Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
COTP (Crypto OTC Trading Platform)
Kafar intanet ɗin da suka yi amfani da ita: cotps.com
OTC yana mazaunin “Over the Counter”. Domin sauƙin gane bayanin, ana iya kwatanta abin da yadda
ake sayar da magunguna a duniyar zahiri. A bisa doka, ya kamata ne masu sayen magani su saya a pharmacy, wato babban shagon
sayar da magunguna da yake ƙarƙashin kulawar ƙwararre wanda ya karanci ilimin magunguna
(pharmacist). Duk da haka, akan samu kemis-kemis a cikin unguwanni a wuraren da
ake sayar da magunguna da ake kira over the counter drugs. Masu waɗannan
kemis-kemis, su suke sayowa daga manyan wuraren sayar da magani, sannan su
sayar wa mutane. Tsarin kasuwar hadahadar kuɗaɗen intanet na OTC ya fito ne da
wannan salo. Sun yi iƙirarin cewa, suna
taimakawa ta hanyar kasancewa ‘yan tsakiya a tsakanin ‘yan kasuwa da
manyan kasuwannin hadahadar kuɗaɗen intanet (misali Binance).
Yayin da mutum ya yi rajista da su, to zai sanya USDT[1] a akawun ɗinsa domin fara gudanar da kasuwanci. Yadda tsarin
kasuwancin kuwa yake abu ne mai sauƙi. Ɗan kasuwa zai danna madanni ne kawai. Kasuwar
OTC su ne za su yi masa duk sauran aikin da ya dace ya yi idan a babbar kasuwar
hadahadar kuɗaɗen intanet yake. Misali, su ne za su shiga kasuwa, su nema masa
masu gudanar da kasuwancin P2P, sannan su yi masa kasuwanci tare da su.
A duk ƙarshen zangon kasuwancin
da OTC suka yi masa, zai samu kimanin kashi uku (3%) na kuɗin (USDT) da ya saka
a matsayin riba. Daga nan kuma ba zai iya sake shiga kasuwa ba sai bayan awanni
biyu (2). Ma’ana dai, bayan awanni biyu, zai iya sake saka USDT a akawun ɗinsa
sannan ya sake shiga kasuwa domin gudanar da kasuwanci.
A nan ma za a iya lura da manyan makamai biyu da waɗannan ‘yan
damfara suka yi amfani da su. Na farko shi ne sun yi amfani da kasala da son
jiki da kuma son banza da mutane suke da su. Ya kamata a ce duk wanda aka tunkare shi da wannan, to ya yi
tunanin cewa shi
kamfanin da yake wannan kasuwanci, idan har da gaske yake yi, me ya sa ba za ya yi wa kansa kawai ba domin ya yi ta samun riba marar yankewa?
Abu na biyu kuwa, sun yi amfani da ƙarancin ilimin mutane game da abin da yake iya
yiwuwa da wanda ba ya iya yiwuwa a duniyar intanet. Ko da ma dai, ƙaryar cewa AI yana yi wa mutane kasuwanci zance
ne da ake yawan amfani da shi wajen damfarar mutane.
Bayan da ‘yan damfarar suka tattara kuɗaɗen mutane, sai suka yi ɓatan dabo.
AI Mining (Haƙon Kuɗin Intanet Ta
Amfani Da Ƙirƙirarriyar Basira)
Kamar yadda sunan ya nuna, wannan harƙalla ce ta damfara wadda aka bayyana ta a
matsayin amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen haƙon kuɗaɗen intanet. A iƙirarinsu, duk waɗanda suka yi rajista, za su
tura kuɗin da za a saya musu kayan aiki (misali kwamfuta da kayan
jone-jonenta). Daga nan za a girke wa mai wannan akawun ɗin kwamfutar a can
wurin aikin su waɗannan mutane (masu Ai Mining). Za a saita kwamfutar ta
yadda za ta riƙa haƙon kuɗin intanet. Sunan kwamfutar da mutum zai
saya ita ce miner (wato dai “mai haƙo”). A yadda suka bayyana tsarin nasu, mutum zai
riƙa cire ribar haƙo da aka yi masa duk bayan kwanaki ashirin (20).
