𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam. Da fatan ka tashi lafiya. Shin alƙunuti da'akeyi asallar asuba wajibine sai mutum ya yi ko liman yana daukewa mamu?
HUKUNCIN YIN ALƘUNUTI A SALLAR ASUBA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Alƙunuti sunane na addu'a da'akeyi awani
bigire kebantacce na tsayuwa wanda aka shar'anta asallar wutiri bayan dagowa
daka ruku'u abisa zance ingantacce cikin zantukan Malamai. Ana yin Alƙunutu idan wata masifa ko bala'i ya
aukawa musulmai sai su dunga addu'a bayan dagowa daka ruku'u akowacce raka'ar
karshe ta sallar farillah guda biyar, Har Allah ya yaye musu wannan bala'i da
ya auka musu yadauke musu shi. Duba littafin (Tas-heehi du'ãã'i na Shaik Bakar
Abu Zaid shafi na 460).
Amma yin Alƙunutu koda yaushe Asallar asuba bai
inganta daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yakebance sallar asuba yana alƙunuti a cikinta koda yaushe ba, Abun da
yatabbata daka gareshi shi ne yana yin Alƙunutu
idan wata masifa tasauka, ya yi alƙunutu
asallar asuba dasauran salloli yana yi wa zakwaan da Usayyah mummunar addu'a
saboda kashe mahaddata Alƙur'ani
dasukai wadanda Annabi yaturasu zuwa garesu dansu sanarda dasu addinin
musulunci.
Ya tabbata ya yi ƙunuti asallar asuba yana rokawa raunana
daka cikin muminai dabasu samu damar yin hijiraba saboda rauninsu Allah
yakubutar dasu daka Abokan gabarsu, bai dawwama a kan hakan ba, halifofi
shiryayyu suka tafi a kan haka a bayansa, Abun da yake alheri ga limamai shi ne
su takaita dayin Alƙunutu
asallar asuba dama sauran salloli sai dai idan wata masiface ta aukawa
musulumi, anan yahalatta aita Alƙunuti
har Allah yayawa musulmi wannan masifar. Kamar yanda hadisinda Asha-bul Sunan
suka ruwaito banda Abu dauda daka Abu malik Al'Ashja'iy Allah ya kara masa
yarda. Albani ya Ingantashi a cikin Irwa'u (435).
Mafificiyar shiriya ita ce
shiriyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam. fatawa lajnatul da'imah
(7/47)
Sannan ba a iyakance wata
addu'a damutum zai yi A'alƙunuti
na wata masifa data samu musulmai ba, liman zai yi addu'a wacce tadace dahalin
da'ake ciki dakuma masifar kamar yanda aka ruwaito Annabi sallallahu Alaihi
wasallam ya tsinewa wasu kabilun dasuka bijirewa sahabbansa suka kashesu,
dakuma rokawa raunana da suke makkah Allah yakubutar dasu. Amma Akwai wasu
sigogi da'aka ruwaito Annabi sallallahu Alaihi wasallam da shabbansa sun yi a
addu'ar ƙunuti a cikin sallah kamar yanda baihaiƙi yaruwaito (2/210) Albani ya ingantashi
a cikin Irwa'u (2/170).
Ya halatta kayi alƙunuti da addu'a takashin kanka kamar
yanda Imamun Nawawi yabayyana a cikin Almajmu'u dinsa (3/497).
Dan samun karin bayani a kan
za ka iyayin wacce aka ruwaito sannan kakara dataka duba (ƙiyamu ramazhan na shaik Albani (31)
Hadisai da'aka ruwaito a kan
alƙunuti dakuma ingantaccen zance na
malamai shi ne ana yinsa bayan dagowa daka ruku'u idan kayi kafin tafiya ruku'u
babu komai kanada zabin idan kagama karatun sallah kayishi kafin tafiya ruku'u
sannan za ka iyayin ruku'u idan kadago saikayi alƙunutin.
Kamar yanda shaik Usaimeen yabayyana a cikin Sharhin Mumti'i Alã zhadul mustaƙni'i (4/64)
Dan haka yin Alƙunuti asallah baya kan mamu, liman ne ke
haƙƙin yinsa, shi mamu zaidunga
Ameen ne lokacinda liman yake addu'ar Alƙunutin.
Alƙunuti wanda muka tashi mukaga ana yi
akasar nan kowacce sallar asuba dakuma siga daya da sunan mazhabar malikiyyah
bidi'ane bai tabbata daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ba.
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.