ku. Ku saurara! Haƙƙin su a kan ku shi ne ku kyautata musu, tufatarwa da ciyarwa. " Imam Tirmiziy ya ruwaito.

 An karɓo daga Mu'awuya Ɗan Haida (R. A) yace: Ya Manzon Allah! Mene ne haƙƙin matar ɗayan mu a kan sa? Sai yace: "Idan ka ci, kaciyar da ita, ka tufatar da ita idan ka tufatu, kuma kada ka doke ta a fuska, kuma kada ka musguna mata, kuma kada ka ƙaurace mata sai a cikin ɗaki. "

 An ruwaito daga Abdullahi Ɗan zama'a (R. A) cewa: Annabi (S. A. W) yayi wa'azi dangane da al'amarin mata, yace yanzu ɗayanku zai tasarwa matarsa ya yi mata duka irin dukan bawa, sannan kuma idan dare ya yi ya kwanta da ita? Bukhari da Muslim suka ruwaito.

HAƘƘIN MIJI A KAN MATARSA: Akwai haƙƙi mai nauyi kuma mai girma da miji ke da shi a kan matarsa wanda ya shafi na girmamawa na, bin umarni ko hani. Haƙiƙa biyayya ga miji ba ƙaramin al'amari ba ne, saboda ko da sha'awa ta taso wa miji in ya buƙaci matarsa to dole ne ta masa kira, domin kuwa matuƙar taƙi to lallai za ta shiga fushin Allah, saboda in har mijinta na fushi to sai ta bashi haƙuri sannan za ta kuɓuta.

وعن أبى هريرة رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشة فلم تأته فبتا غضبان عليها العنتها الملائكة حتى تصبع. متفق عليه.

An karɓo daga Abu-Hurairah (R. A) , yace Manzon Allah (S. A. W) yace: Idan miji ya kira matar sa zuwa shimfiɗarsa, watau ya nufi ya kwanta da ita amma ta ƙI, ma'ana ta ƙi yarda da shi, har shi mijin ya yi fushi da ita, Mala'iku zasu yi ta tsine ma ta har zuwa asuba. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

 فى رواية قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: والذين نفسى بيده ما من رجل يدعوامرأته إلى فراشة فتأبى غليه إلاكان الذى فى السماء ساخطا عليها حتى يرضى عنها.

A wata ruwayar, an ce Manzon Allah (S. A. W) yace: Na rantse da wanda raina ke hannun sa, babu wani miji wanda zai kira matar sa zuwa shimfiɗarsa don su kwanta amma ta ƙi, har sai waɗanda suke sama (Mala'iku) sun yi fushi da ita har sai ya yafe ma ta.

 Akwai wani hadisi ya ƙara nuna ƙarfin yin biyayya ga miji, kamar inda Manzon Allah (S. A. W) ya ce da zan yi umarnin wani ya yi wani sujada da na umarci mata ta yi wa mijinta sujada.

 Bayan wannan kuma akwai wani hadisi kuma da yake nuna matsayin haƙƙin miji kamar inda aka yi bayanin cewa Aljannar mace tana ƙarƙashin duga-dugin mijin ta in ta bi shi, ta shiga Aljannah.

 Bugu da ƙari, akwai inda aka nuna cewa ko da ibada ce mace za ta yi, sai ta nemi izinin mijin ta, kamar misalin azumin nafila, hadisi ya nuna cewa ta sanar da miji, ko ta nemi izini sannan ta ɗauka.

 Duk dai a kan nuna girman biyayya ga miji, inda aka nuna ko da mace tana tuya gurasa ko waina, in har miji ya nuna yana buƙatar ta, wato sha'awa, manufa yana so ya kwanta da ita, to dole ta amsa kira, ta je su kwanta, ya biya buƙatarsa ko da kuwa gurasar ko wainar za su ƙone.

 Akwai bayani da ya zo da ya nuna a lokacin Manzon Allah (S. A. W) yana raye a zamanin wata matar wani sahabi ya yi tafiya sai aka aiko cewa mahaifin ta bashi da lafiya, don haka sai ta aika tana neman izini daga wurin Annabi (S. A. W) don ta tafi ta dubo shi, Annabi yace shin mijin ta ya bata izini? Sai tace a'a, sai yace to ta haƙura. Bayan haka sai kuma aka aiko cewa mahaifinta ya rasu, duk da haka ba ta fita ba, ta haƙura har sai da mijin ta ya dawo. A kan wannan ne Annabi (S. A. W) ya aiko cewa an sanar da shi cewa an gafarta wa mahaifinta, saboda biyayyar da ta yi, duk da mijin ta baya nan, kuma ta haƙura har ya dawo.