Kuɗin da ake biya ya bambanta, sannan ya danganta da nau’in miner
da mutum yake son saya. Ga yadda suke kamar haka:
a. Miner 1 - $20
b. Miner 2 - $40
c. Miner 3 - $80
Su ma waɗannan sun ci wawa sun watse. Sun rufe da kuɗaɗen
mutanen da tsautsayi ya rufta da su.
A cikin harkar baki ɗayanta, za mu iya lura da cewa kwaɗayi ne da
kuma rashin ilimin ƙirƙirarriyar basira suka jefa mutane wannan tarkon
damfara. Babu wani kamfani da haka kawai saboda zuciyar son al’umma zai yi ta
saya musu na’urori yana yi musu haƙo domin su samu kuɗi. Idan har da gaske zai iya
sayen na’urori ya yi haƙo ɗin, to zai yi ta ƙara wa kansa arziki ne, ba wai ya nemi kuɗaɗe a
hannun mutane domin ya ɗora su a hanyar samun wannan banza ba.
Wannan wani haƙo ne na damfara da aka yi a shekarar 2023. An fara shi
yayin da yake da suna Gleam. A cikin ƙanƙanin lokaci aka kammala haƙonsa. Ma’ana dai, an fara haƙo aka dakatar ba tare da an ɗauki wani tsawon lokaci ba.
Daga nan ne kuma aka sauya masa suna daga “Gleam” inda aka mayar da shi “Aqua
Protocol.” An yi haƙon ne a kan bulokcen da ake
kira “Ton Blockchain”.
Bayan sauya masa suna zuwa Agua Protocol ne
kuma suka bayyana cewa sun yi haɗin guiwa da Nomis App (wani kasuwanci
mai suna Manhajar Nomis). Daga nan kuma sai suka buƙaci kowa ya saka Ton 0.1 (wani adadin kuɗin
intanet) a matsayin gas fee. Sun nuna cewa, da wannan gas fee ɗin
ne za a yi amfani domin yi wa mutane rajista ko sama musu gurbi a Nomis App.
Wannan mataki (na yin rajista da daidaituwa a matsayin mamba a kan Nomis
App) sun kira shi da minting.[2] Sun
bayyana cewa, da zarar mutum ya yi minting, za a nuna masa adadin
sulallan da ya haƙa, wato waɗanda zai iya amfani da su yayin da
aka ƙaddamar da kuɗin intanet ɗin (misali, ya zai
iya sayar da su). A maimakon cika wannan alƙawari, sai da aka ɗauki kimanin watanni biyu (2) da yin minting
kafin suka bayar da damar fara motsa abin da mutane suka haƙa. A nan ne suka bayar da damar tura su zuwa lalitocin
kan intanet irin su:
a. Tonkeeper
b. My Ton Wallet
c. Phantom Wallet
A yayin tura wa zuwa lalitar ma, dole mutum
ya biya Ton 0.2 a matsayin Gas Fee. Daga ƙarshe dai, duk wahalar da aka yi ta tashi a banza domin
bai yi daraja ba. Sun yi wasa da hankalin mutane, sannan sun ɓata musu lokaci.
[1] USDT - Kai-tsaye yana mazaunin kuɗin intanet
ne da ake kira Tether. Akan kira shi da "ticker symbol for the Tether
stablecoin cryptocurrency", wato taƙaitawa da take mazaunin
alama ko take wakiltar Tether. Domin ƙarin
bayani game da Tether, a duba: https://tether.to/en/.
[2] Ko da ma dai, minting a hadahadar
kuɗaɗen intanet yana nufin yin rajista da daidaituwar da mutum yake yi game da
wani kuɗin intanet bisa tsare-tsare da ƙa’idojin bulokcen.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.