Ticker

6/recent/ticker-posts

Tuwo Na Lukuya Mai Jiki Duk Tsoka: Tsokaci A Kan Tuwo Jagoran Abincin Bahaushe

TAKARDAR DA AKA GABATAR A MUJALLAR ƊUƊAYE JAMI’AR USMAN ƊANFODIYO SAKKWATO 2021

DAGA:

MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD PhD

 DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES

 SULE LAMIƊO UNIVERSITY KAFIN HAUSA, JIGAWA STATE

TUWO NA LUƘUYA MAI JIKI DUK TSOKA: TSOKACI A KAN TUWO JAGORAN ABINCIN BAHAUSHE

 Tsakure

 Wannan nazari zai dubi abin da ya shafi tuwo da matsayinsa, da tasirinsa a rayuwar Bahaushe. Tuwo an ɗauki dogon lokaci ana gudanar da shi a matsayin limamin tuwon Bahaushe. Ana iya cewa an samu tasirinsa a kusan dukkan harkoki na al’adun gargajiya wanda Bahaushe ya gada tun iyaye da kakanni. Maƙalar zata kawo bayanai tare da fito da rawar da tuwo ya taka a yanayin zamantakewar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar tuwo tare da hanyoyin samar da tuwo da kuma fagagen da tuwo ya kankane ta fuskar cimaka, dalilai, da tsawon lokacin da Bahaushe ya ɗauka yana cin tuwo. Nazarin ya kawo irin yadda Bahaushe ya bai wa tuwo muhimmanci. Haka kuma za a kalli irin yadda Hausawa kan yi musayar tuwo a tsakaninsu a wasu lokuttan bukuwa da wurare. Maƙalar zata kawo jirwayen tuwo a adabin Bahaushe na baka, daga ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

1.0. Gabatarwa.

Al’ummar Hausawa sun kasance suna rayuwa bisa doron ƙasa tun wani zamani mai tsawo wanda ba za a iya yin hasashensa ba. Ita kuma rayuwa ba ta yiwuwa dole sai da tuwo, saboda Allah Ya albarkaci Bahaushe da tuwo iri daban-daban tuwo kuma na daga cikinsu. Wannan bincike na da ƙudurin yin nazari a kan matsayin tuwo, da gudummowarsa, da tasirinsa a rayuwar Bahaushe. Maƙalar zata kawo ma’anar tuwo, da ire-irensa, da fagagen da ya mamaye, tare da gano irin shaƙuwar da Bahaushe ya yi da tuwo ta yadda har bai iya gudanar da wasu abubuwa na rayuwarsa sai da shi.

Bugu da ƙari wannan nazari ya ƙara fito da muhimmancin tuwo a tunanin Bahaushe. Bayan wannan kuma, nazarin ya ƙara nuna muhmmancinsa a fagen magani da na tattalin arziki a rayuwar Bahaushe. An kuma ƙara fito da so, da irin girmamawar da ake yiwa tuwo a Bahaushiyar al’ada. A ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

1.1. Ma’anar Tuwo:

Abubakar (2015: 467) Tuwo: tuwon hatsi da aka yi da tuƙaƙƙen garin gero,ko dawa,ko alkama,koshikafa, ko tsabar shinkafa. Tuwon ƙasa, da tuwon suna, da tuwon girma.

Ƙamusun Hausa (2006: 448) Tuwo: tuwo da akeyida garin dawa,ko gero, ko masara, ko kuma ayi da shinkafa a tuƙa da tafasasshen ruwaaka kwashe,ana cid a miya. Tuwon yau da kullum.

Bisa la’akari da bayanan masana magabata, ana iya cewa: tuwo wani nau’in tuwo ne daga ire-iren tuwon Hausawa, wanda yake da babban matsayi a rayuwar Bahaushe. Babu shakka ana iya cewa Bahaushe yana da tarin nau’in tuwo daban-daban, amma dukkansu babu wanda yake da matsayi irin na tuwo.

Yadda ake yin tuwo, a kan samu tukunya a ɗora a kan murhu a hura wuta. Bayan ruwa ya tafasa sai a samu ruwan sanyi a dama gari sannan a ruɗa talge, sannan a bar shi ya dafu. Da zarar ya nuna sai a ɗauko gari a tuƙa tuwo da muciya sannan a bar shi a kan wuta ya sulala. A ƙarshe za a sanya muciya a sake tuƙawa sannan a sanya mara a kwashe.