BIYAYYA GA MIJIN TA. Biyayyar mace ga mijinta wajibi ne, saboda wani hadisin da Annabi (S. A. W) yai umarni cewa: Da mutum zai iya yiwa wani mutum sujada da an umarci mata ta yi wa mijinta sujada. To amma da yake ba zai yiwu ba, ba a yi wa kowa sujada sai Allah (S. W. T) , amma shari'a ta yi umarni mace ta yi wa mijin ta biyayya matuƙar dai bai umarce ta da ta yi saɓon Allah ba.

DA WANI ZAI IYA YI WA WANI SUJADA, DA MATA TA YI WA MIJINTA.

 وعن أبى هريرة رضى الله عنه، عن النبى صلى الله عليه وسلم قال: "لوكنت أمرا أحدا أنيسجد لأحد، لأمرة المرأة أن تسجد لزوجها. رواه الترمذى حديث حسن صحيح.

 An karɓo daga Abu hurairah (R. A) , daga Manzon Allah (S. A. W) yace: Da mutum zai iya yiwa wani mutum sujada da an umarci mata ta yi wa mijinta sujada. Tirmiziy ne ya ruwaito shi.

MACE BA ZA TAYI AZUMIN NAFILA BA SAI DA IZININ MIJIN TA.

وعن أبى هريرة رضى الله عنه أيضا، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: لايحل لأمرأة أن تصوم وزوجها شاهدا إلا بإذنه، ولا تأذن فى بيته إلا بإذنه. متفق عليه، وهذا لفظ البخارى.

 An karɓo daga Abu hurairah (R. A) yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: "Bai halatta ba ga mace ta yi azumin nafila ba kuma mijin ta na nan, sai da izinin sa. Kuma ba za ta shigar da wani cikin gidansa ba sai da izinin mijinta. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

HAƊARIN BUTULCEWA MIJI.

 عن ابن عساكر، عن عائشة رضى الله عنهما: قال النبى صلى الله عليه وسلم: إذا قالت المرأة لزوجها ما رأيت منك خيرا قط فقد حبط عمنها.

An karɓo daga Ɗan Askar, daga Aisha (R. A) tace: Annabi (S. A. W) yace: "Duk macen da ta wa mijinta bata taɓa ganin alheri daga wurin sa ba, to haƙiƙa ta ɓata ayyukan ta.

ADADIN MATAN ZA A IYA AURA: A tsari irin na shari'ar musulunci, ba a bar komai haka ba, sai da aka yi masa iyaka tare da ƙa'idoji. A kan wannan ne, aure ma ba a bar shi haka ba, sai da aka shimfiɗa ƙa'idoji da hukunce-hukunce. Allah (S. W. T) a cikin Al-ƙur'ani ya ƙayyade ko iyakance adadin mata da za a iya aura tun daga mata biyu ko uku ko huɗu, amma sai aka yi gargaɗI in mutum ya san ba zai yi adalci a tsakanin matansa ba, to ya auri mace ɗaya.

 وإن خفتم ألا تفسطوا فى اليتامى فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثلاث ورباع، فإنخفتم ألا تعدلوا فواحدة أو ما ملكت أيمانكم، ذالك أدنى ألاتعولو.

MATAN DA SUKA HALASTA A AURA.

Allah (S. W. T) ya baiwa mata wani irin matsayi a ƙarƙashin inuwar shari'ar Musulunci, wanda babu wani tsari da aka taɓa samu a kafin musulunci da kuma nan gaba.

 Wannan irin matsayi ya sanya dole a girmama mata. Allah (S. W. T) cikin hikimar sa ya halasta yin aure, to amma duk da haka, sai ya tsara mata kashi biyu, kashi na farko ya haramta aurensu ga dukkan mutum musulmi, kashi na biyu kuwa waɗanda basu faɗa cikin waɗancan da aka ambata ba da farko, ya halasta su, watau za a iya auren su.

