Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Cold Wallet
Cold Wallet ma ya zo ne da sigar
kuɗin intanet. An yi haƙon sa
a kafar Telegram. Ya kasance a ƙarkashin
bulokcen da ake kira da BNB
Blochain. Sun zo da tsari mai wahala wanda sai masu juriya ne kawai za su
iya bi. Duk bayan awanni biyu (2) ne ake shiga domin a taɓa.
Bugu da ƙari, a duk awa biyun mutum ba ya
wuce ya tara sulalla 0.023. Idan mutum bai shiga ba bayan awanni biyu, to haƙonsa zai tsaya. Hakan yana nufin sulallansa za su daina taruwa har sai
lokacin da ya sake hawa ya taɓa.
A lokacin da suka yi kusan rufewa,
sun buƙaci da a saka BNB wanda ya
kai kimanin Dala biyu ($2) a matsayin gas fee. Duk wanda bai saka wannan
gas fee ɗin ba, to za a ƙona
duk sulallan da ya tara.[1] A
wannan lokaci, masana kirifto daban-daban sun yi kiraye-kiraye a kafafen sada
zumuta cewa, idan dai sulallan mutum ba su haura goma (10) ba, to kada ya saka
wannan gas fee ɗin. Dalili kuwa shi ne, ko da mutum ya saka, da wuya darajan sulallansa bayan ƙaddamarwa su kai yadda zai iya fanshe abin da ya kashe.
Da aka kammala saka gas fee, sai
Cold Wallet ya yi ɓatar dabo. Babu shi babu masu shi, babu labarinsu.
Yayin da mutum ya hau kan lalitarsa domin duba abin da ya tara, to zai ci karo
da bayanan da suke nuna masa manhajar ta daina aiki. A duba misali a hoton da
yake ƙasa:
Hoto
Na 5.5: Duba Balas Ɗin Cold
Wallet a Cikin BNB Wallet (Lalitar BNB)
A ƙasan wannan kuwa, yana nuna ƙarin bayani kamar yadda aka
nuna a hoto na 5.5a da yake ƙasa:
Hoto Na 5.5a: Duba Balas Ɗin Cold Wallet a Cikin BNB Wallet (Lalitar BNB) – Ƙarin Bayani
Ko da mutum ya saka gas fee ko
bai saka ba, wannan shi ne abin da zai gani yayin da ya hau lalitar BNB domin
duba balas ɗin sulallansa na Cold Wallet.
5.3.7 Tomato
Tomato (🍅) shi ma haƙo ne da aka yi a kan kafar Telegram. An fara shi sannan an ƙare shi a shekarar 2024. Ya yi tashe sosai a tsakanin
Hausawa. Hausawa da yawa sun mayar da hankali sosai a kansa. An yi haƙo a kan manhaja a waya. A duba misali cikin hoton da yake
ƙasa:
Hoto Na 5.6: Manhajar haƙon Tomato
Kamar yadda ake gani a cikin wannan
hoton da yake sama, ita wannan tsiron tumatur a cikin awanni shida take girma
ta yi ‘ya’ya har su nuna lugub. Daga sun nuna, sai batun roro. A cikin manhajar
ma, da roro suka kira abin cikin harshen Ingilishi (harvesting period). Da
zarar mutum ya hau kan manhajar, to zai danna wurin da aka rubuta Start
Farming (wato “fara noma”). Bayan dannan wannan wuri, a cikin awanni 6
wannan bishiyar za ta zuba ‘ya’ya guda dubu biyu da ɗari
ɗaya da sittin (2,160). A duba misali a hoton da yake ƙasa:
Hoto
Na 5.7: Bishiyar tumatur ta fara jefa ‘ya’ya
A wannan hoto da yake sama, za a iya
lura da cewa tsiron tumatur ɗin ya fara jefa ‘ya’ya. A ƙasa an nuna cewa ana kan noma (farming). Haka za a ci
gaba da wannan noma har sai lokacin girbe amfanin gona ya yi (harvesting time).
A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 5.8: Lokacin girbi (harvesting time)
Yayin da lokacin cire amfanin gona ya
yi (kamar yadda ake gani a hoton da yake sama), mutum zai danna domin kwashe
adadin amfanin da ya samu zuwa cikin lalitarsa.
Shi ma wannan kirifto ya zo da tsarin cin
task da kuma gayyata (referral). Duka hanyoyi ne da mutum zai iya tara
tumatur ko bayan noma (farming) wanda aka yi bayani a sama.
An yi haƙon wannan kirifto na tsawon kimanin watanni 4. Daga nan
suka fitar da sanarwar cewa kowa ya haɗa akawun ɗinsa
da Bitget Wallet.[2] Sun ce duk wanda
yake da kadarar da ta kai darajar dala biyu ($2) a cikin Bitget Wallet ɗinsa,
to zai samu wata kyauta (garaɓasa) yayin da ya mayar da Tomato ɗinsa
zuwa can. Ba su bayyana wace irin kyauta ba ce.
Hausawa da dama sun sayi kuɗin
intanet mai suna Ton sun saka a Bitget Wallet ɗinsu
domin samun wannan garaɓasar. Hakan ya faru ne saboda Ton ya fi sauƙin samu. Da alama Tomato sun yi haka ne domin cim ma wata
manufarsu ta bunƙasa Bitget
Wallet.