Bahaushe ya sanya wa tuwo suna a dalilin yanayin kwashewar da aka yi masa kamar haka:

v Marar tuwo.

v Malmalar tuwo.

v Kaɓakin tuwo.

v Madurguji.

v Kankaren tuwo

v Lomar tuwo.

v Ƙanzon tuwo.

v Gutsiren tuwo

v Gayan tuwo

v Sauran tuwo

v Kwaɗon tuwo

Idan aka gutsiri tuwo aka sanya a miya aka kai baki don a ci, sai a kira shi da loma.

 Bayan wannan kuma, sunayen tuwo a dalilin abubuwan da aka sarrafa don yin shi da su, akan kirashi da:

1. Tuwon Dawa.

2. Tuwon Gero.

3. Tuwon Alkama.

4. Tuwon Acca.

5. Tuwon Masara.

6. Tuwon Shinkafa.

7. Tuwon iburu.

8. Burukuku tuwon wake.

9. Tuwon Ɓula.

10. Tuwon biski.

11. Tuwon datsa

2. 0 Tuwo A Mizanin Al’ada

Bisa al’ada tuwo na taka rawa a mu’amular Bahaushe zai gudanar babu tuwo. Domin haka ne aka ƙirƙiri sunan kowacce harka aka alaƙanta ta da tuwon kamar haka:

v Tuwon Dare (Jibi).

v Tuwon Gona

v Tuwon Sallah

v Tuwon Gayya.

v Tuwon Jere.

v Tuwon Jego.

v Tuwon Ɗankaciya.

v Tuwon buki.

v Tuwon Suna.

v Tuwon Ƙauri.

v Tuwon Sadaka.

v Tuwon Sayarwa.

2. 1 Tanajin tuwo.

Akwai wasu abubuwa da aikace-aikace da Bahaushe kan yi don ganin tuwo ya samu. Da farko ya kan tanaji hatsi ko gero, dawa ko Masara. Bayan an yi sussuka, za a yi surfe, sannan a yi niƙa a zo a yi tankaɗe don a samu gari.

2. 2 Miya:

Bisa dalili cewa tuwo bai ciwuwa sai da miya, to dole Bahaushe ya ƙirƙiri cefenen miya.

Miya ita ma Wani nau’in tuwo ne mai ruwa-ruwa kamar romo da ake zubawa a sandarrun tuwo don samar da Ɗanɗano don jin daɗin cinsu, Miya kan samu ta hanyar harhaɗa ‘ya’yan itatuwa da kayan lambu irin su, tumatur tarugu, da tattasai, da albasa, da gishiri da mai a wani lokaci da nama da kifi ko daddawa ko magi. Bahaushe ya ƙirƙiri miya don ya inganta ɗanɗanon tuwo a bakinsa ko kuma duk wani nau’in tuwo da yake buƙatar miya. Bahaushe kan yi wa miya hidima ko ɗawainiya, ta hanyar haɗa nau’o’in tsirai da itatuwa don samar da itatuwan dake samar da ɗanɗano iri daban-daban gwargwadon buƙata.

Akwai miyar da akan yi ta don ɗanɗanon ɗaci wanda ake yi da shuwaka ko a saka mata gwauta. Akwai wadda ake yin ta don aji ɗanɗanon tsami wadda ake yin ta da yakuwa ko barekata ko alayyahu ko rama.

Akwai wadda ake yin ta don aji bauri: wadda ake yi da kuka, da tafasa, da gantsalwa.

 Akwai miyar da ake yin ta don ɗanɗanon zaƙi kamar Taushen kabewa da Taushen kankana. Taushen kabewa ana yin shi idan aka samu kabewa aka fere ta aka yayyanka, sai a zuba ta a tukunya, idan ya tafasa sai a sa gyaɗa da kayan miya (jajjage) da gishiri da mai.