MATAN DA SUKA HARAMTA A AURA: Shari'ar musulunci ta haramta auren wasu mata ga musulmai maza. Wannan haramci ya dogara ne bisa ga wasu dalilai, sannan kuma an kasa kashi huɗu kamar haka: -

1. Akwai mata waɗanda dangantaka ta jini (haihuwa).

2. Akwai mata waɗanda alaƙar auratayya ta hana (surukai).

3. Akwai mata da alaƙar shayarwa ta hana (mariƙiya).

4. Akwai mata da saɓanin addini ya hana (mushirikai).

1. Haramci a dalilin nasabar jini (haihuwa).

a. Kaka (mahaifiyar uwa ko uba. b. Uwa. c. Inna (yar uwa, ƙanwar uwa).

d. Gwaggo ('yar uba, ƙanwar uba). e. 'Yar tsatso. f. Jikanya. g. 'Yar jika.

h. Yaya da 'ya'yanta mata. i. Ƙanwa da 'ya'yanta mata.

2. Haramci a dalilin auratayya.

a. Matan uba (kishiyoyin uwa). b. Uwar mata (Suruka).

c. Ɗiyar mata (agola). d. Matar ɗa (suruka).

e. Ƙanwar ko 'yar mata (idan tana da rai) , ba a haɗa su a lokaci ɗaya.

3. Haramci a dalilin shayarwa (raino).

a. Matar da ta shayar da mutum nonon ta. b. 'Ya'yan ta.

4. Haramci a dalilin saɓanin Addini (waɗanda ba musulmi ba, ba kiristoci ba, ba Yahudawa ba).

a. Maguzawa. b. Riddaddu (waɗanda suka yi ridda). c. Matsafa.

HARAMCIN ƘAURACEWA MIJI A SHIMFIƊA.

 Shari'ar Musulunci ta yi hani ko haramta mace ta ƙuracewa mijinta a shimfiɗa, watau lokacin kwanciya in ya buƙaceta, ma'ana ya kirata saboda haka zata shiga fushin Allah, mala'iku zasu yi ta tsine mata har sai gari ya waye.

وعن أبى هريرة رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشة فلم تأته فبتا غضبان عليها العنتها الملائكة حتى تصبع. متفق عليه.

 An karɓo daga Abu-Hurairah (R. A) , yace Manzon Allah (S. A. W) yace: Idan miji ya kira matar sa zuwa shimfiɗarsa, watau ya nufi ya kwanta da ita amma ta ƙi, ma'ana ta ƙi yarda da shi, har shi mijin ya yi fushi da ita, Mala'iku zasu yi ta tsine ma ta har zuwa asuba. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

JIRWAYEN AURE A ADABIN BAKA:

Tabbas an samu jirwayen jigon a adabin bakan Bahaushe, musamman a rassansa guda biyar. Kamar Karin Magana, da take da kirari, da tatsuniya, da almara, da maganganun azanci da sauransu. Wannan ya ƙara nuna matsayin aure a al’adar Bahaushe.

KARIN MAGANGANU: Game da karin maganganu a kan aure da al’adar Bahaushe ta yi, suna da yawa, kamar haka:

1. Idan da rai saurayi ma ango.

2. Da kamar wuya tsohuwa da nesa.

3. Yakamata auren na gida.

4. Amarya ba kya laifi ko ta kashe ɗanmasu gida.

5. Ango hana gaɗa.

6. Ango baka ji asalatu.

7. Allah ya yi aure da mara wuri (kuɗi).

8. Biki na farar kaza belbela ba gayya ba.

9. Biki wan shagali.

10. Biki-biki da zani kowa ya raina ka ba nashi ba ne.

KIRARIN AURE: Game da kirarin aure da al’adar Bahaushe ta yi, suna da yawa, kamar haka:

1. Aure jibadau kayan nauyi.

2. Auren fari na dakushe haukar balaga duk wanda aka yi wa zai yi hankali.

3. Auren fari dabaibayi ga tuzuru.

4. Aure yaƙin ‘yanmata.

5. Na guga marmari daga nesa.

 6. Aure kafi ƙarfin yaro.

IRE-IREN AURE.

