Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Ciwon Hanta Da Koda Daga Zogale

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Ciwon Hanta Da Ƙoda

A wannan fagen za a soma bayyana ma’anar waɗannan abubuwa guda biyu kafin a ce wani abu. Hanta Bahaushiyar kalma ce da take cikin jerin kalmomi jinsin mata, jam’i kuwa hantuna ko hantoci a wani karin harshen. Ita hanta wata tsokar nama ce mai laushi mai launin baƙi da surkin ja (launin da ake kira kukkumadi ko kunkumadi) wadda ake samu a cikin tsuntsu ko dabba ko mutum, daidai da anta a wani karin harshen.

Aikin hanta a jiki shi ne tace duk wani abu mai lahani ga jiki da yake ƙunshe cikin abinci, sannan ta tura shi zuwa ga ƙoda, kamar yadda East da Imam (2007 sh. 344) suka nuna.

Ƙoda kuwa kalmar Hausa ce da take cikin jerin kalmomin suna jinsin mata. Jam’in kalmar shi ne ƙodoji. Wani dunƙulallen nama ne mai kamar hanta da yake lulluɓe da kitse a jikin mutum ko dabba wanda yake taimakawa wajen tace fitsari.

Ƙoda ita ce mataci na ƙarshe. Ita take ƙara tace duk wasu sauran abubuwa marasa amfani a cikin jiki. Abubuwan da take tacewa, narkakku ne, tana tura su ne a wata hanya, su faɗa cikin mafitsara. Yayin da mafitsara ta cika sai a fitsare su.

Jinin nan da yake zuwa ta ƙoda yana ƙunshe da abubuwan da jiki yake buƙata, kamar narkakken gishiri. Idan ya yi yawa a jini sai ta daidaita shi. Sauran marasa amfani sai ya shiga mafitsara, a fitsare shi (East da Iman, 2007 sh. 344).

A wajen magance  matsalar cutar hanta da ƙoda, sai a nemo ganyen zogale da ‘ya’yan ɓaure, a daka su har sai sun koma gari. Garin nan za a rinƙa sakawa a nono ko kunu, a sha sau uku a yini. Insha Allahu za a sami lafiya (Sifawa, 2015). A binciken Samuel (2013) ya nuna cewa: “Zogale yana daidaita lafiya da ayyukan hanta da ƙoda.” A binciken Axe (2016) an bayyana cewa, zogalana hana zaman daskarewar jini a ƙoda (Kidney Stone). Kodayake ba a bayyana yadda za a yi amfani da ita ba. A gudummawar Godinez (2015) ya ce shan ruwan zogale yana bayar da cikakkiyar garkuwa ga kamuwa da cutar hanta. Ya ƙara da cewa, yana inganta sinadirin furotin da yake cikin hanta. 

Post a Comment

0 Comments