 Taushen kankana kuma ana yin shi idan aka samu kankana aka fere ta aka yayyanka sai a zuba ta a tukunya, idan ta tafasa sai a sa gyaɗa da kayan miya (jajjage) da gishiri da mai shi ke nan. Ana samun ɗanɗanon daɗi daga miyar dage-dage. Da farko za a wanke kayan miyar sannan a markaɗe. Daga nan sai a wanke nama kaza ko nama a sulalasu, har sai sun yi laushi sai a ajiye a gefe. A ɗora markaɗaɗɗen kayan miya a wuta ya yi ta tafasa har sai ruwan ya tsane. Sannan a zuba man ja a yi ta soyawa, har sai man jan ya soyu, sannan a zuba kayan miya shi ma ya soyu sai a ɗauko romo nama a zuba su magi da kori da sauransu, sannan a sake gaurayawa, sannan a sake gauraya. A rufe na tsawon mintuna biyu, sai a ɗanɗana a ji in da tsami. Idan da tsami sai a jiƙa kanwa murfin kwankwalati fanta sannan a gauraya idan miyar ta nuna sai a sauke a ci da farar shinkafa,ko waina ko doya. Bahaushe na yi wa miyar dage-dage kallon sarauniya ce a cikin sauran nau’o’in miyar da yake dasu. Dalili kuwa ba kullum ake yin ta ba, sai ranar salla ko kuma domin muhimmin baƙo.

“Dage-dage baƙuwar miya

Daga sallah sai sallah

2. 3 Gudunmowar Tuwo A Sana’o’in Bahaushe

Baya ga sana’ar sayar da tuwo, to haka kuma tuwo na taimakawa Bahaushe wajen gudanar da wasu sana’o’in kamar haka:

v Sana’ar dukanci, Baduku na amfani da gayan tuwo wajen liƙe laya, kube gafaka da sauransu.

v Sana’ar dakan shikafa: Mata masu dakan shinkafa na yin amfani da gayan tuwo don surfen shinkafa don ta yi haske ta ƙara kyau.

v Sana’ar Su: Masunta na yin amfani da gayan tuwo wajen maganin fitar da ƙayar kifi idan ta maƙale a wuyan wani.

v Sana’ar Tsubbu: Ana shan ruwan ƙanzo don maganin farin jini.

v Sana’ar Magani: Magori da ‘yar mai ganye suna amfani da gayan tuwo wajen cin magungunan wasu cututtuka ta inda ake barbaɗa garin magani a miya, sannan a ci tuwon da ita.

v Sana’ar Bokanci: Bokaye da masu tsibbu, na yin amfani da tuwo wajen yin sammu ta hanyar bayar da magani na mallaka ko cutarwa ko halakarwa.

2. 4 Ƙimar Gidan Bahaushe Sai Da Tuwo:

Bayan haka kuma, mallakar tuwo ko samun tuwo a gida na nuna cikar kamala ko cikar darajar Maigida. Domin duk gidan da babu tuwo a kan ce ai babu tuwo, kuma gazawa ce ga mai gidan wannan na iya sa wa a hana mutum aure. Haka kuma, aure na iya mutuwa a dalilin rashin tuwo ko tuwo. A wata fuskar kuma, iya yin tuwo na ƙarawa mace ƙima da daraja, sannan kuma idan mace bata iya tuwo ba, tana iya haɗuwa da wulaƙanci daga wurin maigida ko kishiyoyinta da sauran abokan zama. Matuƙar aka ce mace na yin ɗanyen tuwo ko yana gudaji, ko kuma bai isar kowa a gidan, ko tana yin tuwon dare, aurenta na iya mutuwa.

Bahaushe kan ce “don kan ki, ‘ya ta ƙi sarkin noma”. “Ko tuwon amarya ya yi gudaji ba a faɗa”.

2. 5 Tuwo A Harkar Aure

Tuwo yana da muhimmanci ga rayuwar Bahaushe, don kuwa rayuwarsa ba ta yiwuwa sai da tuwo, koda yake babu gidan da ba’a yin tuwo don ci, to amma shi tuwon biki yana da amfani ga harkar bikin aure ko ga ‘yan gari ko baƙi watau matafiya.