 Aure dai kalma ɗaya ce manufa ɗaya, sai dai kuma yana da rabe-rabe kamar kashi goma sha biyu. Duk da rabe-raben zaka samu ƙudurin su ɗaya ne, ko da za a samu bambanci, sai dai ɗan abin da ba a rasa ba. Don kuwa zaka sami mata da miji suna ƙaunar juna da girmama juna ko da haihuwa ko babu. Muna da aurarraki kamar haka: -

1. Auren Kuɗi. (wanda aka biya sadaki, da sauran ɗawainiya. )

2. Auren Sadaka. ( wanda aka sadaukar da sadakin)

3. Auren Zumunci. (aure na ‘yan uwa, dangin uwa ko na uba. )

4. Auren Dole/Ƙi. (an yi bisa tilas, ko ango, ko amaryar wani bai so. )

5. Auren ɗauki sandar ka/takalmi. (a auri mace tana gidanta daban )

6. Auren Jeka da kwarinka. (a auri mace tana wani gari daban. )

7. Auren Jari. (a auri mace saboda kuɗinta ko na iyayanta. )

8. Auren Ɗaukar buta. (auren tsoho da tsohuwa,don ta zuba mai ruwa).

9. Auren Ɓoyon wata. (auren da akan yi kafin azumi, in ya wuce a fita).

10. Auren kashe wuta. (auren da akan yi don a koma gun tsohon miji).

11. Auren huce takaici. ( auren da akan yi don a share hawaye)

12. Auren kangara. (auren da masu arziki kan yi, a tayar baikon wasu).

TATSUNIYA: Akwai tatsuniyoyi da dama da aka samu jirwayen jigon aure aa cikinsu. misali:

1. Tatsuniyar Barewa ta auri mutum.

2. Tatsuniyar auren gaurakiya da biri.

3. Tatsuniyar shaida kurciya.

4. Tatsuniyar kaza ta mazuru.

5. Tatsuniyar Gizo da ƙoƙi.

KAMMALAWA;

A ƙarshe wannan muƙala ta ɗan taɓo, wani abu da ya shafi rayuwar aure da matsayinsa. Haka nan an nazarci matsayin aure da muhimmancinsa ga dukkan wani abu mai rai. Tun daga mutum har dabbobi, da tsuntsaye, ƙwari, da tsirrai. An kuma fito da dalilai da suka sanya Bahaushe ya bai wa aure babban matsayi. An bayyana yadda Bahaushe ke kallon duk namijin da ya riƙa (balaga) , ma’ana ya isa aure amma bai yi ba, a matsayin mai rauni kuma ba cikakken mutum ba. Bugu da ƙari kuma, an kawo yadda Bahaushe ya karkasa mutane marasa aure zuwa gida uku ko huɗu. Kowane daga cikinsu akwai irin matsayinsa a al’adar Bahaushe, tare da dalilai da suka sa aka bashi sunan. Haka kuma, an kawo falalar dake tare da aure, sannan ga jirwayen adabin bakan Bahaushe da sauransu.

Domin haka,ina fatan wannan muƙala, ta zama kamar matashiya ce ga masu hankali daga cikinmu maza da mata. Allah Ya sa mu dace amin. Assalamu alaikum.

 MANAZARTA

 A SuyuɗI ( ) Jami’ul Hadisi

Bargery G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary Ahmadu Bello University Zaria

Yaro Y. I. (1971) Tatsunniyoyi da Wasanni. Oxford University Press, Ibadan.

S. Aliyu (2001) Addu’a’u min kibabi was’sunnah

 Maktabatu Anwaru Abdullahi, Kurmi Market, Kano.

Abdullahi Fodiyo ( ) Sabiblil Najati. Jafaru Bin Alhaji, Hussaini Alkamawa Sakkwato.

Zaid A. A ( ) Risala Fssarar Hausa. Kurmi Market, Kano.

Gumi A M. (1980) Al-ƙur’ani mai girma,Tarajamar Hausa.

 Hadimil haramaini, Sharifaini Makkah.

Malik I. (1970) Muwaɗɗa Malik. Darul fikri, Beirut Lebanon.

Annawawi I. ( ) Riyadus salihin. Darul fikri, Beirut Lebanon.

Ladan Y. (1980) Zaman Duniya Iyawa ne. Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

East R. (1966) Ikon Allah (Dabbobi). Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Imam Z. ( ) Kitabul Kaba’ir, Darul fikri, Beirut Lebanon.




[1] Bargery G.P. (1934) A Hausa-English Dictionary. And English-Hausa Vocabulary.pg498.

[2] Bargery G.P. (1934) A Hausa-English Dictionary. And English-Hausa Vocabulary.pg1189.

[3] Bargery G.P. (1934) A Hausa-English Dictionary. And English-Hausa Vocabulary.pg813.

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments