Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Misalan Kudaden Intanet (Kirifto) Da Suka Rufta Da Hausawa

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

Wasu Misalan Kuɗaɗen Intanet Da Suka Rufta Da Hausawa

Akwai jerin kuɗaɗen intanet da suka rufta da Hausawa. Hasarorin da Hausawa suka yi sun kasance a matakai daban-daban. Haka kuma, salo da sigar kuɗaɗen intanet ɗin sun bambanta. Wannan ɓangare na littafin ya yi ƙoƙarin kawo taƙaitattun bayanai game da wasu daga ciki. Waɗannan bayanai za su taimaka wa masu ƙoƙarin shiga harkar kirifto wajen samun haske da kiyaye faɗawa tarko makamancin waɗannan.

Inksnation

Kafar intanet: www.inksnation.io

Wannan wani shiri ne da aka kawo mai sigar kirifto a shekarar 2019. Masu shirin sun lashi takobin cewa za su kawar da talauci a Nijeriya a cikin watanni tara (9). Sun ƙirƙiri kuɗin intanet wanda ake kira PinKoin. Haka kuma, sun ƙirƙiri katin cire kuɗi tamkar dai yadda bankuna suke da katin ATM. Sunan wannan katin nasu PinKard. A duba hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 5.4: Samfurin katunan InksNation na wasu Hausawa

katunan InksNation na wasu Hausawa

Madogoara: An tattara waɗannan katunan a Sakkwato sannan aka ɗauki hoton su ranar 20/01/2024

Waɗannan hotunan da aka kawo a sama, hotunan katunan wasu Hausawa ne. Su ne katunan da ake kira PinKard.

Masu Inksnation sun zo da alƙawarin cewa, za su riƙa biyan duk ‘yan Nijeriya da suka yi rajista da su. A karon farko, sun yi alƙawarin biyan duk wani ɗan Nijeriya da ya yi rajista kuɗi da ya kai naira dubu ɗari da ashirin (₦120,000) kowane wata. Sun nuna cewa, bayan sun kammala da kawar da talauci a Nijeriya, za su faɗaɗa zuwa Afirka da ma duniya baki ɗaya.

Ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruɗar da mutane da suka yi amfani da su shi ne ƙirƙirarriyar basira (AI) da na’urantarwa (automation) waɗanda mafi yawan mutane suke da ƙarancin ilimi game da su. Sun bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2025, kashi tamanin (80%) na ayyuka za su koma na’urantattu waɗanda ake gudanarwa da taimakon ƙirƙirarriyar basira da injuna. Hakan zai sa mafi yawan mutane, musamman ‘yan Afirka, su rasa ayyukansu.

Yana da kyau a lura da cewa, gaskiya ne ana kan samun sauye-sauye masu yawa da ban mamaki a duniya a ɓangarorin kimiyya da fasaha. Bunƙasar ilimin ƙirƙirarriyar basira da saƙago suna matuƙar tasiri wajen maye gurabun ayyuka masu yawa a duniya. Duk da haka, ‘yan damfara musamman a duniyar intanet suna amfani da ƙarancin ilimin da mutane suke da shi a wannan fannin domin dulmiyar da tunaninsu tare da yunƙurin damfarar su. Dole ne Hausawa su fahimci cewa, duk da cigaba da waɗannan abubuwan zamani suke kawowa, ba su da ikon samar wa mutane kuɗi nan take.

A shafin Inksnation, an rubuta bayani kamar haka:

Instead of making humans compete with AI for jobs, we are proposing and building a new ecosystem where AI itself becomes our national & universal housemaids, servants and messengers while we the human assets live like kings & queens that God had programmed us to be. www.inksnation.io

Fassara:

A maimakon mutane su riƙa fafutukar samun ayyukan da ƙirƙirarriyar basira suke yi, muna bayar da shawara tare da gina tsarin fasahar na’urori a inda ƙirƙirarriyar basira da kanta za ta kasance baiwa a gare mu a matakin ƙasa da kuma matakin duniya, za ta kasance ‘yar aiki a yayin da mu kuma mutane za mu yi rayuwa irin ta sarakuna kamar yadda Allah ya tsara mu kasance.

Idan aka duba wannan bayani da suka kawo a sama, za a lura cewa zuzutawa ce da kirarin kambama. Sun jera kalamai na alwashi da cika baki masu jan hankali. A zahirin gaskiya, ƙirƙirarriyar basira ba za ta iya samar da arziki a duniya baki ɗaya ba. Hasali ma, babu wani tsari da zai iya azurta mutanen duniya kasancewar kowane shiri yana da iyakokinsa, sannan linzamin tattalin arzikin duniya yana hannun gwamnatoci.[1]

Inksnation sun fitar da tsarin yin rajista mataki-mataki. Kowane mataki yana da suna da kuma farashi, wato adadin kuɗin da mutum zai biya domin yin rajista. Albashin wata-wata da za su riƙa bayarwa ya danganta da nau’in rajistar da mutum ya yi. Ga yadda abin yake:

Jadawali Na 5.1: Azuzuwan Yin Rajista Na Inksnation

Package

Price (Naira)

Monthly salary (converted to Naira)

Bronze

1,000

120,000

Silver

10,000

180,000

Gold

100,000

240,000

Diamond

1,000,000

300,000

 

Kafin wannan kasuwa ta watse, an kawo kayayyaki a wasu jihohin Nijeriya. An yi cinikayyar waɗannan kayayyaki (misali manja da taliya da sauransu) ta hanyar amfani da PinKoin. Ko bayan haka, akwai mutanen da suka sayi PinKoin daga hannun waɗanda suke da su. Sun yi hakan ne bisa sakankancewa kan cewar InksNation za su sayi waɗannan PinKoin ɗin daga hannun al’umma bisa farashi mai armashi.

Daga ƙarshe, InksNation da masu shi duk sun yi ɓatar dabo. Hausawa masu yawa da suka shiga harkar sun tafka hasara. Waɗanda suka sayi PinKoin da niyyar sayarwa bisa kuɗi mai daraja, sun yi harasar kuɗaɗensu. Waɗanda suka biya kuɗin rajista ma sun yi hasarar kuɗaɗensu. Haka kuma, dubban mutane sun yi hasarar lokacinsu da datar wayarsu.

Telegram P2P

P2P yana nufin “peer-to-peer”. Wannan tsari ne na kasuwanci na mutum zuwa mutum. Ma’ana dai, tsarin P2P yana bai wa mutane damar yin kasuwanci a tsakaninsu kai-tsaye. Mai sayar da kaya zai saka farashin da ya ga dama sannan ya tallata. Shi kuma mai sayen kaya zai duba wanda yake son ya sayi kaya daga gare shi. Daga nan mai sayan kaya zai sayi kaya kai-tsaye daga hannun mai sayarwa (a maimakon saya daga kasuwar kan intanet).

Telegram P2P wata harƙallar damfara ce ta kuɗin intanet da aka aiwatar da ita a kafar Telegram. ‘Yan damfara sukan buɗe zauren Telegram na P2P. Sukan bi hanyoyin da za su tabbatar da cewa mambobin zauren suna da yawa. Misali kowanne daga cikin ‘yan damfarar yana iya kasancewa a cikin zauren da akawun mabambanta. Daga nan za su riƙa sanyo mutane zuwa cikin zauren. Za su yi bayanan cewa zaure ne na gudanar da kasuwancin kuɗin intanet bisa tsarin P2P, kuma sha yanzu magani yanzu.

A cikin zauren, ‘yan damfarar za su riƙa sanyo rasit-rasit na ƙarya dangane da hadahadar kasuwancin kuɗin intanet. Wani lokaci kuwa, za su riƙa tura wa junansu kuɗaɗen intanet ɗin (a matsayin sayarwa), sannan wanda aka tura wa ɗin ya biya farashin da aka yi yarjejeniya da shi kuma ya turo rasiti zuwa cikin zauren. Sukan yi hakan ne domin yaudara da jan hankalin sababbin mambobin zauren da aka sanya domin a damfare su.

A mafi yawan lokuta, admin ne yake kasancewa a matsayin escrow[2]. Mai sayar da kaya zai tura masa zuwa akawun ɗin admin. Shi ma mai sayen kaya zai tura kuɗi (misali naira) zuwa akawun ɗin admin. Bayan admin ya tabbatar da kaya sun shiga (misali Bitcoin) sannan kuɗi ma sun shiga (misali dubu ɗari biyar (₦500,000)), to sai ya tura wa kowa (ya tura kaya ga mai saye sannan ya tura kuɗi ga mai sayarwa). Kada a manta, duk waɗanda suke cikin zauren ‘yan kore ne idan ban da waɗanda ake shirin damfara.

Duk waɗanda suka faɗa wannan tarkon damfarar za su ga cewa ai sauƙi ya samu. Daga nan za su tura kuɗin intanet ɗin da yake gare su (idan sayarwa za su yi). Idan saye za su yi kuwa, za su tura kuɗin kaya. Da zarar sun yi haka, to lallai kuɗaɗensu sun bi shanun sarki. Ana iya fitar da su daga cikin zauren nan take.



[1] Samuwar yanayi ko lokacin da kowa zai kasance cikin wadata ƙudura ce ta Ubangiji wanda zai iya wanzarwa cikin buwayarsa.

[2] An kawo bayanin escrow a cikin jerin kalmomin fannu na wannan littafin.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307 

Post a Comment

0 Comments