Tuwo yana da wani al’amari ta inda mafi yawa zaka samu mata ne suke samar da shi kuma su raba ga mahalarta bikin. Ko da yake akan samu wani lokacin maza na yin rabon tuwo musamman waɗanda suke abokan ango ko ‘Yan uwa,

Cikar biki shi ne yawan mutanen da suka halarci wuri, sannan da wadatar tuwo da aka ci aka sha. Wannan yasa har ake cewa a wurin bikin jama’a maza da mata ba masaka tsinke, wurin yayi cikar kwari mutane kamar kasanya ƙwarya ta zauna. Akwai tuwo iri-iri daban-daban. Kamar haka:

 Tuwon Wuni,

Tuwon Biko,

Tuwon Saukar Amarya,

 Tuwon ‘Yan Zaman Zuru,

Tuwon Saukar Gara,

 Tuwon Jere,

 Tuwon BuƊAr Kai

2. 6 Tuwon A Bukin Sallah

Tuwon Sallah yana da muhimmanci ga rayuwar Bahaushe, sallah babba ko ƙarama, don kuwa bikin salla ba ya cika sai da tuwo, koda yake babu gidan da ba’a yin tuwo don ci, to amma shi tuwon sallah yana da amfani ga jama’a ranar bikin sallah ko ga ‘yan gari ko baƙi watau matafiya. Bahaushe kan ce: tuwon sallah ga yawa gad aɗi, tuwon sallah maganin mai haɗama.

Tuwo yana da wani al’amari ta inda mafi yawa zaka samu mata ne suke samar da shi kuma su raba ga gidajen maƙwabta, da ‘yan uwa, da baƙin da suke kawo ziyarar zumunci. Cikar bikin sallah shi ne yawan a gurin Bahaushe shi ne, mutane su halarci wurin ibada, da sanya sababbin tufafi, sannan da wadatar tuwo da za a ci.

3. 0 Jirwayen Tuwo a Adabin Baka:

 An samu jirwayen tuwo a adabin Bahaushe, ma’ana ya yi naso a dukkan rassan adabi na baka da rubutacce. Domin an samu karin magana, kirari, da waƙar baka.

 3. 1 Karin Magana.

Ø Lomar hasafi ta fi kaɓakin tsiya.

Ø Zo ka ci tuwo, ya fi tuwon daɗi.

Ø Tuwon Sallah maganin mai haɗama.

Ø Tuwon Sallah ga yawa ga daɗi.

Ø Maras kunya ke cin tuwon gidan buki har ya ce a ƙara masa miya.

Ø Tuwon girma miyarsa nama.

Ø Baƙar tukunya mai fitar da farin tuwo.

Ø Ba a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare.

Ø Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha.

Ø Mai tuwon dare kya ci da buzuzu.

Ø A rashin tuwo akan ci wake a kwana.

Ø Tuwo da zafi ba shi da daɗi, kowa ya ɗiba sai ya mayar mai ƙwazo ke cinye abi nai.

Ø Don tuwon gobe ake wanke tukunya.

Ø Cin tuwon kishiya ramako ne.

3. 2 Kirari.

Ø Tuwo na luƙuya mai jiki duk tsoka.

Ø Tuwo da kana da ƙashi da sai dansarki.

Ø Tuwo naman talaka.

Ø Tuwo jurau gidan kowa da kai.

Ø A ci yau a ci gobe sai tuwo.

Ø Tuwo shalashar baduku.

Ø Tuwo kafi ƙarfin jefarwa.

Ø Tuwon gayya ba a cin ka a zauna.

Ø Tuwo sa rigima, hana rigima.

Ø Tuwon datsa ka fi kwaɗon rama da rumace.

Ø Tuwo ko ka bushe ka fi ƙarera.

3. 3 Maganganun azanci.

Ø Ƙadda baƙon dole, a ci tuwo da kai a yi tsadar kai kwano.

Ø Kankaren tuwo abin ba maƙiyi, ko ɗan kishiyar da ba shi da gata.

Ø Tuwon Masara Malam Hassan, in ya ji taushe Alhaji.

Ø Da yunwa ta kashe ni, gara tuwo ya kashe ni.

Ø Tuwon cushe ba ya daɗi.

3. 4 Tuwo a bakin Mawaƙan baka:

Haka a wata waƙar Alhaji Mamman Shata ta Hauwa mai tuwo:

“Hauwa mai tuwo matar Lado

Idan kin yi miyarki ta ‘yan birni

Shi za ni saya in ba baƙi

Sai kin yi tuwo na gwamnati

Shi za ni siya in ba baƙi

Alhaji Musa Ɗanƙwairo a waƙar Aliyu ‘Yan doto cewa ya yi:

“na iske ‘yan Sarki suna faɗa

A kan rago”

Mu’azu Ɗan alolo cewa ya yi:

“a samu taushe da nama

Komaɗa duk ta tashi.