An yi tsammanin cewa, da zarar an kammala komawa zuwa Bitget Wallet, to za a ƙaddamar da Tomato domin sayar da shi a kasuwa. A maimakon haka, kawai sai aka sanya wa kowane mai haƙa matsayi (level) daidai da abin da ya tara, sannan aka nuna cewa za a ci gaba da yin haƙa. Haka aka ci gaba da haƙa har na tsawon watanni 2. Daga nan suka saka ranar ƙaddamarwa wadda ta kasance 20/12/2024 da misalin ƙarfe 1:00 na rana a agogon Nijeriya. An baje kolinsa a cikin kasuwannin hadahadar kuɗaɗen intanet (exchangers) guda biyu, wato:
i. Bitget
ii. Gate.io
Daga nan sun juya (converting) ɗin maki (points) da kowa yake da shi zuwa $TOMA. Wannan $TOMA ɗin shi ne mutum zai iya sayarwa a matsayin kuɗin intanet. $TOMA ya fito da mummunan farashi mai maƙasƙanciyar daraja. Ya fito a kan farashi kwatankwacin $0.0000020549 zuwa $0.0000274204 ga kowane $TOMA. Wannan yana nufin cewa, duk wanda yake da $TOMA dubu goma (10,000), to abin da zai sayar da su shi ne $0.021 zuwa $0.27. Dole tasa ‘yan baiwa suka tura musu aniyarsu. Faɗan da ya fi ƙarfinka, sai ka mayar da shi wasa.
Goats
Goats ma ɗaya ne
daga cikin haƙo da aka yi a kafar Telegram. An
kammala shi a cikin kimanin watanni 3. An yi haƙon ne
a ƙarƙashin
bulokcen da ake kira Ton
Blockchain. Ana iya fassara Goats cikin harshen Hausa da Awaki. A
zahirin gaskiya abin da ake nufi ke nan da wannan nau’in kuɗin
intanet. Dalili kuwa shi ne, ko hoton tambarinsu, zanen akuya ne a cikinsa
wanda aka tsara cikin salo. A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 5.9:
Tambarin Goats
Haƙon Goats ya kasance mai wahala. Yana da sigar cin task da kuma
kyautar kullum-kullum (daily reward) da ake bayarwa, sai kuma garaɓasar gayyata
(referral bonus). Wani ƙarin wahala shi ne, kafin samun damar cin task yadda
ya kamata, dole ne mutum ya saka kuɗin Ton. A bisa haka, mutane da yawa sun
dogara ne kawai da kyautar da ake bayarwa kowace rana, da kuma garaɓasar da ake
bayarwa yayin da mutum ya yi gayyata.
Bayan kammala
haƙo, ba a ɓata lokaci ba sai aka zarce zuwa ƙaddamarwa. An ƙaddamar da shi ranar Alhamis, 5 ga watan Disamba na shekarar 2024 da
misalin ƙarfe 10:00 na safe a agogon Nijeriya. Ya fito da farashi mai matuƙar muni da rashin daraja. Ya fito a kan kimanin $0.00153.
Mafi yawan waɗanda suka yi wannan haƙo ba su da abin da ya kai sulalla 1,000. Wanda yake da
sulalla 1,000 ma, abin da zai samu bai kai dala biyu ba, domin abin da zai samu
kawai shi ne $1.53.
Naɗewa
Haƙiƙa kuɗin
intanet lamari ne wanda zamani ya kawo, wanda kuma yake da matuƙar
muhimmanci. Yana ɗaya
daga cikin manyan fuskokin da tattalin arzikin duniya ya sa gaba a yau. Ma’ana dai, yana ɗaya daga cikin muhimman linzamai ko akala
da suke juya lamuran tattalin arzikin duniya a yau. Hausawa suna daga cikin
al’ummomin da suke cin gajiyar kirifto. Akwai Hausawa masu yawa da suka kama
kirifto a matsayin kasuwanci a yau. Duk da haka, ya zo da ƙalubale masu yawa. Ɗaya
daga cikin manyan ƙalubalen da yake dabaibaiye da harkar kirifto a
yau shi ne damfarar kan intanet. ‘Yan damfarar kan intanet suna amfani
da dabaru daban-daban domin damfarar mutane. Hausawa suna daga cikin waɗanda suke faɗawa komar ‘yan damfara. Lallai ya zama
wajibi Hausawa su tashi tsaye, su yi karatun-ta-natsu tare da bin hanyoyin
neman ilimi domin samun cikakkiyar fahimtar kirifto domin kauce wa tarkon ‘yan
damfara tare da gudanar da tsaftataccen kasuwanci.
[1] Shi ƙona sulalla sababben abu ne a
harkar kuɗaɗen intanet. Akan ƙona sulalla bisa dalilai da dama, ciki har da
rage yawan sulallan da ake da su domin su ƙara daraja. Idan sulalla suka yi
yawa sama da ƙima, hakan yana haifar da faɗuwar darajar wannan nau’in kuɗin
intanet ɗin. Wannan ya yi daidai da abin da yake faruwa a duniyar zahiri, inda
idan aka buga takardun kuɗi masu yawa sama da ƙima, darajar wannan kuɗin zai faɗi.
[2] Wannan
ɗaya ne daga
cikin nau’o’in lalitar kuɗaɗen intanet.
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.