Shi kuwa Muhammadu Gawo fillinge cewa ya yi:

 “Talaka ba shi ya cin kifi soye

 Ballantana rottsin zabbi.

Ibrahin na Rambaɗa a waƙarsa ta Jibadau Binjimin Macciɗo cewa ya yi:

 “mu sha fura cikin nono

 Mu ci tuwo cikin nama

 Mai talaka ya samu

 Sai dai ya ci ɗanwake

Ibrahim Narambaɗa, a waƙar Jibadau Bijimin Macciɗo, ya ce:

“Mu ci tuwo cikin nama,

Mu sha fura cikin nono,

Mai talaka ya samu?

Sai dai ya ci ɗanwake,

Jibadau bajimin macciɗo

Halinka halin girma”.

Haka kuma Dr. Alhaji Mamman Shata Katsina ya bayyana yadda aka karramashi da tuwo a cikin waƙarsa ta Maude ɗan Abdaullahi, inda yake cewa:

“Na sauƙa anan birnin Dabo,

An ba ni tuwon Sallah na ci,

Sannan an ban naman layya,

A’a ban sa babbar riga ba….. ”

Har ila yau, Dr. Alhaji Mamman Shata Katsina a waƙarsa ta Abba siri-siri ya ce:

“Ya ci tuwon shi mai nama,

Ya sha furar si mai nono,

Alhaji unguwan sa ‘yan taba,

Amma fa ba ya shan taba.

Dr. Alhaji Mamman Shata Katsina a Waƙarsa ta Yarinya Lami Shagamu, ya ce:

Ga fura ta mai nono,

Ga fa tuwo na mai nama,

Ashe Shata babban baƙo ne,

Har da makwani mai kyawu,

Kai ko ganin dariyar su umar,

Na Garba don dai suna ganinka,

In ba ka bas u bani kuɗin fura,

Da an ce ka tafi ba sa bani kuɗin tuwo.

Dr. Alhaji Mamman Shata Katsina, a waƙarsa ta Kululu mai tuwo, ya ce:

“Hauwa’u mai tuwo matar lado,

Idan kin yi miyar ki ta ‘yan birni,

Shi zan saya in ba ma baƙi,

Sai in yi tuwo na gwamnati mai tsada,

Shi zan saya in b abaƙi.

Maci tuwo ga Hauwa’u

Duk maso tuwo ga Hauwa

Mai son tuwo wajen Hajiya zaya

Hauwa mai tuwo matar lado”.

“Hauwa mai tuwon matar Lado

Hauwa mai miyar naman shanu

Hauwa mai miyar naman Rago

Hauwa tai miyar naman zabi

Hauwa ga miyar na naman kaji

Idan babu daddawa a biɗo magi

Idan babu daddawa a biɗo magi

Wani miyar shi sai yasa magi

wani daddawa yaka sanyawa”

“ Ga wata daddawa taka jefawa

Hauwa ba ta miya lami

Balle tuma da gayya abin wofi.

Adamu Ɗanmaraya Jos a waƙarsa ta Karen Mota, ya ce:

“Maguzawa na layar asiri,

Goyon sai kwanon ragen tuwo,

Mai ɗaukar bashin uwar tuwo,

Wajen biyar bashi yai dambe,

Iya bani tuwo mota za ta tashi”.

Adamu Ɗanmaraya Jos a Waƙarsa ta Waƙar Aure, ya ce:

“Da can kina gidan miji,

In tuwon dawa maza ki ci,

Tuwon masara in za ki ci,

In shinkafa za ki ci,

Maigida duka ai yai tanadi”.

Adamu Danmaraya Jos a Waƙarsa ta Lebura, ya ce:

Haka masu tuwo miyar kuka,

Mai tuwo ba za ki said aba,

In lebura bai yi aiki ba.

 Maidaji Sabon Birni a waƙarsa ta Sarkin Gobir na sabon birni Alhaji Muhammad Bawa (1975), ya ce:

“‘Yan ban bututuwa a yi man tuwo,

Ya ban kuɗi in sai miya,

Amma kayan in man canyo su”.

Babangida, a waƙarsa ta mu bi al’adunmu, ya ce:

“Tuwon dawa miyar kuka,

In anka haɗa su baki ɗaya,

Said ai a zuba cikin akushi,

In wanke goma in sa biyar,

Don al’adun sun ci gaba”.

Barmani Coge a waƙarta ta kira ga a dinga sana’a, ta ce:

“Ana ta ga tuwo ‘yan barka,

Sakarai ba ta da wayau,

Uwargida ta ce ala raya,

Sakarai ba ta da wayau,

Ita ma ɗayar ta ce mun ƙoshi,

Sakarai ba ta da wayau,

Yaya a ƙi ci a ƙyace,

Sakarai ba ta da wayau,

Wannan tuwo abin ala raya,

Sakarai ba ta da wayau”.

Audu wazirin Ɗanduna, a waƙarsa ta Sarkin Ƙaraye Abubakar, ya ce:

“Yaushe za mu je ƙaraye mu sha harka,

A masauƙina an yi shirye-shirye,

Ga tuwo mai nama inji na Amadu,

Ga ruwan sha inji uban bello,

Ga fura mai nono inji uban daje,

Ga ruwa mai sanyi Garba ya aje,

Ga gashesshen nama ya ajiye,

Ya ajiye yaji a waje ɗaya,

Mu tashi cin naman mu baɗa masa”.

Audu Yaro Maƙarfi a waƙarsa ta caca, ya ce:

“A cikin zauren Ali Malabo,

Ya jani ya turani azure,

Tuwo da miya ya baiwa Audu,

Fura da nono ya ba Audu,

Ya sayo mani taba da goro,

Ya ce mani zo mu zauna”.

 Wani ma ya yi rawa balle ɗan makaɗa, bisa tsari na mawaƙan Hausa, akwai makaɗan bandariya musamman ɗan kama, wanda ya yi fice a waƙoƙin tuwo, inda ya fifita martabar tuwo fiye da kowanne irin nau’in tuwo a cikin waƙoƙinsa da dama. Alal misali; Yana cewa:

“Sai naci tuwo na kan yi wayo,

Gidan da babu tuwo ba za ni ba”.

Salisu Ɗankama Jega, a waƙarsa ta Haruna Sarkin Gwandu, ya ce;

“Yaƙin gabas mai nisa sarki a barmu gida,

 Yaƙin arewa sarki awazina,

 Ka awu sarki a barmu gida,

Yaƙin kudu mai nisa sarki a barmu gida,

Yaƙin tuwo mai nama sarki a samu gaba”.

Malam Adama Ɗankama Kano, ya ce;

“Kanar ɗanwake ya gudu,

Manjo Fura ma ta gudu,

Janar funkaso ya gudu,

Mun ci fanke mun ci waina,

Ƙaryar tuwo ta ƙare.

Allah ya tsaremu da mugun ji da mugun gani,

Mugun ji dai kana zaune ka ji an ce,

Kaza ta zubar maka da fura,

Mugun gani kuwa sai sanwar tuwo a gidanka,

A fara talge tukunyar ta fashe”.

Malam Ashana Ɗankama Kano ya ce:

“Idan kuna so mu shirya,

Ku janye sunan na hana,

Ku aiko da wasu kwabbuna,

Su je gam ai shinkafa,

Mai koko tana faɗi,

Wannan ya ƙi ya fi ƙarfinta”.

“Da kura da Bebeji,

Da daɗin zuwa suke,

A kai maka shirgogo,

Da ka ji a kan tuwo,

A kai maka ɗaki ɗan,

Gajere duƙurƙushi”.

 A waƙar Malam Ashana ɗan kama yana cewa:

“kanar ɗanwake ya gudu

Manjo fura ma ta gudu

Janar fankasau ya gudu

Mun ci fanke, mun ci waina

Ƙaryar tuwo ta ƙare”

A kowacce waƙa da aka kawo a cikin aikin, za mu ga cewa, kowanne mawaƙi ya tabbatar da matsayin tuwo da martabarsa a tunanin Bahaushe, tare da bayyana irin ƙimar da yake da shi a idon Hausawa.

Saboda haka, yanzu za mu yi bayanin wasu daga cikinsu kamar haka:

 Abin bai tsaya a nan ba, Bahaushe yana matuƙar girmama tuwon hatsi da na dawa, wato tuwon laushi da tuwon biski, don haka ne ma wasu daga cikin mawaƙan baka musamman mawaƙan ban-dariya (‘yan kama), wani lokaci ma har da mawaƙan zamani (jemagu), su ma sun yi sharhi a kan tuwo, wato sun waƙe tuwo. Alal misali.

Sani Sabulu ya waƙe tuwo kamar haka;

“Mai tuwon ‘yan gayun garin zango,

‘Yan gayu suna faɗin tuƙa tuwo ko inji,

Kowa ya ci tuwonki ya huta,

Ko da lahira wuta ba ta taɓa ki don tuwonki”.

Barmani Coge ta waƙe tuwo kamar haka;

“Ni na yi godiya na ƙara,

Ga mai tuwo da sunan Allah,

Dan Allah ki tashi kit uƙa,

Ko sha biyun dare kika tuƙa,

Ma saya”.

Ɗan maraya Jos ya waƙe tuwo kamar haka;

“Haka masu tuwo miyar kuka,

Dawa a surfa ta,

Sannan dawa a wanke ta,

 A tuƙa tuwo ai za ki sai da shi,

In lebura ya yi aikinsa”

Tuwo a idon Mawaƙan Zamani (Jemagu) :

 Hausawa na cewa “zamani riga”, ko kuma “zamani ba kan ji magani”. Don haka su ma ba a bar su a baya ba, ta wannan fanni, don haka su ma suna yi wa tuwo kallon girmamawa tare da nuna shi a idon duniya a cikin waƙoƙinsu, cewa tuwo fa abu ne da ya kamata Hausawa su riƙe shi a matsayin tuwon da ya fi kowanne tuwo a gidajensu.

Don haka akwai waƙoƙi da dama da waɗannan mawaƙan zamani suka wallafa ko suka rera ko rubutawa a kan tuwo. Misalin irin waɗannan waƙoƙI su ne kamar haka: nan,

Adam A. Zango da Prince Sulaiman sun yi wa gidan sayar da tuwo da ke garin Kaduna waƙa, na “Maluba”. Inda suke cewa;

“Marmaza zo ki bani tuwo,

Ga tuwon masara nan,

Ga tuwon shinkafa nan,

Marmaza zo ki bani tuwo”.

Kammalawa

A ƙarshe wannan nazari ya kawo wasu bayanai a kan tuwo da matsayinsa, da tasirinsa a rayuwar Bahaushe. Ana iya cewa an samu tasirinsa kusan ya bayyana a dukkan harkoki na rayuwar Bahaushe da ya gada tun iyaye da kakanni. Maƙalar ta kawo tare da fito da rawar da tuwo ya taka a yanayin zamantakewar Bahaushe. An kawo ma’anar tuwo tare da hanyoyin samar da shi da kuma inda tuwo ya nuna shi ne jagora ta fuskar cimakar Bahaushe. Nazarin ya kawo irin yadda Bahaushe ya bai wa tuwo muhimmanci. Maƙalar ta kawo jirwayen tuwo a adabin Bahaushe na baka da rubutacce wato na zamani.

Manazarta:

Abubakar TY (2015) Ƙamusun Hausa Ahmadu Bello University Press Zaria.

Ƙamusun Hausa (2006) Jami’ar Bayero Ahmadu Bello University Press Zaria.

Gusau S. M (2016) Makaɗa Da Mawaƙan Hausa Century Research&Publishing LTD Kano. Ingawa, M. (1970) Iliya Ɗan mai ƙarfi: northern Nigeria publishing company.

Magaji, A. (2002) “wasu Al’adun Hausawa. Yanaye-Yanaensu Aƙasar Katsina” ƙundin digiri na uku (PHD HAUSA), sashen Nazarin Harsunan Nigeriya,Bayaro university,kano

Usman, A. (1997), Taskar Tatsuniya. kanoGidan dabino publishers.

ƊanHausa. A. M. (2012) “Hausa mai dubun Hikima, Century Research and Publishing Company Kano

NNPC, (2002). Labarun na da, da na yanzu. Zaria northern Nigeriyan publishing company

NNPC. (1970), Labarun Hausawa da maƙwabtansu. (1. da 2) Zaria NNPC. L. T. D

Muhammadu Gawo, A (waƙarsa ta ya Allah Gyara wahabu ka Taimaki ‘yan Nigar”

Kantoma, U. A. (2011). Sabon Tarihin Asalin Hausawa. Espee printing and Advertising, Kaduna State

Namangi A. A (1978) Waƙoƙin Imfiraji juzu’I 1-9, Zariya N. N. P. C

 Hausa Post

Post a Comment

0 